Kurkukun Kaddara Book 2 Page 9
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E9_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._
Wuraren Æ™arfe biyar da rabi na marece, Aneelerh ta fito daga cikin toilet bayanta a goye da baby junaid tayi mashi wanka ta É—aura mashi towel, A saman Gado ta kawantar da shi fuskar shi É—auke da murmushi, É—an zaro mashi ido tayi”Why are u smilling at me”?
“Mommy daÉ—i nake ji, Angel zata dawo” aÉ—an ruÉ—e ta bi shi da kallo”Junaid! Waya faÉ—a maka Angel zata dawo”? Da yatsan hannun shi ya nuna mata saitin zuciyarshi, murmushi ta saki haÉ—i da É—an girgiza kanta”my baby boy nima ina ji araina Æ´ar uwarka ta kusa bayyana in sha Allahu nan bada jimawa ba, in dai tana numfashi a doron duniyar nan….”tunkan ta rufe baki yace”Mommy Angel tana sona? É—aga mashi kai ta yi alamar eh”Angel tana sonka junaid tun kafin zuwanka duniya ta Æ™walla fa rai akan son ganin ka,”
Ta yi maganar tare da juyawa ta nufi gaban mirror ta É—auko Mayukan shafawarshi, a saman mattress É—in ta É—aura su, ta soma shafa mashi ajikinshi.
“Aunty Aneelerh,!” muryar zahra ce daga waje take kwaÉ—a mata kira, A hanzar ce Junaid ya buge hannun Aneelerh data ruÆ™e shi, ya damÆ™i towel É—inshi dake yashe saman katifar, Lamarin yai matuÆ™ar É—aurewa Aneelerh kai, ganin yadda yake kiciniyar É—aure qugunshi, duk don saboda zahra kada ta gan shi babu kaya, Kafin zahra ta faÉ—o É—akin tuni ya kammala maida towel É—inshi sai faman haki yake yi, Æ™asa Æ™asa da murya tace”junaid ban kammala shafa maka man ba”, turo mata baki yai”Ni ae bana sho Aunty zahra ta gane min abuna, idan ta tafi sai ki Æ™arasa shafa man….”kumshe dariya Aneelerh tayi abakinta.
“Aunty Aneelerh Abie da daddy suna son Yin magana dake, Na riga na faÉ—a masu komai game da tada zancen 6acewar su tajuddeen, sun amince da yin hakan” Farin Ciki ne ya bayyana akan fuskar Aneelerh”Zahra, zanje yanzu mu yi magana da su, Ga junaid nan ki cigaba da shafa mashi…” kasa Æ™arasa maganar ta yi sakamakon toshe mata baki da Junaid yai da tafin hannun shi, Kallon fuskarshi tayi, 6acin rai ta gani akanta.
Ta6e baki zahra tayi idonta akan fuskar Baby junaid,”Kin ga Aunty Aneelerh Ki tashi ki je suna a palour, bana so damar nan ta wuce mu, Ki barni dashi zan Æ™arasa gyara mashi jikin” amsa mata ta yi da toh, kafin ta sakko daga saman gadon ta nufi closet ta buÉ—e ta curo mayafinta bayan fitarta É—akin, Junaid ya takure kanshi jikin headboard na gadon, lallashinshi ta soma yi”haba habibina meye na 6ata fuska nifa ma mommyn ka ce, zo nan in gyaran maka jikin ka, MaÆ™e mata kafa É—a yai”so ki ke ki kalle mun abuna, ni banso, Zan jira mommy ta dawo”
É—aure fuska tayi ganin zai 6ata mata lokaci yasa ta haye gadon ta cafko shi, ya dinga kuka yana shure shuren Æ™afa, daÆ™yar ta samu ta shafe mashi jikin tana fadin”É—an jakar uba, Jiki duk madara, da ace baka da kyau ko kallo baka ishe ni ba” tur6une mata fuska yai hada jifarta da harara, MiÆ™ewa tai daga saman gadon ta sauko ta nufi closet din kayan su ta É—auko mashi riga da wando, ta dawo ta zauna gefen shi, a tsanake ta zura mashi a jikinsa, tunkan ta kammala Wayar Aneelerh ta soma ringing
“Wayar mommy tana ringing” junaid ne ya sanar da ita
“Ni bana É—aga wayar mutun idan bashi ya bani izni ba” gatsina mata hanci yai”Angel ce ke kira aunty zahra dan Allah ki É—aga, kada ta katse” kwantar da kanshi tai saman Æ™irjinta, faÉ—i yake ni ki sake ni, inje in É—aga kiran Angel” taÆ™i barin shi ya motsa, suman kanshi take shafawa da hannunta, shiyasa ya ke gudun zahra ta É—auke shi, kamar ta samu lallausan bready haka take daÆ™una shi.
Bayan fitar Aneelerh A palour ta taras da Uncle ɗan Iya tare da abie hada Mommy da Ummi zaune saman Sofa, cikin girmamawa ta ƙarasa tare da zuƙunnawa ta gaishe su, A mutunce suka amsa mata, daga ƙasan sofa ɗin da mami da ummi ke azaune ta jingina bayanta, tare da sunnar da kanta tana jiran jin me zasu ce.
