Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Munayamaleek 35


XXXV…
(35)

Maleek yayi kasa da idanun sa, gani yake kamar murmushin da Shakur ya masa ta boge ce, bai taba jin kunyar wani dan adam kamar yadda yake jin na kanin sa yanxu ba, gani yake kamar Shakur zai ce halin sa ne hakan, domin ya ga ya keta wa Munaya haddi, Allah da rabon y’a, sannan yanxu kuma ya ganshi tare da mahaifiyar sa a gado daya, dukkanin su babu sutura a jikin su, innalillahi wa inna ilaihi raju’un, anya Shakur zai fahimce shi? Zai yafe masa kuwa?

“Bro!” Can kasa cikin amon sauti mai dauke da zafin ciwo Shakur ya kira shi, sai kuma ya mayar da oxygen din hancin sa yana sakin numfashi a wahale.

Alhaji Dawood kuwa mamaki ne ya kama shi matuka, domin bai taba tunanin Shakur zai iya kallon Maleek bare yayi masa magana ba bayan abinda idanun sa suka gane masa, ya san cewa Shakur na matukar kaunar Maleek tun Kuruciya, Shakur zai iya hakura da Abu ya bawa Maleek, yana lallaba Maleek da bashi kulawa tamkar shi ne babba, domin wasu mutanen ma na tunanin Shakur ɗin ne babba domin yana da dattako tun a kananun shekarun sa haka zalika yafi Maleek wayo da hangen nesa.

Ya matukar tausaya wa Shakur ɗin, domin bai yi sa’ar uwa da dan uwa ba. And as for Sa’adah bai san me zai ce akan ta ba tukun, bai kuma san rashin imanin ta ya kai haka ba, Duk da baya kaunar ko ganin ta amma ya kamata a ce to zo ganin ɗan data haifa, wanda kuma itace silar kwanciyar sa a asibiti nan yanzu, tunanin sa ya katse a lokacin ɗaya ji Shakur ɗin ya sake sauke oxygen din ya kira sunan dan’uwan sa.

Maleek ya taho cikin Wani irin sauri mai kamar gudu ya dire Gwiwowin sa a kasa, ya kamo hannun Shakur ɗin ya rungume a kirjin sa.
Wasu hawaye Masu zafi suka biyo kuncin sa, kukan da yake nema tun jiya ya ji yana son subuce masa, ya daure iya daurewa sai hura iskan bakin sa yake cin son shanye kukan.

Shakur ya mayar da oxygen din hancin sa, shima hawaye ya biyo gefe da gefen kunnen sa.

Alhaji Dawood ya kasa cigaba da zama domin zuciyar sa karye wa take, ya mike yace “Shakur kada ka yi kuka ko saka damuwa a ranka kan mutanen da basu damu da taka damuwar ba kaji ko” Shakur ya jinjina kansa, sannan a hankali yace “Daddy please go home and rest, ka je ka huta a gida, Maleek is here with me” ya jinjina kansa domin tabbas yana bukatar hutun, duk da baya son ganin Maleek din a asibiti amma saboda Shakur ya barshi, ya shafa kan Shakur ɗin yace “get well soon son, I will be back” da haka ya fice.

MALEEK ya bude idanun sa da suka matukar kadawa, yabi Alhaji Dawood da kallo, fuskar sa tayi ja kamar ta nunanan tumatir, ya goge idanun sa cikin sauri, ya sake hannu ya shiga goge wa Shakur na sa, ya kara riƙe hannun Shakur ɗin da kyau yace “zaka iya min alfarma Shakur? zaka iya neman waje komai kankantar sa a zuciyar ka ka yafe min? only then zan samu nutsuwar zuci na kuma iya yafe wa kaina, wallahi Shakur it wasn’t my fault, ba laifina bane nayi iya kokarina wurin ganin bata samu galaba a kaina ba, amma na kasa, i was damn weak da ko hannuna bana iya dagawa tun bayan data kawo min smoothie daki na na sha, ban taba nadamar karban Abin hannun ta ba sai jiya, Domin da ina cikin hayyacina da ba ka kwance cikin wannan halin yanzu, taya zan san tana da wata nufi a kaina bayan na ɗauke ta tamkar itace ta haife Ni, ina jin rayuwa ta tamkar bata da amfani domin Na saka ka da ma Daddy cikin hali mai wuyar fassaruwa musamman kai dake kwance a asibiti….”

