Ni da Almajirina 4
NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)
Episode 4
_NOTED# WANNAN SHINE LITAFINA, NA FARKO WATAKILA SHINE NA KARSHE 凉 IDAN KUNGA KUSKURE KUYI MIN AFUWAN_
Cike da mamaki suke kallon ta, can daya daga cikin su yayi dialing number Amir inda ya ji wayar a kashe, sake kira yayi yaji wayar a kashe, ba shiri suka bar gidan dan duba shi a waje..
Suna fita daya daga cikin ya’yan Fanne mai suna Zahra tace Ummi ya za muyi idan suka gane cewa yana… ba ta karasa maganar ba Fanne tayi saurin taran numfashi ta da cewa, ya fita kuma bamu san Idan yake ba shine amsar mu ko da kuwa za suyi gunduwa gunduwa mu amsa daya shi zamu basu.
Boys din Amir suna barin gidan suka tambayi yan’uwan su dake waje, ko shin sun ga fitowar Amir? Duk suka ce a’ah.
Boys su kace mun kira wayar sa a kashe, kuma ance mana fita yayi and kunce baku ga fitar sa ba?
Daya daga cikin boys yace mun kira Ya Amir mu sanar da shi,
Daya a cikin su yace kasan dai ba zamu same Ya Amir ba dai ko? Sai de Auta, kai tsaye ya kira Auta ko ba komai Auta ne dan gaban goshin Ya Amir tsabar fikra da kwakwalwa.
Saida wayar ya kusa tsinkewa Auta ya amsa kiran, Wanda ya kira ne yace Amir bamu ga Amir Buba, nan take suka bashi labarin abinda ya faru kafin barin su gidan.
Saida Auta ya dauki lokaci kafin yace Amir na gidan kuyi duk yadda za kuyi ku fito dashi ko a raye ko amace sanan kar ku taba wani acikin gidan. Buba kadai muke bukata, Auta na fadin haka ya yanke kiran.
Komawa ciki boys su kayi unannounced, ganin kowa na gidan na harkar gaban sa ba wani alama dake nuna zargi a tare dasu.
Summoning kowa na gidan su kayi, kowa ya gufanar da kanshi gaban su.
Ina Amir? Su ka sake tambaya suna kokarin karanta abinda ke fuskar kowa?
Jin sunyi shiru basu ba da amsa ba yasa daya daga cikin boys dauko Zahra ya daura mata bindiga a ka, ko fito da Amir ko kuma mu kashe ku daya bayan daya
Jikin Zahra sai bari yake tana kallon mahaifiyar ta, ita ko Fanne ko kallon ta ba tayi balle hakan yasa ta karaya
Can Fanne tace mun baku amsa cewa kuna fita yabi bayan ku.
Daya daga cikin Boys ya ce karya kike yi, Amir na nan dan masu gadi sun tabbatar mana da cewa yana ciki bai fito ba, ko ku fito da shi ko muyi gunduwa gunduwa daku.
Ba tare da wani tsoro ba ko darr Fanne tace to gaku ga gidan sai ku fito da shi, tayi imani kan cewa Allah da ya bata hikimar yin haka shi zai fidasu, tunda har ta iya ganin gawakin mijin ta da na danta kuma ta daure tabbas zata iya jure duk wani abu da zai zo daga garesu.
Falmata
Ya Amir ya kalle Falmata yace gobe zaki zama daya daga cikin mu, zaki zame mana uwa kuma sarauniyar wannan tafiyar tamu na jihadi.
Cike da mamaki Falmata take kallon sa jin yayi magana cikin harshen turanci, but mai yake nufi da zata zame mufi uwa kuma sarauniya?
“I’m not one of you and I’ll never be! “ Falmata tayi maganar cikin daci.
Murmushi Ya Amir yayi kafin yace by tomorrow I’ll become your in-law!
Da na zama one of you gara na mutu,Falmata tayi maganar tana fashewa da kuka, kallon HajjahKaka tayi tace Hajjah dan Allah wake me from this nightmare..
HajjahKaka tace to nide bansa me suke nufi ba damu Falmata? Auren ki za suyi ko kema shigar dake turakar za suyi?
Cikin jin haushi Falmata tace saide su dauki gawana HajjahKaka dan bazan taba kasancewa cikin wa inan dabbobin mara sa imani ba.
