Hariji Book 3 Page 85-86
85&86
*Alheri writers asso.*
Bayan wata biyu
Qarfe Sha biyu Na dare ummi ta farka da wata irin azababban ciwon mara,sosai take qoqarin enduring amma she
couldn’t.wawwaigawa tayi ta hango hajjo sai sharan barcin ta takeyi after long period of time da ta dauka tana waya ,don ummi ma gajiya tayi Tai barci ta barta ,duk da kasantuwar ita take taimaka mata da massage ,saboda yanda jikinta yake yawan kumbura ,gashi ta dunkule tayi jurum ,tafiya wata zubin mugun wuya yike mata .
Ji tayi vein din qafarta ya qulle tamkar jini ya daina biyowa ta jijiyar ,qafar sai wani zumm zurr yikeyi ,Nishi ta fara yi a galabaice,take kiran “Hajjo…ke hajjo ki tashi ” ai hajjo tamkar ana Dada qara mata jin dadin barci tayi ,Sam ko muryar ummi bata iya jiba ,dake magana acan qasan maqoshi .shiru tayi tana son daure zogin,saidai kasantuwar ta Na midwife ya alamta mata kodai labour ne takeyi ? ,Aikuwa da qarfi ya gwale baki ta yanka ihu da qarfin gaske .
“Hajjo ki tashi nace”
A 360 hajjo ta durko a gado,bakinta Na makyarkyata take tambayar “Ummi lpy kuwa?” Numfashinta sama ² take iya bata amsa “ki kiramun ummah ,hajjo zan mutu” ai bata tsaya yayiban dankwaliba ta wuce dakin umma ,ta taso ta ,kafin ayi haka drivern ummi ya daukesu a motarta ya wuce da ita near by hospital
Tun dare ake 6arzan kwakwa har kusan Sha biyun rana ,daga qarshe likitocin suka bada shawaran CS ,saboda yaron yayi fankacece ta ciki kuma a breach presentation yike ,is difficult matsayinta Na budurwa a iya manging dinta ta haihu.
A hakan ma saida sukayi fada sosai akan rashin zuwanta antenatal
Umma da en uwan suna kuka sukace sun amince ayi kawai “kunata abu ku kadai,ina mijinta ? Bakuda mazane a danginku?” “Mijin ta ya rasu!..ke hajjo je Kira abbanku a mota yina can raku6e tareda dreba ,shi duk abun arziki Na ‘ya’yansa baka ganinsa ciki….” ta juya zata wuce sukayi karo da uwale da mijinta,Aikuwa ko zuwan su baisa ta fasa bala’in ba,da aibata rashin zuciya irin Na babansu ummi.
Shidai kunya duk Isar mewada yayi,Daga qarshe dai cikin gaggawa mewada yayi sign aka shige da ita operation theatren, sannan ya roki suyi hakury da maganar tunda wannan personal issues dinsu ne.
Ummi Ana gungurata ankai bakin qofa ,suna biye da ita hajjo Na idasa cire mata dan kunne gwal din da ba a riga an cire ba, sai sharar qwalla suke.
kamo hannun hajjon tayi ta rada mata a kunne “ki Kira Adnan ,kice masa in Na mutu ga amanar yaron quliya,kuma inason yaci sunan quliyar”
Zum6uro baki tayi “Nai maki alqawarin kiran Adnan in fada masa komai ,amma inshallah yaranki bazai Zama marayan rashin uwa da uba ba” tana waving masu bye bye aka shige da ita
Aikuwa kamar ta shiga Da ciwo , anaesthetic bama suyi aikinsu ba,cikin ta ya soma toroqo ,wata Nurse/Midwife dinda tazo da ita suyi handing over ma likitocin theater din da sauri ta saka glove tayi assisting dinta ,cikeda qwarewa ,ta finciko babyn da ke zaune da d’uwawunsa ta fidda shi , clapping doctors din sukayi mata ,saidai tana qoqarin yin delivering placenta ,sai wani nishin . Dakawa ummin tsawa tayi “ke ba’a ta6a ce maki cikin ki en biyu bane?” A galabaice tace “eh amma van fadama kowa ba ,saboda Kar yazo ban Haifa ba”
Cikin fushi ta kalli likitocin “sir twins ne ,kuma na ciki kunga hannune ya leko ,don haka aikin kune” tana fadin hakan ta dauki yaron ta fara gyara shi ,very small baby , weighs 2.4kg .ta nade shi cikin showel ,karkarkar aka fiddo macen ita tafishi girma,saidai ita tayi weak sosai sanda aka fiddo ta ,dukkansu a incubator aka sakasu Na dan lokaci ,kafin aka dinke cikin ta aka gyara ta aka fidda ita ,gamida twins dinta Hassan da Hussaina
Uwale da gudu taje wajen yaran “my love kaga enbiyu kyautar Allah?,kamar ace namu” maqe mata Ido daya yayi ,ya fakaici idon mutane ,ya rada mata “ki bani dama yau,nikuma in banbara maki cikin en hudu ma ba biyu ba,kunsan fa ku sex blood ne ”
“Kaida ka San wannan ,ai muje gidan nan kawai saboda nima Na qosa Ina carafke da dan kaina”
Nikuwa nace tunda aka zubda Na rariya ai dole a nemi Na Sunnah a rasa .
Kiran duniya number Adnan yaqi samuwa ,har sai bayan an fiddo ummi daga C’s ,sannan a lokacin ya shiga…
***
Adnan yina zaune a gaban Sophy tana masa fad’a da nuni akan yanda girma ya fara kama babansa,ya daure yayi aure ko ba don kwadayin Mulki ba,a’ah yanda babanshi baida yawan zuriya shikenan ,to shi sai yayita haihuwar masa yina jin sanyi
“Adnan ka cire idonka ,akan matan Nigeria ,kaji?” Jinjina mata Kai kurum yayi ,ya danna wajen daukar kiran da sauri saboda ganin ummi ke Kira
“Uwar takwas ” ya fada cikeda tsokana
“Aikuwa hajjo ce ,ummin ne dai ya haifi twins ”
“Allahu Akbar” kurum a take quliya ya fado masa a rai saiga hawaye shauu
Cikin sauyawar murya yace “mata ko maza ?” “Mace da namiji amma ita ummin…” Bai tsaya jin me zatace ba ya kashe wayar “Ummi ta Haifa twins zuwa Nigeria ta kamamu,Anty kina mun fadar mata ,to ga matana nan ,tun daga yau ,Na fad’a sahun manema!”
Post a Comment for "Hariji Book 3 Page 85-86"