Gidan Aunty book 2 Page 5-6
BOOK 2
Page 5&6
Da Sauri Abeey ya nufi king da jini ke zuba a hannunsa, idanuwansa sun ‘kara rinewa,
kallan dada kawai yake da tafi kowa firgita , a zuciye ya ‘kara furta “ ina matata ?”, yanxu ma babu Wanda ya iya amsa masa, Abeey na ri’ke hannun Ya fusge ko kallansa be yiba , dada ya nufa kamar zai tsakota, ya ‘kara furta “ ina matata?”, yanxu kam dada rud’ewa tayi ganin yadda ya canza mata kamar ba shiba , itama sai ta ‘kara rud’ewa har tana bugewa sabida yadda tayi baya baya kamar zata fad’i abeey yayi saurin tarota, duk da haka king be hakura ba ya ‘kara nufarta fadan fadan , gabaki d’aya idanuwansa sun rufe , zai ‘karayin wani maganar Abeey ya d’auke shi da mari, azuciye ya juya kan abeey,jijiyoyin kansa na ‘kara Tashi, shi kansa Abeey da yayi marin saida yayi danasanin marin nasa , lokaci d’aya yaji shakkar d’an nasa, kallo d’aya king yayi wa abeey ya nufi kofar fita ko takan wayarsa be biba , gabaki d’aya ukhti da ummey ‘ko’karin tsayar dashi suke musamman ydda Jinin hannunsa yake ‘kara zuba, doctor d’in da ya shigone yana ciwan king, ‘kokarin dakatar dashi doctor yayi, shima king ya d’auke fuskarsa da mari, yana fitowa zaki yabi bayansa cikin sauri ganin yadda ransa yake a had’e , da gudu ya bud’e wa king mota suka bar hospital d’in, tunda ya shiga cikin mota idanuwansa suke a rufe har suka ‘karaso cikin gida, Daidai part d’insa zaki yayi packing, kusan 5 minutes idanuwansa suke a lumshe , cikin kakkausar muryasa ya furta “ Me ya faru?”, sanin ba a ‘bata masa lokacine yasa zaki labarta masa abunda ya faru, tunda ga accident d’in da yayi har zuwa ‘batan Tahee, da yadda aka bincika ba a sameta ba, har kama sojojin da yayi saida ya sanar masa, lokacin da king ya bud’e idanuwansa shi kansa saida ya tsorata da ya nayinsa, gefen wuyansa wata Jijiyace ta fito masa , door d’in kofar ya bud’e tare da sakko da’kafarsa , cikin Sauri sauri ya shiga Cikin building d’in nasa kamar yana so ya gasgata abinda yaji da kun nansa “ Almost a month ?, itama ya rasata kamar yadda ya rasa shi”, tafiya ya soma yi cikin falon da yake da d’an duhu, da ‘karfi yake furta “ No hakan bazaiyuba, I don’t kiss them , bazan iya ba , my wife , my baby, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un “, yadda zuciyarsa take bugawa da sauri sauri ne yasashi yin baya , ga wani irin jiii da yaji yana neman kayar dashi, wani show glass da ya turene ya fashe gabaki d’aya akasa , muguwar yan kan da yayi sai faman zubar da Jini yake, gabaki d’aya Wajan ya baci, saitin zuciyar sa ya dafe, yana rintse idanuwa, bai da mu da yadda Jini ya ‘bata saba , tsugunnawa kasa yayi tare da runtse idanuwansa , da sauri abbey dake shigowa ya nufi inda yake , idanuwansa sun ‘kan’kance kamar yayi wa king kuka haka yake ji, araunane ya furta “ Am so sorry Tahnoon, Allah yayi bazamu ganta yanxu ba , but har yanxu ana kan bincikenta , nasan duk lefi nane da na sani lokacin da zamuje asibitin har da ita, kayi hakuri..” rufe wa abeey baki yayi tare da sakar masa kyakkyawan murmushi, kyakkyawan murmushin dake d’auke da abubuwa masu yawa a ciki, yadda idanuwansa sukayi mugun canzawa ne yasa be kalli abeey ba , ya kara sakar masa wani saban