Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Kanwar Maza 51


 

Dariya ce ta kuwa kufcewa ammi, ta ce “A’a rumaisa wannan maganar dai taku ce ba tawa ba”

Takawa dai ko kallonta bai yi ba, dan ya fuskanci yarinyar ba ta da kunya sam.

“Amma dai ammi ai ni ban taÉ“a ganin maza suna shayarwa ba, shi kuma ya ce mini haka, kuma dai na ga shima Æ™irjinsa babu komai”

Ammi rasa amsar da za ta bawa rumaisa ta yi, can sai hankalin rumaisa ya É—auke daga kan maganar.

“Ammi” ta faÉ—a a hankali.

“Na’am umman sabir”

Rumaisa ta washe baki ta ce “Wayyo daÉ—i, ammi na ji daÉ—i, Allah ya amsa dukkanin buÆ™atinki, na fili da na É“oye ya biya miki buÆ™atunki na alkhairi, na ji daÉ—i da ki ka kirani umman sabir”

“Amin rumaisa, in dai kin ji daÉ—i, ina son ki din ga saka baban sabir a addu’a, Allah ya biya masa buÆ™atunsa”.

“To ammi, ai saboda ke zan yi masa addu’a ba dan halinsa ba”

“Subhanallah, meye da halin nasa?”

“Ba ki ga yadda ya tsaneni ba? Hmm baki san halinsa ba ne”

Wani ƙarfin hali sai rumaisa, mace da ɗan ta, amma tana faɗin ba ta san halinsa ba ne.

Ammi ta ce “Rumaisa takawa mutumin kirki ne, fiye da yadda ki ke tunani, kawai mutum ne mara son hayaniya da shiga sabgar mutane”.

“To ni dai saboda ke zan yi masa addu’a kawai”

“Yauwwa rumaisa, maÆ™iya sun saka shi a gaba, wai cewa aka yi shi ya kashe aisha ya yi tsafi da gawarta, kuma sabir ba É—an sa bane ba”

Ruma ta waro ido ta ce “Wai dama da gaske yasir yake, muna tafiya a hanya ya gaya mini, Innalillahi kam bala’i, to shi kuma yayi shiru” ta yi maganar tana Æ™are masa kallo.

Sai kuma ta sake cewa “To shine yayi kuka da aka faÉ—i haka? Na ga kamar idonsa yayi ja?”.

“A’a ba kuka ya yi ba, addu’a dai zaki din ga yi masa”

Ruma ta ce “TaÉ“, ammi kin san wani abu?”.

Ammi ta ce “A’a”.

“Nifa wallahi dan mutanen duniya sun tsaneni suna yi mini sharri, in dai Allah yana so na shikenan, kin ganni a unguwarmu ce mini ake Æ™anwar maza, wai idan na yi tsokana yayyena suna tare mini, eh wataran suna tare mini, idan aka koma gida kuma su hukuntani, har gida aka je aka cewa mama wai bani da tarbiyya, tun da Æ´an unguwarmu suka yi mini tambarin rashin ji na daina jin nauyin kowa. Idan na yi musu abun arziki ba a zuwa a gayawa mama ko yayyena, da na yi rashin ji, za su zo su faÉ—a. Ni kuwa tun da na gane haka na daina saurarawa kowa, idan na yi tsokana ta ko a zaneni, ko…..

Jin zancen nata ba kai ba gindi ya sanya yasir cewa “Bari mu tashi mu tafi”.

Ammi ta girgiza masa kai, ta ce “Baka ga hira muke yi ba, ina jinki umman sabir”

