Kurkukun Kaddara Book 2 Page 12
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E12_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._
*GIDAN ÆŠAN IYA*
Gaba ɗayan su sun Hallara a bakin Entry hall na shiga palourn gidan, Mommy da Mami sun yi matuƙar yin kyau cikin shigar Lace, Zahra da Aneelerh sai Abie da Uncle ɗan Iya sun yi shiga ta alfarma, Bakomai ne yasa su fitowa ba fa ce tarbar Su Hajiya adama, A ƙagare su ke da ganin baƙin nasu, badajimawa ba su ka kira Aneelerh awaya su ka sanar da ita cewa sun shigo garin abuja, har ta tura masu da addrress ɗin gidan.
Ƙarar Horn ɗin motarsu ne Yasa kowan nan su Sakin fuskarshi, da sauri mai gadi Ya fito daga ɗan ɗakin sa, Ya je ya buɗe masu gate.
A hankali DanÆ™areriyar Motar uncle abdallah Æ™irar Kia optima ta kunna kai cikin gidan kai tsaye ya nufi wurin Ajiye motocin su, bayan yai parking É—in motar, Ya fito daga ciki fuskar nan É—auke da annuri, ya É—auki wankan shadda gezna, Æ™afafuwanshi na asanye da patent leather shoes launin Shaddar shi, Æ™amshi ta ko’ina.
Zagayawa yai ta other side ɗin motar ya buɗe ma Hajiya adama ƙofa, ƙafar ta ta fara zurowa nan take Zahra ta ɗan zaro ido tare da kallon Aneelerh, murmushi gefen fuska Aneelerh ta sakar mata don ta fahimci abunda ya sa zahra mamaki, wato tsadar High hills ɗin dake ƙafar Hajiya adama.
Zahra ta ƙware wurin sanin farashin Kaya, A kunne ta yi ma Aneelerh whispering
“Surukar ki Ta ji naira yasin, Takalman Æ™afarta kalar na saratu obinna ne” girgiza kai Aneelerh ta yi ba tare data tanka mata ba.
Lokacin da Hajiya Adama ta ƙara sa fitowa daga Cikin Motar ba ƙaramin tafiya ta yi da imaninsu ba, saboda tsabar wankan kece rainin da ta ɗauka na tsadadaddan Swiss cord lace launin brown mixed wit yellow, Riga da zani ne ta daura, kanta yasha ɗaurin ɗan kwali, sarƙar wuyanta da awarwaron hannun ta, da zabbanta duk na zinari ne, ta yarfa mayafin kayan saman kafaɗarta, babu make up a saman fuskarta zallar kyan da Allah ya yi mata ne, Hajiya adama akwai kyau ga diri.
Kallon abdallah ta yi fuskarta É—auke da murmushi, da hannu yai mata nuni da surukansu da ke a tsaye suna fuskantar su
“mu je ko?” Sai lokacin ta lura da su, tafiya suka soma Yi a jere tunkan su Æ™araso Zahra take ta faman ingiza kafaÉ—ar aneelerh
“ki je ki tarbo su,”
kunya ta hana Aneelerh zuwa, har saida suka Æ™araso, Abie Yana dariya Ya ruÆ™e hannun Abdalla suka fara yin gaisuwarsu ta manya”Marhaban marhaban lale surukai na gari, Sassannun ku, kun sha hanya, ku Æ™araso ciki” Ya ja hannun abdallah, Mamie da hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su É—auke da murmushi, bayan sun raba jikinsu, Ummi ta miÆ™e mata hannu suka gaisa a mutunce”Sannu da zuwa Hajiya, mu shiga daga Ciki” ta yi maganar, tare da jan hannun hajiya adama wadda idonta ke akan Aneelerh, sai faman noÆ™e kai ta ke yi,
“Kunya kamar bafullatana, Ni kaina da nake bafullatana Bani da kalar kunyarki,” da zolaya hajiya adama ta yi maganar, Yayin da su ke shiga cikin babban falourn gidan, daddaÉ—an Æ™amshin turarensu ya gauraya da sanyin A.c.
