Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Daurin Boye 60

60

*_BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYU_*

 

Misalin sha d’aya na safe jirgin dake dauke da iyalan muhammad khalipha sa’id mai goro ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano dake kano.


Yarinya ce ‘yar kimanin shekara goma sha uku ce a gaba riqe da hannun wani yaro d’an kimanin shekara biyar,bayanta wata matashiyar macace fara tas mai matsakaicin tsayi da dogon hanci,wadda kana mata kallo d’aya zaka tabbatar da cewa hutu jin dadi da gayu sun ratsata take biye da ita,fuskarta qunshe da murmushi wanda hakan ya bayyana dimple dinta dake kumatunta na hagu da dama,tana dauke da wani kyakkyawan yaron wanda baifi shekara uku ba,sak kamanninsa na muhammad khalipha ne mai goro,shine ya fito a qarshe yana ruqe da qananun akwatina masu kyau guda biyu,shima fuskarshi na dauke da murmushi da alama magana suke da uwargida sarautar mata ayshatu dake gabanshi
“Farha….oya bani jawad ki amshi trolly dinku” da gudu jawad ya zame hannunshi daga na farhan yana tawowa wajen aysha,harara khalipha ya jefawa aysha mai nuni da zallar qauna
“Hajar din zan baiwa daukan akwati?” Murmushi ta saki don dama ta sani hakan zata kasance,wata qauna yakewa yarinyar tamkar hajar dinsa,haka suka dinga takowa har zuwa inda motocin MAI GORO suke jiransu.

Dukka qofofin motocin a bude suke suna jiran isowar boss din nasu,suna hangosu a hanzarce suka amshi akwatunan hannunshi suka shige mota guda shi da iyalin nashi gaba daya.

Kwabe fuska jawad yayi yana duban aysha
“Anna…ba gidan anni zamu fara zuwa ba?”
“Ban sani ba tambayi abbinku” ta fada tana gyarawa fu’ad kwanciya a jikinta,duban khalipha yake yana son magana yana tsoro,saboda last time da sukazo yace ba zasu sake zuwa su kwana wajen annin ba,saboda yadda suke qiriniya da rashin ji idan sunje,yace ba zasu hana uwarshi hutawa ba,itama farha kallon abbun nasu take,ita kanta tafison gidan annin,saboda tun suna can sunyi waya dasu amra da afaf (jikokin annin yaran basma da haidar,da ‘yar mus’ab),Dukkansu suna can gidan anni suna hutu daga kai khalipha yyi ya kallesu sae ya maida kai baice musu komae ba jawad ne yakasa shiru murya a sanyaye yace pls abbu akaimu gidan ammi munyi alqawarin bazamu sake pitina ba baice mishi komai ba ganin hakan shima yaron yaja bakinshi yyi shiru.

Cikin yan mintina suka isa kataparen gidansu dake nasarawa meela road tanpatsetsen gidane da khalipha ygina da yadauki shekaru yana ginashi mention house ne nagani napada a parking space duka motocin suka tsaetsaya su jibiril sukaxo suka bude musu qopa taxuro qaparta xata pito daga motar wayarta ta soma ringing saeta dakata da pitar takira farha ta daukar mata fu’ad duba mekiran tayi inna yalwa ce sae tayi mamaki data ga number nigeria da alama ta dawo gida kenan daga jinyar qaparta da khalipha yapitar da’ita saudiyya sagas a tayi tasa akunnenta gami dayin sallama dagacen bangaren inna yalwa ta amsa
“nayi sa’a kardae kice min kindawo?” Murmushi Aisha tayi gami dacewa “nima yanzu a raina nakecewa ashe kindawo”
“Eh wolh kwanana biyar kenan da dawowa ta”
“Toh yaya jikin”
“Jiki alhmdulilahi nasamu sauqi, kitayani yiwa allaji khalipha godiya Allah yasaka da alkhairi,ya qara budi”
“Amin ai babu komai,cikin satin nan ma zamu shigo takai din in sha Allahu,su mero zasu tare sabon gidansu”
“Ma sha Allahu…an gana kenan?,ke dai indo babu abinda xamu ce dake saidai godiya da fatan alkhairi keda halipha,kaf karkarar nan babu wanda baici arxiqinki ba,babu wanda arziqinki dana mai gidanki baibi ta gidansa ba,Ashe haka rayuwa take,bakasan wanda zaka ci arxiqinsa ba….ki yafemin indo bazan daina neman yafiyarki ba har abada…” Ta qarashe maganar cikin rauni da nuna nadama
“Kai inna,ya wuce fa,sai munzo din”
“Allah ya jiqan mahaifinki indo,ki gaidamin da masu gida na da kishiyata”murmushi ta saki
“zasu ji” ta fada tana kashe wayar ta maidata jaka sannan ta qara fitowa daga cikin motar,zuwa sannan tuni khalipha da sauran yaran sun shiga ciki don haka tabi bayansu a nutse,cikin taku na cikakkiyar mace mai ilimi wadda tasan abinda take,wadda ta gogu da ilimi da zaman duniya.

