Ni da Almajirina 3
NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)
Episode 3
Falmata tayi saurin kada kai alamar eh, dariyar mugunta Amir yayi kafin ya saki hannun ta, yace jeki ki warka da ita, yana fadin haka ta kara aguje dan bai wa Batula taimako na gaggawa saide kafin ta isa inda Batula take kawai taji karan bindiga, alburushin bai sauka ko ina ba sai bakin Batula, nan take kan Batula ya tarwatse.
Falmata suma tsaye tayi ganin gawar best friend inta right in front of her yasa Duniyar ta ya tsaya mata cak.
Amir yace kince zaki nema mata sauki, mu kuma muka bata sauki yayi maganar yana muguwar dariya, sauran mabiyan sa, suka taya shi dariya..
Matan dake gun gabadaya hankalin su kara tashi yayi, tabbas sun san mutuwa zasu yi..
Kamar mara laka ajiki haka Falmata ta karasa gun gawar Batula, tana tuno da good times they had together, if she could remember Batula was the first person to welcome her in that school. She could remember all the stories she told her, how Batula lost her parents to car accident. Da burin ta na zama likitar mata don taimaka wa mata.
Fashewa da matsananci kuka Falmata tayi ta fada jikin ta, tace please Batula ki tashi, remember our promise?
Please wake up..!!
Haka Falmata ta dinga kuka har ba ajin sound din voice inta..
Tattara sauran matan akayi gaba dasu, itama dake kwance cikin jini Batula, Gambo ya dauke cak, duk yadda ta kai da kokarin kwace kanta ya gagara, saida ya wurga ta cikin motor da HajjahKaka take kafin zagaya ya shiga mazauni driver seat.
Yo ni naga lugudan iskanci gun wa’inan mutane? Yanzu bawan Allah idan an tambaye ka yanzu kai Muslim ne saikace eh, bacin kai din babbar kafirine..
Wanni mugun kallo Gambo ya wurga ma HajjahKaka, ita ko HajjahKaka ko a jikin ta saima kara kurma masa ashar da tayi.
“To dan uwarka jikata yarka ce daza ka ta cacumarta?” HajjahKaka tayi maganar cikin matsifa.
HajjahKaka sun kashe Batula, Falmata tayi maganar cikin kuka mai cin rai
Inna lillahi wa ina ilaihir rajiun, yanzu wannan marainiyar diyar suka kashe? Kai mugu bai ji dadin rayuwan sa ba, Allah sai ya tsine maku albarka sannan sai kunyi mutuwar wulaqanci, maras imani da tsoron Allah, taka birki da Gambo yayi da karfi, yasa HajjahKaka hadiye sauran zagin da debe masu albarka da take yi..
Ke tsohuwar kago idan nasake jin kince tak sai na saka bindiga na harbe kanki, Gambo yayi maganar cikin wani mirya mai razanarwa.
HajjahKaka tace to ai shi na ke jira Kuma kaima mutuwar kake jira, shege kawai mai doyin baki da doyin najasa..
Wani dogon numfashi Gambo ya ja kafin ya sauke numfashi, ya daga wayar ya kara a kunnen sa yace, Amir wannan tsohuwar kawai a turata barzahu dan bakin ta yaki mutuwa. Amir dake dayan bangare na waya yace masa ko kurzina bai so ya gani a jikin su balle kuma maganar mutuwa, amsawa Gambo yayi da to Amir gamu mun kusa ma.
Mitin biyar suka isa destination din, idan Falmata takara tsorata da lamarin wa’inan mutane, sanye suke cikin uniform mai kamar Camouflage din sojoji saide nasu hade yake da manya manya bakin zane da launin kasa, sanan kowanen su rike yake da Ak27 sangale a kafadar su. Ba abinda kake hangowa a fuskar su face jajjayen idanuwar su, masu ban tsoro dan fuskar tasu rufe yake da masks.
Nuni Gambo yayi ma su Falmata dasu wuce gun da sauran matan ke, ba shiri Falmata ta nufi idan matan ke tsasaye ko wannen su ka kalla kasan cewa sun galabaita, to ko su Falmata da sukayo tafiyar mota sun gaji balle wanda suka taho a kafa.