A saman soma mai mazaunin mutum uku Mami da ummi da hajiya adama su ka zauna, Abie da Uncle ɗan iya su ka zazzauna saman 2 sita, Aneelerh tana zaune saman one sita, Yayin da zahra ta ɗan zauna saman hannun sofa ɗin da Aneelerh ke zaune, sai faman sakarwa juna murmushi suke Yi, Gaisuwa ta musamman suka ƙara yiwa junan su cikin girmama juna da mutuntaka.
Uncle É—an Iya Yana faman washe baki Yace”Abdallah Kai ne ka koma haka?gaskiya mun daÉ—e bamu haÉ—u ba, tun lokacin da ka fito daga cikin mota, idanuwana su ka yi tozali da kai sai da gabana ya faÉ—i araina nace ina muka samu baÆ™in Bature, Abdallah hutu ya zauna maka daga kai har Hajiyar taka kun yada zumunci ko in ce mun yada zumunci Allah dai ya shiryemu” dariya suka saki gaba É—ayan su.
Ummi tace”Ya gajiyar tafiya? Nasan Kun jigata sosai, tafiya daga jos zuwa abuja ba abune mai sauÆ™i ba, kun ma yi Æ™oÆ™ari dana ganku da kuzarin ku”
mami ta É—aura da cewa”Alhamdulillah mun gode ma Allah da ya kare mana ku ya tsare mana ku har ku ka Æ™araso Lafiya, wannan abun farin ciki ne agare mu, gamu ga surukanmu, mutane masu Æ™ima da daraja, muna Æ™ara yi maku barka da zuwa” Maganar Mami ta yi matuÆ™ar faranta zuciyoyinsu.
Musamman Hajiya adama har saida ta ɗan saki murmushin da ya bayyana jerarrun fararen haƙoranta.
A tsanake tace “A gaskiya ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba, ni dama tun da muka fito daga cikin mota raina Ya bani munzo gidan mutunci da karamci musamman da naji gidan Uncle É—an Iya ne Masha Allah, Fatan mun same ku lafiya” atare suka haÉ—a baki”Lafiya lou Alhamdulillah”
Uncle abdallah ne ya soma yin magana cikin dattako da halin girma
“Mun jin daÉ—in samun ku cikin Æ™oshin Lafiya, Abun farin cikine wannan kuma muna godiya da irin tarbar da muka samu, Ina yi mana fatan kamar yadda muka haÉ—u anan, Ubangiji Allah Ya haÉ—amu A gidan aljanna alfarmar Annabi muhammad SAW, kusan atare suka haÉ—u wurin furta kalmar SAW
“Yakamata mu fara yiwa annabi Salati” Abie ne yai maganar, tare suka É—aga hannuwansu bayan sunyi salati ya ci gaba da jero masu addu’o’i Suna amsawa da ameen ameen Bayan ya kammala, Uncle É—an Iya ya wurga idon shi kan Aneelerh da ke ta faman sakin murmushi tana noÆ™e kai
Jin Muryarshi tasa ta É—ago da ido tana kallon shi
DaÆ™uwa ya sakar mata”Ungo nan, jira ki ke sai mun ce ki je ki gaishe da surukan naki? yarinya sai ka ce jinin fulani” Tsuntsirewa su ka yi da dariya gaba É—ayansu, Yadda yai magana yai matuÆ™ar basu dariya hada Aneelerh, Da sauri ta miÆ™e daga saman sofa ta nufi Hajiya adama daga Æ™asa saman carpet ta zauna gefen Æ™afar Hajiya adama, muryarta Æ™asa Æ™asa ta furta”Sannunku da zuwa, Ya gajiyar tafiya, ya kuma aka baro mutanan can” É—aura hannu hajiya adama tayi saman kafaÉ—ar Aneelerh
“Lafiyalou daughter in-law Fatan na same ki Lafiya”
Aneelerh ta amsa da lafiyalou, kafin ta matsa gefen uncle abdallah Ta gaishe da shi, da fara’a ya amsa mata
Bayan sun gama gaisawa da aneelerh, Zahra ta gaishe dasu, suka amsa mata
Kafin daga bisani, Mami tace”bismilla mu shiga ciki, Ku huta kada mu Cika ku da surutu, ” ta faÉ—i hakan ne don tasan yanayi na matafiya yafi buÆ™atar hutu, MiÆ™ewa su ka yi Mami da Abie na agaba Hajiya adama da uncle abdallah suna abiye dasu, wuce abie yai da uncle abdallah zuwa É—akinsa, Itama mami ta wuce nata É—akin tare da hajiya adama bayan tafiyar su.
