Hariji Book 1 Page 15-16
Free page 15&16
*Alheri writers Asso.*
By…Oum Aphnan
Cikin hukuncin Allah da taimakon Æ™uliya ,komai na case É—in ummi ya warware,kuma an gano duk Abunda ya faru,ya farune bisa kuskure,yanda kuwa abun ya faru shine ,a lokacin da sukaje scan É—in,da shi mai scan É—in yayi ya fidda result sai ya aiko wani É—an practical ,yakaima meyin typing result É—in da printing yayi,sai mistakingly ya saka na wata anata…Ummi taji daÉ—in bayyanar wannan gaskiyar batun kukan da ta jima tana riÆ™ewa ne ya samu damar kuÉ“ce mata a yau…godiya kam ,lawyan da aka haÉ—ata dashi ya shata kamar mene ,saidai taso tasan wanda ya taimaketa amma hakan bai samu ba.
Two weeks later
Saiga sanarwa daga kotun Æ™oli na Æ™asa ,tasa acikin dokokin Æ™asa ,Æ™arÆ™ashin nurses and midwifery council Amendament list ,cewar _”Duk wata nurse/midwife da tayi attending haihuwa ,ta tabbatar ta nunawa uwa/mazumuntarta jaririn cikin jininsa da cibiya tun kafin a fidda uwa,don sauÆ™aÆ™a faruwar matsalar,zargi gameda satan jarirai,koda bata hayyacinta ku É—aketa zafin duka ya dawo da ita hayyacinta ,sannan ku nuna mata”_
Mamaki ummi tayi ,wai takaina ne aka zartar da wannan dokan? Who am i, in nigeria??
***
*Ƙuliya* bai samu damar ganin plate disc mai Æ™unshe da duk videon abubuwar da ya faru na shari’arsu ummi ba, saboda ,matsalar rashin lafiyar Adnan daya dama masa lissafi.
Don A halin da ake ciki ƙaramar matsala ta zama babba,bayan fidda bullet ɗin dake cikin jikinsa angano ya kamu da cerebral malaria,ga seizures wanda yayi leading ɗinsa into comatous state.
Yanzu haka suna wani Asibitin kuÉ—i mafi tsada a birnin abuja,wanda akowanne rana suna cin miliyon É—aya da rabi ,na managing patient.
Saidai rashin canji a lafiyar Adnan ,yasa ƙuliya yanke shawarar fitar da adnan zuwa Indonosia,saboda akwai wani chinese da akayi masa tallansa akan ƙwarewarsa wajen treating irin disease condition ɗin Adnan ɗin.
**
*9 na safe Kelina Hospital gwarinpa Abuja*
Adnan kwance yike unconscious a kan hospital bed din quliya yina zaune akan kujeran gefensa yina shafa sumar kansa yina tofa masa addu’ar dik da yazo bakinsa, tun yinayi a 6oye har ya farayi a bayyane
Hajiya Adama (Banufiyar matarsa) ne ta taso tana gyara mayafin kanta “Alaji sanda fa aka kawo son daga yawon dare yike ,so be kamata kai fushi damu don bumuyi attending dinsa da wuri ba,kasani ko muna barci ne? Kayi mana kyakyawar fahimta Yalla6ai…kuma tunda son yakai wa’innan kwana kin yina coma state, y not a maidashi gida ayi masa na Hausa! Kashe kudin yayi yawa ,hospital d’innan akwai tsada aqalla you spent kusan 5 million a kwana ukun nan , in akayi converting dollars din da kayi masu payment zuwa naira.kar kudinka su qare a banza…
Rumtse ido yayi Cikin dandanan 6acin rai,har yinajin d’aci d’aci a makoshinsa
” Adama out from here!”
Ya bata umurni Cikin hargagi na Wanda yike Cikin tsananin fushi
Sototo tayi bata kuma motsa ba
“Adama ki fita kina irritating d’ina.Adnan shine kadai hope d’ina a yanzu”
“Amma Alhaji ka duba kudin da ka kashe,kuma ba asan Wanda zaaci a gaba ba …”
Ke,wai ina ruwanki da dukiyata? Ke sanda tsohonki yayi jinya how many millions na kashe a Tanzania ?
Rau Rau tayi da ido kamar zatayi kuka
“Alhaji harda gori?dadin ta dai baban nawa ya rasu sai ka bishi qarqashin qasa ya biyaka…amma daga gyara kayanka?
Ta qarasa magana muryarta na Neman shaqewa
Yes ke kikaja ,kuma akan son zan iya qarar da duk abunda na mallaka a duniya
” ai sai ayi mu gani in tusa zai hura wuta ,a gama wahala ya qare ya mace”…
“Ohhhoooo thank you Adama da kika fad’a mun qudurin ki akan son,to wallahi in adnan ya mutu sai nayi qararki, da shedar maita kuma saina tabbatar duk tsatsagun zuri’arki sun wuce jail…
Nnenna(Igbon matarsa) had’e kai da (yaroban matarsa) Abike suna gulmar ita adamar da turanci
” Eh matar so yau Asiri ya karye yalla6ai yayi mata fad’a…
Kallonsu tayi ta tsage da kuka, ba fadar da yayi mata yafi mata ciwo ba ,ya tankacin yarfata da yayi a Cikin kishiyoyi.
.
Kallon su dukkansu yayi ,sannan ya korasu duka waje cikeda sababi yina rokonsu karsu sake zuwa masa kurum.
***
Alhmdllh ,tafiyarsu madam Nnenna ba jimawa saiga yatsun qafar adnan ya fara motsi ,lokacin quliya yina duqe yina karatun Quran a kusa da kansa ,Cikin nutsatsiyar murya
“Dad helppppp!”
