Gidan Aunty book 2 Page 10
BOOK 2
Page 10
Da Sauri na ‘kara maida hankali na kan junior , daga nesa idan ka kallesa sak zaka ga tsantsan asalin balarabe, sai da ya matso da fuskarsa daidai inda tata yake kafun
kamanninsa ya kara fitowa dukda kasan cewarsa yaro , amma sosai zaka hango tsantsan kamannin king, sosai suke kama , kamar tasu hartaso baci , banbancin shi junior har yanxu yaro ne , hatta yadda king yake kallan mutum haka shima junior yake , sosai suka d’auki pictures, sun d’anjima a Wajan kafun su kama hanyar komawa gidan bayan siyayyar da yah moh ya kaisu. Tahee na shigowa direct dakin ta tanufa sabida ba ‘karamin gajiya tayi ba , tana shiga wanka tayi kawai ta kwanta , amaimakon tayi bacci sai kawai ta fashe da kuka, Kukane take yinsa tundaga ‘kasan zuciyar ta , diamond ring d’inta da abun hannunta shima diamond da king ya bata take bi da kallo, lokaci d’aya kuma ta saki murmushin da dimples dinta suka lo’ba “ Ammi kin cucenii, kin rabani da farin cikina , why ? , me yasa “, ita kadai take tanbayar kanta,sosai take jin ‘kuna cikin ranta, yau ta kasance mata ranar farinciki da bakin ciki,sosai take sa’ke sa’ke cikin ranta , hannun da taji a kuma tunta ana share mata hawaye ta kalla , junior ne fuskarshi shi kamar zaiyi kuka “ Ammu me yasa kike kuka ?” Girgiza masa kai kawai taheee tayi wasu hawayen na ‘kara sakko mata , duk lokacin da ta kalli fuskar junior fuskar mijinta take gani, he’s eyes , mouth , cute face,he’s everything sak irin na king ne ,” Tohm ki dena kuka kinji “, ynxu ma kanta ta jinjina masa ta kasa magana , rungumeta yayi a jikinsa shima a hankali ya furta “ I love you!!!!!! Ammu”, a hankali ta furta “ Love you more and more my baby“. Kusan 3 minutes suna rungume da suna kafun da Sauri junior ya kalleta “ Ammu na manta, abinci fa zamuci grandpa yace na kira ki”, girgiza masa kai tayi “ Allah ya shiryeka son , bari na wanke fuskata sai mutafi”, tana kai karshen zancantawta wanke face d’inta tare da daukar junior kamar wani baby suka fito down stairs, gabaki d’aya kowa da kowa ya hallara tahee da junior kawai ake jira , kallan fuskarta Dady da momy sukai, duk da alamu ya nuna kuka tayi babu Wanda yayi magana , daman ta sabayin kukan , yau da kanta Mimi tayi serving d’insu abinci, tunda suka soma ci babu Wanda yayi magana sai junior da lokaci zuwa lokaci yake magana , suna kammalawa kowa ya bawa tahee gift ta zamowarta barrister , a nan d’in ma wani saban kuka ta fashe da shi, sun d’an jima a Wajan kafun dady ya mike , momy ta bi bayansa , yayi saura tahee da Mimi, daman yah moh shiya fara futa da junior.
*********
***************
**********
***************
FLASH BACK
Tun lokacin da tahee ta dawo Uk wajan Alhaji isma’il suka cigaba da kula da ita, tun tana kin sakewa dasu har ta fara sabida yadda ko wannan su yake janta a jiki, A bangaran momy ma sosai take bawa tahee kulawa kamar ‘yar da ta haifa da cikinta kome zatayi wa mimi shi zatayiwa tahee, sosai suke bata kulawa babu me nuna mata banbanci, kullum momy cikin dubata take kasan tuwarta kwararriyar Doctor . Shima yah moh kullum cikin siyo mata kayan kwad’ayi suke shi da dady. Gabaki d’aya family sai suke bata kulawa ta musamman. Lokacin da dady yakezo sa tahee a makaranta ta wayarta da baba Malam ya basa yayi anfani ya Fito da soft copy din makaranta dake cikin wayar, duk da yar hanzu be fad’a mata wayar na hannunsa ba . Koda sukaje school sabida kokarin ta yasa aka za tayi iya tafiya university, sosai tahee tayi farinciki da hakan, take a Wajan ta cike ‘bangaran law department, mimi ta cike nursing, haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin ahalin kullum tahee da tunanin a halinta take kwanciya take tashi , fatan ta Allah yasa suna cikin ‘koshin lapiya. A haka rayuwa tacigaba da tafiya da tahee tana samun kyakkyawar kulawa daga mutanan gidan , mimi ma sosai take janta a jikinta har soyayyar da suke wa juna tayi ‘karfi, lokacin da tahee ta fara labour gabaki d’aya family babu Wanda hankalinsa be tashi ba amma cikin iko na ubangiji ta sum’bulo d’anta kyakkyawan gaske fari tass dashi kamar ka ta’basa Jini ya zuba sabida kyansa, hatta Doctor d’in kowa ya gansa sai ya furta “ the baby is so beautiful” basu wani dad’e a asibitin ba aka basu sallama suka koma gida , gabaki d’aya familyn momy saida sukazo hatta wata sister d’in momy Itace tayiwa tahee wanka sabida yanda suke ‘kaunarta suma musamman da momy ta basu labarinta . Sosai dady da yah moh suka nuna bajintarsu ranar sunan kamar d’ansune ya haihu haka akayi tafi nagani na fad’a , baby da maman baby sosai suka tara gift sbd yaro yayi goshi sai san barka . Hatta friends d’inta na school wasu duk sunzo mata , ranar suna yaro yaci suna mohammad , Sabida shine sunan da kullum king yakece mata yanaso ya sa wa babynsu, sai suke masa la’kabi da junior .kullum momy da mimi ne suke kula da junior , har yaro yayi wayo sabida baiwar saurin fahimta da yake dashi, a haka tahee taci gaba da karatunta har zuwa ynxu da ta kammala karatunta amatsayin barrister.
