Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Mijin Malama Book 2 Page 56


Innati ta sharce majina ta ce “Ƙarara baki babu linzami a dinga Sakin tsurar zance? Dafa a makarantun islamiyya ya faÉ—i haka a gigice zasu dinga salatin Annabi, ana kaÉ—a zunubin can wani wajen, Æ´ar bulala É—ari da tamanin É—in nan yi masa ita za su yi”
Majeederh ta yi shiru, Aaliyyah sai dariya take ta ce “Ni a shawarce da islamiyyar kika mayar da shi Innati” Ta yi caraf ta ce “Waa? Ubana daya mutu zai dawo kenan ashe, yanzu da an yi magana ya ce Mijin Malama? Haka Kululu take? Asstagafirullah!” Aaliyyah ta ce “To Allah ya shirya shi” Da sauri ta ce “Amin don nabiyyun rahamati, idan ba zai shiryu ba Allah ya ya fe masa” Ta juya ta kalli Majeederh ta ce “Mijin naki batsa ya yi fa? Ko ba ki ji bane?” Kafin ta ce komai Ƙhulud ta shigo da plate wanda yake cike da zallar gasasshen nama…. Washegari aka RaÉ—awa yara suna Hawwa’u Ibrahim Khalil da Fatima Ibrahimul-khalil, wanda suka ci sunan Fulani da Gimbiya ana kiran su da Noha da Soha, faÉ—ar shagalin da akai É“ata baki ne, duk da cewar family biyun basu da cikakken yawa amma Majeederh ta samu arziÆ™i daga jama’a, hatta Barrister Aliyu Sufyan sai daya bawa babies gift Khalil dai bai ce komai ba, haka Akeeth wanda suka zama friends shi da Khalil, hatta P.a Hammad sai daya basu mahaukatan kaya wanda suka jone shi da Badi tun a Naija har zuwa matakin da zai aureta.

Sarewar dake tashi a hankali wacce ta karaÉ—e Palace bakiÉ—aya cikin Æ™anÆ™anin lokaci shine ya fargar da jama’a zuwa ga abinda yake faruwa acikin masarauta. Su Mami gabaÉ—aya suka fita domin bawa Idanunsu abinci Majeederh dake zaune kiÉ—an na ratsata jinin sarautar nata ya motsa ta miÆ™e a hankali tare da nufar waje, cak ta tsaya daidai window tare da É—agawa idanunta ya sauka akan gwarzonta Dr Ibrahimul-khalil kuma Mai martaba Ibrahim Khalil na 4, a hankali ta dinga binsa da kallo jinin jikinta na tsinkewa ganin wani irin kyau da ya yi mata wanda bata taÉ“a ganin irinsa ba, farar jallabiya ce a jikinsa Æ´ar gasken, an É—ora masa jibgegiyar golden Silver É—in Alkyabba mai mugun tsada, fuskarsa zagaye da rawanin hiramin daya Æ™ara fidda tsagwaron kamala da tarin haibar dake kwance a fuskarsa, baya murmushi ko kaÉ—an ya kame kansa idanunsa ya buÉ—e tare da lumshe su, komai ya gundire shi tashin hankalinsa bai shige kiÉ—an da ake masa a ka ba, da surutan jama’a. Jajayen laÉ“É“ansa sun jiÆ™e da damshin yawu tunaninsa ya tsaya cak sanda ya gama tabbatarwar da kansa fa yau shi ne jagoran mutanen Saudiyya? Nauyi da hak’Æ™in nasu yana rataye a wuyansa.

“Ya Allah” Ya furta a zuciya bisa mamakinsa kuma harshen shi ya Æ™ara nauyi fiye da ko wanne lokaci, jinkimar shi da kame kansa sun Æ™aru fiye da ko wanne lokaci da rana na tsayin ranakun da ya yi a rayuwarsa, a hankali wata nutsuwa ke sauk’a tana mamaye jikinsa ya rage babu wani jini da ya yi saura a jikinsa sai na sarauta. Majeederh ta yi saurin É—auke idanunta ganin ya bar sashin fada ya nufo cikin gidan kai tsaye sauran mutanen fada suka tsaya. Da sauri ta shige bedroom É—inta tana nufar gaban mirror, Khalil kai tsaye sashin Ummie ya nufa ya sameta zaune akan bed tana duba sauran turarrukan da aka kawo mata, idanunsa da suke yawo a kanta ya tabbatar mata da cewa shi ne, sabon Takawar Masarautarsu, ta É—aga kai suka haÉ—a ido ganin nasa ta yi jajur ta ce “Ranka ya daÉ—e?”

