Ni da Almajirina 21
NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)
Episode 21
A guje na nufi idan abinci yake na dauki cutleries knife nayi setin daide wiyar hannun na,inda blood vessels ina suke na ja wukar,nan take jini ya fara zuba, a razane ya fado dakin ganin yana tun karoni na daura wukar daide cikina.one more step and I… Ban karasa maganar ba, naga wujen ya fara min juyi, ga duhu da ya gwaraye dakin,tun daga lokacin ban sake sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi, na ganin da bandage a hannun sannan ga cannular dake nuna min harda karin jinin…
Fara kokarin tuge abin nayi kamar wata wadda kanta ya dare,
Cikin kuka yace don Allah don’t hurt yourself for my sins, na roke ki don Allah kiji tausayin kanki don idan na rasa ki ta wannan dalilin tabbas ni mattace ne.
Ba tare da damuwa da abin da yace ba, na tuge abin karin jinin da karfi, bani da saurar rayuwa A wannan duniyar don haka kabar ni na mutu,mutuwa ze fiye min da wannan bakin ciki da nake ciki, na karasa maganar ina me kuka me kuna da cin rai…
Don Allah Hajjahna karki ce haka, kiyi hakuri ki yafemin…Ya kasa karasa maganar sabida kuka kai kace uwar sa ce ta rasu..
Rai bace Hajjahkaka tace Dallah ka tashi daga nan tunda naga kaima Dodi ne..
Kar ki kuskura kizo idan nake, yanzu na kara yarda da cewa ke ba uwar arziki bace shiyasa ko da shuwari suka kora yarki daga masaurata kika kasa yin kome sabida son abin duniya, nayi danasani sanin ku a duniya, nasan da uwata tana raye baza ta taba barin hakan ya faru dani ba, i hate you…!na karasa maganar cikin tsawa kamar wata zarariya.
Dana san akwai ranan irin tayau da na dadde da rokon Allah ya dauki rayuwa ta, ya Allah ina rokan ka daka dauki rayuwa ta, dan idan ina raye ban sa abin da zan gaya wa dan dake cikina ba idan ya tambaye ni waye mahaifin sa?
Da wani ido duniya zata dinga kallon mu na kasancewa iyalan dan ta ‘adda? Nooooo
Ganin yadda nake kuka kamar raina ze fita ya saka Hajjahkaka fashewa da kuka, ka ga irin ta ko Baanaliye ka ga abin da nike gudu kenan? Yanzu ita a tunanin ta sabida kwadayi na boye mata, bata san sabida gudun haka bane dan nasan reno nasara basu san kome ba illa suce zasu kashe kansu, inna lillahi wa ina ilahir raji ‘un Allahuma arjuni fi musabati.
Ni yanzu ya zanyi da wannan lamari?ni Binta nabi ina naga haske..?
Ganin Hajjan sa na ta ambato mutuwa yasa Baana barin dakin, bayan kamar minti biyar sai gashi ya shigo rike da wayar jin voice din Abba yasa na dakkatar da kuka na.
Ina iklasi, ina tawakali?shin irin adinin da na koyar dake kenan Falmata? Ke awaye ne zaki ki amsar kaddara Allah?
Idan Allah yace zaki taso cikin terrorist haka zaki taso Falmata, duk muslimin kwarai ansa sa da yarda da kaddara wallau me kyau ko mara kyau..?
Wannan bawan Allah be nufin ki da kome face alkhair, yes nasan an aikata miki ba daide ba na aura miki wanda ba kya so, ki tsaya ki fahimce ko shi waye kafin kin yanke hukunci me tsauri akan sa, sannan kuma ki nema masa fatan shiriyuwa gun Allah.
Cikin kuka nace Abba I’m devastated, the pain it’s unendurable, no i can’t take it Abba, i am sorry.
Cikin taushin voice Abba yace yes you can, tunda har kika iya hakuri da rayuwa na rashin mahaifiyar ki, na yarda da Baana kuma nasan ze dawo min dake kamar yadda yayi alkwarin don haka Falmata ki dauki wannan jarabawar a matsayin kaddarar ki, Allah yana jaraba muminai bayin sa wanda sukai imani yaga ya zasu yi?shin zasu bijere masa koko zasu cigaba da bauta masa?
Inda kina so ki kasance cikin al ‘ummah Annabi(S.A.W)zai alfahiri dasu gobe qiyamah to ki rugume kaddara ki ta fuska me kyau, in shaa Allah kome zai zo miki cikin sauki.
Ina me kara baki hakuri akan cutar dake da akayi Falmata kuma zan tayaki da Addu ‘a Allah ya kubutar daku sannan ya baki ikon cinye wannan jarabawar, yana gama fadin haka ya yanke kiran facetime.
Kuka me tsuma zuciya na keyi, yau ni ne dauke da cikin ALMAJIRANA? Kuma cikin terrorist?
Baanaliye zo mu bar dakin, basan haka Musa Buzu yake da spiriyens sai yau ba, gaskiya Allah ya jikar Shafaatu yasa tana kyakkyawar makonci irin wannan mijin da ta aura ba abin da zance sai de na shin masu albarka duka, Hajjahjaka tayi maganar tana share hawayen ta.
Hajjahkaka shin kina tunanin barin ita daya ba matsala? Baana yayi maganar yana kallon yadda nake famar kuka kamar rai na ze fita.