murmushi “ ba laifin ka bane Abeey, I lost Akhieeee for long time, yana sona sosai, and now I lost my wife again, and also her baby?, No Abbeey, tabbas a wannan karan abunda ya faru had’I, I don’t need anyone now , duk Wanda na tabbatar da sa hannunsa, I swear Abeey ko wanene bazan ‘kyalesa ba, the accident, and also ‘batan matata duk zan bun cika ..” rufe masa baki abeey yayi, “ ka dena fad’an irin haka , bana jin dad’i Allah ya ji ‘kan muhammad, na ro’keka da Allah da manzan sa karka yiwa kanka illa, tun lokacin da kayi accident dinnan Ummey bata bacci sosai, bata cin abinci sosai, kasan halin samreen idan ta sawa kanta abu, tana tunanin zata rasaka kaima , na ro’keka ka kwantar da hankalin ka ko suma nasu zai kwanta “, murmushi ynxu ma king ya saki be ce wa abeey kuma ba ya nufi stairs , a
Jiyar zuciya Abeey ya sauke kafun ya kira sumayya ta gyara Inda glass d’in ya baci, gabaki d’aya falon ta had’a ta gyara , sai gashi ana shigo da kayan abincin daga part d’in Mamy da momy, su firdausi na shigowa dashi bayansu kuma samreen ce itama d’auke da wani ‘karamin tray a hannunta , kallan abeey tayi abun tausayi murya a hankali ta furta “ Abeey yana ina ?”, yana sama , ki bashi 20 minutes sai kije and please ki tabbata yaci abincin sannan ki masa dressing d’in hannunsa, Nima zan dawo nayi baki, jinjina masa kai samreen tayi sai da dau kusan mintuna 30 tukunna sannan ta nufi saman d’akinsa, gabaki d’aya ya faffasa glass da yawa na d’akin, sosai ya har gitsa d’akin yana zaune kan sofa idanuwansa a lumshe Jini na ta zuba daga hannunsa , da sauri samreen ta ajje tray d’in hannunta, da ‘kyar take wucewa Sabida in mutum be kulaba zai iya jin ciwo, first aid box ta d’auka zata rike hannunsa ya fincike, ‘kara ri’ko hannunsa tayi ya ‘kara fincikewa, a karo na uku da ta ri’ko hannunsa zai fuske itama a zuciye ta daka masa tsawa, kallanta yyi da mamaki gnin hawaye a fuskarta sai kuma cikin sanyin murya ta furta “ Dan Allah ka tsaya ba danni ba “, kallanta yayi be ce mata komai ba har ta gama dressing d’in ciwansa,tray d’in abincin ta d’auko shi kuma ya mi’ke tsaye zatayi masa magana ya ‘barar da tray d’in abincin, a zuciye cikin d’aga murya ya furta “ get out of my room” da mamaki samreen ta kallesa hawaye a kan fuskarta, “ Ni kake cewa na futar maka a d’aki? Yayi kyau , zan fita daga d’akin ka bani 10 minutes “, bata jira amsar saba ta fara gyara d’akin yana tsaye shima dafe da goshinsa, tana cikin gyarawa kwalla ta caketa da har saida tayi ‘kara da
Sauri ya nufeta zai ta’basa ta dakatar dashi” kana ka kuskura ka tabani, kayi abunda ka keso “ Tana gama fad’ar hakan ta nufi kofa da niyar fita ya ri’ko hannunta “ Ukhtii why please? Zuciya ta ba dad’i, I’m feeling lonely, ina jin kad’ai ci, ina ji kamar….”, rufe masa baki ukhtii tayi itama hawaye cikin idanuwanta” komai yayi zafi maganinsa Allah, karka damu jikina yana bani zata dawo, zaku haifamana baby da yawa , ummey da abeey zasu zama grand parents, dada zata zama grand grand ma , ummey bata ci abinci ba tun jiya na ro’keka ka kwantar da hankalinka ko natama zai kwanta kaji?” Kanshi ya jinjina mata, itama saida yayi mata dressing d’in hannunta kafun ta bar d’akin cike da tausayinsa.
