Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Jarabta 67



Da sallama Farida ta shigo falon Abba ta zauna tareda dukar da kai kasa, Jaridar dake hanunshi ya ijiye agefe ya dago kai yana karemata kallo idan kaga yanda ta rame kaman mai wani ciwo, tai wani irin yaushi, wani irin tausayin tane ya shigi Abba amma hakan bai hanashi daure fuska ba ya kalleta tareda gyara murya yace “ina jinki” dago kai tayi ta kalli Abban ahankali tace “Abba dan girman Allah ka karamin lokaci wlh banda kowa har yanzu ne Abba, dan Allah” takarashe maganan kaman zatai kuka hakan yasa Abba ya kasa dauke idonshi daga kanta da hannu yamata alamun tazo hakan yasa taje gabanshi ta zauna duktai wani iri da ita ya kafeta da ido, hanunta har rawa yake ta daura akan kafarshi tawani irin fashe da kuka tace “Abba wlh na tuba na mugun yin nadaman abinda nama Islam, babu randa zanyi salla da bazan nema mata addu’a samin lpy ba, Abba dan Allah kadena fushin nan dani dan Allah kayakuri kayafemin ka kiramin Islam na rokesu suma” ta kife kanta akafarshi tana kuka hanun Abba dataji akanta yasa ta dago fuskarta ta kalleshi, share mata hawayen yayi dadan murmushi akan fuskarshi yace “nadade da yafe miki Farida komi yawuce” murmushi sosai tayi ta goge kwallar tace “nagode Abba” kanta Abba yasake shafawa yace “inaso kifadi mini gaskiya meke damunki maisa kika rame haka Farida, kar wani ciwon yazo ya kamaki, meke cinki araine” wani sabon kukanne yazo mata dukda yanda taso ta danne kasawa tayi tafashe da kuka sosai da kyar tai shiru Abba yace “inajin ki” wasu zafafan kwalla ta goge ahankali tace “Khaleel, Abba narasa ya zanyi nakasa cire sonshi azuciyana, nina rasa wanan wani irin sone, narasa yanda zanyi da raina, Abba please help me wlh zuciyata har wani zafi take kamar garwashi” sosai Abba yaji tabashi tausayi ya gyara zama yace “inaso kiyi azumi koda uku ne sanan kullum zan dinga tadaki da daddare kidinga kiyamul laili ki roki Allah yabaki ikon cin wanan jarabawan, haka Allah yake abinshi yakan jarabce ka da komi yaga yaya zakayi, so kidage kici wanan jarabawan karki biyema zuciyar ki ta kaiki ga halaka, kikoma ga Allah sai kiga Allah yassare miki matsala dake damunki, bari nabaki labarin Khaleel dinan kiji sabida kingane cewa auren nan nashi da Islam Allah ne kawai yahada, robone atsakanin su saisama har yazo garin nan suka hadu har sukai aure” nan ya gyara zama yabama Farida labarin Khaleel tiryan tiryan yanda su Abba suka bashi, ba karamin mamaki Farida taiba, bakin da Abba yay yasa tafito daga dakin jikinta duk asake.

Post a Comment for "Jarabta 67"