Gidan Aunty book 2 Page 13
BOOK 2
Page 13
*********
Tunda suka fara shiga cikin gidan wani irin gumi ya fara tsats tsafowa tahee kamar ana ‘Kona ruwan jikinta, babu abunda take sai karanta adduar duk da tazo bakinta, ganin
yadda lokaci d’aya jikinta ya fara rawa ne yasa hajiyar tunanin sabida ganin babban gidane yasata rud’ewa haka , bin part d’in gidan tahee ta farayi da kallo , da Sauri ta had’iye kwallar da take ‘ko’karin sakko mata gabaki d’aya ta kafe idanuwanta akan part d’in sa har aka ‘karaso part din Ammey bata sani ba sai da hajiyar ta jijjigata “ ke Menene sai faman kiran ki nake Amma gabaki d’aya hankalin ki baya jikinki?” Amaimakon tahee taji haushi maganar ta sai ta Washe mata hakwaranta da suka sawa abu, da farko idan ka kalla sai ka d’auka hakwaranta haka suke dar harwani baki baki sukai kamar na kod’ewa,”tuba nake hajiya,arabu gidan nagani kamar Aljanna “tsaki hajiyar ta saki kafun tace” fito”ajiyar zuciya Tahee ta sauke kamar cikakkiyar na’kauyiya tafara kici niyar yadda zata bud’e motar harsaida hajiya tazo bud’e mata tana Jan tsaki ,bin ta abaya tahee ta soma tanayi tana ‘kara bin part d’insa da kallo kamar anan ne Zata gansa . Lokacin da zasu shiga part d’in Ammey sai datayi addu’o’in neman tsari tukunna tasaka kafarta da Bismillah, Ammey na zaune kan kujera kafa d’aya da sauri ta tashi tsaye sabida yadda ta jiya zuciyar ta , ta tsinke ga wani bugawa da take yi sosai da sosai , kallan kallo suka tsaya yi ita da tahee da taji kamar taje ta sha’keta mutu , tsanarta na ‘kara shiga cikin zuciyarta Amma gudun kar agano yasa ya wajance da kallan falon tana zazzare idanuwa kamar yadda ‘yan aiki sukeyi, ajiyar zuciya Ammey tasaki dukda lokaci d’aya taji jikinta ya mutu tana bu’katar Hutu shiyasa cike da fara’a tace wa hajiya su shigo ciki, Tahee a ‘kasa ta zauna tana ‘kara bin Ammeey da kudi ya ‘kara zauna mata da kallo , muryar hajiyace ta dawo da ita hankalinta lokacin da taji tana gaishe da Ammey , itama tahee cike da sokwanci da bar kwanci ta gaishe da Ammeey tana bud’e mata hakwaranta ba’ka’ke , da Sauri kuma Ammeey ta kawar da kanta sabida yadda taga bakin tahee , a fakaice tahee ta danna wani abu a wuyanta lokacin da zata agaishe da Ammeey, cikin ikon Allah kuwa sai ga muryarta ta canza kamar ba ita ba , Ammey bata jira jin dogon zance ba bayan sunan tahee da ta tanbaya, yanxu ma tahee washe mata baki tayi kafuntace “ ai aradu hajiya sunana kande kina ganina a ‘kauyan mu nafi kowa cin gasar ‘kyau, “ girgiza kai Ammeey kawai tayi hakanan taji batasan hayaniya musamman kanta da taji ya fara sara mata , sama ta hau shaf shaf kafin ta sauko da wata jaka a hannunta tana mi’kawa hajiya “ zaki iya barin ta anan , duk yadda ake ciki nan da kwana biyu zan sanar dake , idan ta cancanci zama dani shiknn, idan ina bu’katar wata kuma zan sanar dake “ cike da girmamawa hajiyar tayiwa Ammey Godiya bayan shatara ta arzikin da ta bata, falon yayi saura daga tahee sai Ammeey dake bin tahee da kallan ‘kurinla.” Kikace sunanki kande ?” Yanxu ma tahee hakwaran ta washe duk da ydda taji zuciyarta tana tafarfasa kamar gawashi ganin Ammey a gabanta .” Eh hajiya sunana kande , kuma a radu hajiya kome zaki sani a gidan nan zan miki indea zaki dunga bani abincin ku na birni”, wani lallausan makirin murmushi Ammey ta saki tana ‘kara bin fuskar tahee da kallo, wayarta ta d’aga kafun tace ina jiran ki yanxu “, basu ‘kara mintuna biyar ba tahee sai faman barkwancin ta take mata, Asabe ce ta Fito daga wata ‘kofa kamar kullum shigarta na ‘yar aiki ne a jikinta,nuna mata tahee Ammeey tayi “ kikai ta dakin can na ‘kasa ita kadai banaso a had’ata da kowa sannan ai mata abunda ya kamata zanje na huta kafin anjima , cike da girmamawa asabe ta amsa da toh Ammeey , itama tahee har da dur’kusawa wajan godewa Ammeey.
