Munayamaleek 33
XXXIII….
<33>
*MunayaMaleek is a paid book, it’s 500. If you re willing to pay here is the account details 3200689860 Haruna Rukayya first bank, then send evidence of payment to 07082281566*
Maleek ne ke tako wa daga toilet Cikin heavy foot step dinsa daure da towel a kugun sa, sai wani karamin daya rataya a wuyan sa, jikin sa da lema, alamun wanka yayi, zai cire towel din kenan Domin ya shafa mai ya ji an turo kofar, ya dakata yana rike towel din gam, Hajiya Sa’adah taji kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, domin ba Æ™aramin dadi taji data gan shi haka ba.
Yayi saurin samun baƙin gado ya zauna cikin jin nauyin ta, Yana jiran ta fita ya mike ya shirya
Cikin duniyan ci Hajiya Sa’adah tace “ooh I’m sorry my boy na shigo maka ba sallama ko? i was worried zaka ji yunwa shiyasa na fara kawo maka smoothie ka taba”
Yayi murmushi cikin takura kana yace ” thanks mum, amma ba zan iya breakfast ba, na riga nayi latti”
“Haba my boy, Meyasa kake wasa da cikin ka haka uhmm? TOH sha wanna din yanzu karka fita da empty stomach”
Saboda yanda yake a takure, yana kuma so ta fita ya saka bai mata musu ba ya karÉ“i smoothie din ya shanye tas, kiris ya rage Hajiya Sa’adah bata yi ihun murna ba, anya ba rana irin ta Yau taci sunan Sa’adatu sa’ar mata ba kuwa? Domin Yau komai na tafiyar Mata smoothly babu tangarda, lallai ta hango babban Nasara a yau, a kuma yanxu zata kashe Æ™ishirwar data debi shekaru masu yawa tana jin sa.
Ta karbi glass cup din a hannun sa tana masa murmushin samun nasara, kana ta fita.
Bayan ta rufo kofa, Maleek ya mike ya nufi wardrobe dinsa ya fidda kayan da zai saka da kyar domin wani mugun kasala yake jin yana saukar masa, wanda hakan ya bashi mamaki dan ko sanda ya tashi daga bacci bai ji ko kusa da irin ta ba.
Ya cillar da kayan suka zube a kasa saboda yanda hannun sa ya gagara rike kayan.
Ya koma da baya ya zauna kan gado Yana dafe kansa da hannuwan sa, wata matsananciyar buÆ™atar ta mace yake a yanzu haka, tunani yake so yayi Meya janyo masa jin haka, duk da ya kasance cikin maza masu Æ™arfin bukata amma yana kiyaye kansa da kusantan abinda zai sanya shi a yanayin, amma ya gaza sarrafa kwakwalwar sa saboda wutar bala’in da yake ji a jikin sa,
Ya taune labbansa, a lokacin É—aya ji karar budewar kofa amma ya kasa dagowa. Hajiya Sa’adah ce domin ta san zuwa yanzu maganin ya fara aiki a jikin sa ta Kuma Æ™ara tabbatar wa daga yanayin data gan shi a ciki, ta mayar da kofar ta rufe a hankali, ta cire kayan dake jikin ta dazu, yanzu sanye take da wata riga shara-shara mai sirrin hannu kalar pink, tumbin nan ya fito himma ya zauna a cikin rigar, sam bata yi kyawun gani ba, gaba-daya kamshin turaren ta ya cika dakin.
Ta zo gaban Maleek, ta saka yatsun ta biyu ta dago kansa, gabanta ya fadi data ga yanda idanun sa suka dawo jajur kamar an zuba jini a cikin su, jijiyoyin kansa sun fito sun yi rudu-rudu, bin Hajiya Sa’adah yake kawai da kallo, so yake ya budi baki yayi Magana amma labban sa sunyi wani irin nauyi, cikin barikanci Hajiya Sa’adah ta hayo jikin sa ta saka yatsun ta manuniya ta ture shi, ya tafi ya zube kan kafitar, ta kai hannun ta dake rawa ta shiga shafa faffadar kirjin sa, Maleek yaji shi kamar a duniyar mummunan mafarki yake, mum dinsa ce wanna kuwa? Inaa ba ita bace, mafarki yake wanda yake fatan farkawar sa cikin gaggawa, so yake ya hankada ta amma ya gagara tashi, kwantawa Hajiya Sa’adah tayi a jikin sa sosai, cikin Muryar dake nuni da tsananin bukatar sa tace “my boy hold me tight, ka rike Ni da kyau kaji, kasan shekaru nawa na diba ina burin kasancewa da kai? tun kana dan haka” ta gwada tsayin sa da hannun ta, kana a hankali ta kai hannun ta kasan marar sa, wani irin tsalle zuciyar Maleek tayi, bai san daga ina karfin yazo masa ba, ya daddage ya ture ta, amma Ko gezau bata yi ba, ta Æ™ara gyara kwanciyar ta a jikin sa tana mamakin karfin hali irin nasa, tayi dariyar jindadi domin gani take babu ya ita yau a wanna duniyar, ta É—ora hannun ta kan