Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Gidan Aunty book 2 Page 14-15

BOOK 2

Page biyu na had’e muku na jiya da na yau …. ??
Page 14&15

Ita kanta tahee bata san lokacin da dariya ya kwace mata ba musamman yadda ta hango wawulon Ammey ,daka musu tsawa Ammey tayi rai a ‘bace , sai a lokacin suka kula da


abunda Suka ai kata , gabaki d’ayansu shiga taitayinsu sukayi ganin yadda ranta ya ‘baci, wata dariyarce ta so kama taheee amma take ‘ko’karin danne ta gudun kar Ammeey ta ‘kara zuciya, cikin muryar fad’a ta ‘kara daka musu tsawa “ ku ‘bace mun dagani”, bashiri kuwa suka bar Wajan , tahee na shiga d’aki ta ‘kara fashewa da dariya ita kadai idan ta tunano bakin Ammeey sai ta ‘kara fashewa da dariya , knocking d’in dakin asabe tayi kafun ta shigo ciki kai tsaye, Allah ya te mako tahee bata cire face d’in ta ba , abincin ta asabe ta mi’ka mata itama idan ka kalleta zaka san da fara’a a kan fuskarta, lokaci d’aya kuma tahee da asabe suka ‘kara fashewa da dariya sai da sukayi me Isarsu tukunna asabe ta bar d’akin,breakfast d’inta tahee taci hankali kwance tana tunanin shirin da zata yi nagaba kar Ammey ta gano ta . 12 : 10 asabe ta ‘kara zuwa kiran tahee , yanxu ma abincin rana suka fara shirye shiryen yi fuskar kowa da annashuwa musamman tahee da take yi da biyu, har lokacin kuma tun da Ammey ta shige d’akinta bata kuma fitowaba hatta breakfast kai mata a Kai. Yanxu ma lafiyayyen lunch suka yi kusan rabin aikin asabe ce ke yi,sabida kallan tahee da take a bata waye ba bata san yadda ake abincin ‘yan gayuba , suna Kammala girkin asabe ta zubawa Ammeey cikin babban tray bayn ta zuba komai da komai cikin warmer, mi’kawa tahee jug d’in juice tayi ita kuma ta d’auki tray d’in “ Abincin Ammey ne tace na kai mata d’akinta ni kuma sun mun yawa shiyasa zaki rakani kinji”, toh Kawai tahee tace mata dan ko ita da Ammeey ta kawo ta bata ta’ba shiga d’akin ba sai ynxu da zata shiga , bakinta d’auke da addua ‘kasa ‘kasa ta biyo bayan asabe lokacin data bud’e mata kofar d’akin, Ammeey dake kishingid’e kan gado ce ta d’ago azabure , cikin firgita da tsoro gabaki d’aya ta Amma ta da hakwaranta da Suka jire , jikinta har mazari yake da ya bawa tahee mamaki, wani tsawa ta daka musu da Suka ji har saman kansu “ Me ya kawo ku d’akina na rawa asabe ta nuna tray d’in hannunta , a rarrabe ta furta “ da daman abincin ki ne muka kawo miki ganin baki fito ba…” bata ‘karasa ba Ammeey ta kwashe fuskarta da mari sakin jug d’in hannunta tahee taji jiki na rawa zata soma bawa ammey hakuri ta nuna musu kofa “ kafun ranku ya ‘baci banasan ganin d’aya daga cikin ku anan , ku ‘bace mun dagani” cike da Tsoro tahee ta nuna jug d’in da ya fashe “ hajiya bari na fara kwashe abun tangaran nan “, bata kai karshe ba Ammey ta ‘kara daka musu tsawa “ nace ku fita ko?” Bashiri gabaki d’ayansu suka bar d’akin, tahee harda janyo mata ‘kofa, tana ganin ‘bacewarsu ta zu’be ‘kasa tana dafa kanta “ nashiga uku meyake shirin faruwa dani? “ ‘ko’karin danna zobanta take amma ciwan bakinta ya hanata dan tasan abunda zai biyo baya , tana tsugunne a wajan kamar wani aljani ya bayyana a d’akin, inda Ammey take ya nufa shima gabaki d’ayansu a firgice “ me kike shirin aikatawa? Tonuwar asirin mu kike so ko kuma me?kinfi kowa sanin ‘ka ‘idojin bokanya, kara na biyu da kika ‘kara ‘bata mana shiri, bazan lamunta ba “ , na fad’a miki bazan lamunta ba, idan kika ‘karayin kuskuran akaro na uku to tabbas jininki ya zama salwantaccen,” yana kai ‘karshen maganar sa yayi wurgi da ita saida kanta ya bugu, shima gabaki d’aya hankalinsa a tashe ya ‘kara ‘bace wa daga cikin d’akin. Cikin d’aga murya da fita hayyaci Ammey ta soma magana “ bazeyu ba tabbas Kema kande lokacin aikin ki yayi , shirina bazai ‘baci ba, daga rana irin ta yau , aikin da ke kanki zai fara “ ita kad’ai sai surutai take yi .