Bin d’akin da aka kawo ta tahee tayi , katifa ce kawai a d’akin sai wardrobe da gaban mudubi , koda asabe zata fita ynxu ma sai da ta gode mata, maida kallanta tahee tayi kan gaban mudubin d’akin tana ‘karewa fuskarta kallo, duk Wanda ya ganta tabbas zai d’auka yar ‘kauyece musamman yadda jikinta yake da bakin wahala, guntun murmushi ta saki “ idan kinsan wata ai baki san wata ba “ cewar tahee cikin zuciyar ta , dawowar asabe ne yasa tayi saurin ‘karasawa ta kar’bar mata kayan cike da girmamawa “ ga wannan abincin Ammey tace a baki kici ki huta zuwa anjima kafun ta nemeki, amma gaskiya gaskiya kin cika mai sa’a sabida ni banta’ba ganin hajiya ta saka wani a wannan d’akin ba .hajiya na da kirki kiyi mata duk abunda tace ko kinsamu ‘karin albashi “,cewar asabe , tahee kuwa sakin baki tayi tana kallan asabe kafun cikin mamaki ta furta “ Dagaske kike ? Gaskiya hajiya nada kirki, kuma ko me tasani zanyi mata “, itama asabe washe mata baki tayi kasantuwar ta da shegen surutu” gaskiya dai ya kamata,kinga yanxu shirye shiryen biki ake sai kisamu ko atanfa da Jan baki kishiga sabida Kema ki fito cas dake , yanxun kama tahee batacewa asabe komai ba sai hakwaranta data Washe har ta bar d’akin “ tabbas befi wata biyu bikin sis Ilham ba kamar ydda yazama Kema zaki fara irga ranar tonuwan asirinki” cewar tahee cikin zuciyarta. ‘Dakin ta ‘karewa kallo kafun ta kalli tray d’in abincin da aka kawo mata , har zata ‘kici kuma sai wata zuciyar tace karta zauna da yunwa karba fuskanci wani abu, saida ta zauna tayi addu’o’in neman tsari da yanxu bata gajiya da yunsu cikin Bismillah ta zauna taji lafiyayyan abincin da aka dafa tunda tasan aikin asabe ne , kunun ayar da ta gani ne yasata binshi da ido kafin cikin Sauri ta d’aukesa ta juye a sink gabaki d’aya ta dawo da medium abun kunun, katifar da aka ajje mata ba , amaimakon ta kwanta akai sai ta samu gefe tayi kwanciyarta bayan ta kulle d’akin, bata jima ba bacci ‘barawo ya d’auketa.
3:40 tahee ta farka da Sauri ta mike tanufi toilet shaf shaf tayi abunda zatayi tayo alwala, kafin ta d’auko face d’inta da abun bakin ta shash shafa a cikinta , sallar asahar ta rama , Daidai lokacin da ake kiran la’asar shima , tana idarwa ta bud’e ‘kofar takin kamar wata ‘barauniya ta fito daga cikin dakin tana bin ko ina da kallo, “ kina bu’katar wani abune ?”, cewar asabe da take ‘ko’karin kiranta, cikin waske wa tahee ta soma kinkina “ dama dama na d’auka akwai aikin da zanyi ne sabida zama waje d’ayan danayi duk jikina ciwo yake na saba da Noma da ayyukan gida shiyasa nake neman hanya “, Washe mata hakwara asabe tayi “ Allah sarki Aushe baki da ‘kiwa kinga kuwa duk abunda hajiya tace miki kiyi toh shiknn zaku shirya da ita sosai nake fad’a miki yanxu ma catai na kiraki , ina ‘kara jadda da miki kiyiwa hajiya biyayya tana da kirki matarnan,” cikin gamsuwa tahee take d’aga mata kai har suka ‘karaso cikin falon ita kuma asabe ta juna , cikin girmamawa cike da ‘kauyancin tahee ta soma yiwa Ammeey karari, Ammey kuwa sai faman sakin murmushi take kafun ya kalli Tahee da mugun kallan nan nata “ kikace kome aka saki zaki iyayi?” Da Sauri tahee ta jinjina mata kai “ Aradu hajiya kome kika sani