A hankali ya zame rawanin kansa ya Æ™arasa wajenta ya É—ora kansa a cinyarta, yana sakin ajiyar zuciya sun jima haka kafin ya ce “Me kika fahimta a labarin rayuwata Ummie?” Ya É—an yi jim ya ce “Karki duba bangon labaran cikin littafin kawai”
Ummie ta ce “Idan zan fasalta rayuwarka dole na fara daga farko, bangon littafi shi ne abu na farko da jan hankalin mutane zuwa ga sanin abinda yake ciki, rayuwa dole ce ga dukkan mai rai dake wanzuwa a duniya, mutuwa gaskiya ce hisabi dole ne, a wannan littafin naka dole aga sunan Majeederh zane a ciki, kai tsaye zan iya basa suna MIJIN MALAMA, babu komai cikin littafin zai ZANEN ƘADDARA” Yana sake kwanciya kan cinyarta ya ce “Me hakan ke nufi Ummie?”

“Khalil rayuwa ba tabbas, zanen Æ™addara ne ya yi aikinsa cikin littafin nan, da kuma muhimmaci yarda da ita a matsayin mutum Musulmi, muna numfashi da Æ™addarorinmu a jininmu, kasan me yasa na ce sunan labarin littafinka MIJIN MALAMA? Na farko a Æ™addarorin Majeederh akwai farin jini wanda ya tara mata ma nema da yawa kuma a É“oye dalilin asirin da akai mata, shi yasa ba a san da su ba, kayi rayuwa da ita kana Æ™arami ka sake rayuwa da ita a karo na biyu, kuma a hakan kai ba Musulmi bane, bayyanar warwaruwar baÆ™in Æ™ullin daya shuÉ—e da rufewa ya sanya ma neman yin caa” Ta yi shiru can ta ce

“Kasan zaka sameta matsayin mata? Kasan zaka yi rayuwa da ita? Kasan zata haifa maka wannan zuri’ar?” Gently ya girgiza kai ta ce “Why? Me ya sa baka sani ba?”
Ya yi jim kana ya ce “Ina ganin ban cancanta ba Ummie, akwai wanda suka fini nagarta, shekaru, sanin daidai ga ilimi babban dalilin da bata so na” “Good” Ummie ta furta tana shafa kansa ta ce “Bata auri Alpha ba Æ™addarar su ce haka, Ubangijin bai Æ™addara zata aure shi ba, ta auri Abuturab bata zauna da shi ba, ranar data aure shi, shine ya fara amsa sunan Mijin Malama, da Allah ya Æ™addara wa Majeederh aure da yawa to duk wanda ta aura sunan da zai amsa kenan MIJIN MALAMA daga bakin jama’a, dalili a nan ita ce _MALAMA_ akanta labarin littafinka ya fara rubuta “headline” kasha wahala wacce ta kai ka zuwa matakin da kake a yanzu, dalilin Malama kayi rayuwa bisa saka hannun Ubangiji da yarda haÉ—i da amincewar shi, dalilin Malama ka samu tarbiyyar daka rasa wajen iyaye, dalilin Malama ka fara sanin daÉ—in Ahali, dalilin Malama ka fara karatu, Allah ya Æ™addara zaka kasance Musulmi ko wacce Æ™addara mai kyau ko mara kyau akwai sanadi, dalilin Malama ka musulunta, dalilin Malama kasan asalin iyayenka, dalilin Malama kasan waye Mahaifinki” Ta jinkirta ta ce “Idan baka amsa sunan MIJIN MALAMA ba waye zai amsa?” Ya riÆ™e numfashi da kyau yana riÆ™e hannun Ummie ya ce “No one has been as lucky as Ibrahimul-Khalil, the son of Ummie, the husband of Hawwa, the father of Alhassan and Al’hussain, the king of Saudi Arabia”