Gyaran Murya uncle É—an Iya ya yi, hakan yasa ta É—ago da ido ta kalle shi, ya Æ™wama farin Glass a fuskarshi Ya É—an sauko har saman karan hancinsa, a halitta baÆ™i ne wulik, kamar ba jinin Abie ba, yana da Manyan idanuwa hancin shi a wargaje yake, Haka bakin shi manyan la66a ne dashi, wandon shadda ne a jikin shi Daga sama Malun malun ce babi Ƴar Ciki, Ya Æ™wama Hula Akanshi Ga uban sanÆ™o, a saman Kujera mai mazaunin mutun uku suke zaune su Biyu, gyaran murya yai kafin ya soma magana”Zahra ta faÉ—a min komai, a gaskiya kun kawo shawara mai kyau, Kunyi tunani na hankali” yana magana yana watsa hannayenshi ÆŠabi’arsa ce Yin hakan.
“bai kamata don abu ya haura shekaru da faruwa muja baki muyi shiru, tun da har yanzu bamu da tabbacin suna araye ko sun mutu! Idan ko suna araye ba Æ™aramin ganganci mu kayi ba, Na watsar da zancen 6acewarsu, wata’Æ™il Silar tada zancen Allah Ya bayyanar mana dasu…..” tun da ya soma magana suka natsu suna sauraronshi, Aneelerh ta duÆ™ar Da kanta Æ™asa Farin Ciki duk ya cikata, gani take kamar ma har an riga an ganso su.
“In sha Allah zanyi magana da ziyad babban É—an jarida ne muddin labarin nan ya je gare shi ina mai tabbatar baki da cewa cikin Æ™anÆ™anin Lokaci Duniya zata É—auka tamkar bai jima da faruwa ba, a manyan Kafafan sada zumunta za’a yaÉ—a labarinsu, irin su BBc, CNN, and ONt, muma kuma zamu bada gudummuwar mu, wurin YaÉ—a hotunansu a social media”
Bayan Uncle É—an Iya ya takaita da zancen nashi Abie ya É—aura da cewa”kafin Gobe ki tabbatar kin tattara duk wasu hotunansu Tajudden kin tura mashi, Sannan Adage da addu’a duk danasan kina Æ™oÆ™ari wurin yi masu, Mamie ta fadamin kullum sai kin tashi yin nafilfili dare, naji daÉ—in jin hakan sosai, Allah yayi maki albarka” amsa mashi ta yi da ameen, Mamie tace”Ubangiji Allah ya bayyanar mana dasu, Allah yasa silar tada zancen 6acewarsu da za’ayi su bayyana, mungode sosai” godiya suka hau yiwa Uncle É—an Iya, kafin daga Bisani Aneelerh ta miÆ™e tare da yi masu sallama ta Nufi bedroom É—inta tsabar zumuÉ—i kamar zata tashi sama, lokacin da ta shiga É—akin, A kwance ta samu zahra tana fuskantar ceilling hannunta a ruÆ™e da wayarta, ga dukkan alamu Chatting take Yi, Baby junaid tuni ya jima dayin bacci yana kwance saman Æ™irjinta. Jin motsin shigowar Aneelerh Yasa ta É—an kawar da kanta daga kallon wayar ta take Yi ta kalli Aneelerh tunkan ta Æ™arasa shigowa ciki Ta lura da tsantsar farin Cikin dake akan fuskarta
“Yah aunty Aneelerh Ina fatan komai lafiya”tana murmushi tace”abie yace in tura ma Uncle hotunansu tajuddeen wlh bakiji daÉ—in da naji ba,”Zahra na murmushi tace”Allah yasa Adace sister, nima zan tayaku sharing a instagram page É—in mu,” Godiya Aneelerh ta yi mata, ringing É—in wayarta ne Yaja hankalinta ga duban saman pillow, Da sauri ta nufi wayar takai hannu ta dauke ta
“Bansan wanene ke kiranki ba, Tun É—azu bayan kin fita wayar ke ta ringing ban daga ba”
“Why ba ki É—aga ba zahra, Surukata ce fa” ta6e baki zahra tayi”matar da ke son Æ™wace mana baby junaid É—inmu ai Æ™wara daban É—aga ba” picking call É—in Aneelerh tai tare da kanga wayar a kunnanta.
Cikin girmamawa tayi mata sallama”Assalamu akaikum” on the other hand Hajiya adama ta amsa mata da”Wa’alaikum salam daughter In law, ina kika shiga inata kira ba aÉ—agawa”? aneelerh tamkar tana agabanta tace”Bana akusa da wayar ne bansan kun kira ba” gaisawa sukayi kafin hajiya adama tace”guest what”? É—an zaro ido Aneelerh ta É—anyi tana wurwurga eye balls É—in ta can tace”kun dawo Æ™asar”? Sautin dariyar hajiyar adama ne yasa ta saki murmushin farin ciki.
“Mun dawo, in sha Allah end of this month zamu shigo Abuja, two days kin daina kiran layina Why? Ko dan saboda kada na Æ™wace maki Yaro”? Cikin Jin kunyar maganarta Aneelerh tace”ba haka bane mommy, wlh ina ta zucci zuccin in kira ki Allah ne bai nufa ba” Tai maganar a yayin da take kokarin zama saman stool, Ta gaji da tsayuwar, Zahra ta kasa kunne tana sauraron Firarsu.