Tahee kuwa ranta fess suka ci gaba da ayyukansu bayn sunyi sallah, har yanxu idanunta na kan kofar da yah moh ya sanar da ita akai amma har ynxu shiru Ammey bata shiga ciki ba . Sai wajan yamma Ammey ta fito daga cikin dakin , daka kalli fuskarta kamar hadarin kaji, har lokcin le’banta daya kumbura be saceba, “ kande , kande “ , Ammey ta dunga kwalawa tahee kira , jiki na rawa tahee ta zo ta zube mata , kare mata kallo Ammey tayi ganin yadda jikinta yake rawa , kafun ta mi’kawa tahee wata ‘yar ‘karamar jaka , da Sauri kuwa tahee ta karba “ zaki ga bangarori da yawa , ki irga na ukun ciki daga hagu , idan kinga ‘yan mata a falon kice kina neman dada sai kibata, karkiyi kuskure fa “, ba’kin hakwaranta tahee ta bud’e mata “ insha Allahu hajiya bazanyi ba “, kamar sa kai Ammeey tayi daga ganin hakwaran tahee. Da Sauri tahee ta nufi kofar fita , da’kyar ta iya bud’e kofar acewarta wahala ne da kofar ‘yan gayu tana fita har zata nufi part din dada ki tsaye sai ta fara irgawa kamar tanasan cinkar part d’in, sai da tayi almost 5 minutes tana ‘karewa ko wane part kallo kafun ta nufi part d’in dada wani irin sanyi da iska me kamar hadari yana busata. Tana shiga kuwa ta tarar da su ilham sai baman za’ban kaya suke , da sallama tahee tashigo palour gabaki d’aya kallanta sukai lokaci d’aya kuma suka amsa mata sallamarta.jakar ta mi’ka musu cike da barkwanci ta furta “ wai hajiya ce tace a bawa dadu(dada)”,gabaki d’ayansu kwashewa sukai da dariya kafun ilham ta furta “ dada ko?”, washe baki tahee tayi “ kwaran kwatse haka tace , sunan yan gayun ne nakasa fad’a shiyasa “, yanxun ma wani saban dariya suka saki , Daidai lokacin da dada take Fito wa daga cikin d’akin, binta da kallo tahee tayi “ itama ta ‘kara tsufa, farin gashin kanta ya Fito sosai “, cike da girmamawa tahee ta tsugunna ta gaishe ta lokacin da taji hawaye ya sakko mata a ido , da Sauri ta goge gudun kar wani ya gani a gidan , itama dada ba yabo ba fallasa ta amsa mata kafun ilham ta mikawa dada jakar da tahee ta shigo dashi “ Allah sarki , kilishi bata gajiya da d’awainiya , toh Allah yayi albarka “, gabaki d’ayansu amsawa sukai da Ameen banda tahee . Zata tafi ilham ta tsayar da ita , “ kande bari na d’an aikeki part d’in ummey ki kai mata wannan”, tsayawa kallan bakinta da ta furta ummey tayi , zumudi nasan fito mata Amma tana ‘kara dannewa, ta mi’ka hannu daniyar kar’ba taji sallama a bayanta,da Sauri ta juya batasan lokacin da bakinta ya furta “ you!?”, tsayawa kallansu su ilham sukai , tahee sam ta manta suna wajan sai tayi saurin wayancewa da “ You You!! Nayi daidai ?”, yar dariya sukai tare da kawar da shashancin tahee, ajiyar zuciya Tahee tayi tana ‘kara bin Mimi da tashigo cikin shigar ‘yar aiki itama a fakaice ,” Yawwa shikenan tunda kinzo , ita kande ta koma wajan aikinta inyaso ke sai ki kai wa ummey kayannan “, kar’ban kayan Mimi tayi tana cewa toh , dariya duk ya cika mata ciki wato haka tace musu sunanta kande , ita kanta tahee saratu da aka kira Mimi sai da yaso bata dariya Amma tana dannewa , a fakaice ta yadda babu Wanda zai gansu Mimi ta d’aga mata gira d’aya da Sauri tahee ta d’auke idanuwanta tana musu sallama, ita kad’ai a ranta take magana “ yarinyar nan so take asirin mu ya Toni take mun signal ko ? Zan kamata , amma Yaushe ta zo gidan nan itama ?”da wannan tunanin tahee ta koma part d’in Ammey. Yanxu ma Ammey bata falon shiyasa kai tsaye ta nufi makwancinta, kan ‘karamin karfe d’in Wajan sai kayanta datayi fulo dasu har yanxu ta’ki yadda ta hau kan katifar sabida hakanan kawai bata yadda da katifarba. Da daddare ma asabe ce ta kawo mata abinci tunda babu wani aiki da zasuyi, ita kad’ai tana tsaya yadda zatayi magana Ammey. Part d’in king ne ya fad’o mata arai, “ kana ina nayi kewarka sosai !!!!!! Plx kana ina “, duk da acikin zuciya tayi magana dole ka gane kad’ai cin da take ji aranta , sosai yau take missing d’insa so badly, so take kawai tajita a jikinta, bata san lokacin da ta rungume jikinta ba tana lumshe ido gabaki d’aya tsananin kewarsa shida junior d’inta ne ya cika mata cikin zuciya . Bata san lokaci ya ja ba saida ta kalli agogo taga ‘karfe 9, da Sauri ta Tashi tayi sallahr isha’i tare da kulli ‘kofar da lock , sai da ta zauna tayi addu’o’in neman tsari sosai kafun ta soma akaratun alkurani a hankali a hankali, a haka bacci ya d’auketa tana karatun.

