Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Mijin Malama Book 1 Page 45


*AUTHOR’S NOTE*
_*This information is for those who do not understand this book.. Ni ban wani niyyar cewa komai ba, to na ce me? Kowa ya yi ta kansa da haka nasu na barku, to ganin ana ta yagalgala nama na yasa nace bari na tofa tawa. I have a question for you guys! Kunga na gama labarin nan na sauke? No??? Me ya sa aka bawa littafin suna MIJIN MALAMA?babu mamaki mijin nata ke shan wahala, babu mamaki masu neman aurenta suke da yawa shi ya sanya aka ce Mijin Malama Ko kuma ƙaddara aurarraki ta faɗa kanta duk wanda ta aura ya zama MIJIN MALAMA babu mamaki wannan Christa ɗin shi ne mijinta kasancewarta Christa sai a fara kiransa da MIJIN MALAMA…. Idan ƙaddara zata faɗawa mutum daman Ubangiji na neman shawarar shi? Ko kuma idan Allah ya jarabce ka da abu sai kace kada ya sake jarabtarka tunda ya taɓa? Ashe ɗan adam a karan kansa zai iya tunanin Ubangiji bai kyauta masa ba tunda yana ta jarabtar shi da abubuwa kala-kala? Abinda baku sani ba shi ne wannan labarin full of density ne cike yake da zanen ƙaddara, shaidar zur na mutane, ƙalubaleln da masu jinkirin aure suke samu, son zuciya da mugun baki na Iyaye, rashin kulawar su ga yaran su…. Saboda Majeederh ta kasance malama shike nan bai dace ayi ta ayi ta jarabtar ta ba? Ai cikakken mumini wanda ya yarda da Allah da Manzonsa shi, ya yarda da ƙaddara ya yi imani da ita shi kaɗai Ubangiji ke jarabta sbd nuna masa soyayyar shi, mutane wagairawun Ubangiji ba fiya shiga al’amarin su ba. Cewa akai ko wata guda kayi bakai ciwon kai ba, to ka tuntuɓi imaninka Ga misalin Annabawa nan wanne irin ƙalubale ne basu fuskanta ba, suka jure ya zame musu tarihi. Taya zaki haɗa su da Ƙaruna wanda Ubangiji ya zuba musu idanu suna tunanin sun fi kowa Sa’a a duniya? Kuna ganin Fir’auna wacce tsiya ce bai shuka ba? Ga su hamana to haka al’amarin Ubangiji yake, ku bar ƙaddara tayi aikinta plx….. Sannan azana cewa wai ina barin ana taɓa jikinta wanne yaƙunannen kuga ya taɓa ta? Abraham bad boy? To a rayuwa duk abinda kake so Ubangiji ya fi jarabtarka da shi, babu mamaki zunubin hakan ya sameta nan gaba kuma har zuciyarta kallon ɗa wanda ta raina take masa bata taɓa bari ya riƙeta hannunta da nufin wani abu ba. Sai mema matar ta ce ne? Ni Afujajen na karanta write up ɗin nata, wai ina nuna masu liƙab basu da gaskiya? To ban ce komai ba idan kin karantar posting na yau zaki fahimta ni duk takaicina bana biya tayi ba, a wata ƙasar taci karo da shi… A ƙaddarorin Malama Majeederh babu sa hannunta a faruwar komai ni dai bari kawai na yi shiru a nan kada bakina ya yi tsayi ana zama lafiya…. Zamu fara BOOK2 ban yi kuma al’ƙawarin farin ciki har ƙarshe ba, tunda rayuwa bata taɓa tabbata da farin ciki amma nayi muku tanadin wata kalar tsaftacciyyar soyayya mai narkar da zuciyar mai karatu, In sha Allah wacce tayi write up ɗin nan ina zaune zata sake yin wani na yabon bama ita kaɗai ba. THANK YOU I LOVES YOU SO MUCH GUY’S邏殺*_

 

