Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Namijin Zuma 11

NAMIJIN ZUMA PAID PAGE11
Sosai Nabeelah ta kure Aeezad da Ido Ba karamin gigita mata lissafi Aeezad yayi ba, tashiga yanayi me wuyar misaltuwa, kalaman da yake mata tamkar a mafarki take jinsu, wai yau itace Aeezad kecewa yana


sha’awarta wai yana santa har itace Aeezad zece ze aura, kaf sojojin dake gurin sunji meke gudana,sunaji domin da karfi yake mgnr cikin rashin control. Kafin ya karasa kalamansa Nabeelah ta kwace hannunta daya rike, cikin matukar zafi har huci takeyi, beyi aune ba, yaji tafin hannunta a kan kuncinsa,. Cikin zafi ta watsa masa marirrika guda uku masu tsananin zafi, seda tafin hannunta ya kwanta sosai a gefen kuncinsa, kaf Mari ukun a gefe Daya tayisu gefensa na hagu,kuma duk a jere. Sojojin dake tsaitsaye duk suna ganin marirrikan da nabeelah tayiwa Aeezad komi a kan idanuwansu ya wakana, dukkaninsu sun kidime sosai,sun tabbatar yau ba lafiya,har mace ta mari jarumi kmr Aeezad beyi komi ba, “tabbas da gaske yana santa” maiikatan keta tunani tunaninnan. “Sakewar danayi da Kai harta Kai kace kana sona kana shaawata? Kawai saboda ina karkashinku har wulakantata ta Kai kace kana shaawata!” nabeelah ta fadi cikin Kuka da rad’ad’in dake zuciyarta mara misaltuwa iyakar raini yau ta tabbatar Aeezad ya gama rainata, tana gama fadar mgnr kawai se haweye sharrr suka wanke mata kuncinanta. kwata-kwata Aeezad beji zafin marukan data masa ba kamar yadda yaji zafin kalamanta, Sam ma ji yayi kmr ba jikinsa ta maraba ko rike kuncinsa beyi ba, domin zafin da yakeji a zuciyarsa da rad’ad’in da yakeji na Azabar Santa baze taba bari yaji zafin Marin data masa ba, A halin yanzu ko wuta zata cinna masa bazeji zafinsa ba, zafin santa da yakeji yafi masa komi kuna a wannan lokacin. “Ko zaki kasheni wallahi mommy ina sanki Ina shaawarki!” Ya fadi Yayin da wasu irin zafafan hawaye keta bin kuncinsa. Wasu marurrukan ta kara watsa masa ta dayan kuncinsa cikin kunar zuciya yayinda kwallar bakin cikin kalaman Aeezad basu bar kuncin nabeelah ba, Wani irin kuka takeyi me tsuma zuciya, cikin lokaci kankani taji ta tsani Aeezad, a duniya nabeelah ta tsani Raini kalaman da Aeezad ke mata na rainine, taya za ayi ta renesa yazo mata da wadannan kalaman. “Bana kaunarka! Bana kaunarka! Bana kaunarka! Nayi nadamar saninka tinda har kalamannan zasu shigo tsakanina dakai! Wlhi na tsaneka! Banasan ganinka a rayuwata,!” Nabeelah ta fadi tana kuka se marinsa kawai take Tayi tako ina, a lokaci kankani ya fitar mata a zuciya, batayi tsammanin kalamannan daga bakinsa ba,Amma ta tabbatar harda lefinta data sake dashi ,sakewa me tsanani. Kuka takeyi tana marinsa tako ina, yayinda shima kukan yakeji najin zafin kalamanta banajin zafin marirrikan da take masa ba, kukansa harda majina,Nan da Nan fuskarsa ta kumbure sosai abinda da fuskar hutu kuma a duniyar Nan ba a taba marinsa ba se yau itace first a Kai hannu saman fuskarsa a fadin