Hariji Book 2 Page 37-38
36&37
Jimawa kadan suka fara shigowa kowa da kalar style din kukanta,wanda a zahiri duk qarya ne,me dan dama dama a ciki,banufiyar matarsa da take kuka saboda sosai taso shiga zuriyar *Ahlan musannah* ko ta baiwa idonta abincin madaran izzah da al’adun larabawa da suka riqe ,kuma sike amfani dashi kawo yau,don haka kuka sosai takeyi tana jujjuyasa.
kafin ta duqa a gaban fuskarsa ta tallafo gemunsa ,ta watsa masa rinannun idanuwarta a kansa
mijina ya za kayimun haka? ya zaka mutu a lokacin da nike É—aukin zama dakai?ka tashi ka fada mun ba mutuwa kayi ba,ni ina zargin wannan matar tana da hannu a kashemun miji,wayyo allah na na shiga ukuna ina za nine?…”
seat room dinsa aka wuce dashi anan za ayi masa wanka akaisa makwancinsa,saidai ana kaisa maganin da yasha da zai dauke masa numfashinsa da duk wani psycho motor activities dinsa ya daina aiki,instantly ya fara kokarin recap,amma ya kasa,sai dai yasan cctv dinsa ya nadar masa komai
Itakuma bayarbiya uwar Æ´an son kuÉ—i ghana must go ta kira en uwanta suka zo mata dashi bandir bandir,ta ringa ciccika kudi tana sakawa ana firfita mata da kudin gidan
ta hada zufa jagwa6,tana kan jan ghana must go na biyar,ta zo dai dai kofar dakin tayi arba dashi a tsaye cikin farin alawayyo da ake nade gawawwaki,yayi yafe dashi a kafada kamar wanda yake aikin umrah
Ta baya ya damqi damtsen hannunta ,a gigice ta kwantsama ihun da saida ya girgiza duk wasu window glasses na dakin,sannan ya jawo attention din en gidan
“Wayyo allah fatalwa,kayi hakury ban shirya mutuwa yanzu ba,karka kasheni ko kace in bika…”
murmushi yayi yina tuna ayar Qur’an da yike cewa “Lallai matayenku,yaranku da dukiyoyinku fitina ne ,ku gujesu…”
zurrrr hawaye ya sirnano masa a kunci,sannan ya jinjina kai ya furta a hankula “sadaqal lahul azim”(Allah madaukakin sarki kayi gaskiya)
hannunta ya rike kam kam akuma dai dai nan en gidan suka shigo ,itakuwa sai gunjin kuka takeyi
Ai suna ganinsa suka fara jada baya
“Kuliya ya za kayi mana haka ,you rest in peace ,karka 6ata makwancinka”
“Ke shiru !(ya daka masu tsawa)”
“Nasan Allah ya jarraveni da nasaba da arziki maras gaba,shi yasa nasha magani don inga in na mutu wa zai damu? sai na gane duk dukiyata kukeso ,ita wannan ma,out of greed,tun yanzu ta fara futa da jakunkunan kudi,to kuyi mun afuwa,A matsayina na Alkalin Alkalai na qasa ,zan yanke mata hukuncin da ya dace da ita a musulunce wanda ko gaban allah naje zai bani lada…
Yina kaiwa nan,ya saketa ya kama hanyar dakinsa
.
Suwait jikinsu yayi sanyi ,itakuwa da gudu taje ta wawuso kafarsa ,tana kuka kanta a qasa.
Haquri ta ringa bashi tana roqon en uwan zamanta su tayata rokonsa
Saidai sunna fara magana,ya dakatar dasu da cewa
“Meye hukuncin da musulunci ya tanazarwa 6arawo?”
shiru sukayi sun kasa magana ,sai haqury da suke cigaba da bashi
Murmushi ,irin wanda yafi kuka ciwo yayi.
Shi kenan É—an tsumayeni…
ya bata umurni sannan ya shige study room É—insa
jimawa kaÉ—an sai gashi ya fito hannunsa É—auke da envelope ,yaje kan kujeransa ya zauna ,yaja wani matsakaicin tebur dake a gefen sa mai É—auke da tarho
saida ya waina ,sannan ya saka mariƙin a kunnensa
“Kazo yanzu cikin sashena with your tools”
dikda basu san ko wayeba saida gabansu ya fadi dam!
wani ƙosashshen soja ya shigo fuskarsa ba annuri,banda maiƙo da yikeyi na alamun rashin Imani
yina shigowa bai kalli kowa ba ya isa gabansa ya ƙame tare da sara masa
Sannan ya duƙa ya buɗe jakar bayansa ya fiddo wani ƙatuwar ƙulli ,ya kwance a gabansa
wuƙaƙe ne ,masu ban tsoro harda almakasai masu mariƙan noti
cikin wani irin frighten voice,yace “Ina victim É—in chief?”