kuncin sa “my love karka wahalar da kanka, ka bada kai mori ya hau kawai mu ji dadin mu, daga Ni sai kai a gidan nan babu kowa yanzu, zan kai ka duniyar maji dadi, karka ji fargaban komai, babu wanda zai ji kaji, zai zama sirrin mu Ni da kai har Abada, daga yau kuma zan dinga samar mana kebantaccen waje da zamu cigaba da jin dadin mu” sai tayi kasa da Murya sosai kamar mai yin rada tace “idan kaki kuma zan tona asirin da kuka binne kai da dan’uwan ka, kayi mamaki ko? Na san kana da ya da wata shegiya can ta haifa maka, sai dai na gagara gano ta, da ta gane kuran ta, domin ta shiga gonar da ba Tata ba, amma abin da ya saka nake daga kafa domin Ni na ja maka, ranar dana ji kana da ya na kasa bacci, karka yi mamaki my boy na San abubuwa da dama a kanka” ta karasa cikin wata murya dake bayyana matsanancin kishin sa”
Idanun Maleek ya kai kan wayar Hajiya Sa’adah data danna video record, ganin abin yake kamar almara ya runtse idanun sa, a da yana fargaba musamman mummy taji labarin yana da yarinya amma a yanzu babu wanna fargabar, da a ce zai iya sarrafa bakin sa, daya maimaita mata cewar yana da y’a sau dubu ba tare da ya ji fargaban komai ba.
Hajiya Sa’adah ta kai idanun ta inda yake kallo, tayi murmushi mai sauti tace “wanna video ne nake mana, zan adana a wurare mabanbanta, domin a duk lokacin da ka nemi bijirewa wa bukata ta ta zan nuna wa Daddyn ka da Shakur” ta fada tana kokarin kai baÆ™in ta nasa, daidai nan aka buÉ—e kofar da mugun karfi, a razane Hajiya Sa’adah ta juyo idanun ta suka firfito ganin Alhaji Dawood a tsaye, ya dawo kamar ba shi ba, jikin sa gaba-daya rawa take saboda kaduwa, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta fice daga gidan yanda abun ya zo mata a bazat.
Alhaji Dawood ya juyar da kansa gefe domin ya daina ganin wanna tashin hankalin, matar sa ta sunna da dan cikin sa ne a gado daya, innalillahi wa inna ilaihi raju’un yake maimaitawa a zuciyar sa yayinda gabansa ke bugawa, yana wani kalar fitar da numfashi da kyar dama ga shekaru sun ja abin sai ya tarar masa ya mai yawa, ya dinga nuna su da kakarwan hannu amma ya gagara furta komai,, barin dakin nan zai yi domin idan ya cigaba da tsayuwa zai iya kamuwa da cutar shanyewar barin jiki, domin Hajiya Sa’adah na manne da Maleek babu mai motsa wa a cikin su, juyowar sa ke da wuya yaji karar faduwar abu, ya kai idanun sa wajen, Shakur ya gani a kwance babu alamun nunfashi a tare da shi, cikin tashin hankali ya nufi wajen sa, ya shiga jijjiga shi, amma Shakur bai motsa ba, abinda Alhaji Dawood bai sani ba, tun lokacin da yake tsaye Yana sauraran abinda Hajiya Sa’adah ke fada shima Shakur ke bayan sa.
Ganin abinda ya faru ya saka Hajiya Sa’adah ta diro daga gadon ta shige toilet din dakin, Maleek kuwa yana kwance helplessly, sai idanunsa da suka firfito, so yake ya tashi, ya suturta jikin sa ya kuma je ga dan’uwan sa, amma ya gagara motsa wa, zuwa yanzu ya gama tabbatar da cewar wanna halin Da yake ciki Hajiya Sa’adah ce ta saka shi.
Alhaji Dawood yayi kokarin ciccibar Shakur domin kai shi asibiti amma ko tsakiyar falo bai karasa ba Æ™arfin sa ya gaza, ya ajiye shi a hankali kana ya fita da gudu yana kwala kiran sunan ma’aikatan gidan, sai dai mai bawa flower ruwa da kuma mai gadi ya tarar yace musu su taso da sauri, suka biyo shi da gudu zuwa cikin gidan suna sallalami, suna tambayar Alhaji Dawood “Alhaji Allah yasa lafiya” amma ko jinsu Alhaji Dawood baya yi.
Ganin sun nufi parking lot mai gadi yace “Alhaji, ai motar sa na waje da yake yace min wani takarda ya zo dauka” mai gadi ya fada da damuwa, suka nufi wajen, mai bawa flower ruwa ya tattaba aljihun Shakur sai ya ciro mukullin, Alhaji Dawood ya shiga mazaunin driver, yayinda mai bawa flowers ruwa ke tare da Shakur a gidan baya, mai gadi ya shiga musu fatan sauka lafiya da fatan samun lafiya fuskar sa kamar zai yi kuka, mamaki kuma yake, menene ya samu Shakur É—in daga shigar sa ciki, har wasa fa suka yi da shi É—aya zo, wani tsoron Allah ne ya kara Kama shi.