Falmata na sha gaya miki ba gane turanci nake ba idan zaki yi da hausa kiyi, tunda kince ba zaki koya yaren uwarki ba. HajjahKaka tayi maganar tana raraba idanu tana kare masu kallo.
Dariya sosai Ya Amir yayi kafin yace inason wannan kakar ko dan nishadi, ku kai min su fada ina zuwa, yana fadin haka boys insa suka yi abinda ya ce, duk da tirjiya da Falmata ta din ga yi hanka be hana sunyi gaba da su ba.
Wani wooden hut aka shigar da su Falmata, ta waje zaka rena girma hut(bukka)sai ka shiga zaka gane girma sa.
Shigar dasu wani daki su kayi wanda yake dauke da komai da suke bukata, suna ajiye su a dakin suka fito suka basu wuri.
HajjahKaka ta dafa Falmata tace na dafa ki da Alkhair Falmata, ki iya bakin ki banda taurin kai ato idan Ba haka sa aika ki barzahu gara ni idan sun ai kani na dan sha miya shekara ta 70 ba daya a duniya.
HajjahKaka da na kasance cikin su gara sun saka bindings sun harbe ni, Falmata tayi maganar tana kuka mai cin rai.
Kee a tunanin ki zasu kashe ki ne? Ba za suyi ba kuma ban ga alamar za suyi hakan ba, yadda suka ce kawai kiyi indai hakan bai tsabawa Allah ba. HajjahKaka tayi maganar tana kallon abinci dake a jiye ta dauki kunun tsaye dake kwarya ta daura a baki.
Cike da mamaki Falmata ke kallon ta ganin yadda ta kafa baki ta nasha ba tare da wani tsoro ba, HajjahKaka ki san kunun menene kike sha?
Cire kwarya HajjahKaka tayi a baki tace koma dai na menene na sha amma ban yarda ki sha ba. Ki sha ya’yan itattuwar nasa da kyar ace sun yi wani abu a ciki.
I rather starve to death than eat anything that comes from them Falmata tayi maganar ba ko wani darr.
Taurin kan turawan da kika dauko yaci ace shekara daya da kika yi dani kim sauke shi amma ba komai ga ruwa nan kiyi alwala sai kiyi sallah
Washe Gari
12 rana Ya Amir ya shigo dakin su Falmata ya ajiye mata takarda a gaban ta, Sarki Bulama IV ya bada auren ki a bisa yarjejeniya da mu kayi da shi zamu mayar da masauratan hannun sa kuma baza mu sake farmaka cikin garin Bama ba, saide kewaye da bayan gari yana gama fadin haka ya fice daga dakin.
Falmata was dumbstruck and loss for a word, kukar HajjahKaka ne ya dawo daga duniyar tunanin ta.
Lalle shuwari babu Allah a ransu? Yanzu kece zasu bayar a matsayin fansa? Allah baze taba barin su ba Falmata, Allah sai yayi maganin su biiznillah, HajjahKaka tayi maganar tana kuka kamar wata yarinya karama
Falmata dai idonta na samar paper da kudin dake ijiye gaban ta..
Amir Buba
Yaran Amir bincike suka dinga yi cikin gidan har yakai su ga dayan sasan inda suka ga tumin kasa kamar dai kabari, wanda suka ga kasan ne suka kira sauran yan uwan su da su zo su gani…
Jikin Fanne da na ya’yan ta duk ya mutu jin ance anga alamu dake nuna hakkin rami da kuma kabari
Gang leader na ganin haka ya kira Auta yana sanar masa da abinda suka gani
Amsa da Auta ya basa yasa ya tattaro mutane gidan zuwa gun kabarin Sanan ya dura bindiga kan Zahra yace mai a wannan rami?dan wannan rami sabon hakki ne.
Wato kun kashe shi, shine kuka bamu wahala muna ta neman sa tun jiya? Tabbas idan ko shine cikin ramin nan kuma sai munyi gunduwa gunduwa daku mu saka ku cikin rami..
Yara mazan suka umurce su da haka rami, cikin tsoro suka dauki chebur suka fara haka rami, Fanne babu tsoro ko dar a tare da ita sai ma motsi da ta keyi da bakin ta,
Tun kafin suyi nisa a haka ramin sai ga..
Pharteema(DMK)
THANKS
Post a Comment for "Ni da Almajirina 4"