Ni da Almajirina 15
NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)
Episode 15
To Hajjahkaka naga dukda ance cikin be son ganjn sa, amma…ban gama magana ba naga ya shigo a fusace, a tsorace na mike ina kallon sa.
Ba tare da yace kome ba,ya fara tinkaro ni, ina ja da baya…
Ganin yanayi fuskar sa, yasa Hajjahkaka yasa tayi gum da baki tana binsa da ido.
Baana na kira sunan sa cikin sarkewar mirya, dan idonsa abin firgitarwa ne, hannun ya rike ya fizgo ni…
Hajjahkaka na ganin haka tace Baana idan kana son cikin nan to ka nisance kanka da….kallon da yayi mata yasa ta hadiye saura magana.
Dauka na yayi in a bridal way, tsabar tashin hankali nima kuka nayi na rasa, sai addu ‘oi na keyi don ban san ko kashe ni zeyi ba?
Dire ni yayi samar gado ,
nayi saurin mikewa ganin ya fara tube kayan sa, abin da ban taba yi ba shi nayi yau..
Hawaye cike idona nace don Allah Baana idan nayi maka lefi ka yafe min, idan kuma hukuntanin za kayi ka harbe ni kawai na huta, na karasa maganar cikin matsananci kuka…
A kausashe Baana yace miye na miki falmata kika yimin haka ?
Ba tare da sanin abin da nayi ba,.nace kayi hakuri don Allah…nayi maganar kaina a duke..
I want nothing but the true, are you pregnant or not ? Yayi maganar a kausashe.
Hadiye wani abu me sartse da daci nayi cikin wiya ta, wani zufa naji yana keto min kamar wacce tayi sata haka na daburce ina kame kame.
Murmushi me ciwo yayi kafin yace kunyi wasa da hankalina for the first time kuma ba zan sake barin kuyi ba. Now you shall face the repercussion for actions Falmata. Yana gama fadin haka ya fara kokarin aiwatar da abin da ke ransa,yana hade bakin mu da naji hankalina ya fara tashi, amai yazo min ba tare da na shirya ba, kamar wacce cikin ta ba lafiya haka na dinga kwara amai…
Dauka na yayi zuwa toilet, still ba dena amai ba, ina tunanin Allah ya amsa addua ta shiyasa ya sauko min da wannan ciwon ciki…
30Mins nayi a toilet kafin na fito har yan gyara an canza kome,sai kamshi turaren kamshi ke tashi..
Temaka min yayi na zauna kafin ya dauko Borno tea, amsa nayi ina sha, taba tp na yayi yaga normal,
Murmushi me wiyan fassara yayi kafin ya mike yabar dakin…
Hamdallah na dinga yi ina godewa Allah da ba abin da ya same ni, “Ya Allah kasa duk lokacin da yayi yunkurin yimin wani abu nai ta amai ko kuma na suma…
Maiduguri
Ko ina yanzu ya dauka kuma yasan da zaman sojojin jihadi, kasancewa a wani yammaci aka farmake cocina uku da ake ji dasu a garin “Baga da Banki ” yasa kowa ya farka daga zaune da yake, ga kuma hacking gidan TV “The Dairly Record” idan video Ya Amir ya tafi viral. A video ya fito karakara yace su Aikin Allah su keyi na fada da nasara da abinda suka kikiro, kuma yanzu suka soma ba denawa”
Yana gama fadin haka ya yanke video.
Hankali kowa atashe yake barin yadda aka saka bomb a cocina uku.
Kowa ya fito gidan radio yana fadin albarkacin bakin sa bare wata Debora dake cewa
“Wata daya da suka wuce aka deba yan makaranta The Queen’s School dake Bama, a satin aka shiga garin Bama, Marte da Damasak aka kashe dumbi rayuka da dukiyoyi mutane amma haryau ba wanda ya fito ya ce wani abu, manya mu sunyi shuru mutane gari ma sunyi shiru, to masu karyata wannan zance kun de ganin da idonku ko? So suke su mayar da ko wannan dan Nigeria Muslim bacin Nigeria muka fara samu kafin zuwa ko wanne adini idan zamu farka mu farka da wuri don iyayena da kanen na St Mary church da aka sa bomb dake Banki, Debora ta karasa maganar tana me fashewa da kuka”
Maganar da Debora tayi na fadin cewa ana so a mayar da Nigeria ya zama kasar muslimai ya ja cecekuce a kafar yada zumta, inda kristocin Nigeria suka fara wa akan abin da ya faru, kafin kace me jihar Jos ta dauka, nan ma aka fara kashe kashe tsakanin muslimai da kristoci.