************
*********************
A ‘bangaran Abeey kuwa babban Amininsa tun na ‘kuruciya ne yazo duba king, sabida tafiyar da yayi kafun al’amarin ne yasa bezo ba , Abbey yana zuwa falourn sa ya tarar da Aminin nasa , kamar yara haka suka rungume juna , ba kowa bane face Alhaji kabeer, gefenshi kuma khaleed ne , shima hugging din Abbey yayi , cike da alhinin abunda ya faru, kallansa Alhaji kabeer yayi” ban ji dad’in abunda ya faru da son d’ina ba ,shiyasa nace dole na zo na duba shi da kaina dan nasan halinka kamar yadda ka’ki zuwa d’aurin aure na dukda nasan kana da babban dalili, to wannan karan dole a ‘kara d’aura zumunci, suma iyalina insha Allah wata rana zan kawo su,” murmushi abeey yyi “ baka canza ba har yanxu , ina zahra ta ? Nayi kewar ‘yata “, gaishe Abeey Khalid yayi, Daidai lokacin da ilham take shigowa falourn bakin ta d’auke da sallama , gaishe da Alhaji kabeer tayi , kafun ta gaishe da khaleed da ya tsareta da idanu, a fakaice ta dalla masa harara da yasakashi sakin murmushi, tana fita Alhaji kabeer ya furta “ kamar ilham ? “ Aushe baka manta sunayensu “ cewar abeey “ tana zan manta sunayen ‘yayana” tana fita da munti biyar khaleed ya mi’ke gabaki d’aya kallansa sukayi , “ zan d’an sha iska a waje ne , kafin king ya fito” jinjina masa kai sukayi a tare , ajiyar zuciya ya sauke shima kafin ya fito daga falourn, yana fita ya nemeta ya rasa gabaki d’aya bata filin Wajan, ‘karamin tsaki ya saki, tare da bugun ‘kafarsa har zai juya sai ya hangota tafito daga part d’in su zata nufi na dada da sauri ya ‘karasa inda take , d’aure fuska ilham tayi shikuma ya sakar mata murmushi “ kinyi kyau “, banza tayi dashi zata wuce ya dakatar da ita “ me yasa kike haka ? Nasan kin sanni , inaso muyi magana “ sai yanxu ta gane fuskarsa sosai , a hankali tace “ yaya khaleed ?”, oh da baki ganeni ba? , kai ta d’aga masa , ka canzane naga ynxu har d’an ‘kiba da kumatu kayi shiyasa ban gane ka ba sosai , sai anjima “, saurin me kike ? Ba komai , cewar ilham ,” amma kike guduna?” A hankali ta furta “ kayi hakuri “ kai ya jinjina mata kafin ya mi’ko mata kantamemiyar wayarsa “ samun phone number d’inki akwai maganar da zamuyi”, ba musu ta saka masa number d’in tai masa sallama ta bar Wajan, murmushi khaleed ya saki yana bin bayanta da kallo shi kadai yana sakin murmushi, king da ya hango ne yasashi sakin murmushi duk da yadda ya ga fuskar sa a had’e ba fara ‘a yasan daman za a rina , duk da yanayin da king yake ciki hakan be Hanasa hugging d’in khaleed ba kamar yadda shima khaleed d’in ya yi , fuskarsa d’auke da murmushi ya furta “ sorry dude “ be ce masa komai ba ya jinjina masa kai, tare suka nufi falon abeey, Alhaji kabeer na ganinsa shima yayi hugging d’insa “ my son? Ya kake? Ya jikinka? Take heart komai zai daidaita please bana san ganin ka cikin wannan yanayin”, shima king bece masa komai ba bayan gaisuwar da ta had’asu , minti 5 ya mi’ke zai fita khaleed yabi bayansa direct part din ummey suka nufa , gabaki d’aya jiyai yana bukatar mahaifiyarsa yau ko tunanin Ammey be yi ba , ummey na ganinsa shida khaleed ta saki murmushi , shima khaleed na ganinta yayi hugging din ta “ ummey nayi kewar ki sosai da sosai “, wani murmushin ummey ta saki tana kallan king “ Nima nayi kewarka sosai my son “
Ni kuma fa?” Cewar samreen da ke fitowa, murmushi yasakar mata “ Ukhti waya isa ya manta dake kin manta kece ta gaban goshina “ hararar sa tayi , kana dai guduwana sabida nace Kayi aure ko? “ kai ya d’an sosa kadan “ karki damu ankusa insha Allah “ Allah yasa cewar ummey. King na zaune ba abunda yace mikewa ummey tayi batace komai ba ta kama hannunsa zuwa dinning, mamaki ne ya kamasu samreen , ukhti har da yi musu vidoe ganin abun mamaki, abunda ummey ta dad’e batayi ba , da kanta ta zubawa king abinci, shima mamaki ne ya kamasa Amma be nuna hakan ba, mamaki be gama kamasu ba sai da ummey ta d’auki spoon zata bawa king abinci a baki da kanta , ukhtii harda tsallan murna ita da khaleed kamar wasu yara suka fara musu vidoe , murmushi ummey ta sakar wa king kamar wani ‘karamin yaro ta furta “ haaw” bud’e bakinsa kuwa yayi ummey ta fara feeding dinsa, 5 spoon yayi ya d’auke face dinsa amma ummey ta hanasa Tashi saida ta tabbatar yaci sosai , shima king saban abinci ya zuba ya d’auki spoon zai fara bawa ummey abinci, samreen kamar ta taka rawa Sabida ganinsu da tayi cikin wannan yanayi, d’an harararsu king yayi , itama ummey bata bi ta kansu ba ta kama hannun king sukabar Wajan . Ai khaleed kam saida ya taka rawa ko ba komai hankalin abokinsa zai kwanta.