Juya yatsarsa yayi ya sauke akanta,sannan ya daura da cewa “A dazu na tambayeku ,hukuncin wacce tayi sata ,kunki fada mun,so ni zan amfani da sani na ..
Junaid ka datse mata hannun ta na hagu.”
Ya baiwa mutumin umurni cikin qaraji
zaro idanuwasu dikkan su sukayi daidai nan mutumin ya damketa ya fara daureta kamar kullin goro..
“Alhaji wannan ai kafurci ne,billahillazi kana datse hnnunta nabar auren ka!!”
cewar banufiyar matarsa…
“Mtsewww,to se me? a yau inna ji dama ,zan aura wanda suka fiku komai路♂️”
“Æ™uliya inci darajar zuriyar da muka haifa tare dakai,alhaji duba yanda yike Æ™ulleni”.
Dafe ƙirji yayi,ji yayi kamar ta daɗa kunna masa wutar tsanarta.
“Wannan lokacine da ya dace in sanitizing gidana,don haka,ni islamic shari’a zan amfani dashi ,dole a yanke maki hannu ko don ya zamarwa na bayanki aya …yara kuwa da kike cewa,to kin ja masu,don kamar yanda na rubuta maki takardan sakinki anan,haka zaki kwashe gayyar yaranki ku tafi.
saida ya furzo numfashi sannan yace
Mind all of you,Yaro daya allah ya bani ,kuma shine *Mohammadul Adnan* ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka
yina kaiwa nan ya cilla mata envelope É—in a fuska,ga sakin ki nan..
“junaid me kake jira!” da sauri ya dauki wani pintcher me hannun scissors ya saka a wuyar hannunta ya dauko wata wuqa tana tsananin sheki tsabagen kaifi ya aza akan tsakankanun qashin …
Tsam quliyar ya bar wajen
A take taji wani nadama ya shigeta ,ji take kamar ta hadiye ranta saboda kukan da yike zuwa mata,tana hadiyeshi
yau daya ta tsani auren me dukiya…
Suma qwaqwalen sauran hutun wucin gadi suka tafi ,kenan yina nufin duk yaranmu ba nasa bane?
Razananniyar ƙaarar da ta saki shi ya dawo dasu hankalinsu
A Furgice suka miƙe ,a yayinda abunda Nnenna taga yana faruwa da ƴar uwarta ya sata sulalewa ƙasa sumammiya
Tasan ƙuliya in yasan nata tas zaisa a kasheta
tana ganin malaman gyaran jiki ,zata hau yi mata ihu gamida sambatu
“wallahi bazan qara shan komai ba,in ba wani hali kuke neman jefa ni ba”
amma haka zata murje qasa ta tubure tana d’irka mata kayan É—a’a …lolz inji hausawa iyayenmu
Biki sai qara qaratowa yikeyi,gashi yau saura kwana biyu biki,jikin ummy yayi luwai luwai ,saboda gyara da ya samu,nonuwanta sunyi tsantsan suna wani irin sheƙi ,sun gaggallatso riga kamar zasu faso riga
ita kanta kunyar kanta takeji,ta koma yawo da hijabi all the time
saidai duk gyaran nan ba ango ba dalilinsa,ga gyara yina neman haukata masu yarinya,don tana zama ,zakiga ta zabura sai ta dauki buta ,ta tsiyayi ruwa a flask taje tayi tsarki ta chanja pant
Itakuwa uwale ta kafa dariya kenan,hhh shegiyar bisa tasha gyara ,yau ina ustazancin? zo ki fada mun,halan kinji wajan na motsi”
shiru take yi mata sai umma ke bata amsa
“Kinji qyalesu auta,auran dattijo saida gyara,ki burkita masu shi,matansa saidai suyi ta jiyo ihunsa,inkinso ki sashi yayi maki goyo goyo,a gaban dattijan matansa ,ba kunya shine daÉ—in *Auran caraf* É—in,yasan aljihunsa bai kukan banza ba,ki kwantar da hankalinki en uwanki su saita ki a hanya,wallahi sai matansa sun sadaÆ™ar kin riga kinyi masu *Wuf* da miji,mai kuma son abun hannunsa ,saidai yazo ya nemi alfarma a wajenki…”
Tsam ta miqe tabar wajen ,din ta lura ummah ta riga da tayi nisa batajin kira ,sai fatan addu’a…”Nidai bazance banyi sa’a ba ,amma allah ka jarrabeni,allah ka bani ladan hakuri”
***
Gaba daya gidan quliya ya gama rikicewa da kuka,komun rashin imaninka dole in kaga hannunta hankalinka ya tashi,haka ya kira likitansa,yayi mata dressing aka nade da gauze
Saida aka gyarata ya fito tare da umurtanta da su bar mashi gida kafin sa’a É—aya
Post a Comment for "Hariji Book 2 Page 37-38"