??????
BACK TO STORY
Karfe 9:30 na dare dady yabu ‘kaci ganawa da kowa da kowa na cikin family d’in, gabaki d’aya taruwa sukai cikin babban falon dady, lokacin junior na jikin momy yana bacci , taro dady ya bud’e da addua bayan salatin annabi da sukayi, shiru dady yayi yana juya maganar da zaiyi , itama momy shiru kawai tayi batace komai ba , gyaran murya dady yayi kafun ya soma magana , “Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah , ina ‘kara gode wa Allah da ya bani ikon ganin ranar nan, ha’ki’ka nayi farincikin kammaluwar karatunku, ina ‘kara gode wa Allah, sannan ko wannan ku gift d’insa da na basa yana wajan momy a Wajan ta zaku karba , abi na biyu kuma maganata akankine tahee,” lokaci d’aya zuciyar tahee ta buga jin ya ambaci sunanta, amma bata ce komai ba sai ‘kasa da ta ‘karayi da kanta.Ba sai na maimaita abunda suka faru shekaru bayaba, amma yanxu lokaci yayi da za’a wuce wannan ga’bar, lokaci yayi da tabon mutanan da suke cikin‘kuncin ya goge, ko ba’a fad’a ba nasan kinsani junior ya fara wayo, yana bu’katar sanin mahaifinsa, yana bu’katar salin ahlinsa, ke matar aurece na tabbata Indai mijinki na raye to tabbas yana cikin kuncin rayuwa, mahaifiyarki tana cikin bakin cikin rayuwa haka ma d’an uwanki, lokaci yayi da zamu koma Nigeria gabaki d’ayan mu. Ba tahee data d’ago kanta ba hatta yah moh a mugun firgice ya kalli dady kansa na sara masa , cikin zuciyar sa ya maimaita “Nigeria ?”, kamar dady yasan me yake fad’a ya ‘kara maimaitawa “ eh Nigeria, Nan da 2 weeks duk Wanda yasan yana da abunyi yayi kafun nan da 2 weeks dan tafiya ba fashi “, idanuwan ya moh har sun fara yin ja, itama tahee da wani irin shock take maimaita Nigeria cikin zuciyarta. Wata waya ya ciro daga cikin aljihunsa tare da wani ‘karamin hoto da ya fad’i batare da sanin saba , wayar ya mi’kowa tahee “ Nasan bazaki manta da wannan wayar ba ko? Sabida tare da ita aka sameta cikin aljihunta”, ita tahee kuwa gabaki d’aya bata san me yake cewa ba , hankalinta yana kan hotan da ya fad’i a kasa , hakanan zuciyar ta take san ganin hotan, saida dady ya ‘kara kiran sunan ta kafun ta saka hannu zata kar’ba wayan ya su’buce mata a hannu sabida bud’ewar da hotan yayi ita kuma wayar ta gangara inda yah moh yake, da Sauri tahee ta d’auki hotan zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri , gabaki d’aya sai suka maida hankalinsu kanta, kallan Alhaji isma’il tahee tayi kafun ta mayar da hankalinta kan hotan, shima a Daidai lokacin da yah moh ya d’auki wayar tahee da ta fad’i, cikin wani irin zabura tahee ta furta “Oumma?”, da sauri Alhaji isma’il ya mi’ke tsaye yana ‘ko’karin yin magana wayar tahee tayi haske, cikin wani irin shock yah moh ya mi’ke take a wajan ya soma ganin jiri jiri na d’ibarsa , babu abunda yake maimaitawa sai “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”, nuna wayar tahee kawai yake yana ja da baya ga juwar da take ‘ko’karin kayar dashi , mimi har ta soma kuka babu abunda take fad’i sai yaya moh , meke damunka” . Ga baki d’aya sai abubuwan yaso d’aurewa dady kai musamman Wayar tahee da yah moh yake nunawa, kamar daka sama ya furta “ King” da ‘karfi, take a wajan kuma ya sulale ‘kasa . Da sauri dady da su momy suka nufa inda yake, tahee kuwa kasa ‘karasawa inda yake sai fuskarsa da ta tsurawa ido, kusan 2 minutes tana kallan fuskarsa