 

Bata shiga ciki ba sai data kira mummy bayan ta kira ummi ta sanar mata dawowarsu,ta tabbatar da komai na tafiya lafiya cikin sabon gidan da khaliphan yayi musu,ya dauke shima dukkan wata lalura ta mummyn,don daddy wani mutum ne mai muhimmanci shima a rayuwarshi,bazai taba manta alkhairinsa ba a gareshi,tun daga ranar da yasan abinda ke faruwa ya amshe duk wata dawainiya da da ayshan ta akarba yaci gaba da jan ragamarta,zuciyar khaliphan mai kyau ce,ya manta dukkan wata cuta da wani mai cuta yayi masa,ya rama kowacce cuta da alkhairi,hakan yasa itama ayshan ta qara qaimi,taci gaba da kyautatawa duk wani wanda ya jibanceta na kusa dana nesa.

A nutse cikin nishadi da qaunar iyalin nata ta shiga cikin gidan,ba kowa a falon sanda ta shiga katafaren falon da xai sadaka da sassa daban daban na gidan,dakunan matar gidan,dakunan yaran gidan,ban dakuna,kitchen da kuma sashen baqi mata,sai sashen mai gidan,tunda bata gansu ba tasan ba zasu wuce dakin yaran ba,murmushi ta saki ta zare mayafin rolling dake kanta ta nufi kitchen din gidan don duba masu aikin gidan wadanda dattijan mata be guda biyu rak suke mata aiki,sai guda daya da batakai shekarunsu ba,a yanzu haka tasan suna can don sunsan da dawowarsu.

A mutunce suka gaisa,kai baka ce ‘yan aikinta bane,ta dudduba abinda sukeyi sannan ta gaya musu abinda zasu dafawa yara da abinda zasu hada mata wanda zata shigo da kanta ta yiwa khalipha girkinsa.

Daga nan dakin yaran ta nufa,dakin farha na bude saidai labulen a sake yake,budewa tayi ta tura ta shiga don ta dubata,qarar ruwa taji a toilet hakan ya sanya ta saki murmushi tasan wanka take kuma da alamun da qyar idan ba gidan annin zai kaisu ba,ficewa tayi daga dakin ta shiga nasu fu’ad,yana zaune saman gadansu dukka yaran daure da towel,da alama wanka yayi musu,don ga kayansu nan saman gadon yana feshesu da turare,saita samu gefan gado ta zauna kawai tana kallonsu,tamkar yaya da qannenshi,tamkar abokanshi haka wani lokaci yake mu’amala dasu,shi yasa zata iya cewa sunfi sonshi fiye da ita,kusan dukkan wata hidimarsu bai gajiya idan har yana qasar ko yana tare dasu shi yakeyi musu,hakan ya sanya yanzun ma tayi tagumi kawai tana kallonsu tana jin hirarsu da dararrakunsu,a haka ya kammala shiryasu tsaf dai dai sanda farha ta shigo,tayi kyau cikin shadda bubar har qasa yellow mai red din stone work,shigen kayan dake jikinsu jawad yellow and red
“Good qanwata(wani lokaci yakan kira farha da haka),kinfi kowa yin kyau” murmushi ta saki cikin jin dadi,yana son yarinyar sosai saboda kama da take dashi sosai ita da jawad,jawad din ne ya tabe fuska
“Abbi…..abbi” yana langabe kai,yasan me yake nufi saboda haka ya shafa kansa
“Bakaga yadda kayi kyau ba my twinny(shima hakan yake kiransa wani lokacin saboda kamarsa da shi)” sunan yana yiwa jawad dadi sosai,saboda haka ya saki murmushi shima yana sakewa farha gwalo a boye,duka takai masa ya boye bayan khalipha
“Abbi….gwalo yakemin”kamo hannun jawad yayi ya dawo dashi kusa da ita ya kama hancinsa ya dan riqe
“Bana son tsokana,bata haquri” baki a tabe ya bata haquri,shi kuma ya juya ya kallo farha
“Ke kuma big sis ce…..saikinyi haquri” kaman xatayi kuka tace
“Hademin kai suke fa shida fu’ad abbi…..”
“Qyalesu qanwata…..ki cewa anna ta samo miki ‘yar uwa kinga kema kin huta”juyawa tayi bangaren da aysha take tana kallonsu,hannayenta ta hade waje guda,alamun roqo,dan hararar farha tayi kadan saita juya kaman zatayi kuka ta kalli khalipha ta daga kafadunta dukka biyu tana tabe bakinta tana nuna mishi alamun ayshan taqi,shima narkewa yayi ya mata alama yayi mata na abun tausayi ya girgiza kai yana duban ayshan
“maman yara….pls a taimaka mana a sake bamu baby girl” dubanshi tayi ta masa signa da ido na yadda yaran sukayi shuru suna jiran amsar ayshan,ta rasa yadda yaran keda shegen son yara,hatta da fu’ad da bai wuce shekara bakwai ba idan yaga yaro ko yarinya,sai kawai ta miqe ta fice a dakin tana murmushi qasa qasa.

