Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

In Bani 54


Durkushewa Mami tayi tana kuka kuka kaman zata mutu ganin yanda gini ya ruguzo kan Abie, Baffa duk shine mai dan kwari a cikinsu ya kalli su Suleman da muryanshi data dishashe yace “ku wuce kukai yaran nan asibiti we will take care of the rest anan” juyawa duk sukayi Aabid da kyar ya iya daga kafarshi yay hanyar gate dan motarshi na waje har wani jiri jiri yake gani, bude motar yayi ya kwantar da ita abaya yamaida kofar yarufe ya shiga gaba ya tada motar, su suleman ma suka shiga tasu motar bayan sun kwantar da Aadil abaya sukaja motar sukabar anguwan sukai wani babban private hospital dasu inda da gudu Nurses and Dr suka karbesu sukai placing dinsu on admission, Baba Suleman ne yace “VIP room mukeso asasu” nan aka kwantar dasu awani hadadden daki mai gado biyu Dr suka taru akansu ana kokarin saving their lives, ahankali Aabid yatashi daga jikin kofan inda yake leka yanda Dr’s ke battling suna kokarin cetosu ya zauna akan one of the kujera dake corridor da dakinsu yake ya saukar da kanshi kasa yadafe kanshi zuciyarshi na bugawa yanamai zafi, yanamai daci sanan yanamai yaji, for the first time a history din life dinshi yaji ya tsani life dinshi, ya tsani his life he hates who he is, yanzu dama cikin kudin jini Abie ya rainesu? Yasasu makaranta har ya karanci business administration, da blood money ya rayu daman? Thank God yanada aikin kanshi, yanada kampanin kanshi dayay establishing bayan yagama masters dinshi but dudda hakan d thought of yarasu yaci yasha yay karatu da blood money yakasa fita daga ranshi. “Astagafurullah” yafada sounding weak, he promised kanshi daidai da riga daya tak wanda Abie yasaimai shida Brother shi saiya cire ya kona ya zubar, komi na Abie daya saima shida Aadil saiya kona tass.

 