“Ma sha Allah, rayuwa cikin farin ciki no more challenges, babu wani tashin hankalin da zai Æ™ara zuwa ya rusa farin cikin, Ibrahimul-khalil, ÆŠan Ummie, mijin Malama, uban Alhassan da Al’hussain sarkinmu na yau da gobe Takawa Khalil” Ya É—an sauk’e numfashi yana jin wani abu na tsarga masa, a hankali ya miÆ™e ya fice tare da nufar sashin Queen Majeederh, takunsa bisa duga-dugensa wanda ke nuna tsantsar lafiyar gangar jikinsa dana zuciya. Tsaye ya ganta ta juya baya tana kallon makaken photonsa wanda Fatymerh ta maÆ™ala yanzu, ya É—aga kansa ya kalli photon a karo na biyu ya sake ware gajiyayyun idanunsa akan frame gabaÉ—aya ba a jima da yin photon ba, har an yi frame? Aikin Rohaan ne da dukkan alama photon daya gama zaga internet ko wanne sarki gwamna da manya suna posting a twitter akan taya sabon Sarkin Saudiya murna. Ta juya ta kalle shi shima ita É—in yake kallo cike da sahihin so wanda yake fitowa daga Æ™asan zuciyarsa idanunsa ke bayyanar da motsin ji, na daga tafiyar gudun zuciyar tasa, komai nasa ya bubbuÉ—e. A nutse yake bin jikinta da kallo kayan sunbi jiki tare da zama daram, ya kalli Æ™irjinta daya sake cikowa hakan ya haifar da dagulewar riÆ™on da ya kewa yanayinsa a fili, rauninsa ya bayyana, ya zubawa yatsun Æ™afarta dake shimfiÉ—e zane da Æ™unshi kallo, ya juya idanunsa zuwa faffaÉ—an mazaunanta da suka buÉ—e sosai asalin dirinta ya bayyana, baya jure kallon idanunta. ganin bashi da niyyar motsawa ta nufe shi tana tafiya jikinta na rawa wanda ta ke yinta cike da gayya hannayenta ta buÉ—e tare da zagaye shi ta rungumesa tsam a jikinta, hot tears na bin kuncinta, full of love and passion for her husband, she hugged him again, slowly take magane “Ma sha Allah, Alhamdulillah ina taya Takawa murna, Ubangiji ya baka wuyan É—auka da sauk’e hakÆ™in jama’a, na yi farin ciki sosai Takawa” Khalil ya kasa cewa komai saboda jinkansa yake kamar ba Khalil ba, wani daban ne, nauyin kansa ya masa yawa, He believes that any success that a man will get in life, it does not happen without a woman by his side, dalilin Majeederh ya cimma burikansa, duk wani long and short terms na goals É—insa ya yi Achieving dalilin Malama ba zai taÉ“a manta sunan Mijin Malama ba, a shekarun da basu shige huÉ—u ba ya samu cikar victory É—insa, me zaiwa Ubangiji banda godiya? Ba zai taÉ“a butulce masa ba ga tarin darajojin daya bashi.
Majeederh ta É—an bubbuga bayansa a hankali tana shafa kansa ta ce “Ba lokacin Æ™unci ko damuwa bane yanzu a gareka ba Takawa, lokacin farin ciki ne ka zama mai godiya a koda yaushe Sarkina” Ya sauk’e numfashi he needs a shoulder to lean on and cry, he feels like he’s going to cry but he can’t, ya sake matseta a Æ™irjinsa, naman jikinsa na rawa zufa na yanko masa laÉ“É“ansa na karkarwa saboda maganar da yake tattarowa cikin tsananin wahala yana matseta a fusge ya ce “Thank you My Queen” Yana Æ™ara riÆ™eta ya ce “Thank you, thank you And i love you”