Fira ta 6arke tsakanin Zahra da Ummi, a lokacin Uncle É—an Iya ya fita waje domin amsa kiran da akayi mashi a waya
“Wlh ummi takalman Æ™afarta kalar na saratu obinna ne, kinsan ko kuÉ—insu yakai dubu talatin” ÆŠan zaro ido Ummi ta yi” Tab Aneelerh ashe surukan ki Attajiran masu kuÉ—i ne, ai naga sarÆ™ar wuyanta da awarwaron hannunta duk na zanari ne, gaskiya kin taki sa’a, Yarinya mai Æ™ashin arziÆ™i,”
kwa6a fuska Zahra ta yi”ni kuma mai Æ™ashin tsiya ko”? ummi na dariya tace”Ni dai bance ba, kema ina maki fatan miji na gari da surukai na gari” yatsina fuska ta yi Æ™asa Æ™asa da murya ta furta”Suruki na gari kamar Owais, surukai na gari hamshaÆ™an masu kuÉ—i irin hajiya sarauta” Aneelerh dake zaune saman carpet ta miÆ™e ta koma saman sofa ta zauna
Ummi ta kalleta”nasan zasu buÆ™aci ganin jikansu, gashi ya tafi school till 6 na marece za’a tado su saboda lesson na Islamiya da ake Yi masu, ” zahra tace”Zan kira mahboob A waya ya je ya É—auko shi, Ni fa dama can banso aka sanya shi hada islamiyyar ba, ace kullum sai Æ™arfe shidda zai dawo gida, in banda weekend,”
Harara ummi ta É—an watsa mata”Sannu Uwarsa, islamiyarce ke ba ki so ya yi kenan sai dai na bokon” Girgiza kai zahra tayi”Ba haka nake nufi ba ummi, Yaron ya yi Æ™aranta brain É—insa ma Æ™arama ce ta ya ya ki ke tunanin zai Iya É—auke duk abunda aka koya masa”
Tun da suka fara magana aneelerh ta yi shiru tana kallonsu, acan ƙasan zuciyarta kewar baby junaid ce ta addabeta, maganar zahra tasa duk ta ji ba daɗi ita kanta ba ta son Yana kaiwa har ƙarfe shidda sai dai ba yadda za ta yi ita kanta tana so yaronta ya saba da karatun boko dana addini.
Tsawon lokaci suna fira a tsakanin su jefi jefi har aka fara kiran sallah, Abie da Uncle abdallah suka fito da haramar zuwa masallaci, a harabar gidan suka yi arba da uncle É—an Iya zaune saman Kujera Yana danna waya, Abie ya ce da shi Ya tashi su je masallaci, A nan suka jira shi ya shiga gidan ya É—auro alwala kafin ya dawo suka É—unguma zuwa masallacin dake a kusa da gidansu
Acan Cikin Gidan kowa ya koma É—aki domin yin sallar magrib, hankalin Aneelerh YaÆ™i kwanciya, Jin shiru mahboob bai dawo mata da yaronta ba, Gashi har an kira sallah. A zaune ta ke saman darduma hannayenta Biyu sama tana jera addu’o’i tasha dogon hijabinta.