Ta sake gyara zama ta ce “Tun da na fuskanci Æ´an unguwar nan ba sa yaba mini a kan abun arziki, ya sanya na zauna a kan kalmar rashin ji, idan aka ce na yi abu bana jin shakkar in ce na yi ko kasheni za ayi, idan ban yi ba komai za ayi mini ba zance na yi ba. Allah kaÉ—ai nake tsoro shi ya halicceni kuma jin tsoronsa dole ne. Wallahi ammi a kan gaskiyata sai da a kasheni, kin san bala’in da na gani a hannun ‘yan bindiga kuwa? Hmmm ai wallahi idan nice shi, zan kalli duk wanda ya ce na kashe matata na ce na kasheta idan kana da alaÆ™a da ita ka nemi shaida ka kaini kotu.
Ba dai baba mai farin rawani ne baban Anty Aisha ba, kuma ya ce mini ya san baban sabir ba zai cutar da anty aisha ba, to wallahi sai na kalli uban kowa na ce masa na yi ɗin. Ai su yadda na fuskanci mutane, idan suka yi maka ƙage, ka yi ƙoƙarin kare kanka, to zasu yi ƙoƙarin su ga sun sake binciko wani laifin saboda zasu gane ka tsorata, yaya usy ya ce mini, na koyi rayuwa nikaɗai a lokacin da babu wanda zai taya ni ƙwatar ƴancina, sannan na fuskanci abun da yake bani tsoro, aikuwa na ɗauka, ai tunda na gane ƴan unguwa sun gane lagona su kai ƙarata gida mama tayi mini faɗa na fetsare, ka kai ƙarata gobe na yi maka abun ya fi na jiya, idan ka kawo ƙarata aka tambayeni na yi in ce eh, zaɓi ya rage a kasheni ko a barni da rai.
Wallahi ammi idan ya ce wa masu cewa ya kasheta yayi É—in, ya gani idan za a cigaba da takura masa, duk wanda ya damu ya kai Æ™ara, ko kuma tun da É—an sanda ne ya kamosu ya yanke musu hukunci, su faÉ—i yadda aka yi suka san kasheta ya yi, ko kuma ya kullesu ba rannan wata haka ta yi ba, wannan kwamishiniyar ba aka ce wani ya É“ata suna ba, aka kai su gidan yari, ko decoration of character ko me ake cewa oho dai”.

Duk da damuwar da adam yake ciki, sai da ya tattara hankalinsa yana sauraron rumaisa, duk da ba kallon in da take yake yi ba. Shi wasu lokutan har tsoro take bashi, ta wani fannin maganganunta a kan gaskiya suke, da maganar hankali da shirme haka take kwaɓa kayan ta.

Ammi ta ce “Waii, rumaisa an gaisheki, ban taÉ“a ganin yarinya irinki ba, ke kuwa ya Æ´an bindiga suka iya zama da ke?”

Ruma ta yi murmushi ta ce “Haka suka zauna da ni, amma na ci ubana ba Æ™arya ammi. Ni fa tun da ga kano aka É—aukemu da Æ´an bindiga, har kaza suka sai mini da na ce ina jin yunwa, suka nuna mini wata jaka, cike da bullet, har da bindigogi, shugabansu ne fa ya zo in da aka yi garkuwa da mu, ya sakeni ni da sabir, shi wanda ya sai mini kaza, ammi garin da na je, idan ka yi noma ba zaka taÉ“a ba sai Æ´an bindiga sun yi maka izini, ni na je na É—auki masara aka je aka gayawa mai gari, da nake a gidansa.

Da aka yi garkuwa da ni, baki ji abubuwan da suka faÉ—a a gabana ba, na ce idan na kuÉ“uta sai na faÉ—a suka ce kona faÉ—a a banza, la’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, na yi ta karanta musu, ba Æ™aƙƙautawa sai Allah ya kawo mini anty aisha, daga baya kuma muka kuÉ“uta ni da sabir”

Ammi ta yi wata irin ajiyar zuciya ta ce “Amma abun da mamaki, wannan wane gari ne haka?”

Rumaisa ta É—aga kai ta kalli adam, sannan ta ce “Na manta sunan garin”

Adam tambayoyi ne fal a ransa, amma girman kai ya hana ya tambayi rumaisa, gashi ammi ta fara taɓo abubuwa masu muhimmanci, amma rumaisan ta kauce taƙi magana.

Ruma ta yi wa sabir kiss, ta miÆ™awa ammi shi ta ce “Ammi, bari mu tafi, kar mu yi dare ba mu je gidansu Hauwwaliya ba”.

Ammi ta ce “To madalla, Allah ya tsare dan Allah ku gaida mamanku, ku jira bari na baku kuÉ—in mota”.

Ruma ta ce “A’a muna da kuÉ—i, na ga kaya na gode sosai da sosai, baba mai farin rawani ma, ya bani kaya har da kayan gara masu daÉ—i da zuma da nono, da kilishi na gode sosai”

Ammi ta takura ruma, ta basu dubu biyar suka tafi.

Bayan tafiyarsu ammi ta kalli takawa ta ce “Adam, dan Allah ne ka fuskanta game da yarinyar nan, ji yadda take magana kamar ana karanta mata?”

“Ni banga komai ba sai shirme da rashin nutsuwa a tare da ita”.

Ammi ta ce “No, maganganunta abun dubawa ne, a duk lokacin da duniya ta nemi juya maka baya, ka kama Allah ka nuna musu zaka iya rayuwa kai kaÉ—ai, kar ka yi Æ™oÆ™arin lallai sai an yadda da kai”

Ya numfasa ya ce “Ammi wannan shirmenta ne kawai na Æ™uruciya, da rashin sanin ciwon kanta, yaushe ta zo duniyar balle ta san me duniyar ke ciki, tana tunani ne a iya Æ´ar Æ™aramar duniyar Æ™waÆ™walwarta, bari na tafi masallaci “.

