Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Mijin Malama Book 1 Page 38


MIJIN MALAMA na kuɗi ne dan Allah ki biya kafin ki karata ki kuma sauke nauyi…. 08119237616A tsorace take bin shadow ɗinsa da kallo, kasancewarta mai mugun ji da kanta girman kai da kame kanta cike da tarin nutsuwa da kamala ya sanya kai tsaye ba zaka fahimci girman tashin hankalin da take ciki ba. So take ta samu zarafin buɗe baki, ta tambaye why he’s here? But she couldn’t. Ta ruɗe sosai ta can cikin zuciyarta dalilin rashin kayan arziƙin dake jikinta, ɗan ta ne, amma tasan bashi da ikon ganin wani sashe na jikinta. “Little, why are you here? and why did you turn off the light?” Ta ji shiru ba amsa, sai shadow kawai idanunta suke gane mata. Ƙoƙarin Miƙewa take ta kasa sbd wani irin masifaffen ciwon kan dake nema juya gurɓata mata tunaninta,ji take kamar kan zai rabe biyu, ga zazzaɓin daya gama cinye mata kuzarin jikinta, a hankali ta koma ta kwanta tare da ɗora kanta a frame ɗin gadon ta curkuɗe jikinta da white duvet ɗin dake shimfiɗe saman royal bed ɗinta na turkey. “Ok fita a ɗakina idan ba za ka yi magana ba” Majeederh ta faɗa so calmly ba hayaniya a muryar sai raunin dake son bayyana, still bai magana ba, sai hasken da taga ya mamaye bedroom ɗin lokaci ɗaya, ta sauke ajjiyar kana ta juya side ɗin da take tunanin yana wajan, haɗa idanu sukai da shi yana zaune saman ƙatuwar kujerar dake ɗan nesa da bed ɗin kaɗan, ya saka hannunsa guda ɗaya cikin tsakiyar kansa ya birkitata, sumar ta cukurkuɗe har gaban goshinsa idanunsa sun yi wasu mahaukatan jaa, fuska ɗaure tamau. “How are you feeling now?” Ya jima yana kallonta kafin a takaice ya ce “Lafiya ina” Majeederh ta tsaya kallon ikon Allah jikinsa duk bandeji amma wai lafiya yake? Sbd taurin kai da zafin zuciya ta ce “Come, muga jikin” Ya yi mata shiru yama ɗauke kansa daga direction ɗinta. Ta ɗan saki fuska ta ce “Common baby, zo nan yaro ne” Ya juya a ɗan hargitse yana kallonta sai kuma ya ɓata fuska sosai cikin gadara ya ce “Stop calling me boy, am not”
“Oh sure? Shekararka nawa?” Kamar ba zai bata amsa ba ya ɗan lumshe jiƙaƙƙun idanuna ya buɗe a takaice ya ce “16” Majeederh ta gwalo fararen Idanunta waje, kamar ruwa ya kwanta a ciki dan haske. A hankali ta shiga ƙarewa Abraham kallo, idan aka ce namiji daya amsa sunansa to ana nufin Abraham Daniel David. Wata iriyar suffa Ubangiji ya wadata masa a jiki, zagayayyar fuska ce da shi wacce aka cewa Round face, yana da kwantaccen saje mai yalwa baƙi siɗik da shi, wanda ya taho har gemunsa ya haɗe waje guda. Ɓata lokaci ne tsayawa description na how handsome he’s, The first look she gave him. Ganin yadda ya kafeta da idanu ya sa ta hararesa cikin ƙarfin hali ta ce “Yafi na goyaka a bayan nan nawa kamar yadda na saba, meye wani 16yrd na ɗauka ma zaka ce 50” Shi dai bai ce mata komai ba, kallonta kawai yake ta ƙara ɓata fuska ta ce “To mu da a garin nan kake ma, wallahi ina faɗa maka yanzu za a maka kaciya, idan ba a maka ba kuma ka faɗa na kai ka, I want my child to grow up very well” Dake da turanci duka take maganar yasa ba wani big wahala na fahimtar Abinda take cewa ga Abraham. Ya saka ya shafa sumar kansa yana son yin murmushi ko yaya ne amma he couldn’t speaking calmly ya ce “Na zo ki duba?” Ta ce “What?” Nan ma dai ya jima kafin ya bata amsa da “Anyi kacin ka ba ai ba” Majeederh ta yi shiru tana mai da numfashi domin ita har bata bata jin ba daidai ta faɗa ba. “Yaushe ka zo why are you here?” Ya miƙe tsaye yana nufar window ɗin bedroom ɗin nata ya ce “Since 12 at night, Maa check your hand” Baki sake take kallon, kenan tsayin awa nawa yakai zaune yana kallonta tana bacci? Ta juya sai a lokacin ta lura hannunta dake manne da audiga ta ƙara ganin robber na drip daya ƙare da shocked ta ce “Are you a doctor?”