??????
BUNKURE
Tsawan wata d’aya abubuwa da dama sun faru cikin wannan yanayin, ciki har da islamiyya da Matan gidan Suka koma , da yamma kuma suna awarar siyarwa, idan babu makaranta kuma da safe suna yin Koko da ‘kosai, gabaki d’aya rayuwar gidan ta canza , babu Wanda zakaji yana fad’a da d’an uwansa, duk Wanda yyi sallah yanxu sai yayi wa oumma addua dan tayi musu Hallaci sosai , ta mayar musu da alkairi akan sharri, ta tallafesu a lokacin da suke bu’katar taimako, gabaki d’aya sun zanca , ga gyaran gida da Alhaji kabeer yake musu bayan kasuwa da ya saka mazan, duk wannan abun da ke faruwa oumma bata san yanayinsu. Har zuwa tsawan lokacin nan kuwa babu Dije ko bintalo babu alamarsu, Suma mutanan gidan gabaki d’aya babu Wanda ya damu da su, kullum Burunsu Allah ya ‘kara had’a kansu dan ba ‘karamin azabtuwa sukai wajan Dije ba ,yanxu ma marka d’an awara aka kawo musu matan gidun suke yi, kaka tabawa ma yanxu kullum cikin addua take wa oumma da muhammad, bata aikin komai sabida ciwan kafar ta , yan gidan ne Suke komai , babu nuna hantara a tsakaninsu, gabaki d’aya babu Wanda zaice akwai wani abu da ya ta’ba had’asu , sai ma insunga mutum yayi ba Daidai ba suyi kokarin dakatar da shi nayi masa nasiha .
*********
*************
******************
AMMEY ????????????…….
Lokacin da Ammey ta samu labarin farkawar king zaucewane kawai batayi ba , a har gitse ta shiga cikin d’akinta tana neman zoban tsafinta, bata Ankara ba taji ansha’ko wuyanta ta baya an bugata da ‘kasa, bata Ankara ba taji an ‘kara sha’ko wuyanta, mutumin da suke magana kwanaki ne yanxu kamar kullum fuskar sa a rufe , cikin ‘bacin rai ya furta “ kikace zaki kashesa kafin farfad’owarsa, me yasa kike ‘ko’karin ‘Bata mana aiki ? , ya mukayi dake ?karde kin fara tausaya musu?” A wahala Ammey ta fusge kanta daga sha’kar da akai mata,” karka ‘kara sha’keni haka ? me ya kawo ka d’akina ? Ka fice ka bani waje” wata ‘yar iskar dariya ya somayi kafun ya fincikota ya turata kan gado, girgiza masa kai tayi “ karka matso Inda da nake “. ‘Dauke fuskar Ammey yayi da mari” kinaso kisan me ya kawo ni ko? Yanxu zaki ga aiki da cikawa ai “ yana kai ‘karshen zancenta ya hau kan Ammey duk yadda taso turesa abun ya gagara, shima cike da mugunta ya fara faffarkewa Ammey kayan cikinta, be tsaya bi ta kanta ba ya shigeta da mugun ‘karfi cike da mugunta, wata gigitacciyar ‘kara Ammeey ta saka Sabida azabar da taji amma duk da haka be saurara mata ba , cike da mugunta Yake binta, saida ya tabbatar bazata moruba ya mayar da wandan sa ya ‘bace gabaki d’aya inda Ammey take Jini ya ‘bata wajan dan ba ‘karamin ‘barna ya mata ba dukda kasan cewar ba yau suka fara ba, amma yau ko sabuwar amarya ??( Allah shi ‘kara Ammeey ??????).
???????
