In Bani 11
11…
Suna kaiwa airport yabiya musu kudin komi suka jira kafin suyi boarding flight dinsu, tana rike da hanun nun Faruk gam tana bobboye fuska, ahaka harsuka iso kano saukowa sukayi suka shiga taxi dazai kaisu gida.
Sosai taji hankalinta yawani irin kwanta data gansu a anguwan su sai murmushi take tana kallon anguwan su, ta mirror Faruk ke kallon fuskarta yanda take murmushi tana kallon hanya, suna parking a kofar gidansu da sauri tabude kofan motar tafita, Mama ce kadai a tsakar gida da matan dake zuwa musu wankau, wani irin murmushi tayi ta kwala mata kira. “Mama” da sauri Mama ta juyo jin muryan Hamida, wani irin gudu Hamida tayi taje tafada jikinta tana dariya ahankali yanda takeyi, cikin jin dadi da tsananin farin ciki Mama tawani irin rungumeta tace “kedawa yene Hamida?” tai maganan tana cirota daga jikinta dan taji tsoro ganinta kaman an jehota, ko kadan batasan Abba yacema Faruk yaje yadaukota ba jiya da daddare ba, tana jikinta rungume da ita tace “Yaya Faruk yazo yadauko ni fa Maman mu” daidai lokacin Faruk ya shigo gidan rike da jakanta, murmushi Mama tayi tace “to aisai kije ki gaishe da Kakan ku kizo” tasaketa tana kallon Faruk dake karasowa wajen rike da jakanta tace “sannu soja shine ta barka da jakan ko” ahankali ya ijiye jakan agaban Mama kanshi akasa yace “ina kwana Mama” sakin Mama Hamida tayi tai hanyar sasan Kaka, ahankali ta turo kofan ta shiga tana kallon ko’ina tai sallama cikin daga murya Kaka tace “Hamida, Hamida, aini tun ranan dazaki tafi nace saikinsan mekika yi, sai kinsan me kikayi, me kika shirya, saikinsan kirsa da kisisina dazaki hada ki dawo garin nan, Hamida anya bazan kiramiki malamai azo amiki rukiyya ba inaga aljanu gareki fa” dan turo baki tayi tasami waje ta zauna nesa da ita tana wasa da bakin hijabin ta kaman bada ita ake magana ba, zaro ido Kaka tayi tace “nikika maida mahaukaciya ina magana kinmini banza” daidai lokacin Faruk ya shigo dakin, watsa mata harara yayi yace “ke tsohuwar nan kin cika ihu, please inada ciwon kai yau kiyi shiru pls” yay maganan yana karasawa wajen fridge din dake falon, binshi da kallo Kaka tayi baki abude hakan yasa Hamida tarufe bakinta da hijab tana dariya chan kasa kasa, juyowa Kaka tayi ta kalleta ranta abace tace “dan gidanku dariya kike mini” da sauri ta girgiza kai still tana dariya chan ciki gudun karta ji tana kare bakinta da hijabi daidai lokacin shima Faruk yadawo rike da bottle water ya zauna a gefen Kaka zai bude bottle water, duka ta dakamai abaya da sauri ya kalleta cikin fushi yace “auch waike old lady nan me haka kike dukana agaban yara” kaman Kaka zatai kuka ta nuna kanta tace “kafara kirana da wanan yaren yahudancin ko Faruku, to wlh bari ubanku yadawo saina fadamai cin mutunci dakuke shigowa har Sasa na kukemin, ku tashi kufita, kutashi kufita nace, kuma bani ruwan gorana saurayin Zainaba ya kawomin su kusan katan biyar, bani” tafada bacin rai tana mika hannu zata karbi