duniyarnan. Kaf sojojin dake gurin seda sukayi kwallah na tausayin lamarin dake faruwa tamkar a film ko a littafin hausa, haka sojojin ke kallon lamarin cikin tausayi da tausayawa, gashi ba yadda zasuyi se kallo kawai. Nabeelah bata taba nadamar sakinma Aeezad fuska ba se yau, wai har ita a cikin mutane ze zubarwa da mutunci, yace Yana santa kuma Yana shaawarta ,tabbas ya jima Yana mata kallon yadda zeyi yayi fatsikanci da ita shiyasa yake yawan kureta da ido Ashe. “Wlhi ko za a hada wuta asakani in har zan fito sena fadi ina sanki mommy! ” Ya fadi still Yana kuka majina da hawaje baja-baja a kan fukarsa. Wasu marirrikan nabeelah ta kara karfi gun yimasa su, kalmar SO da yake gaya mata ji takeyi tamkar yana soka mata mashi a kahon zuciyarta. “Na tsaneka wallahi !” nabeelah ta fadi still tana Kara marinsa,zafin dayakeji a zuciyarta baze misaltuba, ji takeyi tamkar zatayi hauka, tasan da gaske yake Yana santa taga tabbacin kallansa a kan fuskarsa,tasan wanene Aeezad , tabbas ze iya jamata Abin kunya a idon duniya, gashinanma yaja mata tinda yake fadar wadannan kalaman a gaban mutane tabbas babu abinda baze iya ba. “inajin shaawarki!!!” itace kalmar datafi mata amsa kuwwa a cikin kunnuwanta,. Ta maresa ta maresa harta gaji, gashi kalmar So taki dena fitowa daga bakinsa, har fasa masa baki tayi yanata jini Amma sam be bar fada mata yana santa ba wlhi shi sede ta kasheshi Amma Yana santa. Juyawa nabeelah tayi tana kuka me tsuma zuciya kawai ta nufa hanyar zuwa falo, ta riga ta tabbatar ko zata kashesa baze dena furta mata kalmar so ba, SO dole ta kyalesa gudun kartai masa lahani domin zuciya ta riga ta debeta a kansa. “Nabeelah!!” ya kira zallar sunanta,sunan dabe taba kiransa ba a zahiri a rayuwarsa se yau,. Tsayawa tayi cak dai-dai ta isa kofar dazata sadata da cikin gidan,Wani bakin ciki ya kuma cikata, wato yau itace Aeezad ke kiran zallar sunanta, ta lumshe Ido cikin zallar kunar zuciya still se kuka takeji, tashin hnklin da take ciki baze misaltuba,. Tsayawa tayi cak ta kasa tafiya kuma ta kasa juyowa. “Ina sanki Dan Allah!!…” Aeezad ya fadi da karfi ta yadda kowa kaf sojojin dake gurin seda sukaji, da wasu daga ma’aikatan gidan, se kuka yakeyi tamkar ransa ze fita, majina nata gangarowa zuwa cikin bakinsa Amma sam be damu da hakan ba. Yadda ya fadi kalmar yasa nabeelah juyowa kaf tsigar jikinta seda ta tashi, kuka ya kara tsinke mata. Murmushi ya sakar mata me tafe da launin kuka. “Wallahi Wallahi Wallahi ko ynzu na fadi na mutu sanki na Daya daga cikin abinda yayi ajalina! Wallahi ina sanki, kin kame min zuciya, ruhina ya raunana, gangar jikina ya sare, kwakwalwara ta tsaya a komi se tunaninki, jijiyoyin jikina sun lalace da daskararriyar kaunarki…ni majnuninki ne,, Kiyi hkri mommy ina sanki Dan Allah!” ya fadi still Yana kuka me narkar da zuciya ya zamo daga cikin motar ya tsugunna kan guiwowinsa,kawai seya kara fashewa da Wani irin kukan me fidda sarewar sauti. “Ina