50
Tunda suka shiga cikin jirgin Abraham ya rasa tunaninsa idanunsa jajur kansa a kife yana jin gabaɗaya kamar bashi ba, jikinsa ne kawai cikin jirgin amma tunaninsa da ruhinsa ya barsu a nan Nigeria, babu kuma wanda ya yi attempting kula shi daga Escorts ɗin Dad ɗinsa har Grandpa. 5 hours 42 minutes, ya kai su Germany, jirkinsu ya sauka a airport ɗin Berlin Brandenburg Airport (BER). Ya ɗauki wajan minutes kafin gently ya fito dan kansa, da sauri ya shiga taka matattakalar benen zuwa ƙasa, tun kafin ya ƙarasa wata black ɗin Mercedes-Benz S600 ta tsaya a gabansa, aka buɗe masa back seat ya shiga yana sauke numfashi motar Escorts a gaba ta Abraham a tsakiya sai ta Grandpa na bin baya, sai wasu Escorts ɗin a bayansu. Tafiya sukai sosai sun ɗauki hanyar zuwa Hammerschmidt Villa in Bonn, sai suka samu saƙon gaggawa akan su shige da shi President’s Palace. Suka juya kan motar tare da nufar Bellevue Palace in Berlin. Tun daga bakin shiga Federal President’s Palace ɗin zaka dinga cin karo da wasu manyan manyan sojoji ga wasu Escorts na musamman. Hakan zai tabbatar da yadda shugaban ƙasar yake da ƙarfin iko sosai. Kai tsaye motocin ciki suka shiga tun kafin a gama parking Abraham ya fito da sauri kamar zai tashi sama. Ko’ina na gidan fari ne tas idan ka ɗauke green grass ɗin dake waje, kai tsaye part ɗin daya tabbatar sai samu Dad ɗin nasa ya nufa, cikin sa a ya same shi tsaye ya juya baya da ƙofar shigowa cikin parlourn nasa, hucin da ya ji yasan stubborn boy ɗinsa ya ƙarasu babu mai zarrar shigowa part ɗin nasa kai tsaye dole sai shi. Gently ya juya idanunsa ya sauka akan Abraham dake tsaye jikinsa na rawa sosai ya ce “Wlcm back my dear”
Wani ihu Abraham ya yi yana nuna Dad ɗin nasa ya ce “Who the hell do you think you are? Eh?” Dad ɗin ya ce “Son i need u” A hargitse ya ce “I hate you Dad, i hate you, i don’t want see your face” Dad ya ƙarasa wajan Abraham zai taɓa shi ya ce “Faɗa mini wani abu, daɗin me kake ji a zaman Nigeria? Ko sbd kana son babbar mace Musulma?” Abraham ya yi shiru.
“Buɗe kunne ka ji da kyau, kai da Nigeria har abada, zaka zauna dani a nan, ka je can uban yarinya na wulaƙantan ka bayan ka fi shi komai na rayuwa? You’re my darling, President’s son, kana da komai ka zauna wajan wanda basu da ko sisi” Abraham ya ture hannun Dad ɗinsa daga kafaɗarshi yana huci ya ce “Su ɗin sun fiye mini kai” Dad ya yi murmushi kawai yana ƙara jinjina ƙuruciyar ɗan nasa
“Sbd wacce kake kira Mami? Ta faɗi nawa za a bata da rainon da tayi maka shi kenan?” Abraham ya ce “Aurenta zan yi, ina son ta” Dad ya koma ya zauna saman wata ƙatuwar kujera mai kyau yana girgiza ƙafa ya ce “Ba zaka sauya ba, my child is still young” Abraham ya sa ƙafa ya tar watsa Glasses ɗin dake kusa da shi ya ce
“Young? To ka jira zan kawo maka ɗan da zanwa Jee ciki ta haihu, stay away from my life ka manta kana da ɗa kamar yadda na manta ina da uba, me ka taɓa mini na kyautatawa daga haihuwa zuwa yanzu eh? Sau ɗaya baka taɓa kwana tare dani ba, ban taɓa jin ɗumin jikin ba, ban taɓa ganin soyayyarka ba, cutarwarka kawai na sani, azabarka kawai na sani you’re the reason behind anything duk abinda na aikata kai ne sila, ka zaɓi karuwarka fiye dani” Dad ɗin kallon yaron nasa kawai yake, yana mamakin yadda ya kasa mance lokacin daya same shi tare da Kiristi akan gado, memory na nan a kansa moment ɗin ba zai taɓa goshewa a wajansa ba, wannan ya riga a ransa wanda ya sa ya yi masa tsana mai muni. A hankali ya ce
“Listen Son, zo nan I’ll explain everything to you” Abraham ya ce “Everything?” Ya girgiza kai kawai ya rasa me zai ce tunda ya fara maganar yaƙi yadda ya kalli cikin idanun mahaifin nasa. Ya juya zai fice Dad ya ce “Ina zaka?” Ya ce “Nigeria” Dad ya miƙe ya ce “Kai ba zaka kaji wani iri ba? Ka zauna a inda ake wulaƙanta ka? Kuma waccar yarinyar kake son lalata ƙungiyarka a wajanta? Me ka gani a wajanta?” A hargitse Abraham ya ce “Abinda ka gani a wajan Kiristi, Jee da kake gani tafi mini komai na duniya, mulkin ka ɗin me? Kaga taɓa ji na nemi sisi wajaka Dad? Duk abinda na mallaka kuɗi na ne, halak ɗina ne kamar yadda Jee ta faɗa mini na nemi halak duk wahalarsa, to yanzu na girma baka isa ka faɗa mini yadda zan da rayuwata ba am maturel enough Dad” Dad ɗin masifar ɗan nasa da zafin ransa har mmki yake basa daman can haka yake? Shi ba zai ɗorar da komai akan rayuwar Abraham ba yana sawa dai ana bincika masa. Private Investigators.