Dafashi da akayi yasa ya dago kanshi da kyar idanunshi sunyi jajir, Baba Suleman ne ya zauna kusa dashi yana kallonshi cikeda tausayawa yasan this is hard dole abin ya daki zuciyar Aabid da karfi. Murya chan kasa mai cike da calmness nason kwantar ma da yaro hankali yace “let it out Boy, let it out Hussain, Men cry too, am here for you, am here for you kaji” fadawa jikin Baba Suleman Aadil yayi yace “Uncle m…my….my father is is a ri…ritualist, he did all this thing to my brother, Uncle Abie, he feed us da bloodmoney, he cloth us da blood money, he did everything mana da kudin jini, Abie killed and ruin my brother’s 30yrs of life, Abie yakashe mini kannai n….” zaiyi magana Baba Suleman ya taushemai baki yana sharemai hawayen daya dake zuba nonstop yace “is okay, is okay Aabid, kaddara ce haka Allah yariga ya tsara rayuwan dan uwanka Aadil, ahaka Allah yariga yarubuta zaiyi shekaru talatin a duniya batare da yasan waye shiba, koda Abie baiyi komiba one way or the other saikaga something happen dazaisa yay rayuwanshi ahaka, now lets all hope for the best, muyi creating new beginning and new memories and let’s all forget d past okay, think of your Mum and think abinda take going through yanzu haka, wahala da dawainiyan Aadil tun yana jariri datasha kullum suna hanyan asibiti, sanan ga barin ciki har sau uku yaya kake tunanin takeji yanzu datasan dalilin? Ga kuma dan uwanka a asibiti shida matarshi yaya kake tunani takeji? Let’s pray murokan ma Abie gafara daga Allah kaddara ce, dama annabi yafada aciki hadisi cewa kowace alumma nada fitinarta yace fitinar alumma ta itace dokiya, kaga arayuwan nan wasu mutane can do anything for money, inhar dai zasu sami kudi they can do anything, arayuwar nan tamu tayau mutum ya kasance mai godiyan Allah, d little da Allah yabaka ka godemai and be contented saikaga Allah will give you more masu albarka, one shouldn’t be greedy da mugun son kudi, greediness dason banza can lead you to astray daga hakane zaka fara karban cin hanci which annabi yay hani akai yafadi ahadisi akan Allah ya tsinema mai bayar da cin hanci damai karba, yawan son kudi ma da mutane keso fitina ne, kudi kayane aka dan ranan gobe kiyama saikama Allah bayani akan each and every single kobo daka kashe, how? Tayaya ka kashe su ta hanya mai kyau ce kota hanyar sabon Allah ne sanan tayaya ka samesu ta hanyar halal ce, ta guminka ne kota hanyar haram, duksai kafadi ma Allah, saisa yakamata kowa kowani musulmi ya yawaita yin addu’a Ya Allah kabani dukiya ta halas, Ya Allah ka sanyama dukiyar Albarka sanan Ya Allah kasa na kashe su ta hanya mai kyau bata hanyar saboba, Allah yasa mudace kawai Aabid, Allah kuma yasa karshen mu tai kyau, Allah kuma ya kashemu muna musulmai sanan Allah ya ganar da dukkan musulmai dakeson kawai suyi kudi kota yayane kotahalin k’ak’a ne, sanan Ya Allah ya shiryi musulmai masu hali irin na Abie wayanda are willing to sacrifice koda mahaifiyar suce dandai kawai suyi kudi su sami abin duniya, wayanda zasu iya zuwa su sadu da gawa dan samin abin duniya, su sami kudi su sami na nunama jama’a ace wai wanan fa babba ne Alhaji ne motoci guda dari gareshi baya sati a nigeria yau yana dubai gobe yana china, Allah yarabamu da dukiyar dazata halaka mu, mu koma ga Allah kawai Aadil, is high time malamai sun tashi a tunatar sukuma tsawatar, kaga shi tunatarwa yana karkato da zuciyan mumini sanan yana kara samai tsoron Allah dakuma gujema kaba’ir, Allah yasa mudace, tashi muje masallaci muyi sallan asuba daganan saimu tafi gida dan akai Abdullahi gidan gaskiya, Allah ya jikanshi ya gafartamai yasa yahuta Allah kuma ya gafartamai kurakuran shi, May Allah forgive all his short comings” ahankali Aabid yace “Ameen” ya share hot hawayen daya zubomai deep down ko Allah yasani yanason mahaifinshi danshi shaida ne akan yanda mahaifinsu ke sonsu, sune komi na Abie amma wat can he do abu daya kawai zaimai shine ya rokamai gafara, yamai addu’a sanan yabude abubuwan sadakatun jariya wanda lada zai dinga kaimai kabari, saida Baba Suleman ya dagashi sanan ya iya tashi ko kadan baida karfi fita sukayi Baba Suleman da Muhammad suka rikeshi alwala sukayi sukai salla sanan suka fito suka shiga mota koda sukakai anguwan su mutane an cika fal tako ina, cikinsu harda baban Hamida da Abban su Ra’is dudda liman da Baffa sunriga sunce babu kyau fadin mummunan halin mamaci boyewa ake, addu’a kawai za’ama Abie saisa kosu baban Hamida ba’a fada musu gaskiyan abinda yafaru ba, banda limaman nan guda uku dasu babu wanda yasan zancen, ancedai wuta ce takama shine ginin ya zubo yafado kan Abie, sanan sukace musu antafi da Hamida da Aadil asibiti sosai su Aban Hamida sukai addu’a sanan sukai musu jaje aka dauko motar daga gidi aka daga ginin aka tattaro pieces din jikin Abie aka atattare awuri daya, rayuwan fa kenan! Saisa in this world d best thing to do shine kabi Allah koka samu kyakkyawan karshe, yau ina Abie dakeda kudi ghana masgo manya manya sama da dari na yan dollars? Ina Abie mai kampanin mota? Ina Abie maisa hadadden shadda dake kyalli yahau jeep yafita ina yake? Uban dukiyan daya tara yanzu sun hanashi mutuwa? Dukiyarshi ta taimakeshi? Ta amfane shi? Jama’ar musulmi mubi Allah mukoma ga Allah kar son kudi yarufe muku ido yasa kuyi sata, chacha, gambling, riba ta hanyar karban loan kabiya with interest and other ways, kisan kai, cuta, and many more, all kudin at d end of the day bazasu miki komiba bazasu tsinana miki komiba afarin kyalle za’a kaiki/ka, Allah ya gafarta mana kura kuran mu ameen yabamu ikon cin jarabawa dan no body is perfect, Allah saidai yasamu a aljanna dan rahaman sa badan aikin muba dan we are not doing enough.

 

Haka aka tattara Abie bayan an sallace shi aka kaishi makwancin shi duk dauriya da taurin zuciyan Aabid saida ya dinga kuka wata irin nadama ta shigeshi shima ya shiga tubanma Allah akan kurakuran shi, shan giya bin mata yay taubatan nasuha yama Allah alkawari bazai karaba, dawowa gida akayi ana amsan gaisuwa, Mama da Anty Lami da Kaka harda Zainab da Ihsan suma suka shiryo sukazo gidan gaisuwa ananta lallashin Mami da idanunta suka kumbura sosai babu wanda zai ganta dabazai tausaya mataba bayan sun gama aka kaisu hospital sukaje duba Hamida da Aadil danhar lokacin bacci suke bama asan ranan farfadowan suba.

 

 

***
_Bayan Wata Daya_

Yauwa yanzu labari zai fara dadi na zare Abie 

 

Ya Allah ya gafarta ma wayanda suka rigamu gidan gaskiya, Allah kasa mucika da imani.
..

 

Post a Comment for "In Bani 54"