Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

In Bani 55


Fita daga dakin Mami tayi tawuce dakinsu Aabid din dantai magana da Aadil, sallama tai tareda tura kofan dakin Aabid kadai tagani zaune kan kujeran dakin daure da towel a waist yadaura laptop akan cinyarshi yana aiki gefenshi kuma dan karamin cup ne na black coffee dayake sipping kadan kadan yana aiki, kan gado kuma Aadil ne kwance sanye da white bathrobe yana bacci peacefully dan daga fitowarshi daga wanka yahau kan gadon tsabagen baccin dake damunshi, jin anbude kofa yasa Aabid yadago kai suka hada ido da Mami, hakan yasa yay dan murmushi yace “Mami na” hararanshi tadanyi tace “keep that system katashi kasaka kaya kafin nabatama rai kasan jikin ka baisan sanyi ko” murmushi yadanyi saikuma ya ijiye system din yana kallonta a shagwabe yace “Mami nagaji ne wlh kiwiyan neman kayan nakeji” murmushi kawai tayi ta shigo dakin tai hanyar wardrobe dinsu tabude tana kokarin fitomai da kayan dazaisa tace “bakaki aure ba, bama kasan amaka maganan aure, get ready bakariga kaga komiba nan gaba har takalmin ka kasa dauka zakayi sabida kiwuya” dariya yayi ya janye cup din coffee daga bakinshi yace “Mami na ai u are here xaki nemamin ko” zaro hanger dawani riga da wandonshi ke jiki bakake tayi tadan waigo ta watsamai harara tace “eh sabida ancema banda aikin yi kullum sai nemama kayan dazaka saka ko zantayi, common taso kasaka kayan katada dan uwanka shima yasaka kuwuce kutafi masallaci is time for magrib” tashi yayi ahankali kaman zaiyi kuka yataho wurin gadon ta mikamai kayan ya karba taja kunenshi, dan kara yayi yace “wash Allah Mami kin katse kunen” “tukunna dai duk randa nakara kamaka kai wanka baka tashi ka shirya ba ranan ne kunen duka zan cisge nasa amaka pepper soup dashi” tasaki kunen tajuya tafita daga dakin, kaman zaiyi kuka ya shirya tsaf cikin kayan ya feffesa turaren ya shiga bathroom yaje yay hanging towel din a hanger sanan yadawo yana kallon Aadil dake baccin shi bilhakki yana fitar da numfashi ahankali ahankali, karasowa yayi yana kallon fuskarshi yanda lips dinshi sukai ja sosai kaman mai zazzabi hakan yasa yataba wuyanshi jin ba zafi yasa ya dakamai duka acinya. “hey rascal” bude ido kadan Aadil yayi dasuka dan chanza kala sabida bacci yace “stop it Bid, am sleepy” hanunshi Aabid yaja yana murmushi yace “baka isaba wlh, time for magrib tashi jor” lumshe ido yayi agajiye yanadan turamai baki, kara jan kafarshi Aabid yayi yace “kaifa miskili ne, common tashi mutafi mosque lazy ass dude” tashi yayi ahankali yana kallon Aabid din dakemai murmushin keta, tashi tsaye yayi da kyar yana dafa jikin gado Aabid yace “yauwa jekayo alwala to bari naciroma kayan dazaka saka” gyadamai kai yayi batare dayace wani abuba yajuya ya shiga bathroom yanajin ciwa ciwan ciki kadan kadan, alwala ya dauro yafito kayan da Aabid ya ciromai irin na jikinshi ya shirya tsaf cikinsu bakaramin kyau sukamai ba kamanin su daya yakara fitowa kawai dai Aadil looks cooler than Aabid, kana ganin nature Aadil from facial look zaka gane bamai yawan son magana bane, while Aabid kana ganinshi kaga mai raha ga murmushi, turare ya feffesa ya zira takalmi,
