Ni da Almajirina 22
NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)
Episode 22
A fusace Baana ya mike ze bar dakin,a hankali na bude bakina da yayi min nauyi nace i want tea.
Cikin hanzari ya juyo yana kallona kafin yace is that all..?
With a French toast,
“i don’t wanto be the bad guy idan ma zai mutu gara ya mutu bawai ta dalilina ba, coz idan in har aka kashe shi akaina nasan har na mutu bazan mance da cewa ALMAJIRANA ya mutu ne ta sanadiya ta, da wannan tunanin yasa na ce ina jin cin toasted bread ko dan na kawar da tunanin sa..
Cike da jin dadi ya fita dakin, yana barin dakin Hajjahkaka tace ko ke fa?
Daure fuska nayi kafin nace ni bance na yafe miki balle ki zo ki ishe ni da surutu.
To Allah yaso ba kece Salma balle fushin ki yayi tasiri akaina? To sanda kika daga kanti patari ki akayi miki abin manya ina gun ?ko nine nace yayi miki abin manya da zaki ce baki yafe min ba,to ka Allah yasa ki yafe din, to wai ma wa kika mayar Dodi minal Dodi to kin rantse cewa kwanaki ba kuyi abinku ba’..?
Cike da jin kunya nace daman kin saba yi wa mutane sharri ai sai kiyi tayi.
To ki rantse so daya kacal kuka taba yin abu manya tayi maganar daide lokacin da yake shigowa…
Tsabar kunya na rasa ina zan sa kaina, shima de kanshi sai da ya ji abin bangaragwan, amma yayi kamar be ji ba, ya zo ya ajiye tray a gabana kafin yace na taimaka miki?
Ba tare da nace kome na fara kokarin mikewa, saka hannun yayi ya dauke ni sai toilet.
Salalami Hajjahkaka ta hau yi tana mamaki rashin kunya irin ta ya ‘yan zamani, bayan kamar minti biyu ya fito daga toilet.
Hajjahkaka tace ko pim din India ba ayi wannan rashin kunya ba balle kai dake bakikinri da kai, anya zaka iya barin yarinya nan ta warke kuwa ?
Ba tare da yace kome ba ya zuba mata tea hade da dibo soyayyen naman rago ga sauce din albasa a gefe ya mika mata, sannan yace Hajjahkaka anjima me zaki ci?
Daukar tsoka daya tayi ta dibo sauce ta saka a baki can ta dago ta kalle shi tace gaskiya kun iya samo me girki , tasan sirrin soya nama ba karni ga kome yaji zuwit, Baana bara na koma can daki na ba yara waje, ka ga can dakin nafi sakewa naci nai hani ‘an ko ya kace? Kar kuce wata irin yar iskar tsohuwa ce ni ato ko baku fada ba nasan hakan ne cikin ranku.
Murmushi Baana yayi kafin yace to bara na kai miki can, bayan ya rakata ya dawo dakin ya same ni zaune ina hawaye…
Abinci be maki bane ?ko kina ra’ayin cin wani abu ne ?
Yayi maganar cikin damuwa.
Goge hawayen nayi kafin na sa tea a cup, na kafa baki zan sha amma sai na fashe da kuka…
Please na roke don Allah ku cire cikin nan,bana son ciki…
Kwalla ne ya taru a idonsa,maganar zuci ya fara, shin kiyayyar da Falmata ke masa har yakai tana kyamar jinin sa?
Ganin yadda take kuka yasa yace miye sa kika sa daukar wannan cikin a matsayin kaddarar ki Hajjahna ?
Allah yasan dalilin da yasa cikin ke zaune jikin ki.
Cikin kuka nace idan dana ya tambaye ni waye mahaifin sa ko kuma wanne irin aiki yake me zance masa?
Cikin breaking voice yace kice masa ALMAJIRIN KI shine mahaifin sa, ALMAJIRI ne dan usuli wanda ya fito daga tsarko malaman adini dana boko, amma rashin uwa da kuma mugunta da kiyayyar kishiyar uwa ya jefa shi cikin duniya tun yana dan shekaru hudu a duniya, kuma nayi alkwarin cewa iyalai na ba zasu fuskanta abin da na fuskanta abaya, burina daya ya rage a duniya shine naga jinin na wanda zaki haifa min, ko yau kika haifamin dana na miki alkwarin cewa zan mayar dake gun ahalin ki sannan na baku dukkan wani kulawa da kariya da yadace ace uba yayi wa ya ‘yansa Hajjahna, ya kare maganar yana goge gutun kwallar sa…
Rasa abin cewa nayi ina kallon sa, yau a karo na biyu ina son nasan waye ALMAJIRINA
I wanto know you.