“Sweetheart na tara maka dukiya, na ajjiye maka komai na jin daɗi Debeka na jiranka hatta gidan da kake son rayuwa sai ka zaɓa, I am the president of Germany, I am your father, I have the power to choose what is right for you, I will decide, wancan Musulmin old woman ɗin ta maka ƙatuwa kaje ka nemi wacce zaka ji daɗi tare da ita, ba zaka taɓa komawa Nigeria ba” Wani irin dariyar takaici Abraham ya yi har yana durƙoshewa a ƙasa idanunsa na zubar da hawaye ya ce “Exlty, that’s exactly who you are” Ya girgiza kai yana jan numfashi tare da riƙe ƙirjinsa ya ce “I need love and care not money, soyayyar ma dana nema a baya a wajanka ka wulaƙanta ni yanzu ban so ban so” Yana faɗin hakan ya miƙe zai fice daga cikin Parlourn Dad ya ce “Come in”
Wasu sabbin Escorts ne wanda Abraham bai sani ba, suka damƙe shi “Take him out” Abraham ya ce “Don’t do this to me, ina son Malumana i love jee i love Mamina ka sanya su cika ni na mata al’ƙawarin zan koma” Ya fara abu kamar hauka hauka hakan yasa Dad tunanin ya samu matsala few minutes ya saka akai masa wata mahaukaciyar Injection ta bacci akai kai sa wani part can ƙarshen Palace ɗin aka garƙame.. Har wajan sati uku Abraham sunan Majeederh a bakinsa ya yi ta surutu shi kaɗai damuwa ta samu gurbi a zuciyarsa tayi daram, ya daina cin abinci ya daina magana daman dariya bata dame shi ba zai ma iya irga sanda ya yi ta. Haka aka dinga masa allura ana saka masa drip sbd rashin cin abinci. Dad ɗin ya ce da dai Abraham ya auri Musulma kuma older gwara kawai yaga gawar ɗan shi duk da irin son da yake masa. He will never allow him to be MIJIN MALAMA ba. Ba zai taɓa barinsa ya zama MIJIN MALAMA ba, wannan babban abin kunya ne ga mabiya addinin su na Kirista magoya bayan Yesu su ji labarin ɗan shi yana auran Malama, ba zai taɓa faruwa ba hakan zai iya sawa ya samu matsala da kujerarsa ta shugaban ƙasa,He doesn’t want that to happen hakan ba zai taɓa faruwa…
After 1 mnt. Majeederh na zaune a dining room tayi shiru tun ranar data dawo daga hospital ta koma shiru shiru. Yau kuma ta tashi bata jin daɗin gabaɗaya tayi tunanin ko al’ada za ta yi? Tana wannan tunanin Latifa ta yi sallama Mami ta ce “Latifa da sanyin safiya?” Latifa ta ce “Wlh Mami, an tashi lafiya?” Ta ce “Allahamdulillah” Latifa ta zauna tana kallon Majeederh ta ce “Lafiya kike?” Ta ɗan lumshe jiƙaƙƙun idanunta tana girjiza kai can a hankali ta ce “Headache” Mami ta ce “Gashi bamu da paracetamol a gidan nan” Latifa ta buɗe jakarta ta ce “Ga wani maganin ciwon kai mai kyau ne, tun sanda Aliyu ya ce waje da bashi da lafiya maganin yake yana da kyau sosai” Majeederh ta kalli maganin sai kuma ta jawo gorar ruwa tare da zubawa cikin cup maganin kala biyu ne ta haɗa ta watsa a baki, ta haɗiye da ƙyar dan ba zata iya kallo ai mata wata allura ba. Ji tayi amai na zuwar mata ta kifa kanta ta kifa saman dining tana mai da numfashi. Mami ta ce “Latifa ki rufawa kan ki asiri kina zama ɗakin mijinki, ki daina biyewa yawon majeederh kada azo ayi haihuwar guzuma dake da ita, ita ba aure ke kuma ki kashe naki” Lafita ta ce “Haba Mami, wai ba zaku yadda da ƙaddara bane? Mene laifin Majeederh a rashin aurenta bafa yin kanta bane itama da zaɓi za a bata wlh da tuni tana gidan mijinta da yaranta, amma miji bai zo ba zata auri kanta ne?” Mami ta ce “Ke wane ya ce miki miji ne bai zo ba? Bata niyyar aure ne amma a yawon da take na Ngo da faɗar kar da matan da take kaɗai ya isa wani ya ganta ya ƙyasa, ba lissafin aure a cikin lissafin rayuwarta” Latifa ta girgiza kai ta ce “Jinkirin aure ne kawai ta samu, Ubangiji kaɗai ya san manufar hakan itama ba da ra’ayinta ba, nasan Majeederh nasan halinta da