Shakur ya juyar da kansa dayan gefen, hoton yadda ya ga Hajiya Sa’adah cikin mummunar shiga mai kama da tsiraici ranar da zata je dakin Maleek ya hasko masa, amma a lokacin bai taba yi mata wani bahaggon fahimta ba, taya ma zai yi mata munanan zato bayan ya dauke ta ya kuma bata matsayin uwa, da a ce Allah ya bashi iko sanin halin mahaifiyar sa ɗaya san yanda yayi wurin ganin abubuwan basu tabarbare haka ba,tsoron sa daya, yana fargaban yiwa Maleek din wata tambaya amma kuma yana tsoron amsar da zai samu, domin Maleek never lied baya karya komai girman laifin daya aikata, ba tare da ya juyo ga Maleek din ba yace “ta kusance ka?” Yayi maganar da rufe idanun sa, yayinda bugun nutsuwar sa ta karu, abinda ba’a so kenan.

“No she didn’t!” Maleek ya fada Cikin jin nauyin Shakur ɗin.

Shakur ya yi saurin bude idanun sa, domin gani yake Maleek din ya fadi hakan ne domin kwantar masa hankali.

Maleek ya daura hannun sa a zuciyar Shakur inda ba na’ura yace “trust me Maleek, you know I never lied to you, wallahi bata kai can ba, she was trying to, shine Allah ya kawo daddy, ka amince dani” Maleek ya fada gwanin tausayi, domin so yake ya yarda da shi kamar yadda ya saɓa yarda da shi, bayason yardar dake tsakanin su ya lalace har abada.

Shakur ya sauke wani irin ajiyar zuciya, nauyin da kirjin sa yayi na raguwa.
Ya rike hannun Maleek din da kyau cikin nasa, sannan yace “i will forever trust you my blood” Shakur ya fada yana sakar masa murmushi.

Maleek ya mayar masa da martani cikin dadi a ransa, shima ya saki Wata ajiyar zuciya. Ya janyo kujerar da wajen daf da gadon sosai Domin bai son barin kusa da Shakur ɗin ko kadan, bayan ya zaune ya mayar masa da oxygen ɗin.

Shakur ya cire, Maleek ya ƙara mayar Wa, Shakur ya sake cire wa yana murmushi “kai baka gajiya da murmushi ne, baka ga baka da lafiya ba? Rufe idanun ka kayi bacci” ya fada yana dan tapping kansa.

“Ina ruwan ka toh, Ni bazan iya daure fuska kamar ka ba, ai sai fuskanta tayi ciwo, Ni hira nake so muyi,
How far little Amnah, kaje wajen su kuwa?”

Maleek ya dafe kansa domin wallahi shaf ya sha’afa da yarsa saboda tashin hankali daya shiga, ya cire hannun daya dafa kansa da shi Sannan ya ce “ban je ba, idan ka warke sai mu cigaba da zuwa yanda muka saɓa”

“Duk da haka dai ya kamata kaje, banajin zaka iya ɗaukar Tsawon lokaci baka ga angel ba”

“Zan iya saboda kai, kuma ba Lallai su barni na gan ta ba idan suka ga ba tare muke ba”.

“Ko dai tsoro kake ji?” Shakur ya fada Cikin tsokanar Maleek din.

“Kai ka san i fear anybody, wa zan ji tsoro?” Maleek ya mayar masa da sigar tambaya.

“A’a shikenan ba sai na kira suna ba” Shakur ya fada.

“Nufin ka waccan yarinyar?” Maleek ya fada yana haɗe fuska.

