Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Gidan Aunty book 2 Page 11

BOOK 2

Page 11.??

??????

WASHE GARI

Tunda suka tashi kowa da farinciki kwance akan fuskarsa , kowa kaganin cikin fara’a junior tsalle yake idan ya juya ya kalli


Ammunsa tana murmushi sai ya juya ya kalli Mimi itama yaga tana murmushi, sai ya tsaya kuma ya fara bin kowa da kallo tun daga kan yah moh harzuwa su dady, shima sai murna yake abunsa. Kowa jira yake dady ya ‘kara kiransu amma dagari ya waye sai sukaji shiru har sukai breakfast suna jiran tsammani, sai wajan 11:30am dady ya Bu’kaci ganinsu , gabaki d’aya familyn sun hallara , bud’e taro dady yayi da addua kafun yayiwa Allah kirari yana ‘kara Godiya ga Allah kafun ya soma magana “ nasan ko wannan ku a cikin ku yasan abunda ya faru jiya basai na maimaita ba , cikin iko na ubangiji ya nuna ikonsa ,yar uwata da nake nema cikin iko na ubangiji sai ya fara nuna mun jininta , tabbas zuwanki cikin family d’innan alheri ne babba, ta sanadiyar junior komai da komai zaizo ‘karshe , insha Allah babu wani abun cutarwa da zasu ‘karayi muku cikin ikon ubangiji”, kafun ya mayar da hankalinsa kan yah moh da ya d’an sunkuyar da kansa kad’an “ Mohammad , inaso nasan Menene ya faru har matar mahaifinta take ‘ko’karin salwantar da rai, Menene ya faru a wannan lokacin?” A hankali ya d’ago idanuwansa da sukai jajawur sabida ‘bacin rai, amma bece komai ba har sai da dady ya ‘kara maimaita tanbayarsa kafin ya sauke a jiyar zuciya yana shafa kan junior da ya lafe a jikinsa , cikin sanyayyiyar murya ya soma magana “ cikakken sunana Mohammed zayed Al-Nahyan, mahaifina mu hud’u ya haifa Ni, samreen, king, sai baby d’in da har yanxu ban sani ba tana raye ko akasin hakan, familyn Nahyan babban family ne da gabaki d’aya a halin mu suke rayuwa a ciki , cikin so da ‘Kaunar juna, sosai muke san junanmu musamman ni da king dukda be cika magana ba Amma gabaki d’aya familyn sunfi jin shakkarsa, gabaki d’aya cikin family din babu Wanda baya tsoran yi wa king kuskuren koda sau d’aya ne musamman idan hakan ya shafeni ko samreen, shiyasa muke matu’kar san junanmu mutane da yawa idan suka ganmu tare sai suyi tunanin ‘yan biyu ne mu duk da shi duka kamannin parents dinmu ya d’auka , a haka muka cigaba da rayuwa cikin san junanmu kwatsan sai Abeey ya tado da maganar ‘kara aure , babu Wanda beyi mamakin zancen ‘kara aurensaba musamman yadda kowa yasan soyayyar abeey da oumma , alokacin sosai ran king ya ‘baci duk da Nima banso auren ba amma haka na cigaba da kwantar masa da hankali, still ina tausar ummey duk da bata fito fili tayi magana ba sai albarka data sawa auren bata ‘kara ce wa komai ba.Ba’ai 2 weeks ba sai ga zancen auren ya ‘kara tashi har aka d’aura Auran ta da Abeey, shigowarta gidan sosai take nunawa kowa so da ‘kauna , hakan ya janyo soyayyar yaran gidan har ya zamto kullum suna part d’inta ban dani da king da ko kallan inda take bayayi bare gaisuwa ta had’asu, hakanan Nima naji gabaki d’aya matar bata kwanta mun arai ba amma gudun d’aukan Alhaki yasa na cire zancen Arai na saka harkar makarantana a gaba, 2 weeks da auren abeey abubuwa da dayawa suka soma canzawa , cikin har da wata irin soyayya da gabaki d’aya familyn suke mata kowa kaji maganarsa d’aya biyu sai ya had’a da sunan abeey , hakan shike ‘kara tunxura king sau da dama Ammey idan ta gansa ko da ace tare yake da abeey shi zata farayi wa magana , abun mamaki ba’afi 1 week ba sai gashi yawanci lokuta king yana part d’insa da yana tanbaye sa sai cemun ai tana da kirki sosai , sannu a hankali king ya fara janzawa har yazamto kullum a can part din yake cin abinci ya dena ci a wajan ummey, har yazamo baya cin komia na ummey gabaki d’aya rayuwarsa a part din Ammey yake yi hakan ne ya fara samun zarginta duk da banfito fili na fad’a ba , kwatsan wata rana ina neman king amma ban gansaba ranar da na fara tunanin shiga part din Ammey a rayuwa,ko da na shiga babu kowa a cikin falon har zan juya sai na dunga jin motsi da surutu cikin wani d’aki da ba kullesa sosai ba , kamar na share sai zaciyata ta’ki bani damar hakan, abunda nagani ne yafi komai tadamun hankali kasancewar computer software na karanta cikin Sauri na soma yi mata vidoe , ba komai naga Ammey na yi ba sai shan wani Jini da take ta zagaye d’akin da wasu nan fitulo jikinta duk sanye yake cikin jan kara, sam hankalinta be kawo kaina ba gabaki d’aya hankalinta yana kan tsafin da take yi, abun glass din da na bege nesani sakin ‘kara kadan da Sauri Ammeey ta jiyo cikin tashin hankali mukayi ido vidoe da ita, kururuwa naga ta farayi ni Kuma cikin sauri na far wajan ina kiran sunan Allah .
Ranar da matsanan ciyar ciwon ‘kafa na yini gabaki d’aya na rasa wa zan tun kara da nayi kokarin tunkarar abeey ko ummey sai naji ma’kogarona kamar ana sukamun wu’ka, sai da nayi kwana biyu duk lokacin da zan kwanta sai na dunga ganin wad’ansu abubuwa kamar masu rai, hakan yasa na dawo kulla kurani a d’akin,vidoe da nayi mata kuma sai na sashi cikin memory. Har zuwa lokacin ban had’u da Ammeey ba.
Sai ranar da na ‘kara kwanta wa rashin lapiya sabida yadda naji jikina kamar ana huramun huta ta ciki gabaki d’aya sai faman gumi nake yi, a fakaice Ammey ta kalleni ta kashe mun ido d’aya ganin su ummey basa kallanta ,cikin bariki ta dunga nuna Al’ajabinta tana mun sannu. Haka muka ‘kara sati d’aya da ita tana harin rayuwata Allah na kareni. Ranar da bazan ta’ba mantawa da ita ba ranar Sunday lokacin dana ro’ki king ya rakani company zan d’aukowa abeey wasu mahimman document , alokacin kuma bamu d’auki masu tsaro ba nida king kawai muka fita har nasashi driving, munyi nisa a tafiyar mu wata babbar trailer tayi ta kan motar mu, gabaki d’ayan mu saida muka bugu sosai , Allah ya bawa king sa’a ya ‘balle motar da ta fara ci da wuta kad’an kad’an, Amma duk da haka hannu yake mi’komun nima cikin mawuyacin hali na mi’ka masa nawa da nayi nasarar balle ‘kofar Nima, bamuyi aure ba wasu mutane sanye da ba ‘kaken kaya suka soma dukan king amma duk da haka bata su yke ba so yke ya cece , king beyi aune ba kawai sai motar da nake ciki ta saki ‘karar bom Adaidai lokacin da suka harbi king, ni muma d’aya daga cikinsu ne da ya kula dani yayi saurin te maka mun tare da turani wani rami gudun kar sauran su ganni take a wajan kaina ya bugu da bishi yar wajan , ban ‘kara sanin inda kaina yake ma sai muryoyin mutanan da yake tashi sama sama d’aya daga cikin sune yake “ mun kashe shi hajiya “, Wannan ne abunda ya faru harnabar gida tsawan lokaci ,duk da nasan akwai wani na jikin mu da yake temaka mata da har ynxu bangane ko wanene ba , nasan zuwa yanxu kowa yana tunanin na mutu ko? “ ya ‘karasa yana tanbayr tahee da take d’aga masa kai itama da Mimi gabaki d’aya kuka suke , Mimi ji take da zata samu shegiyar Matar nan da babu abunda zai hana taci ubanta, shegiya me idan agwagwa,” abunda Mimi take rayawa a zuciyar ta , yah moh kuwa sai faman sakin murmushin takaici yake , ran taheee ma ba ‘karamin ‘baci yayi ba sosai .