Ba zato ba tsammani ta ji saukar mutun saman Bayanta, Ya Æ™anÆ™ameta Yana tiÆ™ar dariya”babyn mommy is back” Gabanta harya faÉ—i sai da taji muryarshi tukunna ta sauke ajiyar zuciya, haÉ—i da É—an sakin murmushi jin ya kirata da sunan da malamansu suke kiranshi wato babyn mommy, bayan ta shafa addu’ar, ta zagayo da hannunta ta ruÆ™o damtsen shi ta zagayo da shi tare da zaunar da shi saman laps É—inta, Kamar kullum fuskarshi duk jirwayen hawaye, uniform É—in jikin shi riga ce fara sai wando red colour, daga saman rigar akwai Æ´ar coat launin Ja, kafin ya ta fi school saida ta gyara mashi sumar kanshi amma yanzu da ta kalli sumar kan nashi A hargitse ta ke.
Idanuwanshi luhu luhu ya furta”Mommy, kin ga banyi kuka ba yau ko? Ai kince in daina” smiling softly tace”jirwayen menene akan fuskarka” tai maganar tana nuna hawayen da indext finger dinta, kwa6e mata fuska yai”mommy ai ni bake nayi ma kuka ba, uncle mahboob ne da safe da zamu school, Ya cinye min chocolate É—ina da kika saka min a basket”
idanuwanshi cike tab da ƙwalla yai mata maganar, ranshi ya 6aci.
ÆŠaure fuska aneelerh tayi”Na rasa gane me ke damun mahboob, shi bai siya maka ba sai dai ya cinye maka? Tir wlh andai ji kunya”
“Mommy don’t worry, Ni ma ai na rama”
“Dame ka rama” da mamaki ta yi mashi tambayar, hannu taga ya zura cikin aljihun wandonsa, ya zaro É—an Æ™aramin box mai kyan gaske Ya nuna mata
“Menene wannan”? Shu’umin murmushi babyn mommy ya saki”pls mommy kada ki yi min faÉ—a, inaso yadda ya sani zubar da hawayena shima ya yi kuka, A motar shi na samu wannan, buÉ—e ki gani abun da ke a ciki” yai maganar yana miÆ™a mata box din, bayan ta kar6a ta buÉ—e akwatin, haÉ—aÉ—É—en zoben azurfa ne, na mata mai kyan gaske stone É—in jikin shi har Æ™yalÆ™yali Ya ke yi,
Jinjina kai aneelerh tayi”Lallai Mahboob Ya iya kashe na Æ´an mata kuÉ—i amma bai Iya kashe ma Æ´an uwan shi ba, dama irinsu babu mai cin moriyarsu sai mata, kowace mai sa’ar ce wannan Ya siyama zobe kuma daga gani mai tsada ne”
“Mommy daga ni sai ke, kada ki faÉ—a mashi ni na É—auka, Mubar shi yai ta wahalar nema shima Ya ji idan akwai daÉ—i” Cikin 6acin rai ya ke yin maganar.
“Babyn mommy, ai ni farin cikinka shine nawa, don haka kar6i box É—in nan ka 6oye mana shi cikin rigar pillow,” kar6ar zoben junaid yai da gudu ya nufi gado ya haye tare da ruÆ™o pillow ya zuge zip É—inshi Ya tura box É—in, abun mugunta ya samu sai faman sakin murmushi yake yi kamar gonar auduga
MiÆ™ewa ta yi daga saman sallayar, bayan ta cire hijab din jikinta ta tura a wardrobe, Baby junaid ta É—auka ta nufi toilet dashi, Wanka tayi mashi bayan sun fito ta É—auko mashi riga da wando na shadda, ta zura mashi kayan ajikin shi, ta feshe ko’ina na jikin shi da turare bayan ta kammala gyara mashi sumar kansa ta É—auke sa suka nufi Palour, kafin su Æ™arasa sai da ta yi mashi huÉ—uba akan ya natsu ya gaishe da kakanninsa kada ya bata kunya, ya amsa mata da toh, Lokacin da suka Æ™arasa palourn babu kowa duk suna a dining area sun hallara domin Cin abincin da aka shirya masu, dukkansu Ne a zazzaune saman dining chairs, zahra da Ana ke yin aikin zuba masu abinci.