“Idan ma don saboda dashi ne to ki kwantar da hankalin ki, babu wanda zai raba ki da É—anki, Munyi magana da abdallah Ya fahimtar dani game da cutuwar da zakiyi idan muka ce zamu raba ki da shi, Ni kaina bazanso Inyi silar sanya ki baÆ™in ciki ba….” buÉ—e ido Aneelerh Tayi Wani irin farin cikine tsantsa akan fuskarta, Zahra da ta tsareta da ido tana kallonta, sai faman yi mata mimi da baki takeyi donta fada mata me Hajiya adama ke fada mata wanda yasa ta farin ciki
“Zan kira mamin naki mu yi magana, Sannan akwai wata gagarumar kyauta dana shirya maki idan mun zo zaki gani” Hawayen farin Ciki ne su ka wanke fuskar Aneelerh, kasa jurewa tayi batasan lokacin da kuka ya kubce mata ba. Muryar Hajiya adama a É—an ruÉ—e take fadin Aneelerh why? Kuka kuma? Meya faru? cikin shessheÆ™ar kuka tace mata kukan farin Cikine, taji daÉ—in Æ™aunar da take nuna mata, tana alfahari da su, samun surukai irinsu abune mai wuya, Hajiya adama taji daÉ—in daÉ—aÉ—an kalaman da Aneelerh take faÉ—a mata, tsawon lokaci suna waya Kafin daga bisani Tayi mata sallama, Idanuwanta acike tab da Æ™walla ta wurga su kan fuskar zahra tambayarta ta shiga me suka tattauna da Hajiya adama? Nan Aneelerh ta sanar da ita komai, Fasa ihu zahra Tayi tare da jefar da wayarta gefenta, ta sauke junaid daga saman jikinta a hankali ta kwantar dashi, kafin ta sauko daga saman gadon ta nufi Aneelerh ta rungumeta kamar zata maidata ciki, Farin Ciki duk Ya cikasu, MiÆ™ewa Aneelerh tayi bayan ta ajiye wayar gaban mirrror, Rawa suka soma takawa ita da zahra, hada É—ebo shoki suna kifawa saman goshinsu, Yayin da suke sakin Dariyar murna.
*EVIL FOREST*
A Æ™alla yau satin su É—aya acikin kogon dutsen ba tare da sun motsa ba, saboda marasa lafiyan cikinsu, jikinsu yai tsauri, duk da haka suna Æ™oÆ™arin basu kulawa ta musamman, Danish Ya haÉ—a masu garin maganin da su ke sha suna samun warakar raÉ—aÉ—in ciwonsu, A cikin gorar ruwansu ya ke jiÆ™a masu maganin, Bayan haka duk in za su yi tsarki da ruwan zafi su ke yin shi, danish ne yai masu dabarar yin hakan, Alhamdulillam Jikinsu Azeeza yayi kyau sauÆ™i ya samu, ba su rasa ci da sha ba, kullum ne sai sun ci abinci sau uku, Danish ne ke Æ™oÆ™arin yi masu farautar abunda zasu ci wani sa’in zoman daji yake kaso masu ko tsuntsaye hada kayan marmari ya ke samo masu, saboda su ya ke hana idonshi bacci, A zaune yake kwana shi da Angel dinsa, tana É—ebe mashi kewa, shaÆ™uwace mai Æ™arfi a tsakaninsu.
Burinsu marasa lafiyar cikinsu su ƙarasa wartsakewa ko sun samu su cigaba da tafiya.
Yau tun da sanyin safiya ta soma Jin hayaniya acikin kunnuwanta, ƙasa ƙasa take iya jin maganganunsu, Tsantsar mamaki ne ya kamata Jin muryoyin su Batul, tamkar a mafarki, a harzarce ta buɗe idanuwanta tare da miƙewa zaune tana ƙarewa Kogon dutsen kallo, Haris ne kaɗai ya rage a kwance yana bacci, Ya ƙudundune kanshi cikin bargo, ƙoƙarin tariyo abunda ya faru jiya ta soma yi, da wata irin kasala ta miƙe tsaye tare da yin hamma, abu biyu ya ɗaure mata kai da farko tayi tsammanin zata ga su Azeeza sai dai bata kowa ba.
Hankalinta A matuÆ™ar tashe ta fito tana Æ™arewa Dajin kallo, Kamar daga sama tajiyo muryar Jemimah tana ambaton Sunan da take kiranta dashi”Genie!’ ras taji gabanta Ya faÉ—i, A ruÉ—e ta wurga Æ™wayar idonta kansu, Gaba É—ayansu ne banda Haris, Yau wata rana sun fito daga kogon dutse jiki yayi kyau, Sai wasa suke Yi suna tsalle tsalle, Farin Ciki duk ya cikasu, Bakunansu awashe kamar gonar auduga, ba ta san lokacin da hawaye suka soma wanke fuskarta ba, Nan ta ke ta zube saman gwiwowinta tare da kifa kanta Æ™asa ta yi sujjada tana godewa Allah da ya nuna mata wannan ranar, HaÆ™iÆ™a tayi farin ciki mara misaltuwa, kafin ta É—ago daga sujjadar Jemimah ta watso da gudu ta faÉ—o saman bayanta, sai tiÆ™ar dariya ta ke yi tana fadin”Genie DaÉ—i kamar zai kashe mu, Wlh daÉ—i muke ji, wannan wurin mai kyau bamu ta6a ganin irin shi ba, Genie Yau zamuje gidan daddynki ko”? Kasa É—agowa Angel tai, wani irin yanayi take jin kanta.
