Jarabta 73
Bakaramin wahala Khaleel yabata ba dan wlh ta gurzu, tun tana iya rokonshi daya ya hakuri har takasa magana sai ajiyar zuciyar wahala take tana kuka, wuraren 3 ya saketa tafashe da kuka kasa kasa tana saukar da numfashi juyowa yay ya kalleta fuskar nan adaure yace “get out” da sauri ta dira daga gadon dan wani irin mugun tsoron shi taji tanaji anan kasa ta tsugunna tadau towel dinta ta daura tana goge hawayen dake zuba, sanan tafita daga dakin tanadan dingishi ta shiga dakinta bayi ta wuce direct.
Runtse idonshi yayi da karfi sabida yanda kukan ta ke taba rashin shiya rasa wanan wace irin jarabta ce, da kyar yatashi ya shiga bayi yadan dade sanan yafito ya tsane ruwan jikinshi da towel yasaka jallabiya yahau kan dadduma yafara salla. Da aka tada salla asuba ne yafito yawuce massallaci saida gari yay haske yadawo yawuce dakinshi ya shirya cikin shirin zuwa aiki yafito kofar dakinta yabude da sauri ta tashi zaune kan gado jikinta har wani bari yake sabida yanda taji wani irin tsoron shi daya shigeta bakinta har rawa yake tace “in ina kwana” bai amsa taba saima harara daya jefeta dashi yace “ki tashi ki shirya ina jiranki amota” barin wurin yayi so yake ya kaita gidan su ko tadan walwala, yasan idan ya barta a gida haka zata wuni tana kukane. Yakai kusan 15 minute amota ta glass ya hango ta tafito sanye da riga da zani na brown and yellow atampa tasaka brown hijab da takalmi da brown jaka fuskarta dadan hoda da kwalli sosai tamai kyau tana tafiya ahankali, bude kofar gaban tayi ta shiga ta zauna hakan yasa yaja motar batare daya cemata kala ba har gidan su, parking yayi ababban compound dinsu yafito hakan yasa tafito tana biye dashi har suka shiga gidan da sallama su, Ihsan dake falo dan dama yariga yakira Ammi yace suna zuwa suka taso da gudu suka wuce shi suka rungumeta suna ihu Ammi da Abba dake sakkowa dan rakoshi tayi zai tafi aiki tace “karku karyamin daughter bafa hankali cikakke gareku ba Ilham” sakin ta sukayi suna dan turo baki, murmushi tayi tazo gaban su Ammi kanta akasa dan bakaramin kunyan su takejiba tace “ina kwana Abba, Mummy ina kwana” dagota Ammi tayi tace “daughter ya jiki” Abba yace “kun iso lpy” murmushi tayi tace “Alhamdulillah” Ilham ne tazo tace “muje dakin mu Amaryan Bros” dan murmushi tayi suka riketa Ammi tace “kujata ahankali mana” shidai yana zaune a dining yadau apple yanaci yabisu da kallo dan ajiyar zuciya ya sauke ganin murmushi akan fuskarta, tareda Abba suka fita yacema Ammi zai biyo ya dauketa idan yataso daga aiki. Abinci Ammi tahada mata sanan takira Ilham ta sakko ta dauka ta kai mata sai nannan suke da ita sai wajen karfe sha daya sanan suka shirya badan sunso ba suka tafi school shima sabida test din dasuke dashi ne. Ita kadai suka bari adakin hakan yasa tai shiru tana tuna jiya wani zazzafan hawaye ne taji sun fara zubo mata, kofar dataji anbude da sallama yasa ta share hawayen da sauri amma Ammi tariga tagani tashi tayi ta zauna akan gadon Ammi kuma ta shigo ta zauna a gefenta tana kallon idonta tace “lpy daughter kike kuka menene?” girgiza kai tayi tareda kakalo murmushi tace “bakomi Ammi” hanunta Ammi ta rike tace “menene karki boyemin komi, ni mahaifiyar kuce un menene daughter fadamin wani abin yamiki?” girgiza kai tayi da sauri tana kokarin tsayar da wasu hawayen dake shirin zubowa ahankali tace “Farida ne batada lpy Mummy” da sauri Ammi tace “subhanallah tun yaushe?” “tun muna chan” cike da tausayi Ammi tace “oh Allah meke damunta?” fashewa tayi da kuka hakan yasa Mum ta shafa bayanta tace “bansani ba amma tanata tarin jini Abba yace bama tasan wanda ke kanta ba” “shine baisan ya kaiki tun jiya kuje dubiya ba, zaizo ya sameni ne, in sha Allah gobe goben nan zansa shi ya kaiki kuje ku dubo ta, dena kuka kinji tashi muje dakina kin zauna ke kadai awanan dattin dakin nasu” dan murmushi tayi dan ba tawani ga dattin da Ammi ke fadaba banda kayan sawan su dasuka tara akan gadon, tashi tayi suka fita daga dakin tareda Ammi sosai tasaki jiki da Ammi ganin yanda taketa janta jiki tabata wasu magunguna tasha sanan tahada mata wasu aleda dazata tafi dasu ta dinga sha da yogurt, Ammi ta kunna mata kallo wai dukdan tasaki jiki.
Bayan sallan magrib ya shigo gidan afalo yasameta dasu Ihsan suna bata wani labarin novel sai dariya take dan bama ta lura dashi ba, hada ido sukayi da sauri ta hadiye dariyar ta janye idonta daga nashi ganin yanda yake kallonta, daure fuska yayi dukan su suka gadaishi bai amsa suba yawuce dining dan yunwa yakeji sosai, warmer yabude yadebo potato porridge dayaji nama ya zuba a plate yasa spoon, Ihsan tace “Ya Khaleel Ammi na kiranka” daukan plate din yayi yawuce sama dashi, da sallama ya shiga dakinta ya zauna akan gadonta yanacin abincin, kallonshi tayi ta daure fuska tace “mesa bakakai Islam ta gaishe da yar uwarta ba” plate din abinci ya ijiye agefe baice komiba hakan yasa Ammi ta sassauta murya tace “haba son koma me Farida tayi yariga yawuce ai, so kake karaba su danka auri wanan, karka manta fa tare suka taso koma me yar uwarta tamata bazata taba dena sonta ba eh son, kai yanzu idan aka cema Ihsan ko ilham basu da lpy basuma san inda kansu yakeba yazaka ji eh?” shiru yayi hakan yasa Ammi tai murmushi tace “don’t be selfish, inaso gobe kubi jirgin safe kutafi yola” ahankali yace “Ammi aikina fa” “nadai goben, gobe ai Friday basai kudawo ran sunday ba, haba Son” dan murmushi yayi yace “shikenan naji” abincin shi ya dauka ya cigaba daci ya cinye, fridge dinta dake nan daki ta bude ta daukomai ruwa agora tabashi ya karba yasha sanan ya sauka kasa wanan karan basa falon massallaci yawuce yaje yayo Isha sanan yadawo tareda Abba suka shigo, afalo suka sami Ammi suka zauna sunata hira sai wuraren goma sanan Abba yacemai oya yatashi yadau matarshi sutafi, Ammi ta tashi tawuce sama, dakinta takira Islam din tabata abubuwa dayawa aleda sanan tamata addu’a suka fito har wajen mota suka rakata, Abba dakanshi yabude mata gaban motar ta zauna yarufe duk suka daga musu hannu jitayi kaman karta tafi sukabar gidan, amota shiru dukansu sukayi har suka kai gida tabude mota zata fita batare daya kalleta ba yace “ki shirya gobe da safe zamu yola” yafita daga motar batare dayajira cewarta ba bayanshi tabi ta shiga dakinta wanka kawai tayi ta kwanta.
Post a Comment for "Jarabta 73"