Farin Ciki a wurin Hajiya adama baya misaltuwa, shima Uncle abdallah sai murmushi yake saki ganin jikan nashi, Yayi matuÆ™ar tafiya da hankulansu, tun daga kan yadda ya zuÆ™unna kamar wani babban mutun ya gaishe da su, Hajiya adama ta É—auke shi Tana shafa sumar kanshi tace”Masha Allah, Yaro kamar rainon turai, Jawur dashi” atare suka ci abinci, tana ci tana bashi abaki, Junaid an samu jikin Granny, Ya Æ™anÆ™ameta yana zuba mata shagwa6a shi ala dole ga jikallen Hajiya adama da uncle abdallah.
Bayan sun kammala Cin abincin, aka fara kirayen kirayen sallar isha’i, Mazan suka tashi domin zuwa masallaci.
Shigowa cikin kitchen Mahboob yai fuskarshi a É—aure babu annuri, Ana dake a tsaye bakin sink tana wanke kwanukan da aka 6ata, Jin motsin mutun yasa ta waiwayo don ganin wanene, ganin mahboob ne atsaye sai ta saki fuska tana faÉ—in”mahboob sannu da dawowa ashe kaine banji motsin shigowarka ba” Yamutsa fuska yai muryarsa agajiye ya furta”kin ban mamaki Ana, Yanzu hada ke aka haÉ—a baki wurin yin almubazzaranci? Sai ka ce gidan Obinna abinci har kala Biyar? Ina laifin ko shinkafa da wake ne adafa masu In yaso sai a yayyanka masu kayan lambu asama” ranshi a matuÆ™ar 6ace yake yin maganar, Fuskar Ana da alamun ruÉ—u take kallon shi
“Mahboob me kake nufi”? Hura mata hanci yai”magana nake akan almubazzarancin girka abinci da ku ka yi saboda surukan Aneelerh” dafe kai tai da hannu É—aya
“Pls mahboob ka daina magana kada wani daga Cikin su Ya faÉ—o kitchen É—in ba tare da sanin mu ba, bansan meke damunka ba, menene damuwarka idan an girka masu abinci kala Biyar? Ko sisin ka babu acikin kuÉ—in girkin” harara ya wurga mata tamkar Æ™wayar idon zata faÉ—o kasa, rai a6ace ya ce”Abar zancen, Zuba min abinci yunwa nake ji”
girgiza kai Ana ta yi kafin ta nufi dish rack ta ɗauko plate ta zubo mashi dambun shimkafa, Ta miƙa mashi, Matsiyacan kallo yabita da shi
“Shi kaÉ—ai aka girka? da mamaki akan fuskarta tace”yanzu ka gama zazzaga min masifar almubazzaranci na girka abinci Kala Biyar, yanzu kuma ka ke tambayata shi kaÉ—ai aka girka? Dalla ni kar6i plate if not shima zaka rasa ne”
fuskarta a É—aure ta yi mashi maganar, hakan ba Æ™aramin kayar mashi da gaba yayi ba, sassauta muryarshi yai”nifa wasa nake yi maki, dan Allah ki zuba min komai da aka girka yunwa nake ji, idan na gama cin abincin akwai wata kyauta da zanyi maki” magiya ya dinga yi mata daÆ™yar ya samu Ana ta zuba mashi abinci kala Biyar ta É—aura masa saman dinner table na kitchen Yana ci yana santi, Musamman da ya zo kan Farfesun ganda, duk ya bi ya susuce hada siÉ—ar hannu kamar É—an maroÆ™i.
Bayan kammala sallar isha’i tun akan hanyar dawowa daga masallaci Uncle abdallah yace da abie Yana so zasu wuce idan sun koma, abie yace ba zai yiwu ba, dama ba kwana zasuyi ba? uncle É—an Iya da ke atare da su Yace”Yaya ka Æ™yale shi, sai mu ga ta Æ™ofar da zai fita, Dama Hajiyar shi na cikin gidan dole shima Ya shiga, Haba Abdallah yanzu ku kwaso uwargajiya sannan ka ce zaku tafi? A wani masauki zaku sauka ne da yafi namu? Uncle abdallah yace”A hotel ne zamu sauka” ya 6oye masu cewa sunyi gida a abuja, Uncle É—an Iya na jin haka yace”ai da kuÉ—in hotel É—in da zaka bayar Æ™wara ka dunÆ™ule su ka bani sai ku kwana a gidanmu dan na fahimci kuÉ—in ne su ka yi maka yawa” dariya suka saki gaba É—ayansu suna tafiya suna Yin fira gwanin ban sha’awa, Bayan komawarsu gidan uncle adallah da abie suka nufi É—aki atare.
