Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Jarabta 61


61 & 62

Yafi minti biyu ahaka sanan ya saketa ahankali yana kallon fuskar ta dan taki yarda su hada ido, murmushin gefen baki yayi sanan yadau teddy yarike tareda rikemata hannu daya yace “let’s go” ahankali ahankali take tafiya yana binta ahaka har suka fita daga dakin hasken wuta bau data gani awajen yasa ta daga dayar hanunta taka kokarin kare fuskarta dan tadade rabonta da haske, sai kakkauda kai take, daukarta kawai taji yayi hakan yasa ta kalleshi afirgice, gira daya ya dagamata hakan yasa tadanyi murmushi tamaida kanta ta kwantar akan kirjinshi, ahaka ya dinga tafiya yana kallon fuskar ta harya fito da ita sanan yasata acikin mota Ihsan nata musu dariya sanan ya koma ciki asibitin ya karbo magungunan yafito ya shiga gaban motar mai motar ya tada suka tafi, sai kallonta yake ta madubin kanta ta daura akan shoulder Ihsan dake nunama ta wani game datake bugawa, ajiyar zuciya yadan sauke sanan ya maida kanshi yana kallon hanya. Agaban gidan su mai taxi yay parking Ihsan ta fito tabude mata kofa ahankali ta fito ta tsaya satan kallonshi karaf suka hada ido yana kokarin bama mai taxi kudi da sauri tadan dauke kai kaman bashi take kalloba, akwatin su Ihsan taciro daga bayan mota shikuma ya karaso wajen zai dauketa ta girgiza mai kai kaman zatai kuka, hannunta ya rike yasa key yabude kofar suka shiga ciki, ko ina agyare tsaf tsaf sai kamshin room freshener dakin keyi, dakinshi ya bude ya shigar da ita Ihsan kuma tawuce dakinta. Akan makeken gadon dake dakin dayaci zanin gado fari da bargo fari ya zaunar da ita sanan ya kunna na’urar dake sanya daki dumi sabida sanyin garin, bayi ya wuce ya shiga ya dauro alwala jin ana kiran sallan magrib dan anguwan akwai massallaci, fitowa yayi daga bayin yana kokarin warware hanun rigar jikinshi daya nannade sabida alwala dayay ya kalleta yace “bari naje massallaci, kema tashi kije kidauro alwala ki salla” fita yay dadan saurin jin antada, a kitchen yaga Ihsan na kokarin dafa abinci hanyar fita daga dakin yay yace “kibar girkin nan zan taho da takeaway” kashe gas din Ihsan tayi ta wuce dakinta dayin salla dama wlh tagaji.

Da sallama ya turo kofar dakin ya shigo yana kallonta ganin ko motsawa batayi daga inda yabarta ba, maida kofar yay yarufe yakaraso cikin dakin yazo kusa da ita stool din gaban mirror yajawo ya ijiye agabanta yazauna akai, hanunshi yakai yafara warware vail din kanta anatse yace “kinyi sallan?” girgiza mai kai tayi, karasa warware gyalen yayi ya ciro ya ijiye akan gadon yasa hannu yadaga habarta hakan yasa ta kallai murya chan kasa yace “kingaji ko?” gyadamai kai tayi akasalance dan batada karfi ko kadan, kafarta ya dauko ya daura kan cinyarshi yace “sorry, dazaran kinci abinci zaki sami karfi” takalmin ya cire ya ijiye akasa sanan ya dauko dayar kafar ya daura akan cinyarshi ya cire takalmin yana kallonta, ahankali ya ijiye kafar akasa sanan ya mike tsaye ya dauketa tadan tsorata dan bata zaci ita zai dauka ba hakan yasa kirjinta yabuga tana zazzaro idanun tana kallonshi atsorace, murmushi yamata sanan yajuya yay hanyar bayi da ita batare daya dena kallonta ba itama haka, Karan bude kofa dataji ne yasa ta janye idanunta daga nashi tai maza ta juya bayi taga ya shiga da ita, akan wani irin kujeran datagani abayin kaman bishiya ya zaunar da ita sanan yahada ruwa a bathtub maidan zafi sabida sanyin da akeyi sanan yadau goran sabulu ya tsayaya a ruwan ya rufe ya maida ya ijiye, wani irin kamshi ne ya gauraye duka bayin tashi yayi yadawo inda take zaune ya mikar da ita tsaye hannu yadaura akan sweater jikinta yana kallon fuskar ta yace “zokiyi wanka zakiji dadin jikinki” kokarin cire mata sweater yake hakan yasa ta daura hanunta akan nashi tana girgiza mai kai kaman zatai kuka, mayar da hanunta kasa yayi sanan ya karasa cire mata sweater ya wurga kan laundry basket da sauri ta tsugunna ta rungume kanta duka jikinta na rawa sabida shimi kadai ce ajikin nata, ahankali shima ya tsugunna ya shafa kitson kanta daya soma tsufa yace “bakiso kiyi wankan nekuma?” da sauri ta dagamai kai, dan murmushi yasake yi yace “okay tashi am going” juyawa yayi yafara tafiya hakan yasa ta mike tsaye tana goge yar kwallan daya zubo daga kai tayi suka hada ido da sauri ta tsugunna tana kakkare gaban rigar ta, dariya yay yajuya yafita I daga bayin, dadduma ya shinfida mata sanan ya bude wardrobe wani light half gown iya cinya haka yaciro mata mai spaghetti hand jane rigar tanada tauchi sosai dan cotton ce, yadauko mata hijabi da plain zani dan ta daura tai salla ya ijiye mata sanan ya kalli agogo ganin takwas da kwata yasa yafita daga dakin dan zuwa massallaci.

Post a Comment for "Jarabta 61"