Binta dake zaune gida cike da damuwa ganin abinda ya faru, tana cikin kallon tv wayar ta ya fa ra kukan kira, a firgice ta dauka jiki na bari,
Ya Amir dake dayan bangaren na waya yace, Our journalist aiki yayi kyau, ya kare maganar yana me kwashewa da muguwar dariya, yanzu kin ga zaki koma bakin aiki ko dan wannan dalilin na afanin da yaren da gwamnati da mutane gari suke so, yanzu gabadaya hankali Yan Nigeria atashe yake. Yana gama fadin haka ya yanke kiran.
Tagumi Binta tayi tana mamaki wannne irin mutane su wanda basa son zaman lafiya, yace suna fada ne akan boko da aiki gwamnati amma me ya hada wannan da adini?
Tana cikin wannan tunanin kiran ogan ta ya shigo, ta dauka ba tare da tace kome ba,
“ Binta ki dawo aiki yanzu” yana gama fadin haka ya yanke kiran wayar.
Saida ta kira mijin ta ta sanar dashi kafin taje ta dauko yaran ta biyu daga school takai gidan iyayen ta sannan ta wuce gun aiki
BAYAN SATI DAYA
Wani farin ciki na keyi a yan kwananki nan, ganin tunda ya dauko ni nake zazzabi, daga na ci na sha sai nasha maganin na kwanta..
Ina kokarin shiga toilet, ya shigo tare da wata mata, daure fuska nayi kamar bansa wani abu dariya ba,
Ki koma ki zauna za ai maki test, idan ma karyan ciwo kike yi yau zan gane, idan ma kyamata kike yi, yasa kike amai da nazo maki duk ayau zan gane. Baana Yayi maganar a kausashe.
Kamar zanyi kuka nace fisari nake ji.
Matar tace ga wannan ki diba fisarin ki, ki kawo min, amsa nayi na wuce dashi toilet, 5mins na fito rike da abin na mika mata,
Matar ta amsa ta duba can ta kalle shi tace negative amma zan diba blood sample inta yanzu da shi zamu running test dinmu.
Kamar yadda tace zata deba jinin haka ta fito da alura, ganin da tsoron alura da jinin, ba shiri na fara kuka ina cewa kiyi hakuri please karki yi min alura,
Ganin ina kokarin ba ma matar ciwon kai, yasa ya taho inda nake a fusace, ya rikoni gam idona cikin idonsa yace, ki natsu, ya na rike dani har aka diba jinin sai kuka na keyi ina kallon jinin da aka dibo..
Bayan ta gama tace, zai iya daukar 1hour sabida tests biyu zamu yi mata.
Yanzu nake so Baana yayi maganar a hassale.
Matar ta amsa a tsorace kafin tabar dakin,
Tana barin dakin Baana yace inhar akai test ba a gano wani ciwo ba, ba amai ba ko mutuwa za kiyi yau zaki gane yaren da kika kasa ganewa a wacan haduwar tamu, yana gama fadin haka ya mike a fusace yabar dakin.
Fashewa da kuka nayi dan nasan bana jin wani ciwo a jikina, ciwon kai ne shima dan kukan da rashin cin wadatarce abinci yake jawo min ciwon kan.
Addua na soma yi a gano ciwon ko dan na kubuta daga hannun sa.
Nayi kuka har nagaji saida barci barawo ya sace ni kafin na dena kuka.
Ina barci naji kamar mutum a samar kaina, nayi saurin bude ido, idan nagan sa tsaye kaina yana…….
Pharteema(DMK)
THANKS
Post a Comment for "Ni da Almajirina 15"