Hajiya adama na akwance saman gadonta, Har ta canza kayan jikinta daga Lace zuwa Rigar bacci, da har ta yi shirin tafiya tana jiran uncle abdallah ya dawo su tafi, sai ga mami ta shigo É—akin, ganin tana shirye shiryen tafiya yasa ta ce da ita ina zuwa tace ae zasu sauka a hotel ne, girgiza kai mami ta yi ki ma daina faÉ—in hakan don ba zai yiwu ba, ga gida kuma sai ku ce zaku kwana a hotel? Hajiya adama tace”bamu son mu É—aura maku nauyi ne, mami tace”babu wani nauyi wlh, idan ma kina tunanin ko dan saboda gidan Æ™aninsa ne, to ki kwantar da hankalin ki, gidansu ne su biyu, kusan ma rabi da kwata na abunda aka kashe a ginin da kuÉ—in abie ne, Allah ne bai nufa zamu dawo nan É—in ba, sai daga Baya da ya samu Æ™arin matsayi awurin aiki kin ji yadda akai muke zaune agidan, na faÉ—a maki ne don ki kwantar da hankalin ki, idan da kara ae gidan surukai gidan Æ´an uwana ne tun da anzama É—aya, Ga É—an jikanmu junaid ya Æ™ara mana danÆ™on zumunci”
maganar Mami ce tasa hajiya adama fasa shirin tafiyar, mami bata jima da fita daga É—akin ba Kiran uncle abdallah Ya shigo wayarta, ko da ta É—aga kiran sanar da ita yai game da fasa tafiyar su sai zuwa gobe, hankalin ta ya Æ™ara kwanciya, ba tare da 6ata lokaci ba ta canza kayan jikinta zuwa na bacci, tana shirin kwanciya, muryar Aneelerh daga waje ta katse ta, sallama tayi mata, hajiya adama ta amsa mata da wa’alaikum salam, Suruka ta gari shigo ciki mana’
cikin Jin kunya Aneelerh ta turo Æ™ofar É—akin hannunta É—auke da baby junaid, saukowa yai daga jikinta da gudu ya nufi hajiya adama tana dariya ta É—auke shi kafin ta zauna gefen gadon tana shafa sumar kanshi, ganin Aneelerh na Æ™oÆ™arin zama daga Æ™asa yasa ta katse ta da cewa”ki Zaune gefe na, Muyi fira” komawa gefen gadon aneelerh tayi
“Mommy barka da dare, Ya gajiyar tafiya”?