Ƙarasowa Azeeza tayi Hannunta ruƙe cikin na Gabriel, Sauran Ƴan uwansu na abiye da bayansu, agaban inda tayi sujjadar suka tsaitsaya suna kallon ta
“Angel muna son yin magana dake”muryar parveen ce ta ratsa kunnanta, daÆ™yar ta iya haÉ—iye kukan da ke shirin kubce mata ta É—ago da kanta, tare da zagayo da hanneyenta biyu ta ruÆ™e Jemimah gudun kada ta faÉ—o daga bayanta
Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, tun daga kan fuskar Azeeza dake ta sakin murmushi, fatar jikinta tayi haske sosai dama ita can launin skin ɗinta na farar fata ne, da launin gashinta, ta rame sosai ta ƙara komawa ƙarama. ɗauke idon ta tayi daga fuskar Azeeza ta mayar dasu kan fuskar parveen, itama ta faɗa duk sunyi haske kamar fatalwu, Murmushi ta ɗan saki tare da kallon Batul dake a tsaye tana sakar mata murmushin ƙauna.
“Rabin rai kin tashi lafiya, Nasan kinyi mamakin ganin mu awaje muna shan iskar duniya, Danish ne ya fito da mu waje kuma yace da zarar ya sama mana abinci mun ci zamu kama hanya” lumshe ido Angel ta É—anyi tare da ware su kan fuskar Hannah.
Muryar Gabriel ce ta janyo hankalinta ga kallon shi”Muna so muyi maki godiyane akan irin Æ™oÆ™arin da kikayi mana, Angel kin cancanci ayaba maki, babu wasu kalmomi da zamu Iya yin amfani da su wurin yi maki godiya ke da Danish, Allah ne kaÉ—ai zai Iya biyanku” Cikin sanyin murya tace”Allah shine abun godiya Gabriel, Alhamdulillah ala kullu halin, ina taya ku murnar Samun Æ´anci arayuwarku, Kuma inayi mana fatan Allah ya bamu sa’a adukkannin abunda muka sa agaba, Ubangiji Allah yasa Æ™arshen wahalar mu ce tazo….” addu’o’i ta dinga jera masu suna amsa mata da ameen, Sai da ta kai Æ™arshen maganarta, muryar jemimah ta katse ta”Genie ba zamu Æ™ara komawa kurkuku ba ko?” Batul tace”har abada mu da kurkukun Æ™addara, Daga nan sai Gidan daddyn Genie, ko kina son komawa ne”? Zaro ido tai tare da girgiza kanta”banso, Allah ya tsinema su da tsohuwa zafreen, muguwa idan mu ka yi Æ™arfi sai mun kashe su, damu da daddyn Genie, zamu rugurguza kurkukun kowa ya huta, Kuma zamu Æ™wato Æ´an uwanmu da ke a wurinsu” ranta a6ace ta ke yin magana, kumatunta sunyi jawur da su.
Angel tace”In sha Allah Jemimah mune zamu kawo Æ™arshensu, Allah sai ya saka mata cin zalunmu da su ka yi, haƙƙin mu ba zai ta6a barinsu ba, tun agidan duniya zasu fara gir6an abunda suka shuka” tana magana hawaye nabin fuskarta.
“Angel Ba ki faÉ—a mana ina ne nan ba? Munga wasu abubuwa da su ka É—aure mana kai waÉ—anda bamu ta6a ganinsu ba ko a mafarki,” Javed ne yai mata maganar fuskarshi da alamun ruÉ—u.
“Angel munga kalar ganyan da ake kawo mana muna ci a kurkuku,” still fuskarta da murmushi ta yunÆ™ura ta miÆ™e hannunta ruÆ™e da Jemimah, Gabriel ta kalla”meyasa baka yi masu bayani ba”? Ta6e la66ansa yai”sun fi so suji daga bakin ki,” Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa”Okey, Ku jira Danish Ya dawo, idan muka kammala cin abinci, muka kama hanya zanyi maku bayanin komai” amsa mata su ka yi da toh. Kafin wani ya Æ™ara cewa wani abu, Motsin tafiyar Danish ta janyo hankulansu ga dubanshi.
A tsanake ya ke yin tafiya yana tunkaro su, hannun shi ɗaya a ruƙe da kwandon da ya haɗa masu saboda ajiyar kayan abincin su, tunkan ya ƙaraso Jemimah ta sauko daga bayan Angel, da gudu suka nufe shi ita da Azeeza da parveen, atare suka faɗa mashi tare da ƙanƙame shi suna sakin dariyar farin ciki.
Ganin shi suke yi tamkar mahaifinsu, saboda kyautatawar da ya ke yi masu wurin yin jinyarsu, nufo wurin su Angel tayi tana faÉ—in”Sannu da dawowa My Man, Na farka ban gan ka, meyasa baka tada ni mun tafi atare ba” ta yi maganar tare da kai hannu ta ruÆ™o hannun Kwandon da ya ruÆ™o, sakar mata yai ta kar6a tana leÆ™a cikinsa Kayan marmari ne ashaÆ™e cikin kwandon.
