Ni da Almajirina 2
NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)
Episode 2
_NOTED# WANNAN SHINE LITAFINA, NA FARKO WATAKILA SHINE NA KARSHE 凉 IDAN KUNGA KUSKURE KUYI MIN AFUWAN_
Haryanzu Falmata na jibge a kasa kamar kayan wanki, amma kowa ya ganta yasan tana cikin tashin hankali, ba abinda yafi tsaya mata a rai kamar yadda aka tafi dasu Batula, bata san ko suna raye ba ko akasin haka, sai yanzu hawaye ya fara saukowa daga idonta, Jiki a sanyayye ta mike ta nufi dakinta, dauko waya tayi don ta kira Abban ta amma gaba daya ba network, a hankalin ta furta kalmar Inna lillahi wa Inna ilaihir rajiun, haka ta dinga maimaitawa tana kuka..
Tafi karfin minti talatin a haka kafin taji an banko dakin ta, wannan bakon ne ya shigo dakin ya karbe wayar hannun ta kafin yace da ita ta bi bayan sa, kamar mara laka a Jiki haka Falmata ta bi bayan sa, har suka isa wajen gate inda taga HajjahKaka zaune kikam a gaban motar.
HajjahKaka na ganin Falmata tace, to mude gamu ga Allah. Idan ma kashe mu zasu yi to nide sun hutashe ni, amma matsala ta daya shine ke Falmata.
Ba tare da Falmata tace da ita komai ba ta shiga gidan baya kamar yadda Gambo yace mata, kafin ya zagaya ya shiga mazauni driver ya ja motor, tafiyar hour daya ya kai su masaurata Bama. Inda yan’uwa Gambo ne cike a masaurata,kowanen su rike yake da bindiga a hannun.
Allahuma arjuni fi musibati, yanzu masaurata ce ta koma haka? Sai kace ba jini Bulama ba cab? Wai ina shuwari suke? HajjahKaka tayi maganar tana karewa gun kallo ganin mutane kwance cikin jini, Gambo yayi masu jagora har suka isa fadar Sarki.
Daku nake nace ina shuwari da Sarki? HajjahKaka tayi maganar tana kallon wanda ke zaune samar kujeran Sarki.
A fusace Gambo ya waigo yana kallon ta, kafin can yace sunyi biyayya sunyi abinda ya dace! HajjahKaka zata ce…yayin saurin yanke maganar ta da dukawa gaban wani matashi wanda yake sanye da bakaken kaya da rawani da ya rufe fuskar sa, Cikin yaren su Gambo yace “Amir ga yarinyar da kakanta ”
Sai da ya dauki kusan seconds kafin Amir ya bashi amsa da ya mike yaje a tattaro sauran mutane da aka kama.
Cikin kankani lokaci aka tattaro mutane, cikin yaren su Amir ya umurce mazan su koma gefen, maza duk suka tare gu daya haka zalika matan na gu daya, daga bisani aka zakulo tsofafi mata da maza aka ajiye su a gefe..
Saida Amir ya dauki kusan minti goma kafin yace acikin ku su waye ma aikatan asibiti? Ku gufanar da kanku yanzu, nan take doctors and nurses suka fito Jiki na bari,cike da izza Amir yayi pointing wani dattijo a cikin ma’aikatan lafiya, yace mushe, ya sake pointing wani yace tafiya, haka ya dinga pointing daya bayan daya, wanda ya kira su da mushe aka tattara su a kayi waje dasu, tsofafin ma akayi waje dasu ya rage mata da maza, acikin maza aka dibe masu karfin sauran akayi waje, Batula Babagana, Bintu Maita haka ya dinga kiran sunaye mata harsai da ya kira mata goma,kafin yace yau ranar Kwanar ku ne, Gambo ku tafi dasu turaka.. cike da kuka da magiya aka fara kokarin shigar dasu..
HajjahKaka tace wannan wani irin rashin imani ne? Ka hada ya’ya da iyayen su akai maka su turaka to kayi wani tsiya dasu? Ba gara ka harbe su ba da wannan zalinci.
Cikin breaking voice Falmata tace HajjahKaka miye zai dasu?
HajjahKaka cikin kuka tace wai zai hadasu su zama matan sa…
Cikin karfin hali Falmata ta nufi idan Amir yake, tace where’s your humanity? Wani irin rashin imani zai saka yin haka? Ba gara ka kashe mu da abin da kake shirin aikatawa ba? idan ma baka jin abinda nake cewa HajjahKaka ki gaya masa cewa shi ba mutum bane shi dabba ne. Falmata tayi maganar cikin daci.
Mabiyan sa har sun yau kan Falmata ya dagatar dasu. A kausashe Amir yace keeee reno turawa ki iya bakin ki kafin na harbe ki.
Falmata nifa tudan nayi arba da wannan marar imani sai nake jin miryan sa kamar na Baana ALMAJIRINKi? HajjahKaka tayi maganar da karfi babu tsoro. Tana kare ma kwayar idonsa kallo…..
Itama Falmata kallon kwayar idon nasa take da kokarin gane voice insa, ganin sun tsaya suna kallon sa ya mike yace Gambo taho da ita ta ganewa idonta, yana fadin haka ya mike ya nufa waje, Gambo ya cacumota yabi bayan Amir din, HajjahKaka tace ina za kuyi da jikata? Don Allah ku dawo da ita, yarinya ce bata san kome ba, HajjahKaka tayi maganar tana kuka, gashi ba wheelchair bare tabi bayan su.