Hajiya adama tace”ai Gajiya tabi jiki tun da na ga jikana” shiru suka É—anyi kafin Hajiya adama ta ce”Ya haÆ™urin rashin da mu ka yi”? DuÆ™ar da kai Aneelerh ta É—anyi, a duk lokacin da aka yi mata maganar 6acewar su tajudden tamkar an fama mata mikin dake acikin zuciyarta ne, nan take hawaye suka cika idonta, Muryarta na É—an uwa ta furta”HaÆ™uri an gode Allah, muna ta binsu da addu’a,”
“Ko akwai wani abu da ku ke shiryawa ne game da 6acewarsu”? Jinjina kai Aneelerh tayi”Eh mommy, dama na jira ne sai kun huta mu yi magana…..” gaba É—aya Aneelerh ta kwashe komai dangane da tada zancen 6acewar su Uzair ta labarta mata, annurin da ta gani akan fuskar Hajiya adama ne Ya tabbatar mata da zata samu goyon bayanta,
“Kunyi tunani mai kyau surukata, Naji daÉ—in shawarar da zahra ta baki, Yarinyar tana da hankali, duk cikinmu babu wanda yai tunanin tada zancen, idan har akaci nasara silar shawarar da ta bada, Na yi mata alÆ™awarin kyauta ta musamman” Ba Æ™aramin daÉ—i Aneelerh ta ji ba, Mommy adama ta É—aura da cewa”In sha Allah zamuyi magana dashi abdallahn dangane da tada zancen, sannan zamu bada tamu gudummuwar, fatana Allah ya dafa mana, Ya dube mu da idon Rahma, Ya bayyanar mana da su idan suna a raye, ko da basa a raye da buÆ™atar muji meya faru da su”! Cikin girmamawa aneeleeh tace”In sha Allah zamuyi nasara mommy, saboda bana son in rasa surukai na gari irin ku” Sam batasan Ta furta hakan ba, Dariya Hajiya adama ta yi”Nima ai bana so na rasa suruka ta gari irin ki Aneelerh, domin kuwa zai yi wuya asamu tamkar ki,” cikin jin kunya aneelerh ta miÆ™e tana faÉ—in”Bari na kawo maki abun sha” bata jira amsarta ba, ta yi saurin Juyawa ta fuce daga É—akin, Bayan fitarta Hajiya adama ta dubi Baby junaid dake kwance saman Æ™irjinta, Ya tsareta da ido, tun da suka fara magana bai tanka masu ba, ya kasa kunne yana sauraronsu, sai yanzu ya samu damar yi mata magana
“Granny kinsan Angel” jinjina mashi kai tayi”nasanta mana, Inason Angel sosai” marairaice mata fuska yai tamkar zaiyi kuka”baiwar Allah Angela É—ina, Mommy ta faÉ—a min da ita da daddynta da daddyna sun 6ace, ni tsorona ma kada ace 6era ne ya cinye su ba….” Zaro ido Hajiya adama tayi can kuma sai ta tuntsire da dariya
“Granny, mommyna kusan kullum sai ta yi kuka saboda su angel, Æ´ar baiwar Allah, mami ta hanata Yin kuka amma bata Jin maganarta, sai da nayi mata faÉ—a, na nuna mata raina ya 6aci tukunna ta daina” sosai hajiya adama ke yin dariya, Sambatu iri iri junaid ke yi mata ba Æ™aramin nishaÉ—i ya ke sanyata ba,
“Gobe akwai school junaid, mu kwanta mu yi bacci” maÆ™e mata kafaÉ—a yai”Ina tsaraba na”?
“Nayi maka amma sai gobe zan baka, nafi so ka huta yanzu muyi bacci” amsa mata yai da toh mu jira mommy ta kawo mana abun sha ko? in mun sha sai mu kwanta,
Turo ƙofar ɗakin Aneelerh tayi hannunta ɗauke da cup of coffee asaman table ta ajiye mata shi, Godiya hajiya adama tayi mata, daga nan su ka yi sallama da junansu Aneelerh ta fuce,
Atare da junaid suka sha coffee É—in Bayan sun kammala, Hajiya adama Ta kwantar dashi ta tottofe shi da addu’a, sauka tai daga saman gadon ta nufi switch ta kashe hasken É—akin, kafin ta dawo ta hau gadon ta rungume jikallanta aÆ™irji, ahaka bacci ya É—auke su