Da sauri ta É—ago suka haÉ—a ido da juna, murmushi ta sakar mashi”sannu da Æ™oÆ™ari, duk namu ne wannan,” É—aga mata gira yai alamar eh, “mun gode Danish, Allah ne kaÉ—ai zai Iya biyanka,” lumshe mata ido yai kafin ahankali ya ware su akan fuskarta.
Su Parveen sun Æ™i sakin jikin shi tun da su ka rungume shi ba su É—ago ba, faffaÉ—an tafin hannun shi ya É—aura asaman kawunan su a hankali ya ke shafa sumarsu kan su, sai Æ™ara Æ™anÆ™ame shi suke Yi, a hankali ya furta masu”Ya Jikin naku”? Jemimah da Azeeza suka haÉ—a baki”Ai mun warke, Gidan daddyn Genie zamu je yau”
Ganin sunÆ™i sakin shi yasa Angel yi masu magana”ku sake shi mana, Ko mun samu muyi sauri muci mu tafi, idan har ba barin Dajin nan mukayi ba Hankalina ba zai kwanta ba” Jin maganarta yasa suka sake shi, Ya ruÆ™o hannun Azeeza dana Jemimah suka jera atare suna tafiya, Cikin Kogon dutsen su ka koma gaba É—ayansu, suna shiga suka tarar da Haris zaune shi kaÉ—ai, bai jima da farkawa daga bacci ba, A Æ™asa kowanansu ya zauna, Angel ta curo kayan marmarin ta rarrabamasu, A tsanake suke sha suna kallon Juna, bayan sun kammala sha, Suka fara shirin tafiya, Ba tare da 6ata lokaci ba, Angel Ta goya jemimah abayanta da mayafi ta É—aureta, Gabriel Ya goya Azeeza abayanshi, sai daÉ—i suke ji an goyasu har gwalo suke Yima Parveen, Batul kuma ta Goya Back pack É—in Unaiza abayanta, Javed Ya ruÆ™e masu akwatin kayansu, basu bar komai acikin kogon ba, Hatta Gorar ruwansu acikin kwandon kayan marmarinsu su ka sanyata, Parveen ce ta ruÆ™e kwandon a hannun ta.
Matafiya sun shirya tsaf saura tafiya ta rage masu, kafin fitarsu daga kogon dutsen saida Angel ta yi masu addu’o’i tabi kowan nan su ta tofe shi tun daga Æ™asa har sama ko da ta zo kan Danish sai ce wa yai me take yi haka? ta daina watsa mashi yawu baiso, dariya tayi batare da tace mashi komai ba, Danish ne ke ruÆ™e da Haris saboda rashin Æ™warin Jikin shi.
Suna tafiya suna fira a dokar dajin, Su parveen sunga abubuwan da suka ɗaure masu kai, Komai suka gani sai sun tambayi Angel menene shi? Lokacin da rana ta ƙwalo Kowannansu Ya zazzare idanuwanshi suna kallon Sararin samaniya inda rana ta hudo, Angel sai ƙoƙarin hanasu takeyi akan su daina kallonta, gudun kada hasken ranar ya kashe masu idanuwan su.
Bakomai yasa su yin hakan ba face tsantsar mamaki da al’ajabi, su fa duk É—aukarsu Fitila ce aka ajiye sama, kamar dai yadda ceiling É—in É—akin su na kurkuku Yake, Parveen sarki kwa6a magana da ta gaza jurewa tace da Angel ta faÉ—a mata tayaya akai har aka É—aura fitilar sama? Ita bata ta6a ganin fitila mai hasken ta ba,” Dariya Angel tasaki tare da cewa”Kai parveen Nafa ta6a faÉ—a maku saboda gudun haka, Rana ce wannan da kuke Gani, Babu wanda ya É—aurata Yana daga cikin halittar ubangijin mu Allah, bayan ita akwai Wata da taurari suma duk Allah ne ya halicce su, Idan Dare yayi zan nuna maku su, taci wahala wurin wayar masu da kai daÆ™yar ta samu suka fahimce ta, kusan saida ta maimaita masu karatun data koya masu tukunna suka Iya tunawa, A Æ™alla sun shafe awanni suna kutsawa cikin Dajin babu alamun zasu shigo cikin Garin, Wani irin kurman Dajine ta ko’ina acunkushe yake da tsirrai.
Gaba É—aya sun gaji da tafiya, Dama jikinsu bai saba da wahala ba, Ga6o6in jikinsu duk sun raunata, Mutun Biyune basu jikata ba, Jemimah da Azeezah, hankalinsu kwance Har bacci ya É—auke su a goye sai daga bisani suka farka,
“Wlh mun gaji Angel, Wai haka zamu dinga tafiya ba tsayawa? Ƙafafuwana duk sun rurruÆ™e, Ga yunwa inaji” Parveen ce tayi maganar,
“Ya ki ke so muyi parveen dole muyi tafiya da da halima hada gudu, in ba haka ba zamu Æ™are acikin Dajin nan ne,” fuskar Angel ayamutse ta yi maganar,
Danish duk yana sauraronsu, hankalin shi na akan Haris daya ruƙe.