“Yhh, I am” Da mamaki ta ce “But me kake zuwa yi B.u.k a Department na politics Democracy? Yaushe ka zama doctor a ƙarancin shekarunka you’re too young da zama likita, likitan me?” Ta girgiza kai ta ce “Kayi yaro da yawa Baby, ban ma yarda da karatunka ba” Ta juya ta kalle shi taga yana tsaye harɗe da hannu ya zuba mata Idanu, idanunsa har yafi baya rinewa. “Zo nan ɗan yaro na” Majeederh ta sake faɗa, domin idan tana ganinsa komai na zuciyarta yayewa yake, sosai take son ɗanta kamar ko wacce uwa. Da sassarfa ya ƙarasa inda take tare da zube ƙafafuwansa a ƙasa ya ɗora kansa a cinyarta da wata kalar murya ya ce “Ki daina ce mini yaro Mami, am not a child” Dariya ta so kamata tayi shiru ta ce “To idan ba yaro bane kai mene? You’re just 16 fa haba Khalil” Abraham ya ƙare haɗa fuska tare da zuba idanunsa cikin nata sun ɗauki daƙiƙo suna kallon tsakiyar idanun juna ya ce “Ni ba yaro bane” Majeederh ta ce “Ni dai a wajena kai yaro ne,kaje can inda kake firgitarwa da ƙaton jikinka, amma ni bai fi na goyeka ba” Gani tayi da gaske yake baya so gabaɗaya Annurin fuskar Abraham ya ɗauke kamar an watsa wuta Ya ce “Ohk” Ta share ta ce “Ɓangaren me ka karanta? Ba dai kayi mini allura ba” Ya ce “No! Yanzu zan miki”
Nan da nan ta haɗe fuska itama ta ce “To wallahi na ji sauƙi ma, lafiya ta lou dan ka ji” Ya miƙe cikin wata tafiya ta masu izza da ji da mahaukan kuɗi ya nufi wajan bed side table ya ɗauki wata injection yana zuƙar ruwan ciki, a hankali yake kuma lumshe idanu yana jin kamar kansa zai rabe biyu, Majeederh ta ruɗe domin babu abinda ta tsana sama da injection ta ce “Zo ka fice mini daga ɗaki, Allahamdulillah na ji sauƙi sosai” Bai kulata baz domin a maganarta ba kana jin masharsharar zazzaɓi, gabanta ya faɗi ganin ya nufu inda take tama mance daga ita sai under wear ta miƙe jiri na kwasarta ta nufi har bathroom, tako ɗaya ya yi ya saka hannu ya riƙo ta. “Wayoo Son Allah ban so, kayi mini mutuwa zan yi” Ji ta yi ya saketa, ta sauke numfashi.
