Jarabta 71
Dafe kuncinta tayi tana shafawa, jikinta har wani irin barbar yake sabida yanda taga fuskar shi bata taba ganinshi hakaba, nuna ta yay da yatsa cike da bacin rai, dawa ta irin kakausar murya yace “ni kike gayama magana haka akan wacce ta kusan kaiki lahira? Ni kike ma rashin kunya?” kasa magana tayi saima jada baya da tafara yi tana kuka sabida yanda taga idonshi ba karamin tsoron shi taji ya shige ta ba, wani irin kallo yamata abubuwan data fadin mai yana yawo akanshi juyawa yay yafita daga dakin tareda bugo kofar sabida tsabagen yanda ranshi yabaci.
Zubewa tayi a wurin tafashe da kuka sosai tafi hour daya tana kuka daga baya bacci yay gaba da ita anan kasan.
Dakin Ihsan ya shiga ya zauna tareda dafa kanshi yafi minti biyar ahaka dan rashin yay bala’in baci da kyar ya mike tsaye tareda fuzar da iska yawuce ya shiga bayi ya dauro alwala yadawo dakin yasaka jallabiyar shi daya dauko ya kabbarta salla.
Ahankali take bude idonta ganin gari yay haske yasa ta mike tsaye da dan sauri, cije baki tadanyi sabida zafin dataji ta bude kofar bayi ta shiga brush tafara yi sanan ta gasa kanta tai wanka ta dauro alwala tadan lumshe ido sabida yanda taji kanta namata ciwo, towel ta daura tabude bayin tafito hada ido sukayi yana sanye da jersey ya zauna abakin gado yana daure igiyan sport shoe din kafarshi, kallo daya yamata ya dauke kai tareda cigaba da abinda yakeyi kasa karasowa cikin dakin tayi ta tsaya a wurin tana wasa da yatsun ta wani irin shakkar shi taji tanayi karan fesa turare dataji yasa tadaga kai tadan kalleshi yana tsaye gaban mirror yana fesa turare ahankali tace “ina kwana” ijiye turaren yayi bayan yagama fesawa yajuya zai fita daga dakin batare daya kalleta ba yace “kintashi lpy” baijira mezata ceba yabude kofa yafita daga dakin, kofan tabi da kallo yanda yabuga kofar har cikin ranta saida taji ta runtse ido, wani irin kuka ne taji yazo mata tafara kukan da kyar ta shiru tawuce wardrobe taciro wata simple doguwar riga ta saka tadau hijabi tasa tai salla, ta dade zaune tana azkar daga baya tamike ta cire hijabi ta ijiye jin tanajin yunwa sosai. Dakin tafara gyarawa tass tafashe ko ina da turaren daki sanan ta shiga dakin Ihsan din nanma ta gyreshi tass sanan tawuce falo ta gyara dudda babu wani datti ta shiga kitchen din, shiru tayi tana kallon ko ina wani irin kuka ne taji yazo mata, Indomie da tagani kawai ta iya dauka da kwai daya ta dafa ta juye adan karamin plate tadau fork tawuce dakinsu tadan ci dan jitayi batada wani karfin cin abincin, magungunan ta dake gaban mirror tagani wani kuka takara ji yazo mata inda yana nan dashi zai bata da kyar ta mike tsaye ta dauko su tasha tahada da paracetamol duk tasha tafito da kwanon tazo ta ijiye ta kwanta akan doguwar kujera tana kallon TV ahaka bacci yay gaba ita. Wuraren 2 ya shigo gidan na rana ya dade tsaye afalo yana kallonta karfin yawuce ciki yayo wanka ya fito daure da towel ya zauna akan kujera yaja laptop dinshi booking flight yamusu dazai tashi gobe dan shima jitayi duk ya gaji da garin gwara ya koma Abuja kawai yafara aikin shi, karfe 11 nadare jirgin nasu zai tashi gobe mayar da laptop din yayi yarufe ya dauko mai ya shafa sanan yadau kayan dazaisa yafita daga dakin yakoma dakin Ihsan yay kwanciyar shi.
Post a Comment for "Jarabta 71"