Learn to love me then you know me, dazaran ranan da na fahimce kina sona daga ranan zaki san ko ni waye? Yayi maganar a kausashe.
Baka tunanin sanin ko kai waye zai sa na so ka ?
So nake ki so ni a matsayina na ALMAJIRIN KI, ki dena kyamatata ko kaskanta ni dan ina matsayin Almajirin ki Hajjahna.
Shiru nayi ina kallon sa kamar ina kokarin gano wani abu a fuskar sa , can de na dauki wani cup na sa tea, tura abinci na dinga yi bawai ina jin dadin abinci ba.
Ganin naci sosai yace min Thank you. Da zaran kina bukatar wani abu long press on this bottle yayi maganar yana nuna min kafin ya bar dakin.
Bayan Sati Biyu
Labarai kulum babu dadi, abu de ya koma kamar fadar adinin, jihohi uku na under curfew sabida..
A yayin da kuma yau Jumma ‘a ana cikin wani babbar masalaci dake Niger, Malam Zakariyya shine me limaci yau kawai aka ji tashin bomb, an rasa dumbi yawan rayuka a ranan irin ta yau.
Ya Amir dake can Iraq tare da Baana sako ya iso gare sa akan cewa an kardamar da abin da yace.
Wani dariya yayi kafin yace duk saina ga bayanku kafin ku ga bayana tudan kunce gwamnati kuke yi.
Wani irin kallo Baana ke masa kafin yace Ya Amir baka tunanin taba malaman da muke yi zai ja mana wata matsifa me tsanani?
Dariyan manya Ya Amir yayi kafin yace lokacin da na fara zuwa Nigeria na sauka inda naga na da manya malamai akan wannan litafin da ake boyewa al ‘ummah muslimai , dayawa acikin malamai su kace wai zamani ne yazo da haka don haka basu san da wannan litafin da yake criticism on western education .
na koma Niger nan ma suka kore ni batare da saurara na ba, daga nan ne na koma Borno inda na same ka a dalilin kane na gina sojojin jihadi sama da yara 100 a shekara 2000
Daman naci alwashin cewa duk sai naga bayan su tunda sun zabi yahudu da nasara akan dan ‘uwan su.
Shiru Baana yayi kafin yace Abba I think ya kamata mu dena taba malamai munyi concentrating akan gwamnati ze fi.
Murmushi AMIR yayi yace yaushe rabon da naji ka kirani da Abba? Naji dadi tuno min da good times we had before, to zan dakata, amma bara mu jira negotiation dake tsakanin mu da gwamnati shin zasu yi koko aah, idan suka juya min baya tabbas kowa sai ya jita.
Abba yakamata na koma kasan cikin na na wata hudu.
Murmushi Ya Amir yayi kafin yace to ka bi helicopter kaya ka koma, nasan kayi kokari da har kayi sati biyu ba ta, amma yaushe kake shirin mai da ta?
Ban san rana ba Abba amma na fi so idan ta haihu.
Wannan tsohuwar fa ?zaka bar mana ita ne ? Ya Amir yayi maganar yana dariya, shima dariyan Baana yayi yana tunanin yau wannan drama zasu kwasa shi da Hajjahkaka
2Am
Ya shigo dakin, inda ya same ni zaune ina cin bread, ko riga babu duk da sanyi da dakin ke bayarwa
Cikin mamakin ganin Sa yasa nace ta ina ka shigo ai mun rufe ko ina?
Ya jikin naki abinda yace kenan kafin ya tako zuwa inda nake,
Jawo duvet nayi na rufe kirjina dashi kafin na amsa da sauki,
Ina Hajjahkaka ?yayi maganar yana kallon bed,
Munyi fada da ita dazun tace yau bazata kwana anan ba.
Shiru yayi yana kallona cikin deam light, kina bukatar wani abu ne?
No.na amsa ina cin bread, ganin ya tsaya be zauna ba nace can you massage me please?
Cike da mamaki yake kallona kafin yace yeah sure, yana fadin haka ya zagayo ya zauna ta bayana ya fara massaging shulder na.
Wani dadi nake ji dan gabadaya jikina ciwo yake min ga zafin da nake ji.
Where have you been?har kusan sati uku?
Mamaki yake wai har da counting tayi na rashin sa? Can yace bana kasar ne.
Ban sake cewa kome ba shima be ce ba, bayan kamar 30mins yace ya isa?
Shiru nayi ina tunanin dan yanzu ba abin da nake so kamar sannin waye uban abin dake cikina, cikin karfin hali na juyo ina kallon sa kafin na kai bakina, cike da mamaki yake kallona kafin shi ma ya exclaiming lips ina….
Pharteema(DMK)
THANKS
Post a Comment for "Ni da Almajirina 22"