In Bani 3
3….
Cike da fushi yawani irin daga hannu zai dauketa da mari daidai lokacin Kaka ta leko, da sauri tace “wlh katabamin ita Faruku Allah ya isa, nitama laifi bakaiba, tamin laifi kaitamawa dazaka fara hukunta? Wanan rapkeken hanun naka mai kama dana basamude zaka zuba mata salon ka nakasamin ita mugu mai zuciyar sojoji, cikata” takaraso wajen tana nishi ta janye hanun Faruk din daga jikin hijabin ta ta ingizata ciki tace “wuce ciki kijirani miskilan yarinya” cikin tsananin fushi Faruk ya fizge hanunshi daga na Kaka yace “dalla chan ki sakeni karki sama fararen kayana datti ni” da sauri ta kalli hannayenta tace “Allahu Akbar wlh babu dauda a hannuna fa Faruku, yi hakuri kaji dena fushin” ta kawo bakinta saitin kunenshi kaman zatai gulma tace “nafiso na hukunta ta dakaina ne, inna bari ka hukuntata aisai ka karasata baka ganta daban bane acikin yaran Sama’ila guda bakwai da Allah yabashi, kabarni da ita nasan maganin ta” hararanta yayi yajanye kunenshi yace “dalla ni kidenamin gulma a kunne, kuma wlh bazan siyomiki namijin goron ba” zata kamoshi yawuce yafice abinshi haba takama tana hararan bayanshi tace “chan ka karata, sojan banza sojan hofi yanda kakeda zuciya inna barka kashe wanan ja’iran yarinyan zakayi” tajuya tashiga dakin a zaune ta ganta akasa jikin dogon kujera tana wasa da yatsun ta, wani mugun kallo ta zuba mata tace “daga ina kike? ina uwarki ta turaki tun safe kikaje kika labe?” girgiza kai tayi tai shiru batare datace komiba, kwafa Kaka tayi tace “nikika maida wawiya ina miki magana kinmin shiru? badai uwarki ke bataki ba to wlh zan gyaraki ne, zan gyara miki zama Hamida, bari zaki gani, kina dawowa daga legas dinan yinaki yinaki zaki tattaro ki dawo nan sasa na dazama ja’iran yarinya kawai, ga furanki chan a fridge inkin ga dama ki dauko kisha” tashi tayi ahankali tai hanyar fridge din ta dauko furan tadawo ta zauna tafara sha, kasama sha tayi sosai sabida yanda Kaka keta jifanta da mugun kallo kaman zata kasheta, ahankali ta ijiye cup din ta mike tsaye, hararanta tasake yi tace “ina zaki? Baki barin sasan nan harsai anshigo da Ayush namata fada sanan zan rike ki da kaina na tura ki a mota, ja’irar yarinya marason mutane, saisa haryau batada mashinshini ko daya, duk yayyinki sunyi aure ga Ayush nan itama tayi, ga Zainaba samarinta har kadasu nake tsabagen yawansu kullum dai kina ganin dakin nan nawa da yar bakan leda samarin su suke shigowa dashi, keko mai bakin jini ko mashinshini kwara daya baki dashi balle nasaran koyar dubu biyu wataran nasamu tasanadin ki, Hamida, Hamida wlh ki chanza hali inba hakaba zaki tsofe a gida ko mahaukaci bazaice yanayi ba balle namiji cikakke mai mutunci, macen dabata shiga jama’a ina zata taba samin mashinshini iyye?” tai maganan tana buga cinya, hawaye ta share tana turo baki tace “salla zanyi” mugun kallo tasake watsa mata tace “wuce ai kinsan hanyar pampon jekiyo alwalan kizo kiyi sallan bance kihadani da Allah ba” juyawa tayi tafita daga dakin ahankali tsugunnawa tayi gaban pampoo ta daura kai akan cinya tana kuka mara sauti tayi minti uku ahaka sanan ta dago kai tashare hancinta dayay jajir, ahankali tabude pampoo tafara alwala tana gamawa ta tashi ta shiga dakin, hanyar uwardakan Kaka tayi Kaka ta nuna mata dadduman dake kan kujera tace “dauko wanan kiyi sallan akanshi bazaki shigan min dakiba” komawa tayi tadau dadduman ta shimfida anan tsakar falon tahau kai tai sallan la’asar, bayan ta idar ta linke dadduman ta ijiye akan kujeran ta zauna akasa ta tankwashe kafa Kaka kuma na ballan namijin goro tanaci abinta, sallaman Mama yasa ta dago kai da sauri ta kalleta, shigowa Mama tayi dakin dauke da karamin trolley da handbag dinta ko inda take batayiba ta ajiye ta kalli Kaka dake kallonta tace “Umma ga kayan nan nata” washe baki Kaka tayi tace “yauwa Haleematu kokefa, kinga inmuna mata