3pm
Tunda suka taho wajan karfe 1 suke gun a tsaye, ba ruwa babu abinci, gashi da kace za kayi sallah sai ayi gaba dakai.
“Baku ji ne nace zanyi sallah bane? Falmata tayi maganar da iya karfin ta.. ”
Su Gambo yi su kayi kamar basa jin ta, sai ma kabbara da suka farayi ganin yan’uwa su tare da mutane dasu ka kamo suna tahowa, basu bar kabbarar ba har yan’uwa nasu suka karaso idan suke..
Aikin Ubangiji !!
Aikin Ubangiji !!
Haka suka dinga nanatawa, kafin wani dake sanye cikin fararan kaya ya harba bindiga sama, duk sukai attention kamar wasu sojoji.
Magana ya farayi cikin harshen larabaci,
“Alhamdulillah mu samu nasarori akan makiyan adinin mu, wa’inan mutanen garin sun bar adinin da Al’adar mu sun koma biyewa turawa, to ba zamu fasa yin aikin Allah ba wajan kawo karshen bature da abinda ya kirkira
Sojojin Jihad kuce Boko Haram!
Nan take mabiyan nasa suka maimata
Boko Haram!!!
Amir da yake tare dasu Gambo yace Ya Amir wannan abu zanyi na zama cikaken Amir mai iko kamar ka?
Murmushi Ya Amir yayi kafin yace abu da zai girgiza duniya, abinda hankalin kowa zai dawo kan mu, Alhamdulillah yanzu hankalin jihar atashe yake amma ba kamar yadda nake so ba, dan mutanen cikin gari suna karyata farmakar Bama da kewaye da mukayi, to idan kana so kacika Ya Amir na biyu maza kuje ku isar da sako garin Marte! Sannan ka auro Mahaifiyar ka kuma ka taho min da kan mahaifin ka. Idan kasa yin haka kuma Auta shine zai gaje Ni!
Nine zan gaje ka, sabda ban san wani gazawa ba ko rauni a cikin zuciyar na ba, Godiya nake Ya Amir, yana fadin haka Amir yaja gang insa sukai gaba..
Wannan lamarin nasu kara rikitar da Falmata ya keyi, jin yadda HajjahKaka ke fassara mata abinda suke fadi cikin harshen larabaci da kanuri.
Mutane da aka kama Iya tsorata duk sun tsorata da abinda Ya Amir ya fada. Tabbas wainan mutanen ba Allah a ransu balle kuma wani tausayi
Garin Marte
Ko ina kabi acikin garin sai ka tarar da gawa a hanya, a haka Amir suka dinga tafiya har ya isa gidan su, idan Sojojin jihad suke gadin gida.
Ya na isa cikin gidan ya tarar da yan’uwan sa da iyayen sa, ba tare da bata lokaci ba ya summoning kowa na cikin gidan, tunda dama gidan su babbar gida ne.
“Malam Bukar” Amir ya kira sunan mahaifin sa kai tsaye, cikin tsoro mahaifin sa ya amsa da na’am dana?
Dariya mai firgitarwa Amir yayi kafin yace, Bukar ayau ne ni Buba zan sha jinin ka kuma na aure matar ka.
Cike da mamaki kowanen su ke kallon sa, Acikin yan’uwan nasa wani yace Buba uwar da ta tsuguna ta haife ka ita kake cewa zaka aura? Sannan kuma ka kashe mahaifin ka? Wacce irin muguwar akida ce ko kuma adinin da ya hallata wa da ya auri mahaifiyar sa?
Ba tare da ya ba sa amsa ba ya saita bindigar sa ya harbe dan’uwan nasa sannan ya sake harbe mahaifin nasa ba tare da wani dar ba..
Danne kukan ta Fanneh tayi, ganin dan da ta haifa ya harbe ubansa a gabanta sannan har yake ikirarin zai aure ta?
Kannen sa suka saka kuka ganin gawar mahaifin su da na dan’uwansu a gaban su, daya daga cikin kanen sa zai magana, maman tayi karfin halin taren numfashi sa da cewa
Buba ni kake so ka aura? Tayi maganar tana kallon sa ido cikin ido, ba tare da bata lokaci ba yace eh, Fanneh so nake ki zauna a gefena kamar yadda kika saba yi.
