Ni da Almajirina 14
NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)
Episode 14
Cike da mamaki Baana yace Wacce yarinya?
Cikin tsanar da kyamar ganin sa nace ni ka fice min daga gani, nayi maganar cikin tsawa.
HajjahKaka tayi saurin cewa Baana idan baso kake cikin nan ya fita yanzu to kabar nan, danye ciki ne fa ajikin ta kake sata wannan ihun?
Hankali tashe Baana ya fito daga toilet ya nufa idan HajjahKaka take, ya zauna. Cikin taushin mirya yace HajjahKaka Don Allah ki kulamin da ita da cikin, idan kuna bukatar wani abu ku gayamin.
Yamutse fuska HajjahKaka tayi kafin can tace dazun de tace tana bukatar danderu hakarkarin rago da kunun madara.
Kallon time Baana yaga to 11, can yace to HajjahKaka zan sa akawo maku yayi maganar yana mikewa daga zaune da yake,
HajjahKaka tace ba fa danderun gashin inji ba,na gashin tukunyar kasa take so, sannan ka canza mana yar aikin nan, Walhi warin da gafin gawasa kawai ke tashi a jikin wannan figigiyar mata, kai maza ma sam ba ta ido, habawa ace ina Namiji ai me zanyi da me duwawai kamar kobiyu?
Ganin surutun HajjahKaka bame karewa ba ne yace to, tana bukatar ya’yan itattuwa?
Ba dole ba, wannan aika aika da kayi ga kuma danye ciki zuke jini ya keyi.
Cikin hanzari ya fice daga dakin yana fita, HajjahKaka ta kirani da na fito.
Fitowa nayi na zauna kusa da ita, tace to kinga yadda ake wa Namiji, idan kika tabbatar da yana sonki to sai ki hada da kissa da kisisina bawai kema ki koma Dodi minal Dodi kamar shi ba,
Ina fatan kinyi spiriyens yanzu ko?
HajjahKaka yanzu shikenan baze sake zuwa inda nake ba? Nayi maganar ina murmushi.
HajjahKaka tace to bana ce ba idan kin fi sauran matan gardi da dadi to ki dinga ganin wannan tokareren katon kenan amma kissan ki ze kora shi.
Kai Falmata ashe Baana kyakkyawar mutumin ne haka?sai yanzu nake ganin kyawun sa,ashe rashin tsabta ne da kula yasa ya tirke,bakinkirin amma yanzu dube shi duk ya koma bakin balarabe
Rai bace nace to ina ruwana da wani kyaunsa HajjahKaka?
To wa ya san miki ko kyaun sa ne ya rijanye ki, kika daga masa patarin naki ya miki abin manya?
Fashewa nayi da kuka…
Sakin baki tayi tana kallona kafin can tace Walhy karki zama me spiriyens ki zama Dodi minal Dodi, Allah dura miki ciki zeyi kin ga zama ya kamaki annan.
Share hawaye na nayi kafin nace me abin so a wannan kazamin dan ta’adar ?ko bata rayuwar yammata da su keyi yaci ace tsine masu akeyi amma shine zaki wani ce wai kyaun sa ne ya rudeni?
To ya isa haka kafin ki batamin rai nakasa cin danderu, HajjahKaka tayi maganar tana kokarin kwanciya, taimaka mata nayi ta kwanta.
Sai wajan 2 dare aka aiko da wannan danderu, HajjahKaka kamar wata mayya ta mike ta soma cin kayan ta
Washe Gari
Journalist Bintu da wuri tabar gida sai parara gudu take akan titi har fita kan titi bata dena gudu ba, saida ta shiga wani jeji kafin ta ja birki ta tsaya, sai raraba ido take, can sai ga wani bakar BMW ta taho ta tsaya daide inda tayi parking.
Wayar ta ne ya fara kukan Kira, ta amsa a tsorace, ko seconds ba tayi da amsa wayar ba ta fito ta shiga BMW, tana shiga driver ya jata, saida sukai tafiyar kusan hour daya, kafin yayi parking, sake kiran ta akayi a waya, ta dauka cikin hanzari, amsawa tayi da to, kafin ta fito daga motar, tafiya ta dinga yi har ta issa wani camp, ta tsaya daide wurin.
Da fara’a Ya Amir ya fito daga rumfar yace barka da zuwa our journalist.
Hadiya wani abu me daci Bintu tayi kafin ta sauke ajiyan zuciya, ki shigo yayi instructing dinta yana kokarin shiga cikin rumfar, jiki na bari Bintu tabi bayan sa idan taga shi daya ne aciki,
Bintu Garba na kiraki nan sabida yabawa da kwazon ki, kuma naji dadi da kika amsa katin gayyata ta.
Kar na cika da surutu mu fara da daukar rohotu, yana fadin haka Ya Amir ya ciro machine guns ya rataya a kafadar sa..
Jiki na bari Bintu ta dinga kwasar rohotu daga gun sa, bayan ya gama yace zan gaya miki when to broadcast it. Kuma ki cigaba da biyyaya babu me tabaki a wannan kasar
I got your back.!
Yana fadin haka yace zata iya tafiya, kamar wacce zata tashi sama haka Binta ta mike hade da yi masa godiya kafin tabar rumfar.
Fadar Ya Amir
6am
Duk wani shiri da sojojin jihad sunyi jira kira kawai suke, su kadamar da kundirin su.
Kamar kulum Baana ya tafi kewaye, farko rumfar mata ya fara zuwa inda sukai ido hudu da Altine.
Tana ganin sa tace da’na daman kana raye? Nida mahaifin ka ba irin kukan da bamu yi ba na rashin ka.