hakan kotanaso kobataso zata dena tsoro da shegen jin kunyan nan, haka zamu dinga chusata cikin mutane dan gaskiya bazan bari tamin kwantai agidaba sonake ayi bikinta tareda Zainaba, amma in kullum tana makale damu, makale a dakinsu bata shiga mutane tayaya zatai mashinshini, daga saman silin din dakinsu Allah zai jeho mata miji? Kidinga sata a jama’a Haleematu kinji” gyadamata kai kawai Mama tayi kaman ba Kakan data mata tatas bane dazuba tace “to Umma in sha Allah zan dinga sata, antashi tafiya yanzu za’a kawo Ayush wurinki kimata fada” sake washe baki tayi tace “to, to shikenan ai, a shirye nake dama dazu rashin ganin miskilan nanne ya konamin rai” juyawa Mama tayi zata fice Hamida takara binta da kallo idanunta sunyi raurau dan ta tsani taga Mama na fushi da ita, dan juyowa Mama tayi suka hada ido watsa mata mugun kallo tayi tasakai tafice daga dakin, nuna mata jakan Kaka tayi tace “zoki kwashesu daganan yanzu za’a kawomin amarya” tashi tayi ahankali tazo taja jakan takomar dasu gefe, matane dayawa suka shigo sasan ana waka ana guda ansaka amaryan datasha alkyabba a tsakiya aka shigo bangaren Kaka da ita, wata kawar Mama tace “kaka ankawo jika kimata fada kisamata albarka” fashewa da kuka Kaka tayi tana soka hannu a lalita tace “Ayush yarinyar arziki, yarinyar kirki ga kwakwalwa wlh ba irin wasu ba kullum nabayan kashi sukeyi a makaranta, Allah ubangiji ya baku zaman lpy da mai gidan ki Muhammadu yaron kirki, Allah yabaku zaman lpy kinji Ayush” kudi taciro yan dubu daidai har dubu ishirin ta kamo hanun Ayush tasaka tace “gashi kina zuwa chan legas din ko albasa ce ki saro kifara saidawa kinji” kashewa akai da dariya awajen sosai danhar Hamida data cusa fuskarta a hijabi saida tai murmushi, hararan su Kaka tayi tace “karki biyema rubabbun nan Ayush dake dariya, aure saida sana’a inka cika tambayan miji bani bani bani gajiya suke afarama wulakanci, zamanin mu babu abinda ban sayar ba, daddawa, kuka, wata tsiya wata tsiyace dukna siyar, Allah miki albarka kinji Ayush dita” gyadamata kai Ayush dake kuka sosai tayi, Kaka tace “to kutashi kutafi karkuyi lattin jirgin saman dazakubi” ta juya ta kalli Hamida data makale jikin kujera tana kare fuska da hijabi tace “tashi kidau jakan ki muje dakaina nan zan saki a mota” fashewa tai da kuka sosai kaman za’a yankata, Zainab taja tsaki tafice daga falon abinta, ta alkyabba Ayush da ake fitarwa waje ke kallon yanda Hamidan ke kuka rabon data sata a ido tun jiya dasafe, tsawa Kaka tamata ganin batada niyyan tashi tace “tashi nace kona kira ubanki nafadamai wlh” da sauri ta mike tsaye, hararanta Kaka tasakeyi tace “ina abin idanunki?” ahankali ta nuna mata handbag dinta, dauka tayi ta mika mata ciro glasses din tayi tasaka kaka tace “dau akwatin mutai” jan akwatin tayi Kaka takama dayan hanunta tajata suka fita daga dakin sukai waje sai sunnar dakai take jikinta narawa sosai ko kadan bataso tai tafiyan nan, har wajen motocin daukan amaryan Kaka ta kaita inda har anma saka amaryan, ihu tayi tana leka jeep din wanda daga Ayush amarya sai Anty Lami dawata kawar Ayush Amina, dawata kawar Mama sai Zainab, da Ihsan da hannu Kaka ta nuna Zainab tace “Zainaba ke da Ihsan ku fito kushiga dayan motan wanan ja’iran nakeso nasa anan dan asaka mata ido ga Lami nan inba hakaba zata iya guduwa tace bazata ba, ku fito nace” tai maganan tana hararan su tana kama kugu, fitowa Zainab da Ihsan sukayi sukai motar gaban su suka shige, Kaka ta kalleta yanda taketa share fuska da hijabi tace “wuce ciki yar tselen uwa” ahankali ta shiga ciki Kaka ta karbi akwatin datake shirin shiga dashi tace “wanan a boot za’a saka” Abokin angon dake sanye da Navy uniform ne ya karbi akwatin daga hanun Kaka ya bude boot ya saka, aka shishiga motar aka tada Kaka ta daga musu hannu, saida taga tafiyar su sanan takoma cikin gida tana murmushi ranta fess.
