Ni da Almajirina 13
NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)
_ASSALAMU ALAIKUM KAWAYEN HAJJAHKAKA DA JIKOKIN TA KUYI HAKURI JIYA KUNJI NI SHIRU UZURI NE DA NI梁_
Episode 13
Ke mike na ganki da kyau, HajjahKaka tayi maganar cikin matsifa, kamar yadda tace haka na mike, salati ta farayi tana karemin kallo kafin ta mayar da duban ta zuwa Baana,
Kai kai mugu beji dadin rayuwar sa ba, yanzu wannan me tsiyayen duwawai saida kayi mata aikin manya? ba tausayi ba tsoron Allah?
Ai tunda kuka doso ni,naga har hazo hazo neke ganin dakin,sabida warin gawasa nan yafi na kulum,nasan da cewa ka murkushe jikata, to Allah sai ya bin mana hakkin mu, HajjahKaka tayi maganar tana kukan harda sake duba cinyoyi na,sai kuma ta sake salalami, zama be gan mu ba Falmata, wanka jego za ai miki dan wannan tokareren kato me tsiyayen duwawai ba karamin aika aika yayi miki ba.
Duk dakewar sa na rashin jin kunyar HajjahKaka sai da yaji,amma sai ya maze da fadin cewa HajjahKaka na dauka abin da kike so kenan? Baana yayi maganar yana murmushi
Wani kallo ta watsa me kafin tace bacin kamin biyayya a baya da nayi maka baki, amma ka jira jikata ta warke zaka san ka shigo gonar mu. Gayen da take bukata da sauran ta lisafa masa.
Baana yace godiya muke HajjahKaka zan aiko da abinda kuke bukata ni zan wuce ya juya zai tafi.
Shege me tsiyayen duwawai uban wa kake wa godiya ko ance maka sabi da kai zanyi? Idan baka sani ba ka sanin yau kayi nafarko kuma kayi na karshe..
Murmushi Baana yayi kafin ya fice.
Can tace da ina cewa ba zaki iya daukar mutumin nan ba sai gashi kin sammace ni da mamaki?a nakara samu spiriyens Falmata, to ke dan ubanki ya akayi har yay maki wannan aika aikan?
Zuciya ta na kuna na fara bata labarin ina kuka..
Kice ke kika siyo da kudin ki? Yanzu Falmata shawarar dana baki kenan?
Eh HajjahKaka.
Rufemin burmamen bakin nan duk kin cikani da warin gawasa, idan kema ba kinaso ba me yasa ba kiyi suman karya ba?kema de son kike kiji abin manya kuma yanzu kinji, sai matsifa HajjahKaka ta keyi kamar ta dake ni. Har wata mata ta kawo abubuwa da HajjahKaka tace tana bukata
Rai bace HajjahKaka tace ke wanke min ganye da gishiri sannan ki daura min a wuta
Wacce aka aiko tace to baaba.
HajjahKaka ta ya mutse fuska tace duk kun cika dakin mutum da warin maza ke kuma naki ya hadu harda rashin tsafta dan gafi gafi ki keyi, HajjahKaka tayi maganar tana toshe hanci.
Harara yar aiken ta watsa ma HajjahKaka harara kafin ta nufi toilet
Kin harara uwarki, kai wasu mazan ma sai a hankali, yanzu in banda Namiji Dodi minal Dodi ne,me a jikin wannan kanjamamiyar?Duwaiwai ta har yafi na Baana tsiyayewa,har kin fita abin arziki fa Falmata,Amma kin gani itama warin mazan take.
Baana
Yana barin dakin ya samu daya daga cikin masu yi musu aiki ya gaya mata abinda HajjahKaka kafin, ya nufi offishin su Amir
Sauran Amir na ganin sa duk suka taso, bayan sun gaisa
Baana yace matasan kuna duba aikin su kuwa?
Amir makeri yace yanzu haka muna da makamai dan wanda nayi training su kayi,sunyi kusan dari acikin sati biyun nan.
Masha Allah Amir, dan wannan taron da aka kirani nasan babban aiki ne
Maganar na karshe shine ku dena farmaka yammatan haka, basu yi mana lefin komai ba, mu da gwamnati muke yi idan gwamnati ta yarda muyi negotiating dasu to kun ga duk sakin su zamu yi.
Daya daga cikin Amir yace ai matan suna cikin garima yaqi da mukai.
Baana yace aah ba yaki mukai ba dan haka ku gayawa sauran cewa umurni ne karsu sake zuwa wa yammatan nan.
Yana fadin haka ya bar wajen ya nufa rumfar matan, inda ya smau wata yarinya wacce za tayi tsara daya da Falmata tana faman ciwon ciki.
Cike da tausayawa yace me ya same ta?
Wa inda suke kanta suka ce yanzu suka dawo mana da ita haka..