“Am sorry Mami” Ta fahimci haƙurin na mene ta ce “Go and ask my father’s forgiveness,not me Khalil, shi ka yiwa laifi ba ni ba, da al’adarmu ta ko akwai bambancin, ka je ka bashi haƙuri” Ya matsa kusa da ita tare da sunkuyar da kansa ya ce “I am sorry, Jee” Sai ta ji tausayinsa shi akaiwa laifi shi za a bawa haƙuri,amma yana da kyau yasan muhimmacin bada haƙuri akan kuskure. Kafin ta sake magana ta ji ya ɗan shige jikinta ya marairaice ya ce “Ka yi haƙuri Jee” Majeederh ta ce “Ok, i for give you, but in one condition” Bai ce mata komai ya shiru akan kafaɗarta ta ce “Bana son sunan nan bad boy, bana son zafin zuciyar nan naka Khalil tun kana ɗan 3yrs kake da zafin zuciya har yanzu nothing changes about that, bana son ƙatuwar sarƙar nan wannan team ɗin ban so idan har ka yarda am your mother, kuma…..,” Cak! Ta tsaya tare da yin ƙara tana ƙanƙame Abraham jikinta na rawa da ɓari sbd shigar tsinin allura da ta ji a jikinta, tsabar tashin hankali da zafin da ta ji numfashinta kusan ɗaukewa ya yi, kamar yarinyar goye haka Majeederh ta saki wani irin raunataccen kuka bakinta na rawa tana kallon Abraham ta ce “Amma ba na ce na ji sauƙi ba, ni Maminka ka yi wa Allura…” Ta kasa magana sai kuka kamar ta kwanta a ƙasa ta yi ta kuka haka take ji ganin idanunsa kawai ya hanata, tunda aka haifeta ba a taɓa yi mata allura ba sai ta saka drip itama da ƙyar, Abraham ya saka hannu ya kama kunnensa ya ce “Am sorry, ban sakewa” Tana shassheƙa ta ce “Da ƙyar wajan bai kumbura ba, ina ji ma ƙafar cirewa za ta yi” Ya ɗan shafa kansa Calmly ya ce “To bari a lailaya” Kafin ya kafaɗu ta miƙe da sauri zata shige bathroom sai kuma ta saka sbd dishi dishi data fara gani kanta ya shiga juyawa, allurar ta fara aiki a jikinta a hankali tayi baya zata faɗi ya yi sauri ƙarasawa ta faɗa saman chest ɗinsa. Sukutar ta ya yi har zuwa saman bed ya kwantar da ita ya ja mata duvet tare da rufeta ya ƙaro gudun A.c Jin ta riƙe hannunsa sosai bakinta na motsawa ya sanya Abraham zama gefen gadon ya ɗora kunnensa a bakinta a hankali ya ji ta na cewa “Stay with me son, Abbu bai so na ya tsane ni ba wanda ya tsana a duniya sama dani, tayaya zan fito da miji a kwana biyu? Good 31yrs bani da farin ciki sai yanzu dana ganka, my son are still alive kada ka barni, Abbu ya tsane ni” Zame kansa ya yi yana jin maybe ya kashe Abbu kawai, Aure? Miji? Sati biyu?” Sune abubuwan da bai gane ba ya jima zaune yana jinta tana surutu a hankali bacci ya ɗauketa kuma ya taɓa wuyanta ya ji ba fever ya sauka…. Washegari wajejen 8 na safe kiran Uncle Isma’il ya farkar da ita daga bacci ta miƙa hannu da ƙyar ta ɗauki wayar tana kaiwa kunne ta ce “Assalamu alaika, barka da safiya Uncle” Cikin sakin fuska ta wayar ya amsa mata da “Allhamdulillah Hawwa’u” Ta yi jim can ta ji ya ce “Hawwa’u da gaske yaron nan ɗan rainonki ne?” ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke tana jin nutsuwa jin maganar Little ta ce “Shi ne Uncle” Uncle ya kalli Anti ya ce “Ikon Allah, mene sunan shi?” Ta ce “Khalil” Uncle ya ƙara cewa “Oh, Ibrahim-Khalil kenan? Amma kin san ba Muslim bane?” Ta jinjina kai ta ce “Eh” Ya ce “Good, ki bashi address na gidana anjima ya zo ya saman” Ta yi shiru ita yanzu ina zata sake ganinsa ma? Uncle Isma’il ya ce “Kin ji ko?” A hankali ta ce “Bani da Digits nasa, kuma Abbu ya hanani fita” Uncle Isma’il ya ce “Akan me kuma? Aikin naki fa?” Ta ce “Wai na fito da miji immediately cikin 2days” Cikin ɓacin rai Uncle Isma’il ya ce “To