Sosai take share hawaye a mota hanunta har rawa suke, ahankali Ayush dake zaune kusada ita ta mika hanunta ta daura kan nata ta rike, da sauri ta dago rinanun idanunta ta kalli Ayush din hada ido sukayi itama idanunta sunyi ja ta girgiza mata kai, da baki tamata alamun “stop crying” hakan yasa ta share hawayen ta damke hanunta gamgam ahaka harsukakai airport suka fiffito daga motan kanta akasa ta rike Ayush gam har suka shiga jirgi jirginsu yadaga jitake kaman zata kurma ihu.
_Lagos_
Misalin 7:25 jirginsu ya sauka a Lagos, wasu manya manyan hadadun cars ne sukazo dukansu har lokacin tana rike da hanun Ayush kanta akasa kaman zatai ihu, suka shiga mota, abokanan ango suka kaisu gidan Ayush dake cikin Navy Barrack, gidane mai kyau hadadden gaske, sai alokacin hankalinta ya kwanta ta natsu ganin su kadaine agidan, barin musu dakin da aka aje Ayush din tayi tafito ahankali tana kalle kalle Ihsan biye da ita ta shiga dayan dakin dake corridor, dakin katifa ne da ledan jikinta kejiki, ko shimfida gadon ba’a yiba dayake ba’a gama jere ba, hand bag dinta ta ijiye ta wuce ta shiga bayin dakin tadauro alwala daidai lokacin Ihsan ta bude kofan ta shigo tace “salla zakiyi Anty Hamida?” gyadamata kai tayi tace “inane gabas?” karasowa cikin dakin Ihsan tayi bayan ta kulle kofan tace “bansaniba nima Anty” “daukomin wayana muduba compass” da sauri Ihsan taje kan gadon wurin jakanta tabude taciro wayar ta kawo mata bude wayar tayi kasancewa ba key tabude compass ta nemi gabas sanan tai murmushi tamikama Ihsan wayar tace ajiye kiyo alwala kizo muyi salla to tace tawuce bayin, kabarta sallan tayi Ihsan tafito ta zauna gefen ta saida ta idar tace “to Anty kiban hijabin ki nibanzo da hijabi ba” hararanta tayi tacire hijabin ta mikamata ta tashi ta koma kan gado tadau wayar nata tabude tana dube duben hotunan su, Ihsan na idarwa tai tsalle tafada bayanta hakan yasa tasaki kara. “wash Allah na, Ihsan zaki karyaniii” tai maganan kaman zatai kuka, dariya Ihsan tayi tana kallon hotunan su datake kallo awaya tace “kawo wayanki kiga Anty Hamida” hararanta tasake yi dayawani irin karama fuskanta kyau tace “bazan bayarba salon ki kara batamin waya kaman wachan lokacin ko” “Hamidaa!” Anty Lami ta kwala mata kira da sauri ta tashi daga kan gadon tace “na’am” fita tayi da sauri Ihsan tabi bayanta da kallo tace “yes, ai yanzu na iya waya har chatting na iya bakaman da ba” facebook dinta ta bude tana murmushi tana dube dube ganin bata da friends banda su Anty Ayush, zainab dasu Anty Rukayya yasa taja tsaki tana turo baki, tace “dukma yan gidanmu ne friends dinta” suggestion din da Facebook ke nuna mata na add friends tashiga tana kallo tasake turo baki tace “ai wlh sainai adding dukansu” d sauri tafara adding mata friends din, tai adding friends yafi dari da hamsin da kanta tagaji da clicking ta saukar da ajiyan zuciya tace “Allah sa suyi accepting I will check gobe kokuma cikin dare yau when she’s sleeping” kashe data tayi ta fita daga facebook din ta shiga dialog tana dubawa daga Mum sai Anty Ayush sai Anty Lami yawanci suke kiranta, tsaki tasakeyi tace “wayar Anty Hamida is so boring bakaman na Anty Zainab ba, wai yaushe Anty Hamida zatai saurayi ne” ajiye wayar tayi da sauri tafice sabida kiranta da Anty Lami tayi itama, hadadden abincin da aka kawo musu duk kowa ya dibi cinshi, kadan Hamida ta iyaci ta tashi takai plate din kitchen Anty Lami tabita da kallo tanajin su Zainab da kawayenta na hiran Pharty da za’ayi gobe a ship wanda abokan mijin Ayush suka hada akan ruwa za’ayi Pharty, tabe baki tayi aranta tace aisai kuyi tayi mayun Pharty, alwala tayi tazo tai isha’i sanan tafada kan gadon sai bacci dan ta mugun gajiya.
_IN BANI _
_M. Shakur_
Post a Comment for "In Bani 3"