kafin cikin shock ta mayar da kallanta kan junior dake bacci, sosai tashiga rud’ani kanta itama ya soma juyawa take a Wajan itama ta sulale. Tashin hankalin da ba’a sa masa date, sai suka rasa kan wa zasu tahee data suma ko yah Moh daya suma , babu abunda dady yake furtawa sai “ruwa ! Ruwa !” Da Sauri mimi ta nufi kitchen , cikin ‘kan’kanin lokaci ta dawo d’auke da bottle d’in ruwa guda biyu, momy ta karbi d’aya shima dady ya karbi, ruwan suka shafamusu gabaki d’aya suma sun rikice ganin abunda yake shirin faruwa . Tahee ce ta soma ajiyar zuciya har yanxu hotan data d’auka yana hannunta ta ru’keshi gagam. Yah moh kuwa har yanxu baya motsi abunda ya ‘kara tayar da hankalinsu, abunda ya bawa kowa mamaki, tahee tana farkawa inda yah moh yake a kwance ta zube tana fashewa da wani saban kuka , cikin murya kuka take furta “ Na ro’keka katashi, katashi dan Allah”, kasa magana dady yayi ganin irin kukan da tahee take ,sai abu yaso had’e masa ga momy data tayar da hankalinta ga mimi itama da take masa kuka, a ‘bangaran tahee ma gashi tana bashi tsoro ganin yadda take kuka akan Moh ya Tashi. Yana kara fesawa yah moh ruwa , ya fara motsi a hankali, bakinsa babu abunda ya ke am bata sai “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un “. Temaka masa dady yayi ya zauna sosai , da sauri tahee ta d’auki wayar tata tana nunawa yah moh, cikin rawar murya take nuna masa wayar , da ‘kyar ta samu bakinta ya furta “ yaya king” sannan ta nunasa a hankali kamar tana tsoran magana ta furta “ Akhieee?” Shima
Fuskarsa gabaki d’aya tayi jawur bakinsa yayi nauyi ya kasa cewa komai sai d’an motsa mata kai da yayi alamar eh , murmushi da hawaye tahee ta fara lokaci d’aya sai momy da dady da kuma mimi suka zuba musu idanu gabaki d’aya sun kasa magana , maganar yah moh ne ya ‘kara rikitasu da ‘kyar ya kalli tahee kafun ya nuna junior dake kwance yana bacci, sai kuma ya nuna wayar hannunta “ junior !? Is my son”,murmushi tahee ta sakar masa tana d’aga masa kai , duk da haka sai da ya ‘kara furta “ junior is my brother’s son? ‘Dana ne ? ‘Dan king d’ina ? My dearest brother is now a father ?finally zan ‘kara ganin king d’ina ? Ummey? Abeey?Samreen? Dada?” Kai kawai tahee ta d’aga masa dan gabaki d’aya ta kasa magana , Sabida farincikin da ta shiga “ her lovely husband zai ‘kara samun farinciki? Wana irin farin ciki zai shiga idan ya ga brother d’insa , together with his wife and his baby?” Duka wad’an nan tanbayoyin kanta tahee take yiwa . Dakatar dasu momy tayi kafun ta furta “ kunsa mu cikin duhu, daman kun san junane?” Lokaci d’aya suka girgiza mata kai alamar a’ah . A sanyaye , dady ya furta “ kuyi mana bayani yadda zamu gane amma kafun nan inaso na tanbayeki tahee, naji kinkira matar cikin wannan photon da oumma ko kinsan me kama da ita ne?”. Sai yanxu hankalin tahee ya dawo kan hoton tana sakin murmushi, Oumma tace tare da brother d’inta da ya ‘bata “ da Sauri dady ya kalleta tare da nuna hotan “ oumman ki? “ yanxu ma kai tahee ta jinjina masa murmushi kwance a kan fuskarta. “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” cewar dady, hotan hannunta ya nuna sannan ya nunata , a hankali ya furta “ ke.. ke yar maryam ce ?”, dukda tahee tayi mamakin yadda yasan sunan oummanta hakan be hana ta amsawa da “eh” wani irin farin cikine ya kama dady har ya kasa ‘boyuwa