zanyi miki ,” yanxun ma wani murmushi Ammeey ta saki kafun ta ciro wasu Abu a cikin jakar gefanta da wasu ma’kudan kudi ta fun ta nuna tahee “ idan kika bi abunda nace toh tabbas zaki samu ninkin su ba masu ba “. Sai ta nuna wasu wani abu Aroba “ yanxu idan nace ki zubawa wani wannan fiya fiyan zan baki 50k zakiyi”, waro idanuwanta da aka sawa ‘kwayar iho tahee tayi , da farko Ammeey ta d’auka ihu zatayi ne sai kuma tafa sa’banin hakan “ Haba hajiya yo ai wannan me sau’kine , dubu hansin ba ? Idan akai mun kayan d’aki nida iluna ai sai nafi kowa gata , Nidai kome kika sani hajiya zanyi miki dan saida a kaimun fad’a a gida akan duk inda kud’i suke innemo ,”yanxu ma murmushi Ammeey ta saki tana raya wani abu acikin zuciyar “yanxu nice shugabanki, duk abunda nasaki shi zakiyi , idan kika kuskura kika sa’bamun sai dai in wata bake ba , sannan maganar ta tsaya tsakanina dake idan kika kuskura najita abakin wani toh tabbas daga lokacin bazaki ‘kara magana ba “cikin tashin hankali tahee ta zaro idanuwanta tana had’e hannayenta biyu “ tuba nake hajiya aiko me kika sani shi zanyi miki ni babu ruwana da kowa umarnin ki kawai zan bi “, wata yar iskar dariya Ammeey ta saki ita kad’ai tasan me take rayawa cikin zuciyarta , kafin ta danna wani abu? Babu jimawa asabe ta ‘kara fitowa “ kinuna mata yadda ayyukan suke , da tsare tsaran komai bana san kuskure”, insha Allahu hajiya ai duk abunda kika ce shi za’ayi , kafun tayi wa tahee alamar ta taso, cike da ‘kauyanci tanayi tana ‘kara kallan falon haka suka bar falon . Duk abunda take akan idan Ammeey shiyasa ta d’auko wata kanta memiyar wayarta , wata number ta saka , ba a jima ba a ka d’auka , bata jira jin maganar me wayar ba ta soma magana cike da ‘kosawa “ tabbas muna gab da cika burinmu dan nasamo wacce zatayi mana komai namu kawai umarnine “, banji me aka ce mata ba sai ‘kara sakin wata dariya da tayi kafun ta kashe kiran , jinta take yau sakayau ga wani farin ciki da ya cikata ganin burinta yana ‘ko’karin cika cikin sau’ki.
A’bangaran tahee kuwa yadda ake anfani da komai na kitchen asabe ta koya mata shima saida asabe taci uwar kwakwa kafun tahee ta nuna mata tagane dan har yadda ake kunna gas sai da sabe ta nuna mata ya kai sau goma dan data kar’bi asha na zata kunna gas sai taja baya wai wuta zai kamata, Asabe ba ‘karamin wuya Tasha ba kafun tahee ta fuskanci abunda ta Goya mata , duk tsarin part din Ammey sai da ta sanar da ita da inda ake shiga da inda ba a shigar mata musamman lambunta da ba a shigarsa. Cike da bin umarni kuwa tahee take furta ta gode , sai wajan 6:30 sannan suka gama , lokacin da asabe zata ‘kara nuna mata d’akin da take dan cewa tayi ta manta hanyar, d’akin da yah moh ya sanar dasu ta kalla kafun ta saki wani lallausan murmushi , har ta koma masaukinta. Shima sai data kulle ‘kofa tukunna tayi sallah kafun ta ‘kara shafa ba’ki ba’kin abun nan , tasan tabbas idan tace zatayi wanka ynxu zasu iya fahimtar wani abun shiyasa ta hakura da yi, bata fito ba har saida tayi sallar isha’i, lokacin da Ammey ta sanar dasu tafiyarta part d’in dada . Kamar tahee zata kurma ihu haka take ji ganin babu damar fita . Zagaye ta somayi cikin d’akin nata, tunanin