Parveen ta hanasu sakat, don dole Naufal Ya goyata abayanshi, Jemimah hada tsokanarta”Æ™atuwa dake dole sai an maki goya irin namu” Harara parveen ta watsa mata. Ba tare da tace komai ba.
Zogin da ƙafafuwansu suka fara yi masu ne yasa suka yada zango agaban wata ƙatuwar bishiya suka zazzauna suna faman yin haki, Gorar ruwa parveen ta curo masu, Bayan tasha ta miƙa ma Naufal yasha ya miƙa ma Hannah, sai dakowa yasha ruwan, Sun natsu suna faman lumshe idanuwansu,
“karfa kuyi mana bacci anan, bamu gama tafiya ba, naga kuna rufe ido,” Angel ce tayi masu magana, Fuskar Parveen atur6une tace”kaÉ—an zamuyi, ” batul Ta natsu tana kallon Bishiyoyin dake a kewaye dasu,
“Angel Su waÉ—annan basu gajiya da tsayuwa ne”!? Fuskar ta aÉ—aure tayi maganar babu alamun wasa
“Su wa kike nufi” Angel ta tambaya tana kallon fuskar Batul, Da hannu ta nuna mata Bishiyoyin dake fuskantarsu, ÆŠan zaro ido Angel tayi tare da kallon Danish dake kallon fuskarta, kiris ya rage ya saki murmushi jin wautar Batul. hankalinta a kwance taci gaba da cewa”tun da muka taho suke ta tsayuwa babu motsawa, Itama rana sai binmu takeyi da gudu duk inda mukayi sai na ganta, to wai su basu gajiya ne”? Kalamanta sun rufe ma Angel baki ta kasa bata amsa, daÆ™yar ta iya cewa”Haka Allah ya Halicce su Batul”
Gabriel da ya Æ™umshe dariya abakin shi yace da ita”ke yanzu idan waÉ—annan bishiyoyin suka motsa zaki tsaya? Har kina da bakin cewa Basu gajiya da tsayuwa”? Sai lokacin ta É—an saki murmushi ba tare data kalle shi, shiru su ka É—anyi na wani lokaci, Har bacci ya fara Æ™oÆ™arin É—aukar su Jemimah ta fara ambaton fitsari take ji, ÆŠaukarta Angel tayi tare da miÆ™ewa ta kalli Danish”Zanje nakaita tayi fitsari,”lumshe mata ido yai tare da cewa”No, basai kunje nesa ba, Zata iya yi ko abayan bishiya ne” Amsa mashi tayi da toh, kafin ta nufi bayan bishiyar da ita, bayan sun dawone tace dasu su tashi suci gaba da tafiya kada dare yayi masu anan, MiÆ™ewa su kayi jiki duk ba Æ™wari, Ta maida goyan Jemimah gabriel ma ya goya azeezarshi suka dasa da tafiya.
Allah ya tsare su tunda suke tafiya babu wata muguwar dabbar da suka ci karo da ita, Sai dai sautin koke kokensu da suke ji acan wani sashe na Dajin, Sunyi nisa da tafiya kwatsam Ba zato ba tsammani Akuya ta faɗo wurinsu kamar an jehota, a matuƙar figirce suka watsa da gudu cikin dajin duk su ka tarwatse saboda tsabar firgitar da su ka yi.
Hankalinsu Danish ba ƙaramin tashi yai ba, babban abunda suke jima tsoro kada wata dabbar ta handamesu, Mutun biyar ne suka watse waɗanda suka rage Danish ne sai haris shima saboda Ya ruƙe shi ne ya kasa guduwa, Gabriel dake goye da azeeza sai Jemimah da Angel, Basu ta6a ganin akuya ba sai yau, shiyasa Suka watse, mun shigo uku Danish! Ya zamuyi? Angel ce ta ambaci hakan, Bai amsa mata ba ya kwantar da Haris jikin bishiya da gudun gaske ya faɗa Cikin Dajin don Ya tattarosu.
Jemimah ta ƙanƙame angel sai satar kallon akuyar take Yi, ta yi tsaye tana Lasar baki, Ciyawar dake awurin take Ci,
Ran Angel ya 6aci, Duwatsu ta tsinta a kasa ta dinga jifar akuyar, Da gudu Ta watsa tana kuka, Sautin dariyar Jemimah ne ya karaÉ—e kunnuwansu
“Genie ashe ma matsorayaci ce, wai wannan abun su Batul suke ma gudu, ni sun bani dariya, Ko kunya ma bata ji tana yawo zindir babu kaya a jikinta, Æ´an nonuwanta azube kamar na tsohuwa, Genie itama mutunce kamar mu ko”? shiru Angel bata tanka mata, Damuwace Æ™arara akan fuskarta, Hankalinta ba zai ta6a kwanciya ba idan har ba adawo dasu Batul ba.
Azeeza tana a la6e saman bayan Gabriel, Muguwar matsoraciya tun da akuyar nan ta faÉ—o wurinsu Ko yatsanta tagaza motsawa, Numfashinta ma a dabarbarce yake fita, Jikinta sai kakarwa yake yi, ba dan Allah yasa tana a goye a bayan Gabriel ba kuma ya É—aureta da mayafi da kuwa Silar 6acewar azeeza kenan acikin Daji, Allah kaÉ—ai yasan inda zata kutsa kanta saboda tsoro.