Shiru gabaki d’aya falon ya d’auka tsawan mintuna biyu, babu abunda ya ke tashi sai kamshi freeshner da sanyin Ac da ke ratsa ko ina na falon, momy ce ta katse shirun “ wannan matar bata da Imani hartana iya salwantar da rai , ai ta kai ma’kura wajan tantiranci”, sauke ajiyar zuciya dady yayi “ tabbas a mawuyacin hali na sameka ko sunanka baka iya fad’a har Allah yasa ka samu lafiya , wannan mata babu d’igon Imani a ranta sam sai san zuciya , budulci da ‘kyashi kuma , Amma Allah ya fita cikin iko na ubangiji zai nuna mata bata da wayo ko dabara “.
Yanxu ma shurune ya biyo falan na tsawan mintuna kamar daga sama suka ji muryar tahee “ uncle inasan komawa Nigeria Sabida na tona mata asiri”, gabaki d’aya falon duk kallan tahee sukai , Mimi ma tayi saurin furta “ nima dady zan bita “, da Sauri momy ta katsesu” babu inda zakuje , kunsan matarnan mushrikace bazan juri rashin kuba , sam Hakan ba me yuwa bane “kallan junior daya soma bacci yah moh yayi “ Momy karki damu zan kula miki dasu gabaki d’aya “, sakin baki momy tayi “ kana nufin kai ma binsu zakayi? Ni kuma ku barni an ina ? Kafata kafarku babu me rabani da ‘ya’yana “, .gabaki d’aya kuma sai suka maida kallansu kan dady,ganin yadda suka kafeshi da kallone yasa shi yin gyaran murya “ Naji ta bakinku gabaki d’ayanku, amma bazan ‘karayin gangancin barin ku zuwa Nigeria ba , banasan jin wani ‘korafi na sallami kowa da kowa “,yana kai karshen zan cen sa ya bar falon, gabaki d’aya bin bayansa sukai da kallo mimi zata ‘Kara yiwa momy magana itama ta tashi ta bar falon, a shagwa’be ta maida kallanta kan yah moh, hararar ta yayi shima ya mi’ke ru’ke da junior , falon yayi saura tahee da Mimi, Mimi kamar ta saka kuka haka takeji daman bata ta’ba zuwa Nigeria,ga rashi ga samu. Haka kowa ya nufi d’aki yana sa’ke sa’ken hukuncin dady. Gabaki d’aya yinin ranar tunanin kalaman yah moh ne ya tsaya musu arai musamman Mimi da lokaci zuwa lokaci idan ta tuna abunda Ammeey tayi wa yah moh sai taji kamar tayi fiffike tajita a nigeria , Tahee kuwa jurfin tunanin yadda zata tonawa Ammey asiri take , tuna kalmar akwia wani bayn Ammeey acikin gidan da yke temaka mata yasa tahee ta rubuta sunayen ‘yan gidan kaf tana bin sunansu d’aya bayn d’aya a cikin zuciyar ta da halayyar kowannansu, sosai ta zura tunanin ta ydda zata gano koma wanene babu abunda yke Tashar da ita sai sallah , sai kuma abinci da Suka ci.