Kayan jikinta ta fidda ta soma daura towel,tana tsaka da daurawar taji ya rungumota ta baya,amsar daura towel din yayi tana rungume a jikinsa yana daura mata kanshi saman kafadarta yake cewa
“Kinqi kawo mana agaji nida yarana ko?” Murmushi ta fitar kawai bata ce komai ba,yana gama daura mata ya birkitota gaba daya suna fuskantar juna,yana shaqar qamshin turaren jikinta,idanunshi cikin nata yana mata wani kallo mai tafiyar da xuciya
“Da gaske muke annah….muna son yara ba zaki agazo mana ba” hannunta ta dunqule ta dora a qirjinta tana murmushi
“Allah ya kawo abbi” dan jim yayi sannan yace
“Ameen….muje in wanke matata” cak ya dagata yana takawa a hankali tana dariya tace
“Abbi baka gajiya?,ka wanke yara ka wanke mamansu?” Murmushi ya saki
“Dama ce….ai ina da cikakken time ne,idan kuma ban muku hidima ba wa zan yiwa?” Shuru tayi tana gyada kai cike da jin dadi da hamadala ga Allah.

Sai daya sakata cikin bathtube ya juya ya fice yana cewa
“Ina zuwa” minti daya sai gashi ya dawo,tare sukayi wankansu sannan suka fito,tsaf suka shirya,shi ya bata wasu kaya wanda kalarsu daya da nashi da kuma na yaran,shadda ce irinta farha,tana ta tambayarsa me ake ina zasu baice mata komai ba yace su zuba ido zata gani.

Cikin sabuwar motarshi fara qal suka shiga suka bar gidan,ita dai tanata zuba ido,basu sauka ko ina ba sai gidan anni,sam bata gane meke faruwa ba sai da suka shiga cikin gidan,tafkeken falon annin cike yake da decoration da kayan ciye ciye da qyale qyale,matar mus’ab,basma qanwarta kuma matar haidar da yaransu gaba daya a falon,suna shiga dukka qwayayen dake falon masu dauke da kaloli suka kama,wasu rubutu suka bayyana,ta daga kai tana karantawa,sai a sannan ta gane me yake nufi,murnar cikar aurensu shekara goma sha hudu cif cif dayi ya hada musu.