“Love You too Takawa, Sarki Dr Ibrahimul-khalil” Ya saketa yana buÉ—e idanunsa ya zubawa lip’s É—inta idanu a hankali ya É—an yi murmushin gefen baki cikin firgitaccen yanayi ya suÉ—e gefen bakinsa wasu maganaÉ—isun abubuwa suka shiga motsawa a duka jijiyoyin jikinsa, magana yake son furtawa gareta É—in amma ya kasa, yadda tsakiyar goshinsa ke fidda zufa yasa ta fahimta ta ce “Takawa nawa, ni da yarana, Alhassan Singer kamar Aberdeen Abduljabar Abbas, Alhassan Footballer kamar Abu maleek, Yaa K Dr kamar Dr Abdul-hakeem Bukar Bello, Noha Lawyer kamar Moon, Soha matar malam ce kamar Danejo da Yaa Sheikh Aliyu..” Ya É—an ware idanu sai kuma ya girgiza kai a taÆ™aice ya ce “Lahhh” Ta zauna kusa da shi tana kallon sai marairaicewa yake kansa Æ™asa daya É—ago suka haÉ—a ido ya saka hannu ya shafi fuskarta ya ce
“Idanunki azaba ne ga Takawa” Ta ce “Ka fito ka ce kana buÆ™atar ka” Ya yi Miskilin murmushi bai ce komai ba a hankali ya kama hannunta ya É—ora a Æ™irjinsa yana rufe ido sun jima kana ya ce “Blessing Woman, Allah ya saki Aljanna” Kasa magana ta yi sai kama fuskarsa da ta yi tare da fara masa wasu lafiyayyun sumbata.
Bayan wata uku akai bikin naÉ—a Takawa, tare da bashi sanda da Takofi sai wani haÉ—aÉ—É—en zobe. Soha da Noha sun yi wayo tare da yin wata Æ™iba gwanin sha’awa yaran sun yi jajur dasu kamar na turawa, Yaa K ya sake girma amma jikin nasa sai addu’a ciwon sikila ya sa shi a gaba daman tafi wahalar da maza, ya kwanta jinya asibiti babu adadi, haka kurum hannunsu ya kumbura ba ciwo ba komai ya ja ruwa daga Æ™arshe ya fara kure sai da suka je asibiti akace ciwon sikila É—in ne ya Æ™arya Æ™ashin hannunsa. Alhassan abubuwa suka faskara a halin babansa abinda ya manta ne kawai bai É—auka ba, hatta zane sai ya É—auki Ebook ya dinga zane har cewa yake ya zama Aby da Mimi. Da Æ™yar Takawa ya tasaa Ummie a gaba da roÆ™an ta aure Uncle Isma’il Majeederh hadda kukanta, ita sam gani take raini ne ba don tana so ba ta amince. Rohaan ya yi caraf da Sona Æ´ar Uncle Isma’il. Lokaci É—aya akai gagarumin biki na fidda raini Æ™asa ta É—auka suka tattara suka nufi Naija domin a can za’a yi bikin. Ummie da Uncle Isma’il, Fatymerh da Akeeth, Zizi da Jawaad, Badi da Hammad, Sona da Rohaan, bikin daya tara dubban jama’a. A nan Majeederh take jin iftila’in daya faÉ—awa Abuturab, bayan juyin mulki da sojojin sukai a Æ™asar Naija ya samu karayar arziÆ™i dalili EFCC da suka kama shi, ko mota É—aya bai tsira da ita ba sai É—an ragowar kuÉ—i a banki, gashi duk dare sai ya yi mafarkin Maysoon ta biyo shi tana kuka hannunta riÆ™e da wuÆ™a zata daÉ“a masa, tana zuwa kansa sai Jidda ta shiga tsakani tana rufe shi, abin tun ana ganin wasa harya taÉ“a Æ™waÆ™walwar shi ya zauce duk wata ake amso masa magani a dawanau abin kamar taÉ“in hankali ya zama kamar MIJIN MATACCIYYA.
Da ƙyar ya samu Takawa da Majeederh suka yafe masa, shi kuma Latifa ta nemi yafiyarsa na abinda tayi masa ta faɗawa babarsa komai da saka hannun Hassenat akai haka duk binciken Latifa ta kasa gano dangin mahaifiyarta domin Alhaji Bashir ya ce ya manta ko sunan babarta domin a irin matan da ake safara ya sameta ya yi mata aika aika, abu ɗaya ya sani tana kama da mahaifiyarta.
Alpha ya ware amma mikin son Majeederh na zane a ransa wanda yake jin shi ne zai zama ajalinsa da kuma sonta zai koma ga mahaliccinsa, ta riga ta zama zanen Æ™addararsa, yana Æ™oÆ™arin nunawa ya mance da ita ne, shi kuma ya nemi Maman Alpha ta daina jin zafin Majeederh domin bata da laifi idan da wacce ta cuce shi bai shige Anti ba, ita ce ta yi masa abinda taÉ“on shi gogewarsa sai wani ikon Allah masanin komai, suka dawo rayuwa da matarsa Zaleehat tana son shi, ba zata wulaÆ™anta shi ba, ko dan darajar yaran dake tsakani, yau ta gane kansa gobe sai addu’a, daman kuma rayuwar gidan auren haÆ™uri yafi jin daÉ—in yawa. Abbu duk inda zai samu labarin Ruma ya bincika babu har wajen Æ´an iskan leges É—in nan amma shiru,kamar shawo ya ci shirwa, Raihana tana zaune aurenta ya mutu tuni wannan gorin zaman gidan data kewa Majeederh ya dawo kanta.