Shakur ya zaro ido yace “Ni dadina da kai tsarguwa ce da kai, Ni Kaji na kira sunan wata yarinya anan?”

MALEEK ya shafa sumar kansa yana jingina bayansa da kujera.

Shakur ya shiga masa dariya a hankali, sai kuma ya dafe saitin kirjinsa da alamun ciwo, Maleek yayi saurin dagowa, ya mayar masa da oxygen din sannan yace “ka gani ko? Yi shiru karka kara magana have some sleep please” Shakur ya jinjina kansa yana rufe idanun sa.

“Ko na kira likita?” Maleek ya tambaya cike da kulawa.

Shakur ya bude idanun sa ya girgiza kai, sannan ya mayar ya rufe, Maleek ya sauke ajiyar zuciya.

Little Amnah ke shiga ta tsakankanin dogon hijabin dake jikin Munaya tana wasa, yayinda munaya dake tsaye gefen doctor Abbas ta rike hannuwan ta gudun kada ta fadi ta ji ciwo.

Doctor Abbas ya kara gyara tsayuwar sa yace “kin yi shiru Munaya baki bani amsa ba, ki saki jikin ki ki fada min abinda kike ji game da Ni, domin farin cikin ki shine kan gaba, ba kuma na so na zame miki takura, idan ban miki ba, tell me zan bawa zuciyata hakuri”

Munaya ta dago manya kuma fararen idanun ta da saman idon ya sha eyeliner ta ruwa kawai, amma tayi matukar kyau tamkar wacce tayi wata kwalliya, taya ma zata Iya kin doctor Abbas, Mutum ne shi wanda ko wace mace zata yi fatan samun sa saboda kyawawan Dabi’un sa, mutumin da shine silar wanna kyakkyawar rayuwa data samu kanta a ciki, taya bakin ta zai iya furta ki a gareshi…

“Munaya karki yi wani tunani, ki bani dama na miki alkawarin cire miki wanna tunanin da Kuma tambarin da kika yi wa maza jam’i a kansa, zan tabbatar miki da cewa ba duka aka taru aka zama daya ba” ya fada cikin katse wa munayan tunanin ta.

Cikin jin kunya munaya ta kara yin kasa da idanun ta, tana kallon little Amnah data dago kanta tana mata murmushi, ta dauke idanun ta daga kallon little, a hankali tace ” na amince ya Abbas”

“Alhamdulillah! Allah na gode maka, kenan kina so na?”

Ta kara jinjina masa kai cikin jin kunya kamar ta nutse haka take ji.

“Nayi farin ciki sosai, na Kuma yi miki alkawarin ba zaki yi nadamar bani dama ba in sha Allah”

Ita dai ta kasa dago kanta, murmushi kawai take tana jinjina masa kai.

Ya kara cewa ” yau kunyar tawa ta musamman ce ake ji kenan, ko da yake kunyar soyayya ce ko, jeki toh zan dawo jibi in Allah ya yarda” ya fada fuskar sa da yalwataccen murmushi, kana ya bude motar sa ta fito wa da Amnah wani kyakkyawan keda daya kawo mata mai dauke da kayan makulashe, little Amnah ta shiga murna, Munaya tayi masa godiya sannan suka nufi cikin gidan.

Suna bude kofar falon munaya ta zame hannun ta daga na little Amnah ta nufi dakin ta domin kunyar ta take ji, sai take ganin kamar zata gane duk hirar da sukayi.

Barrister Abrar ta bi ta da kallo, Sai kuma tayi murmushi tuno abinda Shakur yace ranar da ya zo musu da maganar munaya da take masa korafin Baya zuwa, inda Yace Yanzu ai zai dawo da yin zumunci. Lallai sai yanzu ta fahimci maganar sa da kyau, ta Kuma ji dadin hakan sosai, domin Abbas is a good man, and also Munaya, domin a zaman nan da suka yi tare ta fahimci Munaya na da kyawawan halaye, da tausayi, duk da Babu wanda ya sanar mata amma ta fahimci komai, ta fahimci Abbas na matukar son Munaya, addu’ar fatan alkhairi ta musu a ranta, ta dawo da hankalin ta ga little Amnah dake nuna mata abinda Abbas din ya siyo mata.

