Jarabta 76
Saida ta cinye sanan ta ijiye take away a gefenshi tana kallon fuskarshi amma yaki kallonta komawa gefen Farida tayi ta zauna tana Satan kallonshi ganin wayarshi yake ta daddanawa abinshi, dan gyara kwanciya Farida tayi tace “what are u doing Mk” dago kai yay ya kalleta ya sakin mata murmushi yace “kinaso kigani?” gyadamai kai tayi, ya matso da kujeran dayake kai jikin gadon ya nuna mata wayar hakan yasa tadan matso da kanta tana kallon wayar game din ball yake bugawa hakan yasa tadanyi kara ashagwabe tace “nito ai ban iya wanan game dinba kamin bayani” dan gyara zama yay ya saci kallonta yanda take kallonsu kaman idanunta zasu fado kasa yace “kinga wanan shine goal keeper, ga defender, ga midfielders sune yan tsakiyan nan, ga referee shine mu hura wusur, sukuma linesman dinan suke assisting referee, ga strikers suke gaba” janye fuskarta tayi daga wayar ta kalli fuskarshi tace “haka kasan kan kwallo Mk” batare daya kalleta ba yay murmushi yace “best sport dina kenan” ahankali ta mike daga kan gadon zata fita hakan yasa Farida ta kalleta tace “ina zaki kizo mijin ki ya koyamana yanda ake kwallon tare” dan lumshe ido tayi dan sosai takeson danne hawayen dake zuwan mata sanan ta budesu tajuyo tace “namanta da abu a massallaci ne am coming” da sauri ta juya tafita, dan murmushin gefen baki yayi ya kalli Farida yace “ya karfin jikin?” murmushi tayi tace “Alhamdulillah na warware” tashi yayi yace “zan tafi saikuma gobe” da sauri tace “to kajira Islam din tazo saiku tafi” murmushi yay yace “baki da lpy, ai nace ta zauna ta kula dake idan kin warke sainazo na dauketa mu koma gida” sosai abin yamata dadi tace “thank u so much Mk bye” bye yamata yafita daga dakin yana waige waige yana nemanta, fita yayi yanata Kalle Kalle kozai ganta hango ta yayi karkashin wata bishiya ta zauna tanata share kwalla, kasa daurewa yayi ya karasa wurin kamshin turaren shi kadai taji ta dago kai tana kallon fuskarshi daure fuska yayi yace “lpy kike kuka ko bakida lpy ne?” girgiza kai tayi hakan yasa ya tabe baki yace “dama nazo nabaki takardar kine, dan rikemin” yay maganar yana mikama ta byro ya kai dayar hannu aljihu kaman zai ciro wani abu ba karamin racing heart dinta yake ba da kyar har wani irin runtse ido take tace “ta.. Takardar mene?” tsayawa yay da tura hannu aljihu yace “bakince na sakeki ba na auri Farida, am coming jirani anan kaman nabarta takardar a mota” , mikamata byro yayi yace “rikemin wanan bari na dauko takardar saina rubuta miki” bai jira mezatace ba yajuya yay hanyar mota, batasan mesaba amma wani irin kunci da bakin ciki da tsoro taji ya diran mata arai, yar da byron tayi a wajen ta juya da sauri harda dan gudu tai hanyar massallaci ta shiga bangaren mata harda jan kofan tana rufewa ta zauna kirjinta na bugawa sai zazzaro ido take.
Koda yadawo bai ganta a wurin ba bakaramin dariya yayiba harda rike ciki komawa mota yayi ya shiga ya tada yabar hospital din.
Sai bayan magrib ta koma ward din dakin ta shiga lokacin Abba da Anty Hindu da Mummy duk suna wajen gaishe su tayi, Anty Hindu tace tabi Abba su tafi gida ta huta tunda mijinta yace anan zata kwana gobe da safe tazo, Abba tabi da Mumy dan Anty Hindu ke kwana da safe kuma mumy tazo ta wuni.
Wuraren 9 na safe ta sakko shirye cikin doguwar rigan atampan ta na gida tadauko hijabi ta rike da Mumy taci karo tafito daga kitchen rike da kula a shirye zata tafi, wani mugun kallo ta wurga mata tace “ina zaki, karna naji kince asibiti, ba nace ki nisan cemu, nida ita bama bukatar ki Islam kirabu damu, wlh inhar na ganki a asibitin nan kome namiki kekikasiya da kudin ki” wucewa Mum tayi tafita daga dakin ranta abace ahankali ta sulale ta zauna akasan wurin tafashe dawani irin mugun kuka batasan ma meke mata dadi ba tarasa inda zata sa kanta, takai kusan minti 30 tana kuka gashi ba kowa a gidan sai ita, tashi tayi ta zauna akan kujera tai tagumi daga baya kuma ta kwanta tana ijiyar zuciya, sake tashi tayi dan tarasa meke mata dadi hijabin tasaka tafita waje ta zauna kan bencin me gadi tana kallon mutane daidai dake wucewa alayin nasu idanun nan nata sunyi fayau sun kumbura, wani dan yaro da bazai wuce 2 years ba tagani yafito daga wani gida dake facing nasu ya shiga hanya yana wasa da bindigar ruwan hanunshi ga mota na zuwa da sauri ta mike tsaye da gudu taje ta dauke yaron daga kan titin tanamai murmushi har motar ta wuce, yaron mai kyau dashi gashi dan lukuti tace “mesa kafito kai kadai waje”, daidai lokacin wata yar mata haka dabazata wuce 25 ba tafito sanye da dogon hijab.
[7/2, 2:18 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
Post a Comment for "Jarabta 76"