Karfe 2:30am na safe tahee ta soma jin wani irin bugun ‘kofa a d’akin ta, tun anayi a hankali har aka somayi da ‘karfi kamar za’a ‘balla ‘kofar d’akin, a rud’e tahee ta soma karanto duk adduar data zo bakinta , ‘karar abubuwa da jijjigar’kofar da ake ne ya ‘kara tsoratar da ita amma duk da hakan sunan Allah ne a bakinta . Kamar ‘kiftawar ido aka koma side d’in window shima a haukace aka dunga bubbuga windows din kamar za’a ‘balla ga wasu irin kuka da suke tashi ta ko ina, side d’in kofar aka koma shima nan d’in bubbbuga wa akeyi had’e da kuru ruwa , mintuna kad’an kuma ya koma window , haka y dunga yi tsawan lokaci, sai wajan 3:10 kafun abun ya lafa , har yanxu tahee addua ce a bakinta daman tasan za ‘a rina , Ammey bazata ta’ba barin ta Haka ba . Gabaki d’aya tsoran komawa baccin take , saida bacci ‘barawo ya kwasheta.

WASHE GARI

Yau kam Ammey ta rigasu fitowa tunda suka fito take bun fuskokinsu da kallo kamar tana san fuskartar wani abu.har izuwa lokacin kuwa ciwan bakinta be gama sacewa ba, abun dariya facemask d’in da tasaka a rabin face d’inta,amma duk da haka idan tayi magana sai alamun rashin ha’kori ya fito mata. Gabaki d’aya yinin ranar kuwa Ammey a falo ta zauna duk yadda tahee taso had’uwa da Mimi abun yaci tura kamar dama Ammey ta san plan d’insu, duk yadda taso Zillewa Ammey bata , bata wannan damar ba , gabaki d’aya yinin tahee bata had’u da Mimi ba sai hakura tayi .

*****Haka tahee ta cigaba da zama a part d’in Ammey matsayin yar aiki , ga biki da yake ‘kara kusantowa ,duk yadda taso ta Samu evidence akan Ammey abu ya ci tura gabaki d’aya babu wan sheda da zai nuna maka Ammey tana yin wani abu , har lokacin kuma bata ‘kara had’uwa da Mimi ba tun bayan had’uwar da sukayi a part d’in dada . Yau sati d’aya kenan da zuwan tahee , gabaki d’aya lamarin Ammey ya fara d’aure mata kai , duk dare idan ta kwanta wannan buga ‘kofar da ake a haukace me yake tashin ta daga bacci amma Sabida kariyar ubangiji babu abunda ya sameta, tsawan sati kenan har yanxu taheee bata kwana akan katifar d’akin, kome zatayi cikin taka tsan tsan take yinsa gudun kar asirinta ya tonu.