Hajiya Sa’adah data daina jin motsin komai ta fito a tsorace kallo daya ta yi wa Maleek dake kwance ta ruga dakin ta da gudu, gaba-daya ta rasa abinda ke mata dad’i a duniya É“alle tayi tunanin mafita .
Maleek na kwance gabansa na wani irin bugawa da sauri sauri, a haka ya kasance har Tsawon awa hudu sannan ya fara jin sauÆ™i, ya mirgina yayi ruf da ciki, yana saÆ™in wani irin kalar nishi, ya jike sharkaf da gumi, ya mike yana dafe da kasan marar sa, ya sakawa kofar sa key sannan ya nufi banÉ—aki, ruwa mai sanyi ya sakar wa kansa, ya daddage yayi wani Irin ihuu yayinda fuskar sa ke digar da ruwa, ya shiga buga hannun sa a jikin bathtub da karfi, gefen bathtub din ya tarwatse a kasa, kwalbar abin ya soki hannun sa jini ya shiga zuba amma bai damu ba, yayi zaman yan bori a kansa tiles ruwan na kara dukan bayan sa, a yau yana rokon Allah yasa yayi kuka, domin abinda yaÆ™e ji cikin zuciyar sa ba mai misaltu ba saidai kukan yaki zuwa, ya bata mintunan da shi kanshi bai san adadin su ba a banÉ—akin sannan ya mike ya fita, ko kayansa dake Æ™asa bai bi ta kan su ba ya buÉ—e wardrobe ya ciro Wasu riga da wando, ya fice daga dakin, sai yake jin wani iri a jikin sa, kamar ba gidan su ba, kamar ba gidan daya taso cikin ta tun Kuruciya ba, kamar yana wani waje da ya je bukun ta ne sabar yanda duniyar take juya masa, ya fice farfajiyar gidan, ya zuba wa mai gadi ido ya rasa abinda zai ce masa, ya koma dakin sa tuno cewa bai yi sallah azahar ba, yayi alwala ya gabatar da Sallah, ya kalli qur’anan sa dake jere, ya tuno Shakur ya sha fada masa yawan karanta Kur’ani na yaye damuwa, yana kuma saka hasken zuciya, ya dauko na saman, ya bude suratul ikhlas amma ya gagara tada baki É“alle ysy karanta gashi dai a baki zai iya fada amma ga surar nan a gaban sa ya gagara karantawa, bai taba jin ciwon rashin iya karatun Alqur’ani ba sai yau, a yau yake tambayar kansa Meyasa Shakur yake da zurfi a fannin ilimin addini, shi kuma bai da shi bayan tare da suka rayuwa tun Kuruciya komai kuma irin daya ake musu, ajiye Kur’ani ya yi ya mike ya sake fita, wanna karon mai gadi da mai bawa flowers ruwa ne a zaune, ya karasa wajen su yace
“wani asibiti suke?”
Mai bawa flowers ruwa ya fada masa a É—an tsorace domin yanayin da suka ga fuskar Maleek ya firgita su, amma su a tunanin su halin da dan’uwan sa ke ciki kadai ne ya sanya shi hakan, domin su din shaida ne kan irin kaunar dake tsakanin su, cikin sauri ya koma Cikin gidan, har ya dauki mukullin mota sai Kuma ya jefar, ya bude inda yake ajiye kudaden sa ya kai hannun sa ya debo ya saka a aljihun ba tare da ya san nawa bane ya fice daga dakin, masu gadi suka bishi da kallon mamaki Ganin sa a kafa abinda basu taba gani ba.
Maleek Ya tare abin hawa ya shiga yana gaya masa sunan asibitin, bayan sun iso ya saka hannun sa a aljihu ya zaro kudade da bai san nawa bane ya mikawa mai dantsaho kana ya bar wajen, ya bar mai adaidaita tsaho da washe baki.
Saurin da yake ya ragu ne a lokacin É—aya ga Alhaji Dawood yana safa da marwa hannun sa goye a bayan sa, Maleek ya Æ™ara taku uku yayi kasa da kansa, so yake yace “Daddy Ina Shakur?” Amma yana tsoron yin magana, Alhaji Dawood ya juyo ga Maleek fuskar sa babu walwala ko digo, damuwa ce mabayyane a fuskarsa, ya kalli Maleek din da kakkausar murya Yace “koma! Ka fita daga asibitin nan”
MALEEK ya kara matsowa daf da Alhaji Dawood yace “Daddy Dan…” Wani mugun ture shi Alhaji Dawood yayi kana cikin daga murya Yace “i said get out of my sight, na tsani ganin ka”
Post a Comment for "Munayamaleek 33"