Kwanan khaleed biyu a lagos ya fara shirye shiryen komawa Abuja , already alhaji kabeer ya tafi shi tun aranar, sosai khaleed da king suka saka bincike tahee har yau babu ita babu alamar ta , gabaki d’aya ya canza ya koma asalin king d’insa mara fara’a , da surutu, tsakanin su ummey da abeey sai aka rasa wanene yafi kula da king, hatta su momy da mamy ba a barsu a baya , uncles dinsa ma sosai suka bada rawar ganin Wajan bincikar Inda tahee take, aunty ma tazo ta duba sa lokacin Amrah taje kidan su batasan da farkawarsa, Ammeey ce kuwa har yanxu bata shiga ba dan acewarta bata da lapiya, hatta abeey sai da yazo dubata amma bata ko ‘kafar king bata gani ba , dan har yanxu ko ‘kwakkwaran tafiya batayi sosai Sabida yadda ta ke tafiya kamar ‘yar kaciya,kowa na gidan yazo dubata banda king da hankalinsa yake kan iyalinsa.
Karfe 2:30pm jirgin su khaleed zai Tashi, 12:20pm yana zaune falan dada , yana danna wayarsa su sumayya suka shigo falon, gaishe dashi Suka yi amma gabaki d’aya hankalinsa yana kan ilham , sanye take cikin doguwar rigar atampa, ta yi d’aurin zahra buhari, bakinta sai shinning yake , yadda yake kallan ilham yasa sumayya kallansa a fakaice tana danne dariyar ta da ido tanunawa firdausi, ka she mata ido ta tayi suka mi’ke a tare , kallan su ilham tayi” Ina zaku?” Danne dariyarta firdausi tayi kafun ta furta “ karki damu ynxu zamu dawo “ basu jira amsarta ba suka bar falon, da harara ta bisu zata mi’ke taji saukar muryarsa” please ko zan iya samun ruwa ?” Jinjina masa kai tayi kafun ta nufi fridge , ruwan ta d’auko masa had’e da lemo sai cup,tana ajje masa yace ta zuba masa kamar zatayi ihu haka ta zuba masa , “ kinyi kyau sosai kamar sarauniya”, da Sauri ilham ta kallesa zuciyarta na bugawa da sauri sauri, shima idanuwan nasa ya zuba mata, da Sauri ta d’auke nata , “nagode “, har yanxu be d’auke kallansa akanta ba , zata tafi ya furta “ please ki zauna” gabaki d’aya sai nutsuwarta ya d’auke ga bugun zuciyar da take samu , idanuwansa har yanxu akanta, waje ta samu ta zauna ba dan taso ba “ yanxu zan tafi, amma zanyi kewarki”yanxu kam gabaki d’aya ya gama kwancewa ilham notikan kanta, “ me yake nufi ?” Take tanbayar kanta , bata ‘kara sham mamaki ba sai lokacin da ya furta “ please ki kalleni ko zanji dad’i” kunya ce ta kama ilham kamar ta saka ihu, kujerar next to her ya dawo yana kallan yadda ta sunkuyar da kanta ‘kasa “ please baby kalleni “, yadda taji zuciyarta na tsanan ta bugu ne yasa ta mi’kewa zata gudu yayi saurin shan gabanta “ ba sai kin gudu ba ni bari na tafi tunda bakya bu’katar gani na, wani ‘karamin box ya d’auko ya ajje mata akan table , “ gift d’in kine wannan, please ki kulamun da kanki”, yana kai ‘karshen zan cansa ya soma tafiya, zuciyar ilham ce ta soma bugawa ga wani abu da take ji ‘kasan zuciyar ta ganin kamar be ji dad’i bane yasa ta zauna wa kan kujera tana bin ‘karamin box d’in da kallo, sumayya da firdausi ne suka fito daman ba tafiya sukai ba , cikin tsokana feedy ta furta “ please Baby”dariya summy ta saka itama kafin ta furta “ ki kulamin da kanki”, pillow ilham ta d’auka ta jefa musu, Wana ta suka ‘karaso tare da d’aukan box d’in zasu bud’e tayi saurin fusgewa , da ‘karfi ta furta “ banasan gulma”, tafawa summy da feedy sukai lokaci d’aya ganin yadda ilham ta gudu.
????GIDAN AUNTY????
07041879581
Mss Lee??
Book 2
Post a Comment for "Gidan Aunty book 2 Page 5-6"