Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Hariji Book 2 Page 39-40

39&40

Adnan ya kasa furta komai face kalmar “innalillahi wa inna ilahir raji’un” yasan tabbas allah zai basa mafita,don shi yayi alqawarin indai masifa tasameka ka furta wannan kalmar a take allah zai sauya maka da mafiyinsa


Tunanin hakan da yayi a take yaji tawakkali ya shigesa ,tabbas dole in yiwa dad biyayya,amma gobe zan bar nigeria,gwara inkoma madina cibiyata,in shiga cikin dangina ,din na gaji da shiga cases,da na fita wannan sai wannan ..sai dai tambayata daya ce zan iya rabuwa da beelah kuwa?

**
Ummiy ta kar6i gyara na ban mamaki,tsumata sosai tayi dagarurruka da tsumin er gata,don yanzu duk kawaici da kunya irin na ummy,tana ganin malaman gyaran jiki ,zata hau yi mata ihu gamida sambatu
“wallahi bazan qara shan komai ba,in ba wani hali kuke neman jefa ni ba”
amma haka zata murje qasa ta tubure tana d’irka mata kayan É—a’a …lolz inji hausawa iyayenmu

Biki sai qara qaratowa yikeyi,gashi yau saura kwana biyu biki,jikin ummy yayi luwai luwai ,saboda gyara da ya samu,nonuwanta sunyi tsantsan suna wani irin sheƙi ,sun gaggallatso riga kamar zasu faso riga

ita kanta kunyar kanta takeji,ta koma yawo da hijabi all the time
saidai duk gyaran nan ba ango ba dalilinsa,ga gyara yina neman haukata masu yarinya,don tana zama ,zakiga ta zabura sai ta dauki buta ,ta tsiyayi ruwa a flask taje tayi tsarki ta chanja pant
Itakuwa uwale ta kafa dariya kenan,hhh shegiyar bisa tasha gyara ,yau ina ustazancin? zo ki fada mun,halan kinji wajan na motsi”
shiru take yi mata sai umma ke bata amsa
“Kinji qyalesu auta,auran dattijo saida gyara,ki burkita masu shi,matansa saidai suyi ta jiyo ihunsa,inkinso ki sashi yayi maki goyo goyo,a gaban dattijan matansa ,ba kunya shine daÉ—in *Auran caraf* É—in,yasan aljihunsa bai kukan banza ba,ki kwantar da hankalinki en uwanki su saita ki a hanya,wallahi sai matansa sun sadaÆ™ar kin riga kinyi masu *Wuf* da miji,mai kuma son abun hannunsa ,saidai yazo ya nemi alfarma a wajenki…”

Tsam ta miqe tabar wajen ,din ta lura ummah ta riga da tayi nisa batajin kira ,sai fatan addu’a…”Nidai bazance banyi sa’a ba ,amma allah ka jarrabeni,allah ka bani ladan hakuri”

***
Gaba daya gidan quliya ya gama rikicewa da kuka,komun rashin imaninka dole in kaga hannunta hankalinka ya tashi,haka ya kira likitansa,yayi mata dressing aka nade da gauze

Saida aka gyarata ya fito tare da umurtanta da su bar mashi gida kafin sa’a É—aya “Ai quliya ka gama yi mun yankan qauna,ka zalunce ni,ka maida ni *Miskiniyar Æ™arfi da yaji* TaÆ™amarka,kaine AlÆ™alin alÆ™alai,shugaban kotun Allah ya isah! Kafi qarfin doka ko? to allah ya isah ,kuma zan barma gidanka,amma yaranka saidai su zauna a gidansu bazanje dasu gidanmu ba don ba dasu nazo ba”

“Yes kina da damarki na fada mun koma menene,aura aure na ya jamun,saidai inaso in shaida maki ,nasan komai dake faruwa a cikin gidana,yaranki kuwa kodai ki maishesu gidan marayu,ki tona masu asiri bayan sun gama qobon su din yarana ne,ko kuwa ki tafi dasu gidanku ki qare tarbiyyansu su isa aure in masu lillahi wa rasulihi sadaka!! inkuma har yanzu so kike maganar tayi tsaho,to kiyi qarata,ni kuma sai ayi mana Test ,bake kaÉ—ai ba,koma wanene,in tana jin ita wata ce,to tayi magana zan ballatso maki abunda ke rufe…”

“Dad ke nan in yaran nan ba yaranka bane,to shegune?! dad bazaka zauna da maceba in kasan fasiqa ce ba,na tsawon lokaci…”
cewar adnan da shigowarsa kenan ,ya tsinci maganar da ya doki zuciyarsa

Murmushi yayi a take wasu qwalla tazo masa ,amma da yike namijin duniya ne,da sauri ya maidasu

“Son akwai banbanci tsakanin zuciya da qwalwa,kazalika rufa surri shine cikar kamalata,kallon kitse sukewa rogo ,tunaninsu ni din zan mutu suci gado,basu san ina! Ba haka bane,shiyasa na tabbatar na ciccikawa duk yaran gidan nan account dinsu,alamun kallon bansan darajan kudi ba
aah tausayinsu ne ya saka na tabbatar na gina su,ta yanda ko da na mutu ,bazasu tashi ba gado ba..

“No dad,karka cemun,bakai ne babana ba,don wallahi wallahi in zina tayi ta haifeni la shakka ,jininta ya halatta saina kasheta…”

***
Da qyar adnan ya shawo kan gidan sannan ya tasasu suka bar gidan,dukda yasan tana cikin wanda suka quntata masa a rayuwa,amma ai wannan don allah zai yi,saida ya kaita gidansu,sannan ya bata shawaran ta nemi sarkin kano,shine kadai aminin kuliya da zai iya shawo kansa,har a dawo dasu,tunda saki d’ayane…

***

*Rana bata ƙarya*

Yau ta kasance,ɗaurin auren ƙuliya,da ummy zaa ɗaura ƙarfe ɗaya na ranar yau,inda uban ƙasa,mai martaba sarkin kano,zai ɗaura auren,,saidai kuma dik yanda ƙuliya yaso ya shawo kan adnan abin ya faskara,dole ya ƙyalesa ya tafi madina kamar yanda yayi niyya,saidai ya tafi da alƙawarin zai dawo bayan wata ɗaya,yazo yaga amaryan gidan tasu.
wannan kenan!

Post a Comment for "Hariji Book 2 Page 39-40"