Ammi ta ce “Shikenan Allah ya taimaka”.

Sai dai maganganun rumaisa suka cigaba sa shiga suna fita a cikin kwanyarsa, kamar maganganun ta na bisa turba.

Rumaisa sai da suka je gidansu Hauwwaliya, ƙafar Hauwwaliya ta yi kyau sosai, suka din ga murna da ganin rumaisa, ana yin sallar magariba, Yasir ya tasata a gaba suka tafi gida.
A hanya yasir ya yi ta yi wa rumaisa faÉ—a a kan tsinannen surutunta yayi yawa, ko a jikinta tun da muradinta ya cika.

Bayan sallar magariba, Adam da kansa ya je gidansu Jabir, ya tarar da shi da Jamil suna tare.
Jabir ya ce “Ka gama jan ajin ka neme ni kena?”

“Jan ajin me fa?”

“Ai ka fini sani, ka ce zamu haÉ—u amma na yi ta kiran wayoyinki ka Æ™i É—agawa”

Adam ya ce “Ba Æ™in É—agawa na yi ba, kaÉ—aici nake buÆ™ata ne, abubuwa sun sha kaina da yawa”.

Jamil ya ce “Ai kai dama yanzu sai ana yi maka uzuri”

“Hmm baku ga abun da yake ta yawo a social media ba, game da mutuwar aisha? Wai yanzu rahoton cikin gidana shine labarin yaÉ—awa a media dan a É“ata mini suna”

Jamil ya ce “Ni kaina abun ya girgiza ni, na rasa yadda aka yi maganar nan ta fita a haka, tun É—azu ni da Jabir abun da muke tattaunawa kenan, yadda za a shawo kan matsalar nan, amma ya kake gani, me ka shirya gayawa duniya domin wanke kanka?”

“Ba ni da isasshen lokacin da zan É“ata wurin Æ™oÆ™arin wanke kaina a idon duniya, ina da abubuwan yi da yawa a gabana, kuma ba za a kawar da hankalina a kan abubuwan da na sanya a gaba ba, duk wanda yake ganin yana da wani Æ™orafi, ko son tuhumata a kan mutuwar matata, idan yana da shaida ya kaini kotu” yayi maganar yana jin kamar za ayi masa kallon wawa abun da ya faÉ—a.

Jabir ya waro ido ya ce “Yanzu kana nufin haka zaka zuba ido a cigaba da É“ata maka suna?”

“Idan sun gaji zasu daina, idan kuma basu gaji ba zasu cigaba, idan na cigaba da Æ™oÆ™arin wanke kaina, za su cigaba da Æ™oÆ™arin kaini Æ™asa, idan na tsaya a kan Æ™afata na cigaba da karÉ“ar duk abun da za’a ce kaina, wataran gaskiya zata yi halinta”

Jamil ya ce “Amma kana ganin hakan mafita ce adam? Duk abun da ya shafeka ya shafi masarautar garin nan ne fa kai tsaye”

Adam ya ce “In da nake godewa Allah kenan, atleast masarautar nan wani immunity ne a gareni”

Su da suka san Adam da saka abu a rai, da shiga damuwa sun yi mamakin yadda yau ya nuna halin ko in kula da wannan lamarin.

Jabir ya ce “To, bari mu ga zuwa yaushe wannan mafitar taka za ta kawo sauyi ga lamarin nan, amma a ganina kamar kasada ce hakan, Allah ya yi mana jagora”

Adam ya amsa da Amin, ya miÆ™e ya ce “Bari zan shiga gari na ga Bashir, gobe in Allah ya kaimu zai bar gari, ina da muhimman abubuwan da zamu tattauna”.

Jamil ma tashi yayi ya ce “bari nima na gangara gida, na gaida Alhaji, sannan na wuce gida sai sa safenku”.

Jabir ya ce “To Allah ya bamu alkhairi”

Kamar yadda Jamil ya faÉ—a, gida ya wuce ya je ha gaida mama da turaki, sannan yayi aniyar tafiya gidansa, Samha ce ta bi yo shi, tana kiran sunansa.
Ya tsaya yana jiran isowarta, ko sa ta Æ™araso, hannunsa ta ja ta ce “Mu je motarka mu yi magana” bai musa mata ba suka wuce motarsa, suka shiga.
Shiru ne ya É—an ratsa, daga bisani ya É—an numfasa ya ce “Ina jinki”

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce “A duniya bayan mama bani da wani kamarka yaya jamil, mama ta kasa fahimta ta, ban sani ba ko kai zaka fahimceni, domin kuwa kaine dai-dai da zamanin da muke ciki”

Jamil ya ce “Haka ne, ina saurarenki”.