ya garƙame ki a gida tayaya zaki samu mijin? Ko akwai wanda kuke dating da shi ne?” Cike da takaici da ɗacin rai ta girgiza kai ta ce “A’a” Uncle ya ce “Kina kina gida a garƙamen zaki samu mijin aure? Ko shi ne zai nemo miki mijin ne eh?” Uncle Isma’il ya saki tsaki ya ce “Abdul’aziz baya kyautawa kansa kuma kema baki kyautawa kanki ba, ai ba mijin aure kika rasa ba” Yana faɗin hakan ya kashe wayar rai ɓace. Majeederh ta kifa kanta akan pillow tana jin zuciyarta kamar tayi bindiga damuwa ta mata yawa, ita yanzu ina zata samu mijin aure? Waye zai aureta? Wama take da shi ita wallahi bata taɓa soyayya bama bata san ya take ba, daɗinta da wahalar cikinta duka bata sani ba, amma zo da nufin yaudararta babu wanda ya taɓa, ita ko gurgu ko tsoho ne ya zo da nufin aurenta wallahi da gudu zata amince masa ta gaji over gajiya rayuwarta a jirkice take gabaɗaya, ƙaddarar rayuwa ta sanya ta ciki tsaka mai wuya, rana zafi inuwa ƙona, a dangi a goranta mata rashin aure, a gidan da aka haifeta wanda take jin tana da ƴanci nan ma haka, few people suke supporting nata always. Miƙewa ta yi da nufin shiga bathroom idanunta ya sauka akan Card ɗinsa wanda da gayya ya ajjiye ta dauki card ɗin dake ta sheƙi taga an rubuta Dr. Abraham Denial David, so da gaske dai likita ne shi? How? Ita kam ta raina shekarunsa da zama likita, number ta gani uku ta ƙasashe daban-daban ta dubi ta Nigeria taga ganta special one domin kusan duk digit ɗin 1 ne. Ta saka number ta yi saving da _Son My world_
Kira ta yi lokacin Abraham na zaune cikin garden na gidan su idanunsa kwance a saman tsuntsayen da suke yawo wajan, a hankali yake kaɗa ƙafarsa wacce take cikin ruwa hannunsu riƙe da coke yana sha da kuma shisha gabansa. Wani cool ring tone ya shiga tashi kai tsaye ya fahimci me kira, tun ɗazo Gang team ke kiransa amma yaƙi ɗagawa, ya ɗaga kiran yana mannawa a kunne yana jin sanda ta sauke ajjiyar zuciya ta ce “Uncle Isma’il na kiranka, check your inbox za kaga address ɗin gidan nasa” Tana faɗin hakan ta kashe kiran yasan haushin Allura ne dai bata shige ba. Ya cije lip’s yana shafa sumar ƙirjinsa yana gani ta yi mata Dm na address ɗin gidan a hankali cikin ƙasa da murya kamar shi ma da kansa bai son jin maganar shi ya ce
“Mamina mai tsoran allura”….. Innati ta ƙanƙance idanunta tana kallon Mami zuwanta gidan kenan ita da Maman Alpha sbd acan Innati take da zama ta dubeta ta ce “Ke baki isa ba, bana buƙatar lalatacciyar munafukar gaisuwarki, mijinki nake nema maza kira shi” Mami ta ce “Kiyi haƙuri Innati” Innati ta yi shiru ta juya wajan Maman Alpha ta ce “Ai ka ji tsiyar da Maryama ce uban me zai sanya tayi shiru? Kin zo kin jaɓe kamar kayan wanki” Maman Alpha dai ta yi shiru babu jimawa Abbu ya fito cikin wata dakakkiyar shadda shampo sai ɗaukan idanu take ya tsuguna ya ce “Sannu da zuwa Innati, anzo lafiya?” Innati ta yi mitsi mitsi da idanu ta ce “Kai bayan son zuciya ta hakƙin lafiyayyiyar ƴarka mai zuciya mai kyau, hadda bakin uwa ke binka Audil azizu” Abbu ya ce “Subuhanallahi me na yi?” Kamar zata dage shi ta ce “Me kowa na ce kayi? Cewa na yi bari na zo na ji wanne marar tsoran Allan ne yake rusawa yarinya farin cikinta? A wanne dalilin ka hanata fita aiki? Kuma da zaka karkace ɗuwawu bayan ta tara maka arziƙi ka ce cikin kwana biyu ta nemo mijin aure, ita ƴar bori ce ko aiki da ruhainai da zasu bata mijin aure?” Abbu ya ce “Ni Majeederh ta tarawa arziƙi? Duk faɗi tashin da nake har Ubangiji ya dafa mini? Kuma