Majeederh na zaune a bedroom ta yi shiru idanunta akan yaranta wanda gabaÉ—aya shekarar su guda, Ƙamshin turaren Takawa da ta ji na Boadicea The Victorious ya tabbatar mata da shigowarsa, ta kalle shi taga ita yake kallo hawaye ya sakko mata ya Æ™arasa ya zauna yana kama hannunta a taushashe ya jima kafin ya ce “Saboda kina da ciki kike kuka?” Ta marairaice ta ce “Kwanika fa? Yaran nan tausayi suke bani” Ya juya ya kalli beds É—insu kana ya tallafo fuskarta yana É—ora tasa akai a hankali can Æ™asa ya ce “Muna murna, Takawa na son zuri’a karkiyi fushi kyautar Allah ce” Ta ji kalamansa sun kwanta mata sauran da suke kwanika ya suke ji? Ya É—ora hannunsa a cikinta sai ya yi kamilallan murmushi ya ce “Blessing Woman, you’re a darling, ke albarka ce,abar so kin mayaye gidan Khalil da zuri’arki” Ta ce “Mun mamaye dai, ka manta ka ce kai ne kake haihuwar?” Ya shafa kai da idanunsa a laÉ“É“anta ya ce “Sure” Kafin ta yi magana ya haÉ—e bakinsu waje guda, can cikin fitar hayyaci ya ji wayar Majeederh na Æ™ara ya É—auka ganin sunan Alpha ya sa shi lumshe idanu, bata É—auka ba har kiran ya katse wani ya sake shigowa Takawa ya miÆ™e tsaye yana cewa “Pick the call…!” Yana faÉ—in haka ya fice ta É—aga ta ce “Assalamu alaika”

“Sannu, muna hanya zamu shigo, ai kuna Naija still?” Ta ce “Eh, kai dawa?” Ya ce “Idan munzo zaki gani” Ya kashe kiran ta sanarwa Khalil bai ce komai ba, ba jimawa suka shigowa, mamaki ya kama Majeederh ganin, Barrister Aliyu Sufyan, Alpha, Akeeth, Hammad, Jawaad ko wanne da matansa wasu da goyo wasu ciki sosai sukai farin ciki, daga gaisuwa Khalil bai sake cewa komai ba, sai an yi abu zai girgiza kai kawai ko ya ce “Uhm” har dare suna gidan. Takawa na zaune a Main parlour shi da Majeederh da yaransu aka kira Khalil ganin Abbu yasa ya É—aga a hankali ya ce “Subhanallah Gamu nan” A ruÉ—e majeederh ta ce “Lafiya?” Bai ce komai ba sai ya miÆ™e not too long ya dawo cikin nagartacciyyar shigarsa tana tsaye sanye da kayanta da hijab yana kama Hannunta ya ce “Muje”

Post a Comment for "Mijin Malama Book 2 Page 56"