Sun jima a gidan annin ana sada zumunta gami da ciye ciye da shaye shaye,dukkan familyn kana ganinsu kasan cewa cikin farinciki da walwala suke,basu tashi barin gidan ba sai bayan sallar magariba,tun kafin a soma maganar tafiyar dama su jawad suka soma nacin a barsu gidan annin,dama ya shirya hakan saboda haka yace su zauna din,har sun miqe suna mata sallama ta dakatar da khalipha
“Auren amal ya taso fa,inatason gaya maka ita da zeenatu za’a hada” dan sosa kunnenshi yayi kadan sannan yace
“Yanzu ya za’ayi anni?”
“Dukkan abinda ya dace yanda ka yiwa maryam”
“To shikenan ba damuwa…..za’ayi duk abinda ya dace in sha Allahu”
“To Allah ya taimaka ya yiwa dukiya da rayuwa albarka”
“Amin ya Allah anni,amin” da haka suka juya zasu wuce,babban yaron haidar affan dake zaune waje daya yana cin abinci khalipha ya kalla
“Affan ya jikin dai?”
“Da sauqi abbi”
“Ma sha Allah Allah ya qara lpy”
“Amin” ya amsa mishi
“Anty na asha amarci lafiya” fatima matar mus’ab ta fada qasa qasa tana dariya,hararta aysha tayi,sosai jininsu ya hadi da fatiman,tana girmamata kamar yadda basma take girmamata,hakanan itama ta dauketa a qanwa kamar yadda ta dauki basma
“Wane amarci shekaru sha hudu ba wasa ba,ko kin manta daku muka gama murna yanzu”
“Kullum jin kanku da daukar kanku kuke kamar sabbin ma’aurata,abun naku da ban birgewa yake daban sha’awa,kullum hirarku muke da abban ummu salma,wai ba za’a bamu sirrin ba muma mu hau network?” Dariya sosai ta baiwa aysha,tasha jin wadan nan maganganun daga bakin mutane da yawa,kada ma hanan taji labari,har wani lokaci ta rasa amsar basu,itadai tasan qaunarsu daga Allah ce,jigon tafiyarsu shine haquri da juriya,uwa uba kawaici da yiwa juna uzuri,soyayya ta domin Allah bata gushewa haka bata qarewa,indai dukkanku zaku yarda kuna bautar Allah ne sannan kowannenku yayi qoqarin sauke haqqin Allah na dan uwanshi daya da Allah ya dora mishi cikin girmamawa da kyautatawa,wannan sune kalaman data gayawa fatima wadandan ta jima tana yi musu dalla dalla,haqiqa sun qunshi abubuwa masu muhimmanci da dama wanda sai sun samu zama da ayshan sosai zata nemi sani da cikakken qarin bayani akai.

Ita ta soma gama shirin kwanciyarta tsaf ta haye gadon tana jiranshi,duk wani shiri ta gamashi don ta gama karantar mijinta,cikin satin da suke shirin tahowa nijeria yanata zirga zirga bai samu zama ba,tana kallonshi ya gama komai ya isketa,yana murmushi sanyata cikin jikinsa sosai yana shaqar daddadan qamshinta mai shiga rai da tsayawa a zuciya
“Uwaishahh……meye labari,naga bakinki akwai magana da alama” qanqameshi itama tayi sosai,ta zagaya hannunta a bayanshi tana murmushi
“Ina godewa Allah da baiwar da yayimin da kuma ni’imar nagartaccen miji wanda babu tamkarsa kamar kai,kaine baiwa ta farko kuma ni’ima ta farko cikin rayuwata,ina roqa maka alkhairin Allah rahamar Allah da kuma jin qan ubangiji a gareka nan duniya da gobe qiyama……my life…ina maka albishir ina dauke da juna biyu” idanu ya zaro cikin xumudi yake duban idanunta
“Are you seriouse uwaisha?” Kai ta kada
“Da gaske nake maka my babu irin wannan zolayar a tsakaninmu,bazan taba ja maka rai ba kan abinda nasan kana so”
“Allah na gode maka da dukkanin baiwa da ni’imar daka yiwa rayuwata,Allah na gode maka daka bani matar aljanna tun a duniyata,uwaishaaa,duk abinda zan gaya miki a kanki ina kin tamkar na rage darajar so da qimarki da nake gani a rayuwata”
“Ni ya cancani nayi wannan godoyar wa uba giji,farincikin daka baiwa rayuwata baya misaltuwa,ka zama silar warwarewa dukkan wani DAURIN BOYE da ya yiwa, rayuwata dabaibayi,ina sonka abbi,ina sonka sosai abban farha jawad da fu’ad”
“Da unborn ba…..” Dariya ta saki tana sake shigewa jikinsa
“Zumudi dai your royal highness”
“Kinga lafina?,yara nakeson dozen biyu…..bari ma kiga ni na sake bada himma ko zasu zama biyu idan kin tashi haihuwa” dariya sosai ya bata,a ranta take cewa ko ina ake haka?,cikin aminci salama da kuma sallamawa suka shiga wata duniya mai cike da nutsuwa da aminci wa juna.

*Alhamdulillahil lazi bini’imatihi tatimmus salihat*????

_muna miqa dumbin godiyarmu ga dubun nan masoyanmu da suka kasance damu,suka bamu goyon baya,suka kasance cikin group na zafafa biyar,haqiqa soyayya ba qarya bace,Allah ya qara zumunci ya sadamu da dukkan alkhairinsa,rabbi ya yafemana dukkan kurakurenmi cikin rubutunmu,ya hadamu a ladan amin summa amin_

*subhanakallahumma wabi hamdika,ashahadu an la’ilaha illa anta,astagfiruka wa’a tubu ilaika*????????

*mrs muhammad ce*??

Post a Comment for "Daurin Boye 60"