Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

In Bani 56


Yace “D…Dil” murmushi Aadil yamai asanyaye yace “Bid” Aabid couldn’t believe wat he is seeing, ahankali yabude hanunshi alamun big hug dan d way he’s feeling right now happiness din ganin twin brother shi, Aadil as normal person jiyake kaman zuciyarshi zata fashe, da sauri Aadil ya shigo dakin yabude hannayenshi shima da sauri Aabid yataho sukai hugging juna so tight, Aabid sai hawaye yawani irin kankameshi yace “I love you Twin, I love you so much Hassan, I love y…” yakasa magana sai hawaye amma mara kara ta yanda Aadil dinne kadai zai iya jinshi, rungume dan uwan nashi yayi tsam ajikinshi yace “I love you more Twin, I love you so so much, I love you Hussain, am feeling somehow i don’t know wats wrong with my head inajin wani iri, did anything happen to me? ina Abie?” jin kukan Mami yasa da sauri yasaki Aabid ya kalli Mami data zauna akan kujera tana wani irin kuka mai tsuma rai she can’t believe Aadil yawarke bata taba sanin cewa zataga wanan rana aduniya ba dan tariga ta yanke tsammani, ahankali yakaraso yay kneeling agaban Mami yakamo hanunta yarike gam yana kallon fuskarta kaman zaiyi kuka yace “why are you crying Mami?” girgiza mai kai Mami tayi tadaura hannayenta akan fuskarshi tana tattabashi cikin kuka tace “Aa…dil” sashi tayi ajikinta ta rungumeshi a kirjinta tsam tsam tana kuka tadago kai ta mikama Aabid dake share hawaye shima hannu yana kallon su, da sauri yazo tahada su biyun ta rungume su ajikinta tana hawaye, big Mum ma kuka take takasa dena hawaye tana kallonsu, Baba Suleman ne kawai yayta maza bai zubda hawaye ba amma sun bashi tausayi da sauri big Mum ta share hawayen fuskarta tace “laaa Hamida, kai Aadil barinta kai awaje” sakin su Aadil Mami tayi jin an ambato Hamida da sauri ta tashi tsaye tace “dama tare kuke?” “eh harda ita aka sallama” da sauri Mami tai hanyar waje tabude kofa tafita, atsugunne taga Hamidan ta rabe abango ta tsugunna kaman wata marainiya dan tagaji da tsayuwa, da sauri Mami tace “Amatullah” dago fuskarta tayi ta kalli Mami asanyaye, da sauri Mami ta dagata ta rungumeta da sauri ajikinta, jin Hamida take har ranta bubbuga bayanta tayi tama kasa magana sabida yanda taji gabaki daya damuwarta sun kau matar danta da danta duksun warke, sakin Hamidan tayi tai cupping face dinta tace “muje ciki kihuta” shigowa sukayi tareda Hamidan Aabid yakafeta da ido dudda kanta nakasa bai samu yaga fuskarta ba but he’s still very happy ganin ta tashi takuma ji sauki, tashi Aadil yayi daga kan kujeran ya kalli Aabid yace “am sleepy Bid, zanyi wanka, let’s go to our room” hararanshi Aabid yayi cikin tsananin sonshi dawani irin kewanshi yace “dakina dai, kai dakin ka dana matarka daban danawa” kallonshi yayi kaman maison gane meyace hakan yasa ya maimaita maganan shi din yace “dakina dana matata?” sosai Aabid ya danne zuciyarshi dan yariga yay alkawari he’s now a changed man, ya kalli Hamida dake zaune kusada Mami tana wasa da yatsunta Mami na duba jaws dinta da aka cirema bandeji yace “Mami bashi matarshi suje suyi wanka su kwanta duk sun gaji” wani irin juyawa Aadil yayi da kyau ya kalli Mami dakuma yarinyar da Aabid yake cema ace tazo tabi mijinta suje su kwanta sanan ya sake kallon Aadil yanuna kanshi da yatsa yace “matata?” kafin Aadil yay magana Mami ta janye hanunta daga jaws din Hamidan tace “eh matar ka, Hamidar ka baka ganeta bane Aadil?” nuna Hamida yayi da yatsa daga sama har kasa yace “wanan yarinyar ce Matata Mami?” tambayar shi bakaramin dukan zukatan yan dakin yayiba hakan yasa kowa ya kallai, ahankali Hamida ta dago idanunta dasuka cika da kwalla sosai ta kalleshi shima ita yake kallo tunda yamata kallon farko nadazu daya tashi a asibiti sai yanzu ne yasake mata kallo from head to toe saikuma yay dan dariya sama sama irin dariyan mamakin nan daya karama fuskarshi kyau sosai yace “no, no, no Mami this gurl can’t be my wife, tayaya ma zan auri this kind of yarinya? Mami wai wat happen to me ne? Kodai are u guys joking? How can i be this thing husband?” yanuna Hamida kaman yana nuna kashi kanshi namai zafi yana kokarin tuno yaushe yama santa dahar ya aureta shidai yasan su Mami kowa adakin nan but ita wanan dake kama da aljanun ne zai aura zaiyi magana Mami ta dagamai hannu cikin kakkausar murya tace “enough Aadil” ta kalli Aabid da jikinshi yay wani irin masifaffen sanyi tace “wuce kutafi dakin naku tare” juyawa Aabid yayi Aadil yasake yatsine fuskarshi yabi bayan Aabid din yagaji sosai bacci kawai yakeso yayi, daga Baba Suleman har Big Mum jikinsu yay wani irin masifaffen sanyi Mami taidan murmushi tana kokarin danne zuciyarta ta kalli Hamidan da kanta ke kasa takama hanunta tace “tashi muje daki kinji daughter” kasa tashi Hamida tayi sabida yanda jikinta yay wani irin freezing saida Mami ta dagata, jikinta yay sanyi iya sanyi jin kanta take kaman ba itaba, Bin Mami kawai take har Mami ta shigar da ita wani hadadden daki ta zaunar da ita ta yaye hijabin jikinta tace “bari mucire hijabin kisha iska ko” gyadamata kai tayi tana kokarin maida hawayenta ciki Mami ta linke hijabin tace “bari naje nakawo miki abinci nazo nakira miki su Mama da Kaka ki gaisa dasu ko daughter na” sake gyadama Mami kai tayi ahankali, Mami tajuya tafita daga dakin tarufo kofan, jingina da bango Mami tayi ta lumshe ido tana dafe kirjinta, ko ita maganganun Aadil sunmata ciwo bare Hamida….