wani yace yana sonta da aure tabbas zata faɗa mini, Mami da aure da haihuwa duk na Allah ne, amma duk kun bi kun juya mata baya sbd kawai ba tayi aure ba? Idan iyaye basu jawoka jiki a irin wannan condition ɗin da take ciki ba, bai ci ace sun juya mata baya ba, suna bawa jama’ar gari damar d su faɗi duk abinda sukai niyya akan Majeederh, Mami cikar imanin mutum shi ne yadda da ƙaddara cikakken mumini shi Ubangiji yake jarabta ko dan tabbatar da imaninsa, wallahi ba gama garin mutane Ubangiji yake nunawa jarrabawa da ƙuddirarsa akan su ba, mu yarda ne bai kawowa Majeederh mijin aure ba, mu yarda jinkirin aure ta samu” Mami ta ce “Idan mu mun yarda jama’ar gari fa?” Latifa tayi shiru can kuma ta ce “Mami mutum tara yake bai cika goma ba, a jikin ko wanne mai rai akwai zuciya ita take saƙa masa komai, to at this point ba zaka taɓa hana mutane abinda sukai niyyar faɗa ba, haka halin ɗan adam yake, baka da gadonsa yana da gadon maganarka, wani ma bai sanka ba bai san ya kake gudanar da rayuwarka baz bai san komai game da kai ba, ji kaiwa zai yi mutane suna magana ya ara ya yafa ya ɗora nashi akai, sbd kawai baya ƙaunarka ko yana baƙin ciki da abinda kake ko yadda yake gudanar da rayuwarka, wani kuma haka halinsa yake da haɗa ƙanzon kurege haka mutum yake, The world is big, the challenges in it are many, the people in it each have their own character” Latifa tayi shiru tana goge hawayen idanunta ta ce “Human nature is difficult to deal with, whether you do well or not, you will never stop a person from saying what he intends, kinga kenan babu yadda za mu yi, let them says lokacin su ne watarana za su daina, Mami banga aibun auren yaron daka raina ba, tunda bakai ka haife shi ba, ba kuma na nufin rainon yaran da ba kai ka haifa ba illa ne ko haramun ne, amma da Abbu ya bawa Abraham dama nasan dole zai musulunta” Cak Majeederh ta miƙe jiri na ɗaukarta. Washegari gari ta yiwa asibiti tsinke ta nufi wajan Dr Jamal ya gudata ya shaida mata kawai stress ne na gari ya bata magani. Bayan ta koma gida ta samu Abbu da Mami a parlour Mami ta ce “Me Dr ya ce? Akan zazzaɓin?” Majeederh ta ce “Wai stress ne” Mami ta ce “Oh Allah ya ƙara sauƙi” Abbu daman tuni ya zame hannunsa daga kan Majeederh ko gaisuwarta baya amsawa Family ta daina shiga kowa iyaye yake mata akan yana da aure gorin aure ake mata babu ji babu gani, ji take kamar ta mutu ta huta da sauri kuma take Asstagafirullah. Shiru tayi haka kurum tunanin Abraham ya faɗo mata gani take tafi kowa laifi, mai yasa idanunta ya rufe a lokacin ta kasa fahimtar da gaske ba ita ta haife shi ba? Me ya sa take sake masa har yake taɓa jikinta? Bayan tasan ya haramta a gareta, kenan ita ce wacce ta bashi da dama har ya ji ya fara sha’awarta. “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, na shiga uku, Allah na tuba Ubangiji ka yafe mini, ban taɓa tunani hakan ba” Tun daga ranar take neman yafitar Ubangiji da yardar shi, tana jin kamar ta ci amanar addinin musulunci ne, Tunanin Alpha ya faɗo mata haka nan taji tana son saka shi cikin addu’a, shi ma ya riƙe hannunta amma gwara shi yayanta ne, Sai Ajlaal kuma bashi da kunya dama daga gani yafi ƙarfinta ko wanne a riƙe hannunta mistake ne bada gangan ba Abraham kai ta sakewa yanzu kuma tayi ladama kullum cikin neman yafiyar Ubangiji take tana hora kanta da raya dare tana sallah da azumi…..
After a year da ta ƙara zuwa wajan Dr Jamal nan ma ya shaida mata lafiya take. Lokacin tana da shekaru 34 ta jingine komai a gefe, ta ƙaddara Abraham baya ƙasar ba labarinsa babu na Gang team. Lokacin data shiga shekaru 35 farkon shekarar sai ta ji kamar gilamar abu a cikinta ta ɗauka kawai irin abin nan ne da ake kira macijin ciki. Nan ma ta ƙara zuwa wajan Dr Jamal ya dubeta yana murmushi ya ce “Wai mai Malama Majeederh ke tunani ne? Gashi dai har scanning da X-ray duk nayi amma ba komai lafiya lou kike” Ta ɗan yatsuna fuska ta cikin liƙab ta ce “Kawai ban san yin ciwo” Ya jinjina kai ya ce “You’re right, ni kam na tambayeki mana” Ta jinjina masa kai ya ce “Me