Kalmar da ya doki tympanic membrane dinsa kenan ,Cikin karadi na Wanda baya a hayyacinsa
Hakan ba qaramar tsoratar da quliya yayi ba
Da sauri ya duqo gurin kunnensa yina rad’a masa Kalmar ,Cikin dakiyar rai,ya rigada ya cire masa rai kawai da rayuwa,all his thought mutuwa zai yi
Sosai hawaye ke fita daga idonsa ,yina masa fatan haduwa da malaikun rahmah
Daga office d’in Team b,suna kallon abun da ke faruwa ta system dinsu ,don haka da sauri suka yi rushing zuwa wajen su cikeda murna
***
Saida Æ™uliya ya idar da sallar wadha ,kuma yayiwa allah godiya a sujuda da ya farfaÉ—o masa da yaronsa cikin Æ™oshin lafiya,sannan ya samu damar kunna wayoyinsa ,yina duba duk saÆ™onnin da aka tutturo masa ta cikin email da sauransu,saida ya ga Amandement É—in nurses and midwifery council of nigeria ,sannan plate dics É—in shari’ar su ummi ya faÉ—o masa a rai.
A nutse ya ajiye wani er ficilan caxbi mai kyau,yina É—aukan ido ,yaje gaban wani cupboard ya É—auko disc É—in,ya jona a laptop É—insa dake kan gadonsa ,ya kulla yina kallo daga inda yike zaune akan praying mat É—in da ya idar da salllah…shariar ya Æ™ayatar da shi sosai,kuma sosai Tausayin ummi ne yaji yina addabarsa ,wanda ya kasa gane a wani mizani zai É—aura, *Tausayinta yikeji? Ko kuwa soyayyarta ne*
Tabbas wannan abunda yikeji ,yafi kama da ace ,soyyayartane ya daÉ—a tsirga masa a rai,Saidai zullumine ya bai baye masa rai a nan take yaji Zuciyarsa na harbawa fat…fat… tunawa da zallar Æ™uruciyarta ,anya zata soni?? Anya zata iya zaman kishi da mata irin mata na??? Kai da kamar wuya gurguwa da auran nesa!!!
Sosai kansa ya É—auki chaji amma kuma ,yina wani tunani sai yaji sanyi a cikin ransa ,a hankali ya tashi ya rufe laptop É—insa ,yina zancen zuci a hankali
*This is the right time ,that i ought to tell you who i am,My real feature i mean*
**
Sauƙi Alhamdulillah jikin Adnani,sai kyau yike sake yi,saidai komai nasa sabo ya zama ,tindaga cin abinci,tafiya ,magana ,kai komai saida aka koya masa
Ƙuliya yayi farinciki da hakan ,don haka yau ya É—auki aniyar tafiya *Kano* don cika daÉ—aÉ—iyar Æ™udurinsa na kusan shekaru uku da suka gabata…
*Ɗorayi ƙarshen waya, kano Nigeria*
Yau gidansu ummin ,tsit yike duk ma zauna gidan sunfita Neman abunda zasuci na rana yayi saura daga ummi dake zaune tana dakan qulin da zatasha garin kwaki,sai kuwa bazawara uwale ,Wanda zuwa yanzu ta goge mayukan bleaching take shafawa na mutuwa,tayi fara tarr kamar takarda ,kunnenta huji biyar duk ta jeresu da dan maqale sai can saman kunnen ta huda daya ta saka azurfa ,ita a ganinta gayune batasan en mad’igo ke sakawa ba
Ga hancinta tasa hajara (keken maza) ta 6ula mata huji har biyu a hanci guda d’aya, ta zura masu siraran abun hujin hanci ja da fari
Bakinta kuwa haqorin hajjine sama golden qasa fari,wani mugun qamshine ya doki hancin ummi ,Wanda tsabagen qarfinsa har yina mata d’aci a maqoshi
Fitowa tayi Cikin shirin fita tasha gayu Cikin pencil siket na atamfan roba, ta buga daurin ture kaga tsiya,qafarta takalmi toms saidai ta sakama qafa daya sarqa sai walwali yikeyi
Kallon ummi tayi ,ta kya6e fuska ,sannan ta rataya Jakarta ta sa6a mayafi a kafad’a.
“To hajiyan en gida mu mun fita bid’a addu’ar babban mutum ,mai babban aljihu
Kallonta ummi tayi taja tsaki
” allah ya tsari gatari da saran icce wallahi da in maki addu’ar Neman kwarto mai kudi gwara in yiwa kaina fatan cholera”
“To dussa rufe mana massai(bakin ummi take nufi da toilet)
Sai naga ke da kika qi wayewa ,sai an magana kice heeeeee aure zanyi…banza haryau ba mashinshini kinyi badago kamar daddawa a kasuwa…
” Anty uwale don allah kije abinki”
Yanzu kuwa ,aini fita ta gani ,kinga alhaji maiwada ma ke kirana ..
Ta soma magana da kanta tana latsa wajen green na qaramar Nokia ,alamar dauka
“Rabin raina.. Antashi lafiya,ya kwanan kud’ad’enka…
Da sauri ta yi hanyar waje tana d’agawa ummi hannu alamar ta tafi ,tana cigaba da waya da Wanda ta kira da alhaji mewada
*Wannan shine page din kusa da qarshen na kyauta ,in baki biya kudinki ba hanzarta biya ta 7782217014 ,fcmb, Mohammed hassana ko vtu da MTN card ta 09065990265,nagode masoyan Amana*
_Typing ✍_
*HARIJI*
(Original Romantic love story)
Post a Comment for "Hariji Book 1 Page 15-16"