Mami na fita Hamida ta tashi da sauri tabude kofar bathroom ta shiga ta rufo ta kife fuskarta jikin kofar bayin tafashe dawani irin kuka mai tsuma rai, jikinta har wani irin rawa rawa yake, ita kanta batasan meke damunta ba but she just want Aadil, so kawai take ta rungumeshi, but ya tsaneta yanzu, saida taji sallaman Mami ta kwala mata kira yasa ta tashi ta kunna tap ta wanke fuskarta ta share fuskar da towel idanunta sunyi ja sosai, tajuya tabude kofa tafito kanta akasa taki bari suhada ido da Mami daketa kallonta tana observing yanayinta, zama tayi akasa Mami ta ijiye mata tiren abincin agabanta sanan ta zauna gefenta tasa hannu takama hanun Hamidan ta sauke ajiyan zuciya, ahankali takira sunanta. “Amatullah” “Na’am Mum” Hamida ta amsa da muryanta dayadan shake batare databari sun hada ido da Mami ba, ahankali Mami tace “everything will be fine, i promise you kinji” gyadama Mami kai tayi, Mami ta mika mata iPhone dinta tace “gashinan inkin gama ki kira kowa da kowa” gyadama Mami kai tayi ta karbi wayan, Mami tace “am coming”.

Post a Comment for "In Bani 56"