muhimmancin saka liƙab da hijabi ga mace ne?” Ta kalle shi ta ɗauke kai ya ce “Wlh masu saka liƙab da hijabi na mugun birgeni, na taɓa ganin wata ina sonta amma tayi mini kwarjini” Sai a lokacin Majeederh ta ce “A duk sanda kaga mace ka ji sha’awa to ba kai ne mai laifi ba ita ce zata ɗauki zunubi, ita ta baka damar ganin abinda zai sanya ka ji sha’awarta, to me liƙab sirri ne, hijabi mai taraba ne ga ko wacce mace, abu uku zuwa huɗu yake fara jan hankalin namiji ga ƴa mace, na farko da namiji yaga mace idanunta yake fara kalla, a wannan kallon wani zai iya samun matsala, daga nan sai baki, daga nan sai wuya, abu na gana kuma murya, daga nan kuma bayan mace namiji yake gani, to idan zaka saka hijabi ka saka liƙab ka rufe jikinka babu wani ɗa namiji da zai sha’awarka balle ita macen ta ɗauki zunubi, liƙab da hijabi alama ne da tarbiyyr mutum, masu sakawa a fassara mu su da Allah, idan ka duba larabawa za kaga ko wacce da liƙab ɗinta, me ya sa ƴan izala suke sawa matansu suna sakawa? Ka yi tunanin su ɗin suna da kishi kuma sun san amfaninsa” Zai yi magana ta miƙe ta ce “Thank you Dr Jamal” kwanci tashi Majeederh ta ji cikinta ya fara girma tsoro ya kamata har aka ɗauki wata biyar Mami kallonta kawai take. Tana zaune kamar daga sama taga Uncle Isma’il da Uncle Bello “Saka hijabi hospital zamu” Bata ce komai ba ta miƙe suna zuwa asibiti a gabansu akai mata komai da komai Dr ya ce “Lafiya lou take, gaskiya ko da wata cutar mu dai bamu gani ba, ga photon komai na cikinta ai kuna gani” Uncle Bello ya sauke numfashi Uncle I ya ce “Mu je wani hospital ɗin” suna zuwa wani the same abinda aka faɗa musu shi ne suka sake ji, Uncle Isma’il ya saka akai mata medical check up nan ma the results is good dole suka dawo gida. Latifa ta dinga bawa Aliyu labarin halin da ake ciki akan Majeederh shiru kawai yake mata ta ce “Don Allah don Annabi ba danni ba ka duba girnan Allah dana mahaifiyarka Hajia ka amince da auran Malama Majeederh” A hankali yana miƙewa tsaye ya ce “Accepted” ta kurma ihu ta rungume shi. Lokacin data jewa Majeederh da maganar fata fata sukai ta ɗauke mata huta. Tafiya tayi tafiya har Majeederh tayi wata tara cikin shekarar data shiga na 35 haka kurum ta ji hankalinta yaƙi kwanciya, musamman da cikinta ya yi wani irin mahaukacin girma ƙafarta ya kumbura sosai ta buɗe tai wata ƙiba, hijabi ta saka ta ɗauki waya da jaka ta fito, Mami na zaune a a parlour tare da Raihana da Ruma da Aaliyah hadda Sahar data zo ta fito da ƙyar, tunda ta fito Mami ke kallonta ta ce “Wai kinga ganki kuwa? Anya likita ba ƙarya ya yi miki ba? Ji bi ciki kamar wacce akaiwa ajjiya? Majeederh ta ce “Mami ko jiya sai da Uncle Isma’il ya tisani a gaba wajan likita asibiti biyar muka je Mami ki tambaya ki ji” Ta ce “To Likitocin me suke cewa?” Kanta a ƙasa ta ce “Cewa suke lafiya ta lau, ba su ga komai ba” Ta jinjina kai ta ce “Allah ya kyauta” Ta ce “Zani wajan Dr Jamal na kirasa yanzu ya ce yana cikin asibiti kawai zuwa zan” Mami ta ce “To Allah ya kiyaye” Raihana dai kallon Majeederh take tun daga sama har ƙasa tana tuntsirewa da dariya, da ƙyar Majeederh ta ja ƙafarta zuwa waje ta nufi gidan Latifa ta sameta zaune ta ce “Plx ki yi dropping nawa hospital Latifa i can’t drive myself” Ta ce “Ok, amma yau kin fi bani tsoro akan kullum wannan kamar wata mai cikin tagwaye?” Ta miƙe ta ɗauki key ta mayafi ta ce “Sweetheart ya fita zan masa yawa idan mun je” Mota suka shiga Latifa na driving Majeederh a gefe idanunta rufe ta cure waje guda sbd wani irin sanyi da aka tashi da shi yau ga wani masifaffan hazo na tashin hankali, tunda suke tafiya kuma bata ce komai ba rawar sanyi take Latifa ta ɗaga Glasses ɗin motar ta kashe komai na sanyi, amma duk da haka sanyin shiga jikin Majeederh yake tun kuma data shiga motar kanta ke sunkuye, Latifa na lura da damuwar da Majeederh ke ciki, kuma ta yau tafi da ko yaushe, ta ƙara sauri domin su yi su ƙarasa Aminu Kano hospital ɗin amma ina daidai by pass na first bank go-slow ya riƙe su…… _*(A page 1 za a ga ci-gaba daga nan)*_