sanki! Dan girman Allah mommy Kiyi hakuri ina sanki! Wallahi ina San….” Ya gaza karasawa sbda Wani irin mugun kukan Daya Kara kufce masa,. Lumshe idanuwanta tayi yayinda ita kadai tasan me takeji a tata zuciyar, kalamansa suka kuma sata kuka ,yadda yake kuka kmr zeyi hauka ya kuma gigita hanklin nabeelah, Nan da Nan zuciyarta ta shiga bugu, yayinda take barazanar tarwatsewa, da gudu ta fada cikin gidan tana kuka kmr zata narke, Yana jiyo zafin kukanta da kwallarta a tarkon Zuciyarsa. ”Ya Rabbih ka karamin San nabeelah har ya zama shine Ajalina!” ya fadi Yana kuka kmr ze haukace, ya rasa ina ze tsoma ratuwarsa yaji dadih, Nan kasan ya kwanta Yana kuka a zatonsa ko zeji sanyi a zuciyarsa Amma ina, sema zafin yaji ya Karun masa, kmr zararre ya mike ya nufa hanyar cikin gidan Yana fadin ”wlhi ina sanki mommy! ” kaf ma’aikatan gidan seda suka fahimci meke faruwa A halin yanzu. Cikin hanzari Daya daga sojojinsa na hannun damansa adamu, ya karasa cikin hanzari ya riko Aeezad ganin Yana kokarin shiga cikin gidan, gudun kada yashiga cikin gidan asamu matsala yasa adamu rikosa sosai, Aeezad ya dago ya kalli adamu,Yana fadin ”ka bari naje na gan mommyna, wlhi ina santa,….kaji tana cewa bata sona kou? Wlhi karya takeyi tana sona gashinan tanata kuka kmr yadda nima nake kuka,…” Sune kalaman dake fitowa daga bakin Aeezad Cikin kidimewa tamkar mahaukacin daya jima a dawanau. Hawayen tausansa suka wanke fuskar Adamu, Yana kwallar yace “Tana sanka itama sir Dan Allah ka kwantar da hankalinka pls, kaifa babban soja ne, be kamata kadinga kuka a gaban mu ba pls sir!” “bazan iya controlling kainaba, ta lalatamin ruhina da kaunata, wlhi ko a gaban waye zanyi kuka,,, ina santa ne wlhi ! mutuwa zanyi!!’ ya karashe Yana wani irin kuka, Hadi da dafe saitin zuciyarsa. Dai-dai adamu ya karaso bakin motar da Aeezad, wasu sojojin guda uku suka bude motar adamu yasa Aeezad a ciki, shima ya shiga bayan ya zauna kusa dashi, dreva din yayi lock din motar, sauran sojojin Kusan su arba’in suka shiga tasu motocin guda biyu, wasu duk a tsaitsaye duke da bindigogi, dukkaninsu cikin tausayi da tausayawa na Aeezad suke, suka tada motocin suka fice a gidan , Aeezad se kuka yakeyi Yana buga kansa a kan glass din motar Yana kuka Yana Kiran sunan mommynsa, mommynsa! adamu Daya zauna gefen Aeezad ya shiga rarrashnsa cikin girmamawa da dadin lafazi, yana basa baki kuma Yana tofa masa Addu’ur’i Amma sam Aeezad ya kasa samun nutsuwa sede abinda baza a rasa ba, Aeezad ya jawo wayarsa yayi typing message jikinsa na rawa fuskarnan tasa ta kukkumburo bakinsa ya kumbure yaci kuka ya koshi Yanama kan kuka n domin be koshi da kukanba,bejinma ze koshi da kukan. “Ina sanki Dan Allah mommy ki rufamin asiri kamar yadda Allah ya rufa miki wlhi ina sanki!!