Cikin hanzari ya kira wasu maiakata dasu kai yarinya gun HajjahKaka, yasan tasan magunguna kuma zata temaka mata, kamar yadda yace suyi haka matan suka da uke ta zuwa dakin HajjahKaka
Salati HajjahKaka ta saki tace na boni ni Bintu yau da warin gawasa za a hallaka ni, na yi yaki da wannan sai ga wani kuma an doso ni dashi
Cikin tsiwa HajjahKaka tace ku kuma daga ina?
Matan sukace Amir yace mu kawo ta, tana bukatar temako na gaggawa.
Ya mutse fuska HajjahKaka tayi tana toshe hanci kafin tace, Yanzu Baana ne yayi mata wannan danyen aikin?
Su matan da basu gane kan zance ba suka amsa da eh.
Bansa lokacin da na mike daga kwance da nake ba ina kallon yarinya dake famar wai rike da ciki, wani bakin ciki naji ya turnoko ni.
Hawaye suka cika idona, inama ace duk wannan abin wani ze tashe ni daga bacci yace mafarki na keyi? Da nafi kowa jin dadi.
Kamar yadda HajjahKaka tayi min haka tayiwa yarinya nan,gwanin ban tausayi ko zama bata iyayi, bayan sun taya HajjahKaka shirya yarinya, HajjahKaka tace sai kuyi gaba duk ishe mutum da warin maza, kai ina tunanin in bindiga be kashe ni ba, to warin Gawasa ze hallaka ni oh oh ni Bintu? HajjahKaka tayi maganar tana bude humrah ta, ba shiri matan suka fita suka bar dakin.
BAYAN SATI DAYA
10pm
Baana ya dawo ya issarwa sauran Amirs akan meeting da suka yi, da plans su na farmaka gu uku a wannan watan.
Bayan ya gama ko bata lokaci beyi ba, ya nufa dakin Hajjahkaka coz he so much misses her.
Da salama ya shigo amma abin mamaki ya ga basu a dakin, har ya juya zai fita sai gashi sun fito daga toilet.
Hajjahkaka na hango sa ta murtike fuska tana me kallon tuhuma..
Murmushi Baana yayi kafin yace barka da dare.
Kai idan kana son kanka maza ka barnan kafin nayi maganin ka, Hajjahkaka tayi maganar tana jan jiki a kasa, zuwa yayi ya dauko ta cak, ya ajiye ta samar gado
Cikin tsiwa tace uban wa yace ka dauke ni?
Nide ina tsaye jikin bango jikina yayi sanyi, zuciya ta sai bugu take.. Ga tsoro da tsanar sa duk sun cika zuciya ta.
Uban wa ka tsaya kake kallo haka maye ? Cinye ta za kayi koko mene ka tsaya kake mata wannan kallon ?
Hajjahkaka nazo daukar matata ne, yayi maganar yana kokarin zuwa inda nake.
Ka ga wannan me tsiyayen duwaiwai ka shiga hankalin ka tam, yarinya kaje kayi mata aika aika tana fama da jinya ga kuma danye ciki dake jikin ta kake cewa kaqzo daukar matar ka ?
Cike da mamaki Baana yace ciki ?
Munafiki kana yi kamar ba kai ka dura mata cikin ba?kai Baana kaji tsoron Allah, Falmata guda nawa take da zaka daura mata wannan jaraba eh ? Hajjahkaka tayi maganar tana me fashewa da kuka.
Takowa yayi zuwa inda nake nayi saurin shiga toilet, Hajjahkaka tace idan kana son cikin to ka kiyaye kanka da zuwa kusa da ita, dan warin da gafin gawasa ya isa cikin ya zube nide shawara nake baka.
Cikin murna Baana yace nagode Hajjahkaka , na maki alkwarin wheelchair sabida wannan albirshi naki, idan kuna bukatar wani abu ku sanar dani yayi maganar cikin farinciki
Tabe baki Hajjahkaka tayi kafin tace nide addua na daya shine wannan da ‘ kar ya gado wannan baki da murdaden jikin ka, ni abun mamaki wai Falmata ce har ta iya daukar ka? Har kai mata abin manya oh Allah me iko. Ni Bintu nabi ina naga haske ?Tayi maganar tana kare me kallo tana watsa masa mugun kallo.
Hajjahkaka mene kuke bukata yanzu?
Daga cikin toilet nace bana son sake sa fuskar a ido kuma indai kana son cikina ka mayar dani gun mahaifina.
Bude toilet yayi yana me kallona cike da tausayawa,kafin yace kece numfashi na Falmata bazan iya rayuwa ko da na second daya ne baki.
Makaryaci maganganu ka baza su taba tasiri akaina ba,kaje kaji da yarinya da ka bata wa rayuwa you heartless beast.
Cike da mamaki ya…..
Pharteema(DMK)
THANKS
Post a Comment for "Ni da Almajirina 13"