“Yaya jamil game da takawa ne”

Ya dubeta ya ce “Takawa again, me kuma ya faru?”.

“Maganar nan ce dai ta shekarun baya, tun da Aisha ta mutu ina son maye gurbinta, na so na je wurin baba da kaina, amma sai na ga rashin dacewar hakan, ka taimaka yaya kai kaÉ—ai zaka fahimci halin da nake ciki”

“Wai ke samha ba zaki Æ™yal adam ba kamar baki da zuciya? Duk cikin tarin samarinki babu wanda zaki fitar ki aura sai shi dai?”

Kamar ta fashe da kuka ta ce “Da zan iya cire shi daga zuciyata da tuni na yi, dan Allah ka taimakeni yaya jamil”

Jamil ya É—an yi shiru sannan ya ce “Zan fara yi wa adam É—in maganar na ji mai zace”

Da sauri ta ce ‘A’a dan Allah kar ka gaya masa yanzu, turaki zaka fara yi wa zancen”

“To amma kin san magana yanzu ba zata yiwu ba, tun da haryanzu ana cikin alhinin mutuwar nan”

“Ohhj God, to sai zuwa yaushe kenan?”

‘dole ki yi haÆ™uri, lokaci ya É—an tura kaÉ—an”

“To shikenan na gode, ina saurarenka ka gaida gida ” ya jinjina mata kai, ita kuma ta buÉ—e motar ta fita, tana jin a jikinta kamar a wannan karon za ayi nasara.

Kamar wutar daji, haka Zancen mutuwar aisha, ya cigaba da zaga gidan jaridu, da kuma kafafen watsa labarai, yayin da ta ɓangarensa yaƙi cewa kowa komai, kuma yaƙi magana da kowane ɗan jarida.
A yau babu tsammani, mai girma turaki ya karɓi baƙuncin wambai da misalin ƙarfe tara na dare.
Turaki yayi mamakin ganin ɗan uwan nasa a wannan lokacin, amma ya ɓoye mamakinsa, ya karɓe shi.

Wambai ya ce “Na san zaka yi mamakin ganina a wannan lokaci, sai da ba komai ne ya kawoni ba, illa zuwa in sake tabattar da abun da kunnuwana suke jiye mini, kuma ka yi burus, ba ka ce da ni komai ba”

Cikin rashin fahimta, turaki ya ce “Meke nan kake nufi?”

“Maganar rasuwar Æ´ar wurinka aisha mana, ko kai ba ka jin jita-jitar da ke ta yawo a kan mutuwarta?”

Turaki yayi murmushi ya ce “Alhamdilillah, da kai da kanka ka ce jita-jita ne, nima haka nan na tsinci zancen”

“Turaki na zuwa na yi domin mu yi wasan barkwanci ba, gaskiyar lamari zaka sanar mini, gaba É—aya mutuncin masarauta na nema ya zube, martaba da kimar gidanmu adam na ta cigaba da rusata sa shi da uwarsa, wannan wane irin abu ne?”

Turaki ya girgiza kai ya ce “Na san mai É—akina ce ta je ta gaya maka wasu abubuwan, maganar da ke yawo a gari, tabbas aisha ta mutu a hannun ‘yan bindiga, amma ba adam ne sila ba, ko ya kasheta ya sha jininta ba kamar yadda maÆ™iya ke ta kwarmato, kuma yarinyar da aka tsaresu tare ta zo da yaron wurin aisha”.

“Turaki kana nufin goya masa baya wurin É“oye laifinsa, dan me za a ce a Æ™asar waje ta mutu a É“oye gaskiya, wannan banzan aikin da yake yi na shishshigi ga manyan Æ™asar nan da kawo Æ™arshensu, ai gashi shi zasu kawo Æ™arshensa, ko iya wannan labarin an yi mana mummunan tambari, a ce an samu babbar zuriya kamar ta mu da Æ™arya. Dan haka dole a hukunta adam, sai ya yi wa duniya bayanin yadda matarsa ta mutu domin wanke ahalinmu daga mummunan zargin tsafi da kisan kai, ga uwa uba ayar tambaya a kan yaron da ake ce nasa ne, na baku awanni arba’in da takwas, idan har bai yi abun da na ce ba, matakin da zan É—auka a kan sa ba zai yi muku daÉ—i ba.
Kai banda tsabar rashin sanin ciwon kai, kamar ba Æ´arka ba wane irin abu ne haka?”