“Shiru basu dawo ba Angel, Ni inaga zan bi bayan Danish ne” Gabriel yai maganar, da sauri tace”A’a, Kada kaje ko’ina, Inaji araina zasu dawo atare, nasan duk inda suka shiga Danish zai nemo su”
Haris dai Yana a langwa6e jikin bishiya, suna cikin jimamin rashin ƴan uwansu, suka soma Jin takun tafiyarsu da sauri suka Juya baya suna kallon su, a jere su ke tafiya suna tunkaro su, abun da zai baka mamaki Hada naufal da javed su da suke maza, Batul na aruƙe da hannun Hannah, dana Parveen Sai haki sukeyi sun hada uban gumi, Danish na abiye da bayansu, Tunkan su ƙaraso Angel ta fashe da dariya hada dafe cikinta, Hatta Gabriel dariyar yake yi masu, hakan ba ƙaramin ƙona ransu yai ba.
Ko da su ka Æ™araso zazzaga masu masifa Naufal ya shiga yi yana fadin meyasa basuyi masu bayanin cewe akuyace ba, ae su basu son suffarta ba, iya namanta da suke ci ne suka sani,’ Sai da yayi mai isarshi parveen ma ta É—aura da nata faÉ—an akan dariyar da suke yi masu, sauran dai basu ce komai ba, RuÆ™o haris danish yai tare da taimaka mashi ya miÆ™e tsaye. Zuciyarsu Naufal a jagule suka ci gaba da tafiya, Rayuwarsu ta daji gwanin ban sha’awa, Ga cin dariyar kwa6ar su batul komai basu sani ba sai Angel tayi masu bayani, idan dare ya tsala gefen bishiya Danish Yake yi masu shimfiÉ—a, bayan sun kwanta Yabi su da barguna Ya lullu6e su, sannan ya shiga daji Ya samo itace ya haÉ—a masu wuta saboda sanyin Dajin, Tun da suka fara tafiyar nan Danish bai runtsa ba, Su kaÉ—ai suke Yin baccinsu, Baya gajiya dayi masu hidima, basu da matsalar komai Abinci har sai sun ture, Nama iri iri suke Ci na dabbobin da yake yi masu farautarsu, Ga kayan marmari availabe cikin Dajin, wasa wasa kusan Watansu É—aya suna tafiya babu alamun zasu taddo cikin gari, Lamarin Ya É—aga hankulansu, A haka ma Danish yana taimakon su ba tare da sun sani ba, Duk idan dare ya nutsa bacci ya É—auke su É—aya bayan É—aya ya ke É—aukar su Ya nutsa dasu Cikin dajin ya yi tazarar tafiyar awanni dasu, basu ta6a lura da hakan ba, duk don ya sauÆ™aÆ™a masu wahalar tafiyar, shiyasa ya ke yi masu hakan, don kuma su yi gaggawar barin Dajin, Don ya fara Jin alamun wani baÆ™on Yanayin a jikin shi, fargabarshi kada Giant’s heart É—inshi ta motsa batare daya Nisantu daga dajin ba.
*PRISONERS*
Dare Ya nutsa sosai suna akwakkwance suna bacci, Hasken Wutar Dake Ci Ya haskaka zagayen wurin da suke, yana a Zaune gaban wutar idanuwanshi akan shimfiɗarsu, Sai faman lumshe idanuwanshi Yake yi, ga dukkan alamu baccine yake ƙoƙarin fuskarshi.
Angel da ke a kudundune cikin bargo taƙi runtsawa duk don saboda shi, ta kasa samun natsuwa, Yaye bargon tayi tare da fitowa daga Ciki Ta miƙe tana miƙa ta nufi inda yake zaune, Tunkan ta ƙarasa taga yana gyangyaɗi Ƙiris Ya rage ya kifa kanshi Cikin wutar dake agabanshi da gudun gaske Ta ƙarasa tare da zubewa gefen shi saman gwiwowinta, da hannyenta biyu ta tallabo fuskarshi tana bin shi da kallo, Sam ya gaza buɗe idanuwanshi sunyi mashi nauyi, rungume kanshi tayi saman kirjinta, idanuwanta suka ciko tab da ƙwalla, tsananin tausayinshi take ji.
“Danish muje mu kwanta,” muryarshi Æ™asa Æ™asa ya furta mata”bazan iya bacci ba Angel idan har ba barin Dajin nan mukayi ba, Ina jin fargabar wani abu ya same ku ta silar rauni na” Æ™ara Æ™anÆ™ame shi tayi a jikinta”In sha Allah ba abunda zai same mu Danish, Allah Yana atare damu, Kuma Inayi mana addu’a, Kada kaji komai kazo mu kwanta, rashin yin baccin zai Iya ja maka wata matsalar da bana fata” A hankali ya zagayo da hannayenshi saman waist É—inta, kafin ya lumshe idanuwanshi. Jin shiru bai Æ™ara motsi ba yasa tayi tunanin ko baccin ya É—auke shi ne, Kiran sunanshi tayi”Danish” amsa mata yai”Na’am” cikin kulawa tace dashi”nayi tsammanin ka fara baccin ne, pls kayi bacci Danish, inaso ka huta, bana so kana wahala” daÉ—in murya yake ji acikin kunnuwanshi, har baison intana magana tadaina, Yafi son taita yi mashi surutu.