mafita akwai take yi ita kad’ai , ranta har soyuwa yake idan ta kalli Ammey, tana san fita falo amma tana gudun kar Ammey ko asabe su Fito , wani ‘bangare na zuciyar ta kuma yana bata ‘kwarin baiwar fitar danji take idan bata nakasa abeey ba, bazata ji dad’i ba . Shahada Kawai tayi kuwa , cikin ikon Allah kuwa babu kowa a falon, hanyar d’akinsu su asabe ta kalla nan ma shiru da Sauri ta nufi kitchen tana ro’kan Allah yasa kar Wanda ya fito, Daidai ta zuba man gyad’a a cikin ledo kuwa ta soma jin motsi alamar ana nufo kitchen d’in da Sauri ta rufe man gyad’an ta shige ‘kar’lashing dinning din, wata ce itama da kama kallanta kasan yar aikice, cikin sand’a ta bud’e fridge duk akan idan tahee , Ayaba da kankanar da ta gani ta ‘iba kafin cikin sauri ta bar kitchen d’in tana waiwaye , tahee dariya ce taso ‘kwace mata amma ganin bata da lokaci ne yasata fitowa ita daga ma’boyarta . Babu kowa a falon har yanxu da Alama Ammeey ma bata dawo ba . Bakin ‘kofar shigowa tahee ta nufa cikin Sauri Sauri kafun ta d’iga wannan ta ydda ba Lalle hankalin mutum ya kawo wajan ba . A cikin abun flowers ta jefa ledar tare da komawa d’akinta hankali kwance, dan tayi alkawari daga rana irin ta yau Ammey sai ta fara fuskantar hukunci. Gudun kar axo Tashinta yasa ta saka lock ta cikin d’akin har yanxu kuma bata kwanta akan catifar ba , dan bata yarda da komai na Ammeey ba .
AMMEY
Ammey kuwa ba ita ta dawo part d’inta ba sai wajan 10:30, da ka kalli fuskarta za kasan ranta a ‘bace yake amma kasantuwarta shu’umar mata sai ta ‘boye hakan da murmushi akan fuskarta.har ta dawo part d’in ta tana tuna maganganin bikin da aka ‘kara tattaunawa na ilham , ba komai ne yafi ‘bata matarai ba kamar yadda su momy suka zage suna yin abu gabaki d’aya sun toshe ko wace hanya, tazo zata shiga cikin falonta kafarta ta hagu ta zamar da ita sai ji kake kafff , Ammey ta kife tsakiyar bakinta ya daki ‘kasa take jini ya fara zuba , wata gigitacciyar zafin azaba Ammey ta saka ganin yadda ‘kugunta ya bugu ga ha’korinta da take ji kamar babu su a bakinta. Kwalla kiran sunan asabe take amma babu asabe babu labarinta , lokacin da ta fad’i kuwa akunnan tahee dan itama taji ‘karar, ganin aikinta ya cikane yasa taje tayo alwala ta kwanta. Ammeey tun tana faman ‘kwalla musu kira har tayi shiru Sabida azabar zafin da yake ratsata , tafi munti 10 kwance a wajan gashi ba damar kiran wani, da’kyar taja jikinta har ta nufi d’akin tafinta sai kuma ta dakata dan tasan cikin sharad’in boka duk Wanda yake da ciwo toh tabbas ranar Jininsa za a zu’ke cike da wani ‘karin takaici ta
Nufi d’akin kusa dashi, hankalin ta gabaki d’aya be kawo kan man gyad’an ba , ga baki d’aya takaicin ta kaicin dake cin zuciyar ta ya hanata ganin hakan. Tana shiga cikin d’akin taji abu kamar abakinta masu kauyi da sauri ta tufosu waje, cikin gigita ta saki ‘kara ganin hakwaranta biyu sun cire tana ‘kokarin fara karanta maganganun tsafinta hakwaran suka ‘bace duka . A gigice ta fara dubawa d’akin ko zata gansu Amma gabaki d’aya babusu babu alamarsu, da Sauri ta ‘karasa gaban mudubin d’akin cike da tsoro ta bud’e bakinta kad’an, ha’kwaranta biyu data ga babu yasa ta sulale a ‘kasa sumammiya.