Tafiyar minti biyu su kayi, kafin suka isa wani pankacecen rijiyan masaurata, Wanda daga ganin rijiya yana da zurfi da fadi, mutane ake datsa kansu a rijiyan kafin ayi wurgi dasu cikin rijiya, daga tsofafin har mazan da aka fito dasu haka aka dinga masu, ganin yadda aka pille masu wiya ga kuma yadda jini ke falatsa yasa Falmata throw up bata shirya ba.
Amai ta dinga yi idonta na juyi, yanzu ta kara tabattar da cewa wa inan ba mutane bane kuma ko a dabbobi su wani halitta ne na daban, sumewa tayi a wajan tsabar firgici da tashin hankalin..
Farkawa Falmata tayi ta ganta a daki tare da HajjahKaka dasu Batula, cikin kuka Batula tace thanks to you we’re safe now, Amma an shiga da wasu matan ciki, tayi maganar tana fashewa da kuka..
Jiki babu kwari Falmata tace in shaa Allah Batula zamu bar hannun wa inan a zalumai mutane nan, mu dage da addu’a, dan abinda na gani dazun yafi karfin tashin hankali, Batula fa butchering (datse)mutane su keyi kafin su jefa su cikin rijiya, Falmata tayi maganar tana fashewa da kuka,
3am
Karfe ukun na dare aka tattara su Batula akayi cikin jejin dasu tafiyar hour hudu sukai a kafa kafin suka isa,
Gajiya, kishin ruwa da rashin kwari yasa suka zube a kasa…
Falmata na kokarin taimakawa HajjahKaka wajen fitowa daga ban daki, Gambo ya fado dakin cikin hanzari.
HajjahKaka tace wane kafirin ne ya banko min kofa ba salama iye?
Ba tare da Gambo yace da ita komai ba ya dauke ta zai fita da ita, Falmata tayi saurin shan gaban sa tace where are you taking her to?
Hijira zamu yi yanzu. Gambo yayi maganar cikin hausar sa da babu karfi, kamar yar jaririya haka ya dauki HajjahKaka ya sakata a mota, Falmata dake biye dasu a baya tace ina su Batula?
Kala bai ce da ita ba yayi mata alama da ta shiga motar, ganin zata bata masa lokaci kawai ya hankada ciki ya rufo kofar kafin ya zaga ya shiga mazauni driver, yaja motor a guje kamar wanda ake bin sa.Tafiyar minti 40 su kayi kafin suka isa wani kurmumin jeji, dukda cewa garin Allah ya fara wayewa amma har yanzu jejin duhu ne.
Batula na hango Falmata ta mike da kyar tace, ruwa tayi maganar tana hakki, da gudu Falmata ta nufi idan Batulan take tace ku taimaka mata da ruwa dan Allah tana da asthma..
Su Gambo ba wanda yace ufan balle ya taimaka masu da ruwan..
Nan take numfashi Batula ya dinga sama tana tari, idonta duk a bude, hankalin Falmata ya kara tashi ta nufa Gambo a guje tace na roke ku, ku bani ruwa dan Allah, ko dan kadan ne?
Kamar tana magana da gawa haka Gambo yayi tsaye ko gizau.
Can ta koma gun Batula dake famar kokari da numfashin ta, Farkon abinda tayi ta cire mata hijabin sannan ta kwantar da ita flat a kasa, ta daga rigan ta sama sannan ta daura hannun daya sakanin kirjin ta, ganin yadda heart ke bugu a hankalin tayi saurin dan dago da kanta zata daura bakin ta hura mata iska in form of CPR kawai taji an fizgo ta anyi wurgi da ita, cikin karfin hali ta mike tana kallon sa..
Cikin hausar sa da babu kwari yace iskanci da ake koya maku kenan a bokon? Amir yayi maganar yana kallon ta ido cikin ido..
Falmata mayar da duban ta zuwa Batula dake famar kokarin da numfashi ta, duk ta galabaita har idanuwanta sun canza launi, Falmata ba tace dashi komai ba ta sake yunkurin zuwa gun da Batula take amma ko taku biyu bata yi ba ya sake fizgo ta hade da daura mata bindiga a ka.
HajjahKaka na ganin haka tace Dan ubanka ka saka min jikata, in ba haka ba wallahi zan yi maka baki kai mutuwan wulaqanci..
Kallon HajjahKaka Amir yayi, sannan yayi wa Gambo alama da ya tafi da ita, Gambo yayo kan HajjahKaka ya dauke ta cak sai mota sannan ya rufe ta aciki, kuka HajjahKaka take yi tana debe masu albarka.
Sakin Falmata Amir yayi, ta zube a kasa tace don Allah ka bari na taimaka mata idan ba haka ba zata iya rasa ranta, tana nema taimako na gaggawa.
Ba wani mai taimako sai Ubangiji, idan Ubangiji yace zata rayu, zata rayu. Amir yayi maganar a kausashe.
Kallon yadda Batula take kokarin daidata numfashi tayi, Falmata ba tare da tace komai ba ta sake mikewa zata gun Batula, Amir yayi saurin damke hannun ta, yace kina son yar uwarki ta warke ?
Falmata tayi saurin kada kai alamar eh, dariyar mugunta Amir yayi kafin ya saki hannun ta, yace jeki ki warka da ita, yana fadin haka ta kara aguje dan bai wa Batula taimako na gaggawa saide kafin ta isa inda Batula take kawai….
Introvert ✍
THANKS
Post a Comment for "Ni da Almajirina 2"