Hariji Book 1 Page 9-10
Free page 9 &10
*Alheri writers Asso.*
By…Oum Aphnan
A gidakam uwale tayi kwance tayi share share ,tana faman sharar barci ,batareda ko tayi wanka ba..
Cikin rashin tsammani ta jiyo sautin sa
Saida tayi wani irin tambul sannan ta miqe zaune
“Au harka dawo? Er banza ai dama ba abunda ta iya sai 6a6atun jaraban a Baki ni d’in dai, nice matar gaban goshi…
Yawun bakinta ne ya qafe sakamakon miqo mata farar takarda a kanannad’e da yayi
Washe Baki tayi ” woo ni kace mu fara bishasha mijina ya had’u da mutanen arziki sun washeshi ,belloti waya baka takardan office?”
Banza yayi mata ya dad’a turo mata takardan
Zuru tayi masa da ido ba tare da ta kar6a ba Cikin mamaki a ranta tana raya to me ya canja shine?
” Amshi mana ”
Ya bata umurni cikin d’aure fuska da mugun tsawa
A lalace tayi magana kamar wata doluwa
“Ha’ah to Na mene ne?”
“Ki amsa in kinje gida kya bud’e ki karanta
Wallahi kuwa ban kar6a sai ka fad’a na menene ko kuwa ka fitarmun a daki in cigaba da barcina mai dad’i
” to na sakin ki ne”
Zabura tayi ta miqe tsaye tare da dafe qirji
“Saa?.?
” saki”
Dariya ta farayi Kamar ta6a66iya “Ayyah ai tsakanin ni da kai babu saki,wasa ma kakeyi to saki da nayi maka mene ?
” kurum Na gaji da hajircinki ,kije can abi wani sarkin
“Mtswww to ai ban saku ba , ka saki banza wallahi ,kai kayi kidin ka kuma kayi rawanka…allah yaso ban karanta ba ,sai ka tafi da sattaccen gwuiwa”
“Ke jahila bari to in fad’a maki da Baki ،ni bello Na sakeki saki …
” a’ah karka furta ,wallahi bello zamu hau sama mu fado kaji Na fad’a maka
“Nasake ki saki daya KI tsireni,Ina zan zauna mace kullum tana rarikeni a gado in qare da basir da shan tsumi,ai wallahi sai kin tafi…
Wani gigitaccen qara ya saki Wanda ya maye gurbin maganar da yikeyi
Sakamakon muciya da ta gicciya masa a Mara
A guje ya dafe wajen yina kururuwa gamida salati
Wayyo allah ba shikenan,ta dagargaza abokin aikin,allah ya isah uwale kin cutar da hausi
” badai takan wannan jijiyar bace ? To gwara in dagargaza duk mu rasa da in tafi in barwa hausin tana kwasan lagwada ni da zawarci”
Biyo ta yayi zai hankadata waje yina tsiya harda gore gore
Uwale dake riqe da kugu jin yina surutai yina nufota ya tabbatar mata da bai daku ba
Aikuwa kafin ya qarasa tai kukan kura ta damtsi abar taringa ja tana lilo
Aduniya ji yayi kamar zaa zare masa rai
Ihu ya ringa kwararawa yina Neman gudunmawa
Da gudu matan gida suka hankado d’akin,ganin hannunta kam akan mazantakarsa tana lilo, ya firgitasu lalle uwale za ta kashe rai suna Cikin gida
Duka suka rufeta dashi ,kafin da qyar suka qwaceshi
Rikicaaa ya watse can gefe yina ihu yina ,uwale Na sake ki *saki uku* Ashe dama ke makashiyace ban sani ba…allah ya isana…
Kukan kura tayi tana qoqarin cinmasa ana rirriqesa
“Kubarni da ja’iri bakinsa bai mutuba ai ”
***
Matan gida Koran fata fata sukayi wa uwale ,don su Kansu sunyi murnar rabuwar bello da uwale ko sa samu suyi tarbiyyan yaransu lafiya”
Bello kam saida aka dangana shi da gadon asibiti waje ta salu6e ta kumbura tai sintsir hausi ce me jinya itama tanayi tana allah shi qara tsiyar qarin aure kenan yau wa gari ya waya?akan aurenka da uwale ba tozarcin da bakayimun ba ,yanzu kuwa da nayi haquri gayinan duk allah yayi mun maganin Ku INA kallo”
“Ke dai hausi karki since ladanki,yin jinyar nan kikeyi don allah…
***
*Tuna baya*
Tunda bello aka tsaida ranar aurensa da uwale ,hausi take ganin rawan kai nau’i da suffa ,a lokacin suna gida iyayensa mamanshi ta ware masa fili tace yaxo ya danyi ginin qasa a lilli6e da sumunti ya kintsa matansa waje guda
Haka kuwa ya tarkata jarinsa ya qera gini lokacin biki aka sha biki…ranar kuwa da ango zai shiga daki abokansa Na kawosa suka shige d’akin uwargida su gaisa kafin su shigo…shikuma ya shige d’akin amarya ,ya ajiye kazar angwancin zai dawo gurin abokansa .saidai zumbur uwale ta miqe.
