Ni da Almajirina 16
NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)
Episode 16
MASU CEWA NA KIKIRO LABARI TO GA:
[11/28, 15:32] +234 93 75 : Yan uwa wllh garin banki garinane acikinsa aka haifeni akai aure yakin bk ne ya karemu da. Mijina muna jigawa yanxu haka amma iyayen a da yan uwa na duk suna garin banki wannan lbrn ba karya bane da gaske kuma wllh suna auran iyayen su kuma suna kashe iyayen su gaskia littafin nan Masha Allah sai gdy ashe xanje lbrn garinmu a duniya yanxu haka xa ai auren kannaina xanje
[11/28, 15:34] +234 93 75: Sannan har yau idan xaka shiga garin sai sojoji sun muku escort daga bama har cikin banki kuma ana tafia ana harbi ana scanning in hanya ana tonewa bom ai munga masifa a rayuwa saide allah yasaka Mana banana haryau da buluwar bullet a hannunsa na yan Boko Haram
HMMMM
Back to business
Ina barci naji kamar mutum a samar kaina, nayi sauri bude idanuwa, idan naga sa tsaye kaina yana me kallona, yinkuri mikewa nayi daga kwance da nake yayi saurin zuwa ya mayar dani.
A tausashe yace do you need anything?
Hawaye ne ya fara cika idona kamar wacce aka mintsila na soma kuka.
Koma kin kwanta yayi maganar yana kokarin barin dakin..
I’m having cramps and my stomach hurts so bad please ka mayar dani gun HajjahKaka.
Yi yayi kamar beji ba, ya fice gaba daya, kamar wacce aiko wa da sakon mutuwa na cigaba da shan kuka na.
Baana na barin dakin, gun HajjahKaka ya nufa da salamar sa,
HajjahKaka dake zaune tana shan kunun tayi kamar bata san anyi sa ba.
Takowa yayi har inda take yace inda dipto.
Idan kana son ka to maza ka dauki tsiyayyen duwawai ka bar min daki tam. HajjahKaka tayi maganar cikin matsifa
HajjahKaka shin dagaske Falmata na da juna biyu? Baana yayi maganar kansa na kallon kasa
Wani mugun kallo HajjahKaka ta watsa masa kafin tace sai da kaje ka bara da cikin da warin gawasa zaka wani zo kana min tambayar rashin kunya?to ban sani ba.
Cikin taushin mirya yace don Allah HajjahKaka ki gayamin shin kin san tana da ciki? Baana yayi maganar yana kallon ta.
Bama banza ajiyan sa HajjahKaka tayi har kusan minti biyar, saida taji anshigo dakin da salama ta dago tana kallon su tana wani yatsine fuska, amma abinda ta hango yasa ta washe baki. Wheelchair ne nazamani wanda basai an gungura ta ba taga an shigo dashi,
Ga wasu mata rike da warmer s sun kai biyar.
Laa wannan me gafin da warin gawasar ce tayi shadaudau haka abin ta? Yarnan gara da kika yi wa kanki qiyamu laili kika dena bude masu kanti patari yo ba gashi har kin shigo ban gane ki ba?
Murmushi Yabawa tayi kafin ta ajiye mata warmers ta wuce.
Cikin faraa HajjahKaka tace har fa abin duniya ta karo da duwawai a tsiyayye ko ni da nake tsohuwa nafita abin arziki..
Murmushi Baana yayi yana kallon HajjahKaka.
Yawwa Baanaliye me kake cewa ma?
Girgiza kai Baana yayi kafin ya maimaita tambayar yana me murmushi
HajjahKaka tace ka san a haife de saide nayi jika dakai na hudu ko? To tun ranar da kayi mata abin manya nan rabo ya tsaga, ni har sheda saina nuna maka ma bawai papatu ba.
Murmushi Baana yayi kafin yace amma miye sa kika ce mata karya ne ba ciki?
To in banda abinka Baanaliye? Falmata guda nawa take? Idan tasan da cewa tana da ciki ai sai ta kashe kanta kaima sanin kanka ne Falmata ba spiriyens atol. Ni dama so nake cikin idan yayi kwari na sanar da ita ka ga alokacin ba yanda za tayi saide ta rugume sorry. Amma kai kuma sai ka koma Dodi minal Dodi ka kasa gane hakan.
Shiru Baana yayi yana kallon ta kamar wani me nazarin wani abu can yace HajjahKaka ya zanyi ta fara so na?
Ahab abu cikin sauki kaide kawai kabar kome a hannun na, abu daya nake so agun ka shine kayi dan nesa da ita, banda abin manya dan warin gawasa ze iya hallakar da cikin Ato. HajjahKaka tayi maganar tana bude foil plate na danderu da yasha hadi.
HajjahKaka bazan iya ba.. Baana yayi maganar cikin damuwa
Ba zaka iya mene ba? Baanaliye kace ba zaka iya dena yi mata abin manya ba. Iko sai Allah…
HajjahKaka ba abinda nake nufi ba kenan, ina nufi bazan iya zama ko na kwana daya bata.
To dan ubanka da ya kake kwana? Ka ji min wannan Dodi fa, yaushe akayi daren bare gari ya waye? Kai na dago ka fa, so kake kai ta mata abin manya ko?
Shiru Baana yayi yana kallon ta can kuma yace ni zan rena ciki, zan basu dukan wani kariya da suke bukata,yana gama fadin haka ya mike yabar dakin.
Sakin baki HajjahKaka tayi tana kallon sa can tace to da ace na tsuma ta ina ji wannan da anga manno tab. Ya’yan zamani sam ba kunya ta karasa maganar tana yagan Naman.
Komawa dakin yayi ya same ni sai aikin abu daya nike yi wato kuka.
A hankali ya tako yazo idan nake, kukan me kike yi Falmata?
Don Allah karka yimin kome nasan ka gane gaskiya.
Cikin ransa yayi murmushi kafin yace cramps ya tafi?
Raraba ido nayi ina kallon sa, nace da saura.
Ba kya so na sake taba ki? Yayi tambayar yana kallon cikin idona?
Nayi saurin amsawa da eh.
To ki dena min taurin kai, duk abinda nace ki dinga yi kinji?
Kamar wata yar yarinya nace tam, amma a zuciya ta nace zaka ga biyaya kam..
Muna cikin magana wayar sa tafara kukan kira, duba me kiran yayi kafin ya amsa cikin hanzari Da Naam Ya Amir
Ya Amir dake dayan bangaren na waya yace tafiya ta gaggawa zamu wata kasar kuma ina so ka a tafiyar, dan wannan tafiyar na da mahimmanci
Baana yace Ya Amir bata da lafiya kuma tana bukatana kusa da ita.
Zan aiko da jirgin da ze kawo ka sai mun hadu, Ya Amir na fadin haka yanke.
Nikam farin ciki fal raina, Allah ya sa idan sun tafi duk su mutu nayi maganar cikin raina
Falmata zan mayar dake wujen HajjahKaka zamu yi tafiya amma bazan wani dade ba idan kina bukatar wani abu akwai Yabawa ki sanar da ita.
Bana bukatar kome illa….acikin bakin sa na karasa maganar abu kamar wasa yana neman komawa wani abu, ko me ya tuna naga yayi saurin ja jikin sa kafin yace
Nasan burin ki be wuce ace na fadi na mutu, murmushi yayi kafin yace ko na mutu bazan taba rabuwa dake ba
Coz na…..
Pharteema(DMK)
THANKS
Post a Comment for "Ni da Almajirina 16"