ruwan, tsaki yayi yadaura kafa daya kan daya yanashan ruwan shi ahankali Kaka tasaki baki tana kallonshi tace “ai shikenan kasha wuta shege dan buhun uba” fashewa da dariya Hamida tayi dayasa Faruk saukar da ruwan daga bakinshi ya watsa mata wani mugun kallo da sauri ta tashi tafita daga dakin da gudunta yabita da kallo, hararan kofan Kaka tayi tace “ja’irar yarinya, ai wlh Faruk banso kaje ka daukota ba, so nayi jiya da Sama’ila nama maganan kace aiki zaka, baga tanan ba rass bataima kama da wacce tafada ruwaba” juyowa Kaka tayi ta kalleshi daidai ya ijiye ruwan akasa tace “kaje wurin Maman kane yau?” girgiza mata kai yayi yana yatsine fuska, yace “sai anjima da yamma yanzu aiki zan tafi” washemai baki tayi tana kara matsowa kusa dashi tana murmushi tace “Faruku na wai har yanzu ba’ayi albashin bane, kamin alkawarin dubu ashirin fa” hararanta yayi yace “jiya agabana Abba yabaki dubu talatin wai mekike yi da kudi ne haka?” sake matsowa kusada shi tayi kaman zatai gulma tace “na rantse maka Faruku adashi nakeyi, tara kudin bikin Hamida nake” wani irin kallo yamata yace “wace Hamidan?” baki tabude tace “kagamin iskanci munada wata Hamida agidan nanne bayan wanan hamidan data fita daga dakina yanzu?” cikin daure fuska yace “yaushe tai saurayi?” sake matsowa tayi kusa dashi kaman wacce ke shirin yin gulma tace “a’a kaima dai kasan ko mashinshini Hamida batadashi ko, amma so nake kabani kudin dukna hada naita zubin adashi ina tari, inama bikin ta tari, kasan Hamida yar wajena ce, itace mai sunana fa, kaga shegen fadan nan danake mata wlh sonake ta chanza ne dan batayi gadon halina ba, bataci sunana da aka bataba, amma dazaran ta chanza zamu zo mu fara shiri sosai, nama tuna bari naje sasan su hado kayanta zatayi tadawo shashin nan ma yau dinan” shiru tayi tana nazarin yanayin fuskanshi yanda yay kini kini darai, tace “kaikuma lafiyan ka naga kai wani iri” yatsine fuska yayi yace “am fine” ya mike tsaye yana gyara kayan jikinshi yace “natafi aiki” tashi tayi tace “muje na rakaka, kadan tahomin dayar bakan leda kaji inzaka dawo, tunda su Zainaba da Ayush sukabar gidan da yunwa nake kwana Faruku” hararanta yayi yanaji kaman ya bugeta kiri Kiri sai Kaka tabude ido tana karya, dariya tayi sosai ganin yanda yake kallonta tace “bawai yunwan abinci ba na kayan kwadayi, idan kadawo kaza bani kudin aiko? Bazanyi barci ba zan jiraka” hararanta yayi yajuya zai fita hanunshi da damke tace “dan ubanka saika bani danma ina lallabaka” kaman zaiyi kuka ya kalli yanda ta damke well ironed uniform dinshi yace “naji inna dawo zanbaki, ki saken to” sakinshi tayi tana dariya ta dungure mai kai tace “ja’iri barima ubanku yadawo yau zan mishi maganan aurenka ne, wlh koka fito da mata kona je kauye nahadaka dayar aminiyata Iyami” tsaki yayi tsabagen takaici baima tsaya yabata amsaba yawuce yafita daga sasan da sauri tabi bayanshi amma har yay wajen gate hakan yasa tai tsaki ta wuce part din su Hamida.