“Danish naji ka yi shiru baka ce komai ba”? Har saida ta fidda rai da zaiyi mata magana tukunna taji yace”Angel ni wannan ba damuwata bace, i ave told u duk wahalar da zanyi indai akan ku ne bana gajiya, ke ce Æ™warin gwiwar da nike da shi Angel ” murmushi tasaki idanuwanta akan Kitson zanan dake akanshi,
“FaÉ—amin me ka ke ji akaina? sannan Meyasa kake Æ™aunata? Ta yi maganar tare da ÆŠaura yatsun hannunta saman kanshi, tuntuni ta ke son ta kwance mashi kitson da akayi mashi a prison don bata son ganin shi da kitso kamar mace tafi son ta ganshi a Namijin shi.
“Nikaina bansani ba” amsar daya bata kenan,
ÆŠagowa yai da kanshi tsinin hancinsu Ya haÉ—e jikin na juna, Hasken wutar dake cine ya haskaka fuskokinsu
Hakanan Taji gabanta na faɗuwa, ganin launin idonshi na canza mata, duk tabi tasha jinin jikinta, ƙwarjini yayi mata da sauri ta kawar da idonta gefe ɗaya
“Abu É—aya nake fargaba a duniyar nan! Shi ne ace za’a raba ni da ke!” Dawo da dubanta tayi akan fuskarshi, jaddada mata maganar shi yai”Zan iya komai a wannan lokacin,”
“Maganar raba ni da kai ma bata taso ba Danish, dani da kai tamkar anta da jini ne, mutuwace kaÉ—ai zata Iya raba Æ™aunar dake a tsakanina dakai, Amma agidan duniya bani da madadinka” kalamanta sun É—an sanyaya zuciyarshi,
“Ina tsoron ranar da zaki Canza min, duk da bana kawo hakan araina, Angel wani zai Iya Æ™wace min ke, kinga ni bani da komai da zan iya faranta maki da ya wuce kaina” Muryarshi araunace yai maganar.
ÆŠaure mashi fuska ta yi “Danish zaka Iya bari wani ya Æ™wace maka ni”? Girgiza mata kai yai alamar a’a, ya Æ™ara da cewa”Sai inda Æ™arfi na Ya Æ™are, ”
Lumshe ido ta É—an yi calmly ta furta “Yadda muka sha wahala atare Danish, Haka nake so Mu ji daÉ—i atare, Bani da abokin rayuwar daya wuce kai a faÉ—in duniyar nan, Kaine mallakina, masoyi na har abada, ta ya ya kake tunanin zan iya canza ma ka? Ai kaine nake tsoron Ka canza min idan mun shiga Cikin gari, saboda nasan mutane da yawa zasu dinga rububinka saboda kyawun Da Allah yayi maka, Sannan bansan su wanene Iyayenka ba, amma inaji araina ba Æ™ananun mutane bane yadda kake da kyan nan da izza É—abi’unka sak Irin na Æ´a’Æ´an HamshaÆ™an masu kuÉ—i ne, Ni ko ka ga ba Æ´ar kowa bace, Mahaifina É—an Jarida ne kuma ya rasu ma, ” Idanuwanta acike tab da Æ™walla tayi maganar, Æ™wallar na gangarowa saman kuncinta yai saurin sanya tongue dinshi Ya lasheta, nan ta ke ta ji yanayin jikinta ya fara canzawa.
“Ni bani da iyaye Angel, Ki daina yi min maganarsu bana son ji, ke ce uwata kuma kece ubana, Kece gatan da nake dashi, Idan ina dake bani buÆ™atar kowa,” muryarshi a kausashe yake yi mata magana, Ta fahimci bayason zancen Iyayen shi da take yi mashi.
“Meyasa bakason Inayi maka maganar iyayenka? Danish Salsabeel ya faÉ—amin tun kana jariri aka sadaukar dakai, Naji raÉ—aÉ—i jin hakan acikin zuciyata, sai dai Ni bazan Iya yankewa iyayenka hukunci ba, Kada ka manta sadaukarwar kurkukun Æ™addara ba dole sai iyayenka ba, zai iya yiwuwa ba sune suka sadaukar dakai ba, wata’Æ™il ma basu da masaniyar kana araye….” bai bari ta taÆ™arasa maganar ba yai saurin toshe mata bakinta da tafin hannun shi”Is ok, Kije ki kwanta dare Yana Æ™ara yi,” maÆ™e mashi kafaÉ—a tayi”Idan Kaga na kwanta toh muna atare da juna ne,”kafiya ta sanya mashi ya rasa ya zaiyi da ita, A Æ™arshe dole Ya haÆ™ura Ya Æ™yaleta, kwantar dakanshi yai saman Æ™irjinta, Taci gaba da kwance mashi kitson kanshi, Kafin bacci Ya É—auke su saida ta warware kitson duka, A manne da juna suke ta sharar baccin su, Karo na farko da ya fara runtsawa Acikin Dajin❗❗❗
*Boss Bature✍️ Mu haÉ—u gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
Post a Comment for "Kurkukun Kaddara Book 2 Page 9"