sbd kare mutuncin kanta na ce ta fito da mijin aure, shekaru 31 banda ita wa kike gani a family bashi da Aure? Sai fa Sona da Aaliyyah, ka kaf area ɗin nan namu babu mai shekarunta sai dai kullum ta yi wanka ta saka kaya ta shiga mota ta tafi aiki? Ba batun aure a ranta ta mayar da kanta tamkar namiji sbd gogagawa da take da su ta zama kamar wata feminist sai dai ta bawa wasu shawarar zama gidan miji da yadda za su yi haƙuri da rayuwar aure amma ita tana zaune gabanmu tana haɗa kafaɗa da uwarta?” Innati ta ce “Ka gama?” Ya yi shiru ta gyara zama tana saka hannu a ƙirji ta fito da yagulallen nono duk a bushe ta ce “Me ya wannan Audil azizu?” Ya saurin cewa “Don Allah Innati ki yi haƙuri Please” Ta girgiza kai ta ce “Ni fa ƴar banza ce, shiru dai kawai nake bance komai ba, idan kana jin kai ka haifi Kululu to ni kuma ni na haifeka ina umartarka daka gaggauta janye sharaɗin ka akan ta, ko kawai na saki nonon ya faɗi ƙasa kasan me hakan ke nufi” Abbu ya ce “In sha Allah” Ta ce “Maza kirata, ai ba wani yaƙunanne bane ya tara arziƙin gidan” Abbu ya ce “Asabe kirata” Mami ta miƙe tare da nufar part ɗin Majeederh not too long suka dawo tare, ta yi wanka ta shirya cikin wata designer ɗin Abaya mai kyau da tsada tayi rolling kanta kyanta ya bayyana idanunta ya faɗa kamar Balarabiya. Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Ta tsuguna ta gaida Maman Alpha da Innati da kuma Abbu bai amsa ba ya ce “Ki koma aiki” Innati ta ce “A’a daman waye ya sanya ta fara aikin ba kai ba, cewa za ka yi ka janye maganar miji ta nemo a nutse ba tashin hankali” Ya faɗi yadda ta ce Majeederh ta ce “Na gode Abbu” Fita ya yi Innati ta bisa da idanu ta ce “Yanzu ma jin kansa yake wani ɗan iskan me kuɗi ne, rabon daya taka ya je ya gaidani anfi shekara Ashirin wallahi tallahi” Maman Alpha ta ce “Shi ne ina ta kiranki shiru ko Majeederh?” Ta sunkuyar da kai ta ce “Zan zo In sha Allah” Sun jima kana sukai sallama… Yau tunda ta tashi da ciwon mara a hankali take duba lokacin tana jiran zuwan Latifa kafin ta shige B.u.k Allah yasa yau ba mutane a office ɗin nata tana zaune saman duguwar kujera zufa na yanko mata, ta saka hannu ta riƙe wajan dake mata ciwo daidai mara duk iya yadda takai ga dauriya ta kasa jure zafin ciwon jikinta ɓari yake, hannu ta kai da nufin ɗakko wayarta ta faɗo daga kujerar ta kwanta saman carpet rolling ɗin kanta ya cire yalwatacciyyar sumarta tayi ɗaiɗai a saman carpet ɗin sbd zamewar ribbon kanta, kiran sunan Allah kawai take domin ta gama fidda ran mutuwa ma za ta yi idanunta har ya fara ɗaukewa sai fari, shigowarsa cikin office ɗin ya yi daidai da sarƙewar numfashinta a rikice ya ƙarasa shiga ciki yana cillar da wayarsa yana zuwa ya zube a ƙasan carpet ɗin duk da kyan kayan jikinsa da ƙamshin dake ta shi yana zuwa ya saka hannu ya ɗagota zuwa jikinsa gashin kanta na rufe masa fuska ya shiga girgizata ya kasa cewa komai, can ta ja numfashi jinta a jikin mutum yasa ta fashe da kuka Majeederh bata ƙaunar ciwo ko kaɗan balle wannan ciwon cikin da take jin kamar ta mutu bata taɓa jin irinsa ba, ta ƙanƙame wanda take jikinsa sosai a hankali muryarsa na fita da ƙyar ya ce “Sorry, meke miki ciwo?” Ta kasa bashi ba tare data san waye ba sbd bata hayyacinta ta kama hannunsa da manna a mararta ta ce “Zan mutu, ciwo wayyo” Ya yi shiru yana jin kansa na sarawa tsigar jikinsa na tashi ta ƙara danna hannunsa a marar ta ce “Ka danna mini….

 

Post a Comment for "Mijin Malama Book 1 Page 38"