******* Da daddare Dady da wani envelope yashigo gidan gabaki d’aya yana lura da yanayin kowa da yadda suke binsa da kallo, be ce musu komai ba harya kammala cin abincin ya koma falo, suma da d’ad’d’ai suka dawo falon saida yaga kowa ya hallara kafun ya d’akko envelopes dinki, ciki ma wasu envelopes dince a ciki ‘kanana ko wannan su da abu aciki da sunansa , saida ya bawa kowa nashi kafun ya basu umarnin bud’ewa cike da zumud’i suka soma bud’ewa abunda suka ganine yasasu zaro ido suna kallan dady , dariya yayi musu kafun ya furta “ surprises !!! Nan da one week insha Allah zamu tafi Nigeria gabaki d’aya mun , wani irin ihun dadi suka saka mimi da tahee , Dady sai dariya suke , junior ne ya kallesu “ Ammu , Aunt , you’re shouting and dare yayi babu kyau”, gabaki d’aya dariya suka saka , haka suka zauna suna hira a tsakaninsu Mimi har ta matsu one week d’in ma tayi .

Cikin wannan 1 week din gabaki d’aya babu abunda suke sai yadda tafiyarsu zata kasance duk da ba wani abun suke bu’kataba, amma dady yace bazasu zauna a lagos ba gudun kar a gansu , saidai su sauka a gidan sa na Abuja , gabaki d’aya sunyi na’am da zancensa, batare da kowa ya sani ba Mimi da tahee suka je wani supermarket , Suka siyo wani abu da suke ta ‘boyewa kar su momy su gani, ita da tahee sosai suka had’a plan dinsu.

Yau yakama Sunday kuma a yau ne jirginsu ya tashi zuwa Nigeria ???? ??.

????GIDAN AUNTY ????

07041879581
Mss Lee

LEESHARH DATA HUB
BUY DATA AT AFFORDABLE PRICE:

MTN

500mb-120
1gb-240
2gb-440
3gb-620
5gb-1200
10gb-2200.

AIRTEL

500mb-140
1gb-300
2gb-600
3gb-900
4gb-1200
5gb-1500
Validity: 30 days
Account details :
2681892316
Zenith bank , Aisha umar.

For more information contact me through my phone number: 07041879581 .

 

Post a Comment for "Gidan Aunty book 2 Page 11"