??????

Yau ya kama Monday,batasan me ke faruwa ba, sai ayyukan da Ammey ta sasu na dafe dafe da soye soye kamar za’ayi wani babban taro gabaki d’aya Ammey yinin ranar a tsaye take sai faman rawar kai take ga wani farinciki da ya kasa ‘boyuwa akan fuskarta, abinci kuwa kala kala tasa su asabe aikinyi, 6:30 ta saka su asabe zaryar kai abincin part d’in Ammey , ban da wani kunun ayan da ta had’a da kanta sai faman tashin ‘kamshi yake , tahee na tsaye tana kallan ikon Allah ganin ita ba’a sata aikin komai ba , sai umarnin jiranta da Ammeey ta bata . Kiran sallar da akene yasa ta komawa d’aki saida ta kulle ko’ina tukunnan sannan ta cire fuskar, take kyakkyawar fuskarta tafiya kwanin burgewa gudun kar wani ya shigo ya sameta yasa ta yin alwala , tana idar da sallah ma ta mayar da face d’in , sosai take kewar su junior da momy gabaki d’ayansu. Kamar yadda tayi zato taba kammala sallar asabe ta kawo mata abincin Daren, ba musu kuwa ta ‘kar’ba duk da agaban ta akai komai ,snacks din da tayi da hannunta kawai ta ydda taji shima sabida yunwar da take ji hatta leman da aka bata, bata shaba sai ma juyeshi da tayi a cikin toilet. Har lokacin Ammey bata ‘kara nemanta ba , sai bayan kiran sallahr isha’i da ta da asabe kiranta. Tana fitowa taga Ammey ta sha uban kwalliya sai faman walwali take amma ba’kin zuciyarta ya hana a ga kyaun ta sai mununta cewar tahee . “ kande “ cewar Ammey tana katse wa tahee tunanin da ta fad’a , da Sauri tahee ta ‘karasa Inda tace cike da biyayya ta tsugunna , jug d’in kunun ayar Ammey ta nunawa tahee , “shi zaki d’aukomun ki biyo ni dashi”, da Sauri tahee ta amsa sa da to hajiya tana mamakin ne ya hana akai kunun ayar lokacin da ake kai abuncin, babu me bata amsa shiysa ta cire zancen cikin zuciyarta . Tunda suka fara nufar hanyar part d’in dada haka kawai zuciyarta ta soma tsinkewa , ka ‘kafafuwanta da sukai sanyi kamar me shirin zubewa ‘kasa , duk da Haka bata karaya ba addua take karantowa a ‘kasan zuciyarta . Suna shiga falon saura kad’an ta saki jug d’in hannunta, ganin gabaki d’aya ilahirin familyn suna Zaune kamar yadda suka saba , shi kad’ai ne babu sai zoya da samreen da basa nan sai kuma mahma , a d’ad’d’ai da d’ad’d’ai ta soma bin ko wannan su da kallo kafun ta sauke idanuwanta akan ummey, hakanan ummey ta tsinci kanta da sakin wa tahee murmushi , itama tahee murmushi ta d’an sakar mata , kafun ta tsugunna har ‘kasa tana gaishe da ko wannan su d’aya bayan d’ayan kukan da yake shirin kwace mata take ‘ko’karin dannewa sabida kar su fahimci halin da take ciki, gabaki d’ayansu cike da kulawa kowa yake amsa mata gaisuwarta.d’ago idanuwanta tayi ko zataga Mimi Amma gabaki d’aya ba Mimi babu alamarta. A wayance Ammi take Kare bakinta ta yadda basu fahimci cirewar hakwaranta ba, amma abunda bata sani ba Abbey da ummey sun gani shiru kawai sukai da bakinsu ganin kowa na cikin falon. Basu dad’e da zuwa ba gabaki d’ayansu suka nufi dinning area , kallan tahee ummey tayi kafun ta ‘kara sakar Mata murmushi “ idan kika fita ‘nan gare na biyu ki kiramun saratu kinji ?” Da Sauri tahee ta amsa mata gudun kar Ammey tayi magana yasa ta juya cikin sauri sauri ko tunanin ajje jug d’in batayi gabaki d’aya ta manta da wani jug a hannunta. Hadari hadari ne ya soma kad’awa ga wata sanyayyiyar iska da take kad’awa itama , part d’in king da yake d’an