Masallacin suka wuce, bayan magrib suka fito sukayo gida dakinsu suka wuce Aabid namai hira, Big Mum ce ta shigo dakin da sallama atare dukansu suka kalleta murmushi tamusu tace “yan biyun Mami kuzo yaya na kiranku” tashi sukayi suka biyota sukai wani wani babban falo da Baba Suleman ya sauka aciki, Baba Suleman ne zaune a hadadden falon sai Mami dake kan one sitter ta kafe Aadil din da ido kana ganinta kasan tana cikin damuwa, dayan kujeran Big Mum takaraso ta zauna akai kusada Mami hakan yasa Aadil da Aabid suka zauna akasa, ahankali cikin murya chan kasa irin na marason surutu dinan Aadil yace “gani Uncle” dan murmushi Baba Suleman yayi yace “masha Allah, magana nakeso nayi dakai Aadil, Baffa na Nigeria dole aduk inda Baffa bayanan nai representing dinshi, nasan inda Baffa nanan dole shine zaiyi maganan nan baniba, and banda haka dole nai discharging duties dina amatsayina na babba a family nan inaso na gyara komi kafin gobe, dan gobe nida Aisha mukeso mu koma Nigeria ku zaku zauna da mahaifiyar ku harsai tagama takaba saiku dawo gida, dama ciwon datayi bana wasabane yasa muka hadoku duka muka taho daku nan Egypt cikin yardan ubangiji ita tazo tafara samun lafiya kafin ku, Hassan!” yakira sunan Aadil da dan kakkausar murya alamun maganan dazaimai serious magana ce hakan yasa Aadil yadago kanshi yace “na’am uncle” gyara zama Baba Suleman yaya yace “naso ace gobe ne kafin mutafi da safe, alokacin kama kara samin lafiya da karfin jiki da kuzari da komima zanma maganan nan amma dole ce tasa dole nama maganan nan anan wurin akuma yanzu dan kaganmu dukan mu nan we cannot stand hatred dinka ma Amatullahi wato Hamida kodan yayane we can’t stand it” Baba Suleman yafada adan zafafe, dan lumshe ido Aadil yayi yabude ya mayar da kanshi kasa jin ankira sunan yarinyar dazu dinan, gyara zama Baffa yayi yace “dukan mu nan we were shock to see yanda dukka sanmu kakuma ganemu i guess ikon Allah ne yasanya hakan ya karbi addu’an mahaifiyar ka kuma datasha yima, Aadil you’ve been sick tundaga ranan da aka haifeka ma’ana shekaru talatin dasuka wuce na baya dayan watan ni…………” labari ya shiga bama Aadil natun lokacin da aka haifeshi dakomi da komi da Abie yayi da auren shi da Hamida da komi har zuwa yau daya warke yakarake da. “bazamu taba zaunawa and sit back mu kalleka ka wulakanta yarinyar da iyayenta suka mana halacci suka dubi condition dinka batare dasun kawo komiba suka baka auren taba dandai kasamu lafiya sabida tarin jini daka dinga yi alikacin, bari kaji nafada ma kaganni nan Hassan koni bazan zauna nabama mahaukaci y’ata ba inda ina dashi ba inaji inagani, iyayen Hamida sunma wanan family abinda har gobe har jibi bazamu taba mantawa ba and bazamu taba yarda ka wulakanta musu y’a ba ka wulakanta amanar muba da muka karba da hannu bibbiyu ba, nasan all this labari yataho maka wni iri wani iri it will take time kai assimilating everything a brain dinka and accept everything but bamu da lokacin nan, this girl stay with you, ta kula dakai Aadil, sabida kai har koranta saida akayi daga gida daga baya baban Ra’is yakeban labarin bayan munje gidan su, mahaifinka yakusa kasheta ya shaketa ko anan kadai she had the chance tafadama iyayenta amma bata fadiba dudda marin da zagin datasha awurin shi but still ta zauna dakai, yanzu Aadil yarinya haka, yarinya tagari, mai natsuwa da hankali ga ilimin addini dakasamu amatsayin mata ce zaka ji sauki ka juyama baya babu ko kalmar godiya iyye?” Baba Suleman yay tambayan asanyaye yana karkada kafa yana kallon Aadil din babu alamun wasa akan fuskarshi yana jiran amsa, dan lumshe ido Aadil yayi zuciyarshi namai zafi sosai, yanajin wani irin sadness dabazai iya bayanin irinshi ba. “kanaji na kamin shiru Hassan kabani amsa” dan bude ido Aadil yayi idanunshi yay ja sosai ya kalli Baffa da muryanshi data dan shake yace “uncle bansont….” “karka fara kafadi kalmar nan Aadil karka kuskura” Baba Suleman yafada cikin zafi yana buga hanun kujera Mami ma ta watsama Aadil din mugun kallo hakan yasa yay shiru ya saukar da kanshi kasa Baba Suleman ya nunashi