Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

In Bani 40


Shigowa Anty Lami tayi ta tadata da kyar ta iya ta bude idanunta dasuka kumbura dan bacci bai dade da kwasheta ba ahankali ta tashi ta zauna tana sosa ido Anty Lami tace “yi sauri jeki dauro alwala kizo” bayi ta shiga ahankali bata wani jimaba ta fito daure da alwala komi atsanake takeyi dan ko kadan batada karfi tadau hijabin tahau kan dadduma tafara salla itakuma Anty Lami ta shiga bayin tahada mata ruwan wanka da turarukan da ake samata mai zafi sanan tafito taje gaban wardrobe dan ciro mata kayan dazata saka wani hadadden lace pitch tadauko an mata dinki riga da skirt ta ijiye sanan taciro undies din dazatai amfani dasu dukta ijiye ta juyo ta kalleta jinta sallame tace “yauwa inkin gama azkar din kiwuce bayi kiyo wanka ga kayan dazaki saka inkin saka sai zainab tazo tamiki kwalliyan” gyadamata kai tayi ahankali hawaye na taruwa a idanunta Anty Lami tawuce tafita, tana gama azkar din ta linke dadduman ahankali tana kara kallon dakin yanda dakin keda kyau sosai ta share kwallan daya zubomata da sauri tawude ta shiga bayin ahankali, tajima dan taji dadin ruwan zafin sosai kafin tafito daure da towel duk jinta take wani iri she’s not just happy, zama tayi ta shafa mai, sanan ta shirya cikin kayan tsaf dasuka mata kyau bana wasaba, sun kamata sun mata chass ajiki, shigowa dakin Ayush dasu Zainab sukayi suna ihu, Ayush tace “wo amaryan Aadil, amaryan malam Hassan, wanan glow haka aisai kisa angonki ya suma, zee yimata makeup” da sauri Zainab tace “to bari nadauko makeup bag din” Ihsan tazo da sauri tarike mata hannu tana murmushi tana kallonta tace “kinyi kyau sosai Anty Hamida” dan murmushi tamata hawaye na shirin zubowa Anty Ayush ta harareta. “wai kukan bai isabane” daidainan Zainab ta shigo dawata katuwar jaka tazo tafara tsara mata makeup, subhannallah tsarkiya tabbata ga ubangijin daya tsara wanan hallitan! bakaramin kyau Hamida tayiba kaman ka saceta kagudu, sai hotuna suke daukan ta ganin abin nasu bamai karewa bane suna neman su kara sata kuka yasa Anty Lami ta kadasu duk kowa yaje yay wanka dan yau zasu bar gidan nan sukai wanka aka cici gayu kafin Mami ta turo ma’akatan part dinta aka fara jera musu abinci kala kala sanan sukabar shashin da kyar suka tasata agaba tadansha tea da chips aka ccici abinci sanan suka sake gyara gidan ko ina na kamshin turaren yan maiduguri, haka suka wunin mata ranan har yamma jama’a sai shigowa suke suna dubata duk wanda yaga Hamidan saiyay mamakin kyawun matar Aadil din, yan gulma nayi suna cewa hala iyayenta kudi sukagani saisa suka yarda suka bama mahaukaci inba hakaba ina mahaukaci ina wanan shuwa arab din.

Bayan isha’i suka shirya tsaf zasu tafi bayan sunsa tasake wankan ruwan turare ansake mata hadadden gayu, kuka, kuka Hamida bana wasaba takeyi kaman ana yankata dan harda bubbuga kafa akasa hankalinta yawani irin tashi dansai yanzu ta yarda yes anmata auren dan gashi yan uwanta zasu tafi su barta bada ita zasuba, janta dakinta Anty Lami tayi tama yan uwanta da duk sukai wani iri sabida tausayin Hamidan alamu dasu tafi waje su shiga mota sanan ta zauna kusa da Hamidan dake kuka sosai takama hanunta tarike ahankali takira sunanta. “Amatullah” dago jajayen idanunta tayi ta kalli Anty Lami, ahankali Anty Lami tace “kindai tuna fadan da mahaifinki da mahaifiyar ki suka miki ko, still shi zan kara tunatar dake, karkice dankinga matsalan mijinki yasa kikimishi biyayya kokin bin umurninshi, a’a, koyaya yake aljannar ki na karkashin kafarshi, kome yakeso kimishi, komeye bayaso karkimai, ki rufama mijinki asiri sanan ki rike sirrin shi, matsalar mijinki matsalar kice, farin cikinshi farin cikin kine, kikuma dage damishi addu’a nasan koba yanzu ba, koba yauba watarana zai bude ido yay alfahari dake dan kin kasance mace data soshi takuma zauna dashi da lallurarshi, kidau auren ki amatsayin jahadin ki, ki rike Allah nasanki da karatun Alqurani da yawan azkar karki sakesu ki kara rikesu da kyau kinji, kina tare da yan uwan mijinki ne kidinga musu biyayya tsakanin ki da kowa should be mutunci, respect and peace kinji Hamida na” gyadamata kai tayi ahankali tawani irin fadawa jikinta tasaki kuka sosai mai tsumma rai bubbuga bayanta Anty Lami tayi tana murmushi danji tayi kaman zatai kuka itama kafin ahankali ta janyeta daga jikinta tana kallon yana take kuka take haki tace “ina zuwa bari naduba wani abu a kitchen dinki nai plugging abu” da sauri tafita daga dakin tai waje duksu Mami na tsakar gida suka sallama na mutunci sanan ta shiga mota bayan sun hada musu shatara na arziki suka tafi.

