Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Jarabta 63




Wani irin hot romance yake mata kaman wani mayunwaci, sosai take kuka kaman zata shide hawaye ko kaman anbude pampo hakan yasa ya saketa tareda tashi ya zauna abakin gadon yafi minti biyar ahaka sanan yatashi ya shiga bathroom, da sauri tadau rigarta daya yar akasa ta saka tasakko daga gadon hartana neman faduwa tafita daga dakin da sauri, dakin Ihsan ta shiga ta kunna wuta kan gadon tahau ta kwanta agefen Ihsan dake bacci taja bargo ta lulluba kirjinta nabugawa sosai kaman zai fito.

Yadan dade a bathroom din daga baya yafito daure da dan towel a kwankwaso hanunshi Kuma rike da karami yana goge fuskarshi daga kai yay ya kalli gadon ganin batanan yasa yafita daga dakin falo yafara zuwa ganin bata wurin yawuce dakin Ihsan hangota dayay kan gado kusa da Ihsan tawani lullube da bargo har lokacin jikinta bai dena rawaba yasa yadan saki karamin murmushi maida kofar yay yarufe musu yakoma dakinshi.

Ihsan ce tafara tashi ganin Islam kusada ita yasa abin yabata mamaki tashi tai ta shiga bayi ta fito daure da alwala sanna ta tashi Islam din tace “jekiyi alwala” Ahankali ta tashi daga kan gadon ta shiga bayi Ihsan kuma takabbarta salla, bayan ta idar tai azkar sannan tafita danta daura musu breakfast afalo suka hadu da Khaleel sanye da jallabiya yadan dafe kanshi da sauri tace “Ya Khaleel bakada lpy ne” dan yatsine fuska yayi sanan yace “just headache” “ayya sorry, Ya Khaleel inaso natafi fa ance munada test a school next tommorow” zama yay akan kujera tareda jinginar da kanshi yace “maisa yanzu kike fadamin to” komawa tayi cikin kitchen din tabude drawer tace “nima jiya da daddare wata course mate dina take fadamin damuke chatting” dan girgiza kanshi yayi jin yanda ciwon ke damun shi yace “okay bari naduba in akwai flight yau da daddare ko gobe saina miki booking” tashi yay daga kan kujeran ya shiga ciki kofar dakinsu ya bude ganinta akan dadduma yasa ya shiga dakinsu laptop ya dauko yafara searching flight to Nigeria luckily yasami wanda zai tashi yau by 10 nadare dan babu gobe shiya mata booking sanan ya ijiye laptop din akan kujeran yatashi yahau kan gado yaja bargo yadan rufe kafanshi so yake yay bacci sabida yanda kanshi ke kwankwasa cikin kankanin lokaci bacci yay gaba dashi.
Sanye da hijabin Ihsan tafito ahankali tabude kofar ta shiga dakin nasu ta mayar ta rufe kadan kadan take tafiya ganin bacci yakeyi, wajen wardrobe taje ta bude kayanta tagani agefe agoge hakan yasa taciro wani doguwar rigar atampa dasauran abubuwan dazata bukata ta rufe sip din sanan ta juyo ahankali tadan daga kai ta kalleshi yanda yake saukar da numfashi ahankali yasa takafe shi da ido anya tataba kallon Khaleel haka kuwa, Jan kafa tayi tadan matso jikin gadon kayanta data rike ta ijiye agefe tasa hannu taja bargon tadan lullube shi da kyau sanan tadau kayan tajuya tafita daga dakin adakin Ihsan ta shirya sanan tafito tasameta afalo atare suka karasa girkin.

Post a Comment for "Jarabta 63"