Daurin Boye 59
59
Qarfe goma da wani abu na safiya suke takawa cikin asibitin hannayensu sarqafe da juna,duk wanda ya kallesu saiya sake juyawa ya dubesu,kana kallonsu kasan cewa masoya kuma ma’auratan da suka dace da juna,ba
qaramin kyau sukayi ba,shi yana sanye da suit yayin da take sanye da atamfa dinkin doguwar riga,fuskarta tayi wani irin kyau,tayi fresh abinta saika dauka wani makeup tayi,saidai babu komai a fuskar tata sai powder kwalli da man lebe,gab da zasu shiga cikin asibitin ya daga waya ya kira annin ya tambayeta dakin da aka kwantar da kawu idris ta gaya mishi,ya kashe wayar ya maida aljihunsa yana sakin ajiyar zuciya,hannunshi ta riqe sosai tsam saboda tasan yanzun ranshi zaya baci,tasanya daya hannun nata ta zare glass din fuskarta ta lanqwasheshi cikin hannunta,juyowa yayi suka hada idanu saita narke masa tana tsayawa daga takawar da suke zuwa cikin asibitin,gira ya daga mata alamar tambaya,a shagwabe tace dashi
“Ya khalipha pls mana,idan kasan ranka zaya baci ba zaka saki ranka ba ka tsaya ni na shiga,sai na gawa anni kai baka shiga ba” kai.ya kada yana sake mata murmushi,ya kashe mata idonsa daya
“Noo princess uwaisha….muje” da haka suka ci gaba da takawa.
Tun daga varender da dakin yake suka dinga jiyo ihu,haka suka dinga takawa har zuwa bakin dakin,wasu daga cikin yaranshi da ‘yan uwa ne tsaitsaye bakin qofar dakin jugum jugum,duk wanda ka kalla alamun tashin hankali ya bayyana qarara a fuskarshi,hango khalipha ya sanya sukayo wajenshi suna mishi sannu da zuwa,amsawa yayi yana zare glass din fuskarsa gami da kallon qofar dakin da ihun ke fitowa,zame hannun aysha yayi daha cikin nashi yadan sunkuya saitin kunneta
“Ki tsaya anan yanzu zan fito” kai ta gyada jikinta a sanyaye itama,bisa dukkan alamu mai mara lafiyan ne ke wannan ihun da qarajin.
Tura qofar dakin yayi bakinsa dauke da sallama,duk da ihun da kawu idris yake kwararawa bazai bari aji sallamar ba,ibrahim ne yake riqe dashi,matarsa tana gefe tana zubda qwalla,tsayawa yayi khalipha yayi yana dubanshi
“Ibrahim nace maka ka kwaramin ruwa,cikina…wuta ce,wutace take ci ajikina,baka ganta ba,nace baka ganta ba,jikina zafi yake min ibrahim jikina”
“Sakeshi” khalipha ya fada yana duban kawu idriss din,sakinsa ibrahim yayi yana share gumi da qwalla,addu’a ya soma yi yana tofa masa a jikinsa, hankali zafin da yakeji ya ragu sosai,ihun da yake ya tsaya sai qananun surutai
“Na gode khalipha,na gode” ya dinga maimaitawa,kana ji kasan sambatu yake
“Na gode khalipha ka yafemin naci dukiyarku,na cinye dukiyarku,nina kasheshi,nina kashesheki” gabansa ne yayi mummunan faduwar,sai ya zuba mishi idanu,a hankali ya bude bakinsa
“Kai ka kashe wa?”
“Babanku sa’idu,nine dasu hamza suka qi saina kasheshi ni kadai,saboda inason ayshatu inason na aureta” wani irin tuquqi yaji qirjinsa yanayi,take idanunshi suka sauya kala,sannu sannu ya dinga ja baya yana kallonshi,ya yunquro zai cafko khaliphan yana cewa
“ka tsaya karka tafi,tofamin addu’a tofamin,zafin da nakeji ya dawo….ka tsaya mana” juyawa yayi ya fice idanunsa jajur,tashin hankalin daya ji ba kadan bane a sannan,mutuwar babanshi da hajar ta dawo masa sabuwa fil,cikin wani irin zafin nama ya ja hannun aysha ba tare daya waiwaya ya dubi kowa ba suka fice yana jiyo ihun idriss.
Tunda suka sauka a gidansu na cyprus ta kasa gane kanshi,duk wani abu tayi amma ba canji,data gaji kawai saita zauna ta sanya mishi kuka,a rude a janyota jikinsa yana tambayarta
“Meya faru uwaisha?,nine ko?,am sorry kiyi haquri,uwaisha…..shi ya kashemin abba na,me yayi masa haka arayuwa bayan tarin alkhairai daya musu?”sosai maganar ta daketa,saita daga kai tana dubanshi,yau taga ahalin da suka fi nata zalunci,taga ahalin da suka dara nata ahalin mugunta da watsi da zumuncin Allah,maganar ta kidimata,saidai ya zama dole ta rage razanar data yi saboda ta maidashi cikin mode dinshi
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un,gaskiya ne ya aikata babban xalunci akan ran da bata jiba bata gani ba,abba ajalinsa ya riya yazo,koda kawu idris ko babu shi tilas saiya tafi,tsakaninka da abba yanzu haka addu’a ce,haqiqa Allah baya barin wanda ya kashe wata rai ba tare data cancanci hakan ba,ka zuba ido kaga shima zai tabbata ne a duniya?,komai daren dadewa sai ya tafi inda abban yaje” da kalamai masu dadi tayi amfani ta samu kanshi,ya dinga sauke ajiyar zuciya ajejjere,tsananin fushi bacin rai da rudanin daya shiga suna sauka.
Gab da zasu kwanta wayarshi ta dauki kida,ya duba sai yaga haidar ne
“Ya akayi haidar,ina fata kowa lafiya”
“Eh mukam lpy lau,kawu idris ne ya wuce,baku jima da barin asibitin ba yarasu”idanunsa khalipha ya lumshe,maganganun aysha na dawo masa fes aka,kamar a sannan take gaya mishi,sautin haidar shi ya katse masa tunaninsa
” yaya mutanen nan Allah ne kadai yasan zunubin da suka aikata bayan dukiyarmu da suka cinye,kasan gaba daya fuskar kawu idris tayi baqi?,har ya mutu bai daina kiran cikinsa wuta naci a ciki ba