Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Jarabta 78


Wasa wasa yau sati biyu kenan rabonta da Khaleel, duktabi tai wani irin ga Mummy tabi ta tsangwameta wani zubin ma idan su Abba ko Anty Hindu nanan ne take dan sarara mata, jiya aka sallamo Farida amma dakinta takaita, tsakanin Farida da ita kuwa yanzu bakaman da bane suna magana bawai basayi ba amma dai bakaman daba, Farida bata tsaneta ba kawai dai tanajan jiki da itane dan duk idan ta dade tare da ita tuna da takeyi saitaji tanajin haushi, tariga tama Mk alkawari zataji sauki and forget d past, sabida son datake mai abinda take kokarin yi kenan yadawo daga lagos yaga ta warke rass takoma Faridan da, Son datake ma Khaleel wani irin sone da tanajin har abada harta mutu bazata denaba, saisa takedan nisanta kanta da Islam sabida batason tana ganinta zuciyar ta tafara kulla mata wasu abubuwa dazaisa Mk ya tsaneta again, komawane zata aura nan gaba batajin zata daina son Mk ba superman dinta. Idan har Abba ko Anty Hindu basa gidan to tana daki dan batason tama hadu da Mummy, Abba yakan cemata Khaleel yakira shi, Farida ma takan cemata yakirata taita wani jin dadi hakan bakaramin ciwo yake mataba dan baitaba kiranta ba Koda ta wayar Abba bane dagaske kenan rabuwan da ita zaiyi, daki take shiga wani zubin taci kuka abinta ta godema Allah, dan Maman Sadiq sun riga sun koma Abuja amma tanada number ta takan kirata da wayar Maman Miemie idan tazo aiki suci hira, sanan kafin su koma tabata wasu magun guna da kullum take sha dan koyau ma tasha da yogurt adaki abinta, hakadai tacigaba da maneji wani irin mugun kewan Khaleel take da nadamar abubuwan data fadimai dan tariga ta gane duk duniyar nan banda Abban ta shine mutum nabiyu dake sonta so na gaskiya.

Kwanaki sunja lokaci nata tafiya yau kimanin wata daya da kwanaki biyar kenan rabonta da Khaleel, yaukam zazzabin data tashi dashi ne yasa Anty Hindu da kanta ta fadanma Abba nan aka kira Dr, bayan ya dubata yace “maleria ne” magani yarubuta mata Abba yasiyo Anty Hindu tasa tasha, Mum dai zamanta tai afalo tana marking script ko agefen kwalanta, Farida kuma ta debomata abinci dan sosai tabata tausayi takawo mata. (har yanzu fa wanan son dake tsakanin su nanan kawai dai Son Khaleel ne matsalan two sisters dinan)
Wuraren 6 ta tashi na yamma tadanji dadin jikinta, hakan yasa ta shiga bayi tai wanka da ruwan dumi tafito dan pink gown dinta na gida tasa dake tsayama ta a gwuiwa tasaka dogon hijabin ta dake sharan kasa tai sallan la’asar jin anfara kiran magrib yasa tayi sanan tayi azkar din yamma tacire hijabin ta linke ta ijiye ta kwanta akan gado tana maida numfashi, gabaki daya duk tayi wani irin laushi ga jikinta har yanzu da sauran dumi, lumshe ido tayi har bacci yadan soma tafiya da ita sama sama taji ihun Farida daga kasa “oyoyo MK, oyoyoo” da sauri ta tashi ta zauna, kasa hakura tayi tadan mike tsaye tareda saka silifas tabude kofa kadan maganganu taji kasa kasa kaman muryan su Abba, komawa tayi ta zauna abakin gado gabanta na faduwa sosai, bude kofa akayi hakan yasa ta daga kai Farida ne tashigo dakin da gudu jikinta har wani rawa yake tana murmushi tace “Mk yadawo Islam kinga yanda yay kyau kuwa, laa banma bashi ruwa ba” da sauri tajuya tafita daga dakin, harara Islam tabi bayanta dashi jin wani irin kishi ya turnike ta saikace mijinta ne yazo taja tsaki, tashi tayi afusace taje gaban wardrobe dinsu wani ubansu soft material taciro blue da akabishi da zanen flowers gold, zama tayi agaban madubi ta chanchara uban kwalliyan da ita kanta batasan ta iyaba tasaka red janbaki tadan shafa lip gloss akai hakan yasa lips din na wani irin maiko maiko yana kyalli kaman sabon candy da aka gamayi, tashi tayi tabuga uban dauri sanan ta dauko turaren khumar da Husna ta bata na matan aure ta shafe jikinta dashi dakin yadau kamshi sanan tadan kalli kanta amadubi dudda tarame amma baihana kayan karbanta ba tareda fito da kyanta da dirin ta dan sun dan kamata sosai, takalmi tazira sanan tabude kofan tafito tana wani irin kamshi akan bene ta tsaya hango Farida datayi ta zauna akan kujeran dake kusa danashi tanata mai hira, ta wutsiyar ido ya hangota har wani irin ajiyar zuciya ya sauke sabida yanda yay kewan ta yawani juya mata baya yabiye ma Farida suna hira harda dariya, wani irin abune taji ya tokare mata zuciya kasa daurewa tayi takarasa sakkowa daga benen da sauri ta tsaya tana kallonsu, ganin duk sunmaki lura da ita babu wanda yace mata Kala yasa taji zuciyar ta na tafarafasa ai wlh yau saita nunama Faree nan Khaleel mijinta ne ehe, da saurin ta harda wani dan gudu gudun ta taje kaman daga sama tawani fada jikinshi ta kankameshi tana kukan shagwaba ahankali tace “Ya Khaleel nai kewan ka sosai” wlh ya tabbatar da inda yay alwala babu abinda zai hana alwalan karyewa wanan irin runguma haka damafa adaddafe yay wanan wata dayan a Lagos, wani irin kara shigewa jikinshi takeyi tana hahhade kirjinsu tare, kasa daurewa yayi ya sanya hannayen shi duka biyu yay cuddling nata tareda sakin wani irin sassanyar ajiyar zuciya, tashi Farida tayi tabar falon tanajin wani iri iri hakan yasa Islam takara bin bayanta da harara tana tura baki taredayin lamo ajikinshi tana shakan kamshin turaren dayake yi.
[7/2, 2:19 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Post a Comment for "Jarabta 78"