Continuation..
Shassheƙar kukanta His Excellency Abu-turab yake ji har tsakiyar kansa ya ɗauka kukan farin ciki ne, da Allah ya bata shi a matsayin mijin aure, wanda ya ji tausayinta na ƙaddarar daya faɗa mata ya aura, amma sai ya ga kukan tsananin baƙin ciki da damuwa ne a hankali ya ce “Ya isa haka Jiddo”
Ta zame jikinta daga na shi da sauri duk da babu hijabi a tsakaninsa yanzu mijinta ne shi kuma matarsa ce, amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai. His Excellency ya watsa mata rinannun idanunsa cike da zallar so ya ce “Mene na kuka?” Ta yi masa shiru ya miƙa hannu zai riƙo nata tayi saurin barin parlourn ya bita da sauri ta shige bedroom ta banko ƙofa tare da murza key tana sulalewa jikin ƙofar tare da rushewa da wani irin raunataccen kuka. *END OF BOOK 1*

 

Allahamdulillah! A nan na kawo ƙarshen BOOK1 wanda suka labari ne, akan yadda aka samu cikin Khalil da kowa ke cewa ɗan shi. I hope yanzu zaku fahimci labarin daidai idan mun ɗora… Da yawa za kuga kamar Malama Majeederh ba ta yi achieving komai a rayuwarta ba sai baƙin da ƙaddarori da suke ta rige-rigen faɗa mata. Ba zan iya cewa kun ji daɗin BOOK1 ko aka asin hakan ba… Abu ɗaya na tsani tsagwaron labarin yana BOOK2. Akwai wasu ƙalubalen tunda mutum a karan kansa bai taɓa dauwama da farin ciki ba, to rayuwa haka take yau fari gobe baƙi, yau zuma gobe maɗaci. Duk macen da zata buɗe baki ta ce tunda tayi aure da mijinta zaman daɗi suke basu taɓa samun matsala ko saɓani ba, tuni na bugi ƙirji na ce ƘARYA TAKE. Allah ya taɓa zuciyata na fahimci komai na gane komai kuma ina fatan zaku biyoni domin kuma ku fahimta…