Da sallama ta shiga falon su Hamida tagani zaune a falon tanacin indomie data dafa da boiled egg tana kallon zee world tana ganin Kaka tai murmushi tana sunnar dakai, hararanta Kaka tayi tace “aikin kenan ki zauna ke kadai awuri babu kowa shine burinki a duniya miskilan banza, ni ina mamarki?” daidai lokacin Mama tafito daga kitchen rike da tray data debo wake dan gyarawa zatayi tana ganin Kaka tai murmushi tace “yau Umma a shashin mu” da sauri Kaka tace “eh nazo ne, kihada ma yarki kaya sasana zata dawo” turo baki Hamida tayi tana tauna abincin dake bakinta ahankali Kaka ta kalleta tace “ahap ai saidai ki mutu ingayamiki yarinya, yaushe zasu koma ma makarantan yama sunan hutun da sukaje?” murmushi Mama tayi tana karasa shigowa cikin falon tace “mid semester break” da sauri Kaka tace “yauwa shi yaushe zaku koma ke?” tai maganan tana kallon Hamidan dakecin abincinta, dan turo baki tayi tace “ranan Monday” kwafa Kaka tayi tace “saura wanan karan ma ki kwaso zero zero a makarantan kaman na wanchan karan, wlh cema Sama’ila zanyi bazai kara kashemiki koda sule biyar a makarantan ba, aure zamu miki, inyaki kuma nida kaina zan aurar dake” da sauri ta kalli Kaka, gyada mata kai tayi tace “eh kinjini da kyau, wlh aure zansa amiki inhar wanan karan ma kin fadi kaman wanchan tunda kedai bazaki saki ranki ki jona mutane kikoyi abuba, ba nannan zainaba ke zuwa makaranta karatu ba banda ke, malami na koya muku abu kina kakkare fuska kikasa kallon allo, yoto menene amfani Sama’ila yay ta bata kudi akanki har shekara hudu? Kema kinsan naso keda Zainab da Ayush dakuna gama sakandire a aurar daku amma kuma sainazo na hakura da Sama’ila ya nunamin yanaso kuyi karatu amma kam wanan karan bala’i zanyi dashi dan wlh bazan bari dan kudin dayake samu a saida kaji, saida kajifa jama’a yazo yana batasu akanki ba, dan asarace, da’ace nine yabama uban kudaden danasan menayi dashi kuma Allah kaimu mondan, ni nan dakaina zan kaiki har Bayeron incema malamin ku wlh yazane min ke tunda dai kinki maida hankali kiyi karatu” tai shiru tana kallon Hamidan data daura hannu a fuska tana share hawaye, tsaki tayi ta kalli Mama data zauna kan kujera tafara gyaran wakenta ita yanzu bala’in Kaka baya damunta dan tsufa ce yamata yawa, cikin masifa tace “ai cewa nayi kibar gyaran waken nan kitasa keyanta taje dakinsu ta ciro kayanta daga sip dinsu, na Zainab da Ihsan kawai zaku bari a sip din ta tattaro tadawo Sasa na, nariga na share dakin dazan bata tastas, Allah kuma yakaimu Monday zakiga nizan kaiki makarantan na rantse miki saina sa malamin ajinku yamiki bulala goma hala hakan zaisa kifara karatu, kici jarabawa da kyau, kigafa tunda sukai hutun nan banga tabude littafiba fa, kullum tana nanike adakin su daga taci saita bacci sai shegen bacci kaman kaza, ki ajiye kwanon wanan tsutsan kampanin duksu kesaki bakida kyan gani, yarinya taci tuwon dawa da miyan kalkashi abinci mai Gina jiki bazata ciba sai tsutsan kampani” murmushi Mama tayi tace “Kaka indomie ce ba tsutsan kampani ba” cikin daga murya kaman zata fasa gidan tace “injiwa Haleematu” ta nuna plate din tace “ke bakiga yanda abin take a lankwashe ba, wani irin ziza ziza da ita, tsutsa ce saisu busar saisu barbadeta da fulawa fa asaka a leda a sayar” ta kalli Hamida dake share kwalla tana tauna indomie bakinta ahankali tace “ba dake nakeba dan gidanku, tashi kije mamar ki ta tayaki hada tulin kayan ki, dama gobe su Zainaba zasu dawo sa sami sarari adakin suma” tashi tayi ahankali tai hanyar corridor inda dakinsu yake, ajiye waken Mama tayi ta tashi tabita tana murmushi kasa kasa Kaka tabisu da harara kafin takarasa tadau plate din indomie tafice dashi tana hararan abincin takarasa wajen bolansu zubar da indomie tayi sanan ta wuce chan pampo ta ijiye kwanon ta wuce Sasan ta.
_IN BANI _
_Maman Abd Shakur_
Post a Comment for "In Bani 11"