Murmushi karfin hali Fanne tayi kafin tace to Buba naji zan aure ka amma da sharadi cewa baza ka sake kashe wani jini na ba?
Cikin murna Buba ya amsa da eh Umm..sai yayi saurin cewa Fanne.
To shikenan Buba, yanzu bara na girka maka abinda kafi so in ya so sai mu sake tattaunawa yadda za a daura auren namu.
Cike da mamaki sauran yan’uwa da ya’yan ta ke kallon su? Ko shin itama kanta ya zare ne koko tsoran kar a kashe su yasa tayi haka?
To Fanne bara mu zaga gari inda na dawo sai a daura mana aure na tafi dake masaurata na. Fanne tayi saurin cewa aah Ango na, gara ka tsaya kaci abinci,in yaso idan sun dawo sai a daura auren.
Cikin murna Amir yayi musu umurni dasu fita zai kira su. Kamar yadda yace dasu haka suka fita suka barshi a gidan..
Shiga kitchen Fanne tayi ta daura girki, ta nayi tana kuka, harta gama girka masa biski da dandairu taje, gaban sa ta ajiye sannan ta koma dauko masa ruwa shan.
Cike da murna ganin cewa ya na shirin zama Ya Amir ba tare da wani abu yasha gaban sa ba, bai taba tunanin cewa Ummi sa zata yarda da batun sa ba, sai gashi ganin ya kashe mijin ta yasa ta yarda..ko cokali uku beyi ba na abinci ya kware,
Fanne ta fito aguje rike da ruwa a hannun ta jin yana tari, ta same sa rike da wiyar sa idanuwar sa sun banbankalo waje tsabar yadda yake shureren mutuwa.
Cike da bakin ciki Fanne tace nayi danasanin daukar cikin ka da nayi na tsawon wata goma da nayi
Ayau ina me bakin cikin kasancewa nice mahaifiyar makashi kamar ka.
Kai a tunanin ka zaka kashe Dana da mijina sannan nabar ka, ka rayu?
Ina alfahari da na kasancewa nice wadda ta kashe ka da hanun ta.
Yana kokarin maganar ya datse harshen tsabar zafin cira rai. Ya sulale kasa,
Nan take Fanne ta kira sauran mutan gidan, cike da mamaki suke kallon ta, ganin gawar Buba.
Daya daga cikin yaranta yace Ummi? Ya akai kika kashe shi?
Ba tare da danasanin ba Fanne tace guba na saka masa ya ci ya mutu.yanzu ba wannan ba kuyi abinda ya dace kafin sauran su dawo..
Cikin hanzari suka haka rami a bayan gidan da ke dayan sasan da ba mutane a ciki,suka dauki gawar sa suka saka a rami, basu ajiye wani sign daze nuna cewa a birzine shi ba.
Bayan wani lokaci Mabiyan Amir suka dawo gidan, kai tsaye suka nufa falo inda suka ga Fanne zaune taci ado, cikin fara’a Fanne tace ina Ango nawa?
Daya daga cikin boys insa yace, bamu gane ba? Me kike nufi da ina Ango bacin fita mu kayi muka barki dashi…?
Cikin karfin hali Fanne tace, kun ga abinci da na ajiye masa, ko tabawa beyi ba tai maganar tana bude warmers dake ajiye samar tray.
Ke karki raina mana wayo man? Mun fita mu barki da Amir sannan kice baki san inda yake ba?
Fanne tace haba ya’ya na walhi kuna fita ba jimawa aka kirashi a waya, nide abinda yace min wai ku kuka kira bari yabi bayan ku kwa dawo tare.
Cike da mamaki suke kallon ta, can daya daga ciki ya dialing number Amir inda ya ji wayar…
SHIN MIYE ZAI FARU IDAN WAYAR AMIR YAYI RINGING?
KO SHIN BAANA YA NA INA?
COMMENTS
SHARE
DA SHARHI ZAI BAMU AMSOSHI !
Story and written by Pharteema(Dmk)
Edition by MissDmk ✍
THANKS
Post a Comment for "Ni da Almajirina 3"