To da kake tsaye annan me kake yi? Ina sha kuka? Shin kukar ne ze hana ta yin abin da ke ranta?
Yau zamu ga shin tana jin maganar iyayen ta koko Dodi minal Dodi ce.
Hajjahkaka tayi maganar tana barin dakin..
Jiki a sanyayye ya bar dakin, kuka nake yi kamar abin da aka turo ni duniya nayi kenan, nayi kuka har nagaji…
Bayan Sati Biyu
Kulum kuka nike ko abinci bana iya ci balle samun barci, duk na koma kamar bani ba..
Kulum na saka goshina a kasa rokona gun Allah be wuce ya dauki rayuwata ba, don bakin ciki dake zuciya ta hanani sukuni yake…
Ina idar da sallah jiri ya dibe ni, farkawa nayi naga I’m on drip, so nake nayi magana amma bakina yayi nauyi sai bin kowa da kallo nike.
Ya Amir ne a dakin sai Hajjahkaka,
Tudan nake da Auta be taba bijire min ba sai akan ki, idan har kina son iyayen ki da yan uwanki a raye to ki rena abin da yake cikin ki,.idan wani abu ya same cikin nan kin ga har wannan tsohuwar sai na aikata lahira. Ya Amir yayi maganar a kausashe.
Hajjahkaka tace to sai miye don ka kashe ni iye me matsasen duwaiwai?naga fa mutuwa duk za muyi kaima din mutuwa zaka yi , idan zaka bita a hankali ka bita bawai kazo kana mana barazana ba ehe.
A hassale Ya Amir yace bake ba harta shi sai na kashe.
Cike da mamaki Hajjahkaka tace Baanaliye ne zaka kashe?kai ko wannan wani irin mumunar akida ka kikiro? Gaskiya mabiyan ka ba karamin asara sukai ba.. Duk irin biyayya da Baanaliye ke maka har kake fadin haka?
Juyawa Ya Amir ya bar dakin, Hajjahkaka tace ni tunda uwata ta haife ni ban taba ganin mugu mara imani irin wannan me matsatsen duwaiwai kamar na huran biki.
Indai har ze iya kashe Baana tabbas ze aikata abin da yace, tunawa nayi da Faruq da ABBAH shin akan lefina sai na rasa iyayena da yan ‘uwa na ?
Shiru nayi ina ta tunanin abin da yace…
Nurse ce ta shigo dakin, duba BP na tayi kafin tace Alhamdulillah jinin ta ya sauka,.amma don Allah a kiyaye adaina barin ta cikin damuwa sanan adinga bata abinci na gina jiki sabida lafiyar ta shine lafiyar abin da ke cikin.
To mungode nass amma don Allah ina Baanaliye ne rabona dashi yau kwana goma shabiyar cib cib.
Nurse tace ayya baki san bashi da lafiya ba? Ai Mu ‘alim dayawa sun dauka baze kai labari amma jikin da sauki, shima jinin sa yay hau saura kadan da ya shiga stroke.
Sito kuma ? Ina sha sito shine manya shaguna? Hajjahkaka tayi maganar cike da mamaki.
Nurse tace aah da yanzu ya shanye maana gangan jikin sa sun dena aiki.
Salati Hajjahkaka ta saka tace Baanaliye ne jikin sa ya kusa shanyewa? Don Allah kaini naje na gansa,
Ana cikin magana sai gashi ya shigo duk ya zube kamar bashi ba, bayan ya gaida Hajjahkaka ya tambayi nurse ko akwai matsala, Nurse ta gaya masa exact abin da ta gayawa Hajjahkaka
Kamar me koyan tafiya ya tako zuwa idan nike,
kallon sa nake ina tuna abin da Ya Amir yace, ze iya kashe shi akaina, sai naji dan tausayin sa amma nai saurin kawar da tunanin kar tai tasiri cikin raina.
Kiyi hakuri Hajjahna ni nasaka ki cikin wannan halin,don Allah ki yafe min yayi maganar gwiwan sa a kasa.
Bance dashi kome ba sai hawaye dake diga daga idanuna
Allah Sarki Baanaliye duk duwaiwai ya kara tsiyayyewa gaskiya ba karamin jinya kasha ba , na roke ka ka cire damuwa a ranka kar ya haifar maka da ciwon shan inna, Hajjahkaka tayi maganar cike da tausayawa.
Hajjahkaka ki tayani nima gaffara gun ta, bana so tana wahalar da kanta akai na. Don Allah ko so daya ne kiyi min magana Hajjahna.yayi maganar kwalla cike idonsa.
Hajjakaka tace kulum sai na bata hakuri amma taurin kanta yafi karfin ta, inasha har mahaifin ta yayi mata magana irin ta yan boko masu adini da sipiriyens amma ta ki, yanzu nan me matsatsen duwaiwai nan yabar nan yana mata barazana.
A fusace Baana ya dago yana kallon Hajjahkaka yace barazana kuma ?
Hajjahkaka tace kwarai kuwa harda cewa zai kashe mu duka tun daga kanta har zuwa zuriya mu ta uku.
A fusace Baana ya mike ze bar dakin, a hankali na bude bakina da yayi min nauyi nace…
Pharteema(DMK)
THANKS
Post a Comment for "Ni da Almajirina 21"