 

Ita kadai aka bari abangaren sai kuka take, kukan yaki tsayawa, sallama taji anyi a babban falon shiru tayi taki amsawa sai hawayen data cigaba da sharewa, shigowa Big Mum tayi da Baffa, sai Aadil dayaci gayu sosai cikin wata faran hadadden gizna yasaka hula tangaran dake mugun kyalli sai wani irin murmushi yake kaman anmai kyautan maka yana leka dakin kaman zaiga Hamidan da akace za’a kawoshi wurinta sai Suleman da Muhammad atare dashi dan tun safe ba’aga Abie ba, Suleman ya riko ledoji a hannu zama sukayi a falon Aadil sai murmushi yake yazauna kusada Baffa yace “grandfather where’s my Hamida?” kallon Big Mum Baffa yayi yace “shiga ciki kifito da ita” tashi big Mum tayi tawuce tai wani corridor kafin ta tsaya gaban bedroom din tai sallama ahankali tabude kofan sake lulube fuska Hamida tayi da mayafi tana kuka mara kara, ahankali big Mum ta zauna kusada ita ta dafata tace “kukan ya isa haka daughter na, ke yarmu ce bazamu taba cutan kiba kinji, taso muje Baffa na nemanki” tai maganan tana rike mata hannu da taimakonta Hamida ta sauko daga kan gadon tasa takalmi Big Mum takara lullube mata fuska da gyalen sanan takama hanunta suka fita daga dakin tunda suka shigo falon Aadil kewani irin kallonta tundaga kafa harkai dudda baya iya ganin fuskarta sai uban murmushi yake, taba Baffa yayi batare daya janye idanunshi daga kallonta ba yace “grandfather is that my Hamida?” gyadamai kai Baffa yayi big Mum ta zaunar da Hamidan akan kujera, gyaran murya Baffa yayi yabude taro da addu’a sanan yamusu wa’azi sosai mai ratsa jiki kafin ya kalli Aadil yace “she is your wife Hassan take care of her, don’t make her cry, always keep her happy be her companion, kudinga salla tare, kuci abinci tare and do everything tare, dis is your house and she is your wife keep her happy kaji” wani irin cute smile yayi dayawani irin karamai bala’in kyau ya gyadakai yace “I promise you grandfather i will keep my Hamida my wife happy, very very happy, but grandfather i want to see her face” kowa na dakin murmushi yayi Baffa dai saida yadan dara kafin ahankali yakai bakinshi saitin kunenshi yamai magana aciki wani irin murmushi Aadil yayi ya gyadama Baffan kai, Baffa ya kalli Big Mum yace “maida ita ciki saida safenku, Allah yamuku akbarka” dagata Big Mum tayi tamaidata daki tafito sanan su Baffa sukai hanyar kofa Aadil yadaga musu hannu yana murmushi sosai Big Mum sai dariya takemai suka fita wani irin tsalle yayi yadau ledojin da su Suleman suka tayashi dauka yay ciki dasu yana murmushi yana murna, ahankali yabude kofar bedroom din wani irin kamshi ne ya ziyarci hancinshi, shigowa yayi ahankali yana kallonta yanda har lokacin take lullube da gyale sai kuka take tana goge idanunta da gyalen maida kofar yayi yarufe yay wani irin raurau da ido ganin kuka take, ahankali yakarasa gabanta ya ijiye ledojin tsugunnawa yayi ta gabanta ya leka fuskarta yadaura hanunshi kan cinyoyinta yakira sunanta ahankali. “My Hamidah” cigaba da kukanta tayi tai kaman batajishiba dan wani irin haushin shi takeji bana wasaba, kaman zaiyi kuka yay wani irin rau rau da fuska kaman wani maraya yace “stop crying kinji” cigaba da kukan ta tayi kaman bada mutum yake magana ba hakan yasa ahankali ya mike tsaye yazauna gefenta yaja gyalenta yacire gabaki daya ya ijiye, hakan ya bayyanar da riga da skirt na wani material dake jikinta pink anmata hadadden dauri daya bayyanar da tukin gashinta ta tsakiya, wani irin kallo yabita kaman yaune rana tafarko daya fara ganinta gawani irin kamshi datakeyi kaman zai shide sabida dadi, jawota jikinshi da sauri.

Post a Comment for "In Bani 40"