…” Shine abinda yayi typing ya tura mata yayinda kafin ya gama tura mata message din tini kwallarsa ta wanke wayar tasa tass, yana gama typing message din ya wurgar da wayar kasan motar,yaci gaba da kuka tamkar karamin yaro, ya rasa ina zesa rayuwarsa yaji sanyi, ga sanyin AC a motar Amma shi se zufa yakeyi. Direct hanyar Kano suka nufa daga garin katsina,. Dai-dai suna Shirin fita daga katsinar,a Wani daji,kawai se gani sukayi motar sojojin ta gabansu tayoyin motar sun fita duka a lokaci daya, Nan da Nan motar ta mirgina gefe ta kifa, kan kace kwabo motar ta kama da wuta! Ta kone kurmus da mutanen cikinta. Ji kake kiiii dreva din dake tukin motar da Aeezad yake, yaja burki Hadi dacewa ” Akwai matsala an kawo mana hari!” cewar dreva din dake tukin motar da Aeezad yake cikin tashin hnkli Yayi maganar. Nan take hankalin Aeezad ya kara tashi kan wanda yake ciki, kwakwalwaraa ta dauki charge! kan kace kattt aka fara bude sojojin dake motar baya wuta, Nan suma suka zage suka shiga bata kashi da mutanen, Nan mutanen sukayi musu Circle, kusan mutane hamsin,, duk fuskokinsu a rufe da bakin kyallle, bindigogi dake hannunsu na fitar hankali. ,Nan hankalin sojojin ya kara tashi suka shiga bude ma Mutanen wuta, ina Ai sarkin yawa yafi sarkin karfi a kallah su sojojin basufi su ashirin ba. “Fito mu gudu sir…. Kai akeson kashewa mu gudu jawai…” Cewar adamu da hnklinsa ya tashi Ainun, yayinda se harbin motar dasuke ciki akeyi,dande motar batajin harbine, Amma sede tini sun kashe tayoyin motar da harbi yadda bazata tafiyu ba. Tini Aeezad ya fito ya Ciro bindigoginsa kananu guda biyu ya shiga Harbin mutanen dasuka zagayesun. Nan suka shiga Aiko masa harbi Yana kaucewa Amma ina kafin su ankare tini ya kashe mutane goma. Sarkin yawa yafi sarkin karfi nan suka karar ma Aeezad da mutane suka rage mutum biyu,. “Sir mu gudu Dan Allah pls…” Adamu ya fadi da karfi yayin daya jawo Aeezad da karfi, Aeezad na turjewa ina dole seda Adamu ya jawosa suka ruga a guje sbda basu da mafitar data wuce gudun domin zuwa yanzu kaf mutanensu an kashe musu daga AEEEZAD se adamu se Bashir suka rage, Bashir tini ya gudu ya fada daji. Sam Aeezad beso gudu ba dande kawai dande adamu ya matsa ne. Tini hankalin barayin ya dawo kan Aeezad da adamu dake gudu,Suma suka fara binsu a guje, suna binsu suna harbinsu, cikin Sa’ah suka harbi adamu a kafa Nan ya fadi kasa Yana ihu Yana fadin “ka gudu kawai sir…” Aeezad ya tsaya ze dauko Adamu, Nan suka samu nasarar Harbin Aeezad din, seda suka sakar mata bullet kusan goma yana kaucewa dayar ce ta samesa Nan ya zube kasa warwas,idanuwansa suka kulle ruf bakinsa da kalmar shahada. Jin jiniyar motar Yan sanda ga jirgin daya fara zagaye ta samansu, ai tini Bashiri barayin sukayi saurin guduwa , cikin farin ciki sbda sun tabbar sun samu nasarar kashe Aeezad.

 

Ayi hkri da rashin editing tsoffin fans Dina sun San baba editing book.

 

Wannan littafin na kudi ne 08101626484.

 

 

Gamesan Namijin zuma,da namijin duniya ze biya 1500 in kuma daya kikeso zaki biya 1k 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank.

Post a Comment for "Namijin Zuma 11"