****JOS CITY MUN WAYI GARI LAFIYA AGIDAN ALHAJI UBAID*******
zazzaune suke a saman dining suna Yin breakfast A tsanake shiru baka jin sautin komai saina cokulansu, kwas kwakwas kamar zasu fasa plates ɗin, sun natsu suna tura abinci a cukunnansu, Alhaji ubaid na sanye da Jallabiya Hajiya Laila dake agefensa arab gown ce a jikinta launin royal blue ansha uban make up, Alhaji musa ya ɗauki wankan tsadaddun suit sun zauna mashi, mutumin fa akwai kyau kamar shi ya tsara kanshi ya iya ɗaukar wanka ga aji, daga gefen shi Dr shureim ne cikin shigarshi ta gado wato Kayan larabawa, daddaɗan ƙamshin turarensu mai daɗin shaƙa, musamman turaren Alhaji musa fragrance ɗinsa na dabanne. A hankali ya ɗan ɗago yana duban shureim ya lura ba abincin ya ke ci ba, tun da suka zauna yake ta faman jujjuya spoon ɗin hannun shi acikin plate ɗin gabanshi, gyaran muryar da Alhaji musa yai mashi ce tasa shi ɗagowa ya kalle shi
Cikin kulawa ya ke yi mashi magana”meyasa bakasan cin abinci shureim? Na lura tun shekaran Jiya da nazo gidan nan baka ci wani abun kirki ba” Hajiya Laila ta É—an dakata da cin abincin fuskarta a yamutse take kallon alhaji musa aranta tace”ji wani ikon Allah ko’ina ruwanshi da cin shi da shan shi? Ni narasa gane shisshigin nan da yake yiwa shureim, mutumin da bai damu da shi ba, sai yanzu ne yasan da zaman shi’
Cikin sanyin murya shureim ya kalli uncle É—in nashi”ina ci mana, kawai ni nafi sha’awar abincin hausawa ne wannan baya min daÉ—i abaki” Alhajin ubaid yace”Meyasa tuntuni baka yiwa zainab magana ta girka maka ba? Kamar ba ka da bakin magana, komai naka ya zama na shiririta shureim so ka ke ka koma yaro”? shiru shureim yai shi kanshi haushin rashin Æ™warin gwiwarshi yake ji, ya koma kamar wani sakarai komai sai yadda akayi da shi.
“Kada ka damu Yayana, da zarar mun koma abuja zai dawo asalin Dr shureim É—in da ka sani ne, Kasan matata ta iya bada tarbiya zata gyara maka É—anka ya zama namijin gaske”
Wannan maganar ta Alhaji musa tayi matuƙar ƙona ran Hajiya layla, har dai tagaza jurewa
“Me kake nufi? Ni ban iya bada tarbiya ba kome”? Ko kallo bata ishe shi ba saima Ya É—auki glass É—in lemu mai sanyi yakai baki Yana kur6a.
“Haba layla, meyasa bakya iya 6oye fushin ki ne? Laifine don ya yabi matarshi? Harara ta wurgawa Alhaji ubaid tamkar Æ™wayar idon zata faÉ—o kasa
“bansan meyasa kake goya mashi baya ba, idonka ya rufe kwata kwata baka ganin laifin shi, wannan ba adalci bane” rai a6ace ta Æ™arasa maganar tare da buga table din, A fusace ta miÆ™e tabar dining É—in
MiÆ™ewa shureim yai da niyar yabi bayanta da sauri Alhaji ubaid ya dakatar dashi”dawo ka zauna” komawa yai ya zauna
“daddy bana jin daÉ—in hakan, kasan halina tunfil azal bana so inga ran wani daga cikin ku ya 6aci” Shureim ne yai maganar
“ka kwantar da hankalinka, In sha Allah zan sasanta tsakaninsu, Yanzu zan shiga wurinta in lallasheta” Yai maganar tare da miÆ™ewa yabar dining din bayan tafiyar Ubaid Alhaji musa ya É—ago ya kalli shureim
“You should start preparing, Ƙarfe shabiyu zamu bar jos, already nayi magana da pilot É—ina, bana buÆ™atar ka tafi da komai naka, Duk wani abu da za ka buÆ™ata za’ayi maka acan” murmushin yaÆ™e dr shureim ya É—an saki
“in sha Allah Uncle yanzu zan shiga ciki In Æ™ara shiryawa” amsa mashi Yai da toh, Kafin miÆ™ewar Dr shurem P.a ÆŠin Alhaji musa yai sallama daga wajen palourn, Hakan yasa shi saurin miÆ™ewa cikin takun izza ya nufi Æ™ofar fita daga palourn
Ajiyar zuciya dr shureim ya sauke, shi kanshi shakkar Alhaji musa yake ji, mutumin babu wasa a harkarshi.
*Boss Bature✍️ Mu haÉ—u gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
Post a Comment for "Kurkukun Kaddara Book 2 Page 12"