Murmushi me ciwo Baana yayi kafin yace Baana dake tsaye a gaban ki daban da waccan dan shekara hudu da kika yaudara Altine, idan kika kara kirana da danki walhi zan harbe kanki da bindinga.
Hadiye yawun me daci Altine tayi, zata kara magana Baana ya saurin yanke maganar ta da fadin cewa wannan matar ai mayar da ita takin madafa, sannan kusa mata ido sosai, sau daya zaku bata ruwa da abinci a rana,
Yana gama fadin haka sojojin suka amsa da to, a wulaqance suka cacumo ta sukai waje da ita, ba irin kuka da magiya da ba tayi ba dan ai mata sausauci amma Baana yayi kamar baya ji, bayan ya gama zaga ye ya koma fadar sa, kai tsaye ya nufa dakin Hajjahkaka.
Hajjahkaka dake samar salayah tana lazumi tayi saurin dago da kai tana watsa me mugun kallo
Kaga wannan me bakin fuska kamar tsohon duwaiduwai ka kiyaye kanka dani tam,
Baana yace “inda watu”, yayi maganar da taushin mirya yana kallon samar bed ko matar sa na kwance.
Maye ba cewa tayi bata son kara ganin ka ba? Ko so kake danye cikin ya zube?
Aah Hajjahkaka nazo tambaya ne kuna bukatar wani abu?
Fitowa na daga toilet Keenan, nagan sa zaune kusa da Hajjahkaka, rai bace nace fita yanzu karka sa nayi amai dan ban shirya ba.
Mikewa yayi da sauri yace nazo tambaya ko kuna bukatar wani abu,
Juya masa baya nayi nace idan muna so, ai za muyi aike don haka ka fice daga gani na..
Kallon da yake mata ji yayi kamar yaje ya rugume matar sa,shi ya rasa irin son da yake ma Falmata, kome tayi birge shi ta keyi..
To tsohon maye sai ka hadiye ta ka huta muma mu huta, yanzu duk irin aika aika da kayiwa yarinya nan be isheka ba sai ka karasa ta ne zaka huta? Kai wannan me tsiyayen duwawai akwai rashin ta ido, jibi yadda yake binta da ido, ke kuma banza kin juya masa duwawai kamar kobiyu yana kallo, maza ki samu waje ki zauna, HajjahKaka tayi maganar rai bace
Baana be san lokacin da yayi dariya ba, wai kobiyu, ko miye yake hada HajjahKaka da duwawun mutane shi be sanin ba.
Kwana biyu ina murna banji warin gawasa ba amma shine kake so ka kashe ni da warin, ai na gaya mata ga tanan zaune nace warin gawasa shi ya sanadiyar b’arin cikin tagwaye na. HajjahKaka tayi maganar tana watsa mana kallo mu duka.
Baana yace to HajjahKaka naga ai ita bata ce tana jin warin gawasar ba sai ke, kuma cikin ajikin ta yake bake ba.
Amma ban taba sanin cewa kai Dodi minal Dodi bane sai yau,ina maka kallon me spiriyens ashe Dodi ne kai? To tudan so kake nayi ma barau barau to indai kana son cikin nan,karka yi mata abin manya balle har warin gawasa yayi sanadiyar barewan ciki. Kai ko hannun ta karka rike har sai cikin yayi kwari
Shiru yayi Baana yana kallon ta kafin ya mike yace me kike bukata matata?
Ni ba matar ka bace kaje kaji da waccan yarinya da ka bata nayi maganar ina me fashewa da kuka…
Ba Baana ba HajjahKaka ma sakin baki tayi tana kallona, can kuma ta mayar da duban ta zuwa Baana taga yana murmushi
Rai bace HajjahKaka tace kunun gyada da alale wanda yaji hanta zaka kawo sai pepper soup kifi.
Baana zeyi magana HajjahKaka tayi saurin cewa me cikin zaka kashe da yunwa? Maza ka wuce yanzu, ba shiri Baana ya fita, yana fita HajjahKaka ta duma min duka a baya, nayi saurin juyowa ina kallon ta
Shegiya kina wani mirsisi da idanu kamar an soye gyada, kice kinji dadin abin manya da yayi maki tudan gashi kina kukan kishi.
Cikin hanzari nace Walhi na tsanen sa ne, idan na gansa sai na tuna abin da yayi wa waccan yarinya.
Dallah rufemin burmemen bakinan naki me wari, to ke baki ji tausayin kanki ba abinda yayi miki sai ita? Bare ki yayi fa kamar na hayhuwa ba gara ita ba?
HajjahKaka kina nufi ita ya dade…. Sai nayi shiru ina kallon ta
Ah lalle Falmata, a kinji abin manya kin fara kishi har kece kike kishi dan yayi wa wata abu manya?
Cikin bacin rai nace Allah ya tsare ni da kishi akan wannan bakin kazamin mara imani idan akwai wadda natsana a duniyar to shine,ban ki na dauki wuka na dabba me wuka kowa ma ya huta.
To ke Falmata ban da abinki miye na wani cewa ki dauki wuka ki dabba me? Ke da yanzu spiriyens da kika samu guna dashi zaki yake shi, kinga wannan karyan cikin shi ze kwato miki yanci amma idan kika tsaya wannan haukar banza Walh ya dura miki cikin gaske yabar ki da “jus imajin” HajjahKaka tayi maganar tana kallona da kyau
To HajjahKaka naga dukda ance cikin be son ganin sa,amma…ban gama magana ba naga ya shigo a fusace ya….
Pharteema(DMK)
THANKS
Post a Comment for "Ni da Almajirina 14"