1. Wacce rayuwa Majeederh za ta yi a gidan Abuturab?

2. His Excellency zai yarda ya saketa ko ya ya? Zata haihu da shi ko ya ya?

3. Abraham zai dawo kamar yadda ya yi al’ƙawari? Idan ya dawo ya samu labarin Majeederh na gidan mijinta me zai faru? Zai haƙura ya barta tayi rayuwa da mijinta ko ya?

4. Ina fatan baku manta da General Alpha Bello khan ba? Shin bayan ya gudu sbd baya son auren haɗi tsakaninsa da Majeederh ina yaje? Yana raye ko ya mutu ne? Yana cikin hankalinsa ko hauka yake? Zai bar Majeederh ko ya?

5. Aliyu ya ce idan har bai auri Majeederh ba to mutuwa ya yi, shin ya zata kaya? Zai haɗa su kishi da Latifa ne?

6. Kuna ganin Abbu zai yi aman shi ya lashe? Wacce magana Fulani zata faɗawa Majeederh amma bata samu dama ba sai Abbu ta faɗawa.

7. EHEM邏 WAYE AJLAAL SULTAAN Mr ji dakai masu taƙama da rawani, kuna ganin zai dawo Nigeria a karo na biyu? Waye zai yi SACRIFICE a cikin zataran mazan? Su waye zasu haƙura da Majeederh wa kuma kuke ganin ya dace da ita matsayin miji na gari?.

WANNE IRIN ZAMA ZA A YI TSAKANIN MAMI DA ƊAN RAINONTA?藍 BILLAHI DRAMA CE BABBA WANDA BAI BIYONI A BOOK2 BA BABU RUWANA… KUN TAƁA GANIN INDA MATA TAKE GUDUN MIJINTA?DUK MAI SON SHIGA GROUP 2 ZAI BIYA #500 BABU YAWA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER6850917335
Na’ima Shu’aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616 ayi maza a cika group wanda bashi da 500 kada ya karanta na sata yazo na yi masa Discount sbd Allah shi ya taɓa zuciyata ba ruwana. Ina ƙaunar masoyana na amana da gaskiya da duk mai karanta littafina. Ubangiji yabar zumunci da ƙauna Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira ya sadaku da dukkan alheri yayi muku albarka殺Ya hure muku kuɗin siyan MIJIN MALAMA 2 thanks for the love and cares thanks for patronize me 爛kune ni da bazarku nake taƙama kune kuke sawa asan da zamana  Nimcyluv sarauta’s love you❣️

Post a Comment for "Mijin Malama Book 1 Page 45"