Dadaddare bayan Munaya tayi wa little Amnah wanka, ta zaunar da ita kan gado tana shafa mata mai, bayan ta gama ta sanya mata kayan bacci na yara riga da wando, tana gyara mata gashi. “kanwataaa” ta fada kamar yadda tafi kiran ta a mafi yawan lokuta.

“Mummy” ita ma yarinyar ta amsa.

“Ki daina lalata gashin ki idan na gyara miki kin ji ko?”

“Toh mummy na daina” tace tana turo labbanta irin na Maleek gaba.

Munaya tayi murmushi ta ja labban nata kaɗan.
Bayan ta gama, ta kara gyara inda Amnah zata kwanta, tace kwanta, “kwanta kiyi bacci, bari nima nayi wankan sai na zo mu kwanta” ta mike domin Zuwa toilet.

“Mummyyy” little Amnah ta kira munaya.

“Na’am” munaya ta amsa tana dakatawa.

“Ina Daddy na jiya da yau bai zo ba”

“Ya Shakur ko? Kila aiki ne ya mai yawa” Sa’adah ta amsa da zuciya daya domin Shakur ma Daddy take ce masa.

“A’a ba shi ba, ba bakin Daddy ba, farin fa Daddy na, mai ce min angeeellll” ta ja karshen maganar.

Yanda tayi maganar ya sanya Munaya sakin murmushi tilas, domin ta tsira da surutun Amnah sai tace “zai zo” da haka ta fada banɗaki.
Tana cikin yin wanka maganar Shakur ya tsaya mata a rai, domin ta sha’afa da cewar Shakur bai zo ba, haka zalika bai kira waya kamar yadda ya saba ba, tana fitowa daga wanka ta ga little Amnah har ta bingire da bacci, Munaya ta gyara mata kwanciya sannan ta dauki wayarta, ta shiga number’n Shakur ta danna masa kira amma a kashe, sai ta tura masa massage, ta ajiye wayar ta nufi gaban mirror ta fara shafa mai.

Ɓangaren Alhaji Dawood kuwa yana zuwa gida, mai gadi da mai bawa flower ruwa ya tarar a baki gate suna hira, suka gaida shi da tambayar mai jiki ya amsa musu kana ya nufi cikin gidan, ko ina shiru, Alhaji Dawood ya kalli falon wanda da alama ba’a gyara ba, bawai da datti ba, amma bai samu kimtsi kamar kullum ba, Ya nufi dakin sa, ko kallon hanyar dakin Hajiya Sa’adah bai yi ba, yayi wanka ya sanja kayan sa sannan ya fito domin neman abinda zai saka a baƙin sa, abinda bai taba yi ba kenan, ko a kasar waje ne domin a can din ma yana da house maids, kitchen ya nufa, ko gas bazai ce ga yanda ake kunna ta ba, dan haka Ya jona ruwa a Electric kettle yasaka gayen shayi bayan ya tafasa ya juye iya wanda zai iya sha a cup zai fita kenan idanun sa suka kai kan wani kwali mai kama dana magani, sai dai hoton dake jikin kwallin ya ja hankalin sa, ya koma kan kitchen cabinet ya dauko ta, hankalin sa ya ji yana ƙara tashi, har zai yi goggling ya ga maganin menene, amma sai ya tuna ba kodayaushe goggle ke bada information daidai ba idan ka nemi sanin abu, a nan kitchen din ya sha shayin sannan ya fita, asibiti zashi wurin likitan sa domin ya gaya masa maganin menene, kuma amfanin me yake.

 

 

MunayaMaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya FIRST bank shaidar biya ta 07082281566
Thanks for your patronage

Post a Comment for "Munayamaleek 35"