Turaki ya ce “Da Adam da A’isha, duk tsatso É—aya ne, kuma Æ´aÆ´anmu ne, dukkansu…..

Bai Æ™arasa ba, wambai ya É—aga masa hannu tare da faÉ—in. “Ba nasiha nake buÆ™ata ko tunatarwa ba, martabar ahalinmu da sarautarmu nake Æ™oÆ™arin karewa, dan haka ayi abun da muka umarta, ko a ga ba dai-dai ba”

Turaki yayi ajiyar zuciya, ya bi wambai da kallo, da ya tashi fuuuu ya fice.

Yayi ajiyar zuciya yana jin wani irin matsanancin tausayin Adam.

Duk wannan kumfar bakin da wambai yayi, ya biyo bayan ziga da kuma famfon da Mummy ta je har gida ta yi masa tare da taimakon hajiya sauda, shi kuma kamar kullum ya hau kai ya zauna ba tare da bincike ba.

Rumaisa har islamiyya ta koma, in da malamai da ɗalibai suka din ga yi mata barka da arziki na kuɓutowa daga hannun ƴan bindiga, sai dai a wannan karon ma, duk yadda ƴan bugun ciki, suka so ta basu labarin abun da ya faru da ita ƙi ta yi, wasu har suna cewa rumaisa ta koma saliha.
Bayan tashi daga islamiyya, ta wuce gidansu habiba, dan tun da ta dawo ba ta je gidan su habiba, suka rungume juna suna tsalle a tsakar gida.
Daga bisani suka zauna suka hau hira, mamansu habiba ta zubo musu É—an wake, suka kewaye suna ci suna hira.

“Ruma ina yaya Aliyu ne?”

Ruma ta kalleta ta ce “Meyasa ki ke nemansa?”.

“A’a, tun a asibitin nan ban kuma ganinsa ba”

“To meye haÉ—inki da shi, to idan son sa ki ke yi, zaki dinga sai mini kayan daÉ—i kina bani”

Waro ido habiba ta yi ta ce “Astagfirullah, dan Allah ruma ki daina yi mini haka, baki san kirkin da ya yi mini ba lokacin da nake zuwa gidanku da ki ka É“ata, mai sunan baba yayi ta hararata, shi yake rarrshina ya dawo da ni gida”.

Ruma ta kwashe da dariya, ta ce “Allah sarki habibata, kamar ba nan muke kwasar dambe da ke ba, ke ni shawara zaki bani ma”

“Shawarar me” habiba ta yi maganar tana suÉ—e hannunta.

“Mutumin nan da ya Æ™wace mini jaririna, wai ya zan yi da shi ne in karÉ“o É—ana?”

“Wai Æ™wace jaririn suka yi gaba É—aya to saboda me?”

“Saboda wulaÆ™anci mana, kullum da tunanin yaron nan nake kwana nake tashi, babarsa fa cewa ta yi ta bar mini shi, amma ya Æ™wace mini shi. Habiba kin san in da kotu take? Ƙararsa zan je na kai, ba dama an ce zulai ta kai Æ™ara kotu alÆ™ali ya bata É—an ta ba, to nima kotu zan kai shi”.

Habiba ta É—an yi shiru ta ce “Tsoro nake ji ruma, kin san ba a wasa a kotu”

“Na sani, ai ba wasa zamu je ba, Æ™ara zamu kai”.

Habiba ta ce “To, a unguwar su babanmu akwai kotu, dama za ayi sauka a gidan, sai ki zo mu je”.

Ruma ta yi murmushi ta ce”Amma na ji daÉ—i habiba, Allah ya kaimu in sha Allah sai an bani É—a na, bari na tafi gida” ta miÆ™e suka fita tsakar gida suka wanke hannu, ta yi wa maman Habiba sallama sannan ta tafi gida.

Idan har da wanda za’a zarga a kan mutuwar aisha, to ba kowa bane ba face ni mahaifinta, domin ni na É“oye ainihin abun da ya faru, adam ba matsafi ba ne, bai kashe aisha ba, kuma bai yi tsafi da gangar jikinta ba, a madadinsa, ina mai baiwa al’umma haÆ™uri na É“oye haÆ™iÆ™anin gaskiyar abun da ya faru.

Mummy ta yi jifa da wayar hannun ta, bayan kammala karanta abun da turaki ya sanar da Æ´an jarida, ya wanke adam.

Ayshercool.

Post a Comment for "Kanwar Maza 51"