akan fuskarsa “ Alhamdulillah!!! Alhamdulillah!!” Kawai yake furtawa , kallan momy dady yayi itama da take murmushi “ ina tare da Jinina tsawan lokaci Amma ban sani ba ?” Da Sauri Mimi ta furta Dady wacce ?”, farin cikin da ya dad’e beyi bane kwance a fuskar dady , amsawa Mimi ba sai ‘kara kallan tahee da yayi sosai , tabbas tana kama da maryam d’insa , alama yayi mata data matso, ba musu kuwa ta matso d’in hotan hannunta ya kar’ba kafun ya nuna mata oummanta , “ Maryam ‘kan wa tace , nine nan a kusa da ita “, yanxu ma su mimi zubawa sarautar Allah ido sukai har yah moh kallansu yake lokaci zuwa lokaci yana sakin murmushi idan ya kalli junior . Nunasa tahee tayi kafin ta nuna hotan , a hankali ta furta “ uncle isma’il?”, murmushi ya sakar mata sosai yana jinjina mata kai , cikin farin ciki ya furta “ Allah ya ‘kaddara zan ‘kara ganin ahalin Maryam Alhamdulillah, yanxu dare yayi zamu tattauna gobe da safe “, badan sun soba duk suka mi’ke dan gabaki d’aya baccin ya gudu sabida farinciki, kallan tahee ya moh yayi , kafun ya kalli junior “ please ki barshi yau a waje na “, dariya yaso bata kamar yau ne suka soma kwana tare kanta kawai ta d’aga masa , itama fuskarta cike da murmushi ta furta “ bari na d’auko kayan baccin sa “, kafun ta ‘karasa ma Mimi har ta hau sama taje d’auko masa , d’aukan junior yah moh yayi , Daidai lokacin da Mimi ta dawo d’auke da kayan sa, mi’kawa yah moh da yake binta da d’an kallo kawai tayi, har yanxu kanta a tushe yake , ganin komai take kamar a mafarki , jira take kawai gobe tayi . Gabaki d’ayansu kowa goodnight yayi wa junansa kafun su nufa d’akunansu, yau Mimi d’akin tahee ta nufa , lokacin da suka kwanta Mimi sai kallan tahee take har hakan yasa ta tsargu , d’akawa Mimi duka tayi “ wannan kallanfa?” Murmushi Mimi tayi kafin ta sha gefan fuskar tahee , a mai makon ta amsawa tahee tanbayarta “ ban ta’ba ganin farin ciki sosia haka a fuskar dady ba , ya dad’e yana neman ku, da ya samu free time zaice zai tafi Nigeria , wani lokacin har kishi nake , sai na dunga tunanin ko dady yafi sansu akan mune ? Amma yanxu sosai nake farinciki, finally Nima naga familyn dady na “d’an harararta tahee tayi wato da mu kike kishi?” Murmushi kawai Mimi tayi mata , shiru tahee tayi kamar me tunani kafun ta furta “ Yah moh fa”, juya mata baya Mimi tayi tare da kashe light d’in dakin kafun ta furta “ good night, ni bacci nake ji”, dariya ce ta so su’buce wa tahee Amma tayi ‘ko’karin dannewa so take washe gari Kawai tayi, “ one side d’an uwan mijinta da kowa yayi tunanin ya mutu, the other side yayan mamanta.”, a hankali yadda Mimi bazata ji ba ta furta “ ya Allah ! Allah ka bayyana mun su , ko zan ‘kara ganin farincikinsu. Gabaki d’aya ahalin gidan sai kowa ya kasa rintsawa kowa da abunda yake sa’kawa aransa , yah moh tunda suka kwanta yake bin fuskar junior da kallo lokaci zuwa lokaci yana kissing forehead d’insa.
????????
??????????
BUNKURE
????GIDAN AUNTY ????
07041879581
MSS LEE ??
LEESHARH DATA HUB
BUY DATA AT AFFORDABLE PRICE:
MTN AIRTEL
500mb-120. 500mb-140
1gb-240. 1gb-300
2gb-440. 2gb-600
3gb-620. 3gb-900
5gb-1200. 4gb-1200
10gb-2200. 5gb- 1500
Validity : 30 days
ACCOUNT DETAILS :
2681892316
AISHA UMAR , ZENITH BANK .
For more information contact me through my phone number: 07041879581.
Post a Comment for "Gidan Aunty book 2 Page 10"