WASHE GARI
Kiran sallahr azuba a kunnan tahee , dama bata da magagin bacci saida ta fara yin wanka tukunna kafin ta yi sallah, gudun kar azo kiranta yasa cikin sauri sauri ta mayar da fuskarta da kwayar idanunta da yake canza mata kamanni, man da zai yasa jikinta duhu ta shash shafa , tsaf ta fito kande ‘yar aiki abunta, tunawa da muguntar da tayiwa Ammeey ne yasata kwashewa da dad’i, ‘boye abubuwan anfani ta tayi kafun ta fito daga cikin d’akin ynxu ma cikin sand’a , Asabe bata fito ba shiyasa cikin sauri ta ‘karasa inda ta zubar da man, tana zuwa taga Jini Jini alamar harda ciwo Ammey taji , cikin Sauri ta d’auko abu ta goge wajan tass babu ne cewa azuba wani abu a Wajan , dabara ce ta fad’o mata tayi saurin komawa d’akin gudun kar a zargeta , kusan mintuna 10 ta fara cin motsin mutum da Sauri ta kwanta . Asabe ce ta bud’e d’akin ganin har yanxu tahee bacci take kuma a ‘kasa yasa ta fara tashinta, ban’karewa tahee tayi tana bud’e kafun ta waro su duka ganin asabe a kanta “ ya naganki kwance a ‘kasa bayn ga katifa “, kallan katifar tahee tayi cikin zuciya ta furta “ hauka nake ?” A fili kuwa washe ha’kwaranta tayi ,”yo ba ance duk Wanda yake kwana akan irin wannan abu me yaushi aljanin dare na zuwar masa ba , kuma ni inna kwanta a irin wannan abun ai mutuwa zanyi “, dariya asabe ta saka “waya fad’a miki haka ?” Cike da barkwanci tahee ta furta “ malamin Allon mune ya sanar damu kuma yace har ciki a keyi “ ta ‘karasa tana toshe bakinta . Yanxu ma dariya asabe ta saka gudun kar Ammey ta Fito ne yasa ta kallan tahee “ kande ya kamata mu fara aikin mu tun ynxu , kar Ammey ta fito “, toh kawai tahee tace mata suka Fito , suka fara shirin abincin safe kasan tuwar daman akwai masu shara da wanke wanke , farfesun kifi asabe tayi da hot chips sai plantain din da tayi , tahee sai kallan yadda take ai tayi a zuciya ita kad’ai tunanin shigowar king take amma shiru”, a fili kuwa da asabe tayi abu sai ta tafa mata , sai ‘karfe 80:20am Suka kammala asabe sai faman nuna mata ydda ake jere tayi , ita kuwa sai bin motsin kowa take so take taga fitowar Ammey amma har yanxu shiru. Suna tsaye wasu ‘yan mata kyawawa suka shigo falon ko wannansu sanye cikin material gabaki d’ayansu babu Wanda be hadu ba acikinsu, Hutu da kud’i duk ya nuna a jikinsu. Da Sauri asabe ta gaishesu, tahee ta durkusa daniyar gaishesu taji ta farkon ta furta “ gaskiya ilham baki da mutunci ki duba kiga da sassafe kinsa duk mun wani shirya “, da Sauri tahee ta d’ago ta kalleta , cikin Sauri kuma ta bisu da kallo” ilham ? Sumayya? Firdausi?”, Dagaske kunake gani?” Duk wad’annan tanbayoyin kanta take yiwa su, firdausi da ta kula da kallan da tahee take musune yasata sakin murmushi “ ya sunanki?”cewar fiddy, ‘kwallar da take ‘ko’karin zubo mata tayi saurin tare wa cikin washe baki ta furta “ sunana kande “, atare gabaki d’aya yan matan uku suka kalleta , haka kawai suka ji burgesu kodan wani abu da ya ta’ba faruwa da bazasu manta dashi ba . “ Ammey fa?”, da Sauri tahee ta juya wajan asabe , cike da girmamawa ta furta “ har ynxu bata fito ba “. Okay cewar ilham, cike da girmamawa suka bar wajan har yanxu taheee tana tunanin me ya hanasa zuwa part d’in , ta’bata da asabe tayi ne yasata tashiga taitayinta , su ilham basu wani dad’e ba suka bar part d’in sai alokacin Ammey ta fito fuskarta duk a kunbure , dariya ce ta so ‘kwace wa tahee amma ta danneta ganin yadda le’ben Ammey ya kunbura, ganin yadda suke sunkuyar da Kai Ammey cike da kuluwa ta furta Menene kuke sunkuyar da kai, d’agowa sukai a tare suka kalli Ammey ganin babu ha’kwara biyu a bakinta yasa gabaki d’ayan su fashewa da dariya .
????GIDAN AUNTY ????
07041879581
Mss Lee
Post a Comment for "Gidan Aunty book 2 Page 13"