” yoooo INA kuma zuwa?
..Wai zan yowa abokaina jagorancine suzo Ku gaisa,kuma a taraku ayi maku fad’a da er uwar zamankii kuma babata da safe zata kuma sasantaku..
Tsidik ta mike ta warware mayafi ta gyara zaman shi aka
“To mu tafi d’akin hausin tare.. yaudai ranana ne ban bari aci min ko minti”
**
Duk nasiha da ban Baki abokansa sunyi masu itadai hausi batace komai ba
Da zasu tafi tayi masu godiya itama ta mike zata shige uwar d’aki
Sigina da ido uwale tayiwa bellon
Saiga bello Cikin rawar murya yina kiran abokansa da hausin wai su daddawo
“Yawwa hausi kwana nawa zanyi a dakin uwale?
” kaji wani rainin aqalu…adadin kwanakin da musulunci ta tsara maka mana kwana bakwai…”
“Haba hausi bansanki da baqin ciki ba. Ke kuwa ba tun kafin auren nan ba kince zaki qara mun kwanaki ba …don allah jama’a Ku bata Baki
Ya juya yina kallon abokansa
Sakin Baki hausi tayi cikeda mamaki
Lallai bello ko yanzu ya nuna mata yayi aure
” hummm shikenan Na qara maka sati biyu aci angwanci lafiya
A tare uwale da bello suka amsa da amin ,uwale harda godiya
Suka miqe suka tafi,itakuma ta shige uwar daki Cikin rad’ad’in 6acin rai
Yanzu shikenan Dan majalisar tarayyar birnin wandon da Nike taqama dashi ya zama mallakin mu mu biyu….
***
*Abun dariya yaro ya tsinci haqori*
Tun ranar da bello ya tare da uwale kullum bello akan network yike ,kwana hudu cur baya barci ,dare farai ana abu d’aya . tun yina Na marmari yanzu ya koma yin Na wuya
Gashi ta daina barinsa fita,ko d’akin mahaifiyarsa ya shiga saidai tsidik kiga ta banko labule ta shigo itadai karya Dade yazo a cigaba.
Bello kam ya shiga tashin hankali kullum yawo da zariyar wando kacau kacau a hannu ko daurewa baya iyawa
Hutu daya yike samu lokacin sallah..aikuwa lokacin zai gofana sujuda yina rokon wa uwale barci ko ya samu ya huta
Shedanci da karuwanci kuwa iri da kala
A baya babansa ita tasa yayiwa hausi kishiya saidai yanzu duk inda ta zauna sai tayi gulmar su
*littafin kud’i at regular 200 VIP 400 ,plz serious buyer kadai zasu biyo mu din jin yanda zaki biya plz. ,09065990265*
“Allah ya hada Dana da me farar qafa duk ya karkad’ar da komai nasa ya aurota bata tsinana masa komai sai karuwanci da suke isana dashi.. Na qwace huwaila ersa a hanun uwarta na bata kyauta amma da shike ba diyar arziki bane dare nayi zata turo mun ita su rife qyaure garamm
Bazakiji motsinsu ba sai wajen shad’aya shaura na safiya sannan zakiji qoshiyoyi suna qara a cikin faranti a dole suna karyawa
Da murya qwarqwar irin na soyayyun nan da suka tsofe a gida zakiji tana gardama dashi
_Ahh ni Wallahi na fika loma…Ah lomana yafi naki_
To wannan tsinewar yazo qarshe yanzu nan zanje inyiwa tufkar hanci”
Ta dasa aya tana kallon qawarta sala mai waina,ta zura mata ido mai ma’anar domin gyara ko shawara…
_Typing ✍_
*HARIJI*
(Original Romantic love story)
Post a Comment for "Hariji Book 1 Page 9-10"