nesa da ita ta ‘kurawa ido , ynxu hawayen da suke zubo mata batayi ‘ko’karin dakatar dasu ba , tafi tsawan mintuna 5 tsaye a wajan ga inda take da d’an duhu duhu,batayi auneba taji an janyota baya an toshe mata baki ta yadda bazata iya ‘ko’karin guduwa ko yin ihu ba . Batasan ko wanene Sabida yadda aka rufe mata baki sosai har lokacin kuma jug d’in kunun ayar na hannunta.kai tsaye bayan part d’in uncle musaddiq aka jata ta ydda bazata iya Saurin guduwa ba , saida ya nisantata sosai daga wajan masu tsaro , kafun ya gwara kanta da jikin bango, yana ‘ko’karin ‘kara ta’bata kawai ta watsa masa kunun ayar hannunta gabaki d’aya . Duk da fuskarsa a kulle take hakan be hana jajayen idanuwansa fitowa ba , rai a ‘bace ya ciro knife d’in jikin wandansa yana nuna ta da ita, cikin muryarsa mara dad’in saurare ya soma magana “ dole aikina ya cika yau kamar yadda nake cika ko wace makafa haka Kema zanyi anfani da jikin ki wajan biyan bu’katata, idan kika gigin guduma sai na kasheki , na kashe banzan sannan na binneki ta yadda babu Wanda zai ga ko da sassan jikinki ne .”a tsorace tahee take bin fuskarsa da kallo tana san ganin fuskar wanda yake yake magana , ganin ya fara matsota ne yasa ta soma ja da baya, wata shegiyar dariya ya saki ko ‘ko’karin akamasa bayayi, gadan gadan ya nufo tahee da niyar yaje hijab d’in jikinta , take a Wajan kokawa ya ‘Barke tsakanin mutumin da tahee , adduar da take sanyima sai taji bakinta yayi nauyi ta kasa , suna cikin wannan kokawar taji ya saki ‘kara ya koma gefe , da Sauri ta kalli gefensa ,Mimi ce d’auke da dutsen da ta buga masa , da Sauri ta furta tazo mugudu, da Sauri tahee ta mi’ke ko takan jug din Ammey bata biba sai ma wani abu danaga ta du’ka ta dauka kafun su saka gudu ita da Mimi Suka bar mutumin kwance a wajan dafe da kansa. Direct basu tsaya a ko ina ba sai a part d’in ummey suna sakin ajiyar zuciya, dukda da wahalar gudun da suka sha hakan be hana Mimi kwashewa da dariya ba , “ amma anyi d’an iska da banga lokacin da yaje janki ba da uban me zai miki? Wallahi Allah ya temaketa babu makami a wajena da babu abunda zai hana nayi masa sabuwar kaciya, wani saban dariya Mimi ta ‘kara kwashewa da shi , harararta tahee tayi “ dad’ina dake wani lokaci kamar auta Sabida wauta,shima d’an iskancan koma wanene zan nemo shi, sai kuma ta bud’e ta fun hannun ta tana ‘karewa zoben data d’auka na mutumin kallo, wani irin jan zobe ne mara kyan gani , sai hotan idanu ako ina najikin zoben , kallan mimi tayi tana ‘kokarin yin magana tahee tayi mata alama da tayi shiru, shirin kuwa tayi tana bin tahee da kallo, cikin dabara yadda ba’a ji sauti ba ta nunawa mimi lokaci da kiran da ake mata , da Sauri itama Mimi ta d’aga mata kai alamar ta soma ta fiya, hakan kuwane ya faru tahee ta soma tafiya bayan ta ‘boye zoben da ta samu lokacin da take kokawa da wannan mutumin, gabaki d’aya hankalinta a tashe yake “ kenan akwai me bibiyata? Wanene wannan mutumin da ya kesan ta’bamun martabata? Me yake nufi da cikar burin sa?”, batayi aune ba kafarta ta daki wani d’an step d’in da zata hau , Adaidai lokacin da aka fara ruwa kamar da bakin ‘kwarya, azabar zafin da tajine yasa ta saki ihu tare dayin baya zata fad’i, gabaki d’aya ta sada’kar faduwa zatayi , batayi auneba sai jinta tayi ta fad’o jikin mutum .

 

Post a Comment for "Gidan Aunty book 2 Page 14-15"