da yatsa yace “kadena ganin muna sonka muna nan nan dakai inhar kan Hamida ne gabaki dayan mu nan wlh saimun juyama baya, baka sonta kakeso kafadi? Wlh kozaka kwana dari kana fadin haka bazamu yardaba, bazamu taba yardaba Hassan, dan kaso Hamida tun baka hayyacin tun bakasan kokai wayeba, tun kwakwalwarka nata yara, kasota tunkafin ma kafara ganinta so check ur self sonta nanan tattare dakai yana cikin zuciyarka ka bincikoshi aduk inda ya shiga, the love u have for Amatullah natural love ne da banjin zai taba mutuwa ba aranka, you don’t expect us manya damu muzuba maka ido kai abinda zakayi ba at d end of d day mu maida musu da Hamida gida mucema iyayenta ka warkene shine kaga baka sonta karabu da ita, tayaya ma hakan zai faru iyye? Kamaida mu kananun yarane? Kagama musu da y’a ka cuceta yanzu katashi kace baka sonta Allah natuba wat if rabo yariga ya shiga tsakanin ku?” dago kai Aadil yayi ya kalli Baba Suleman dan sosai zuciyarshi ta tsinke da maganan Uncle, da yatsa Baba Suleman ya nunashi yace “katattara kawuce daganan zuwa dakinku chan, Mamarka ta riga ta kaita part dinku, chan dayan bangaren dazunan da muka tafi magrib dan masu aiki sun gama gyara part din, kabarma Aabid dakinshi dan kai ba gwauro bane kanada iyalinka, karka sake ka cutar da yarinyar nan, inka cutar da ita muka cutar Aadil, karike wanan aranka, Allah ya sanya muku albarka, Allah yabaku zaman lafiya, ya maganar mu kaikuma?” yay maganan yana kallon Aabid da kanshi ke kasa “dakainake” dago kai Aabid yayi yadan sosa kai ya kalli Mami harara Mami ta watsamai hakan yasa yace “very soon Uncle” gyadamai kai Baba Suleman yayi yace “nabaka nan da mamanku tagama Idda dazaran kun dawo Nigeria inbaka fito dashi ba zamu fitarma dashine gadai dan uwanka nan kwanan nan zamuzo suna” yay maganan yana dariya shiru Aadil yayi feeling sad sosai tashi Baffa yayi yace “ku wuce mutafi masallaci kana dawowa straight to part dinku dan matarka da mijinta zata kwana bazata kwana ita kadai ba” tashi sukayi duk suka fita daga dakin Aadil binsu kawai yake amma kanshi yay mugun zafi.

Hawaye Mami ta share hakan yasa Big Mum matsowa kusada ita tace “waiba kinmin alkawarin dena kukan nan ba eh Maryam” girgiza kai Mami tayi tace “na dauka matsalolina sun kau sai farin ciki yanzu da kowa yasami lafiya, jibi abinda Aadil yazo dashi kuma Yaya, Yaya yazanyi idan yadage baison Hamida? My heart can not take that, bansan yarabu da yarinyar nan idan yay haka ya cuceta sosai, mun cuceta sosai Yaya, wat if abu ya shiga tsakanin su Yaya? Bakiga yanda yake shishige mataba alokacin and is possible abu ya shiga tsakaninsu dudda yana abu kaman yara ai zai iya komi ko yaya, yanzu soyake ya maida yarinyar mutane bazawara? yazanyi da raina wlh nagaji da komi zuciyata namin zafi sosai zan….” hannu Big Mum ta daura mata akan baki tace “take it easy, dont think Much, auren Aadil da Hamida har jikokin su zaki gani trust me, ai real love baya taba mutuwa saidai yay bacci koya daskare, shi soyayya dakike gani kaman kakide ne wani zubin, time will heat d love kiga soyayyar ta tashi daga baccin datake yi, don’t be weak bakiga yanda Yaya yamai zafi zafi ba bakiga yakasa cewa komiba, kema haka zaki bishi inkikamai sanyi ne zaiyi abinda yaga dama, hot hot zakibi Aadil, kome kika sani ki dinga saka Hamida nayi just tayanda zaki hadasu magana kuma suna tare koda yaushe, ki koyamata kissoshi na mata, zaki gani nan da yan kwanaki kadan zakiga wonders badai namiji bane dole zai shigo hannu ballema Hamida yarinya son kowa kin wanda yarasa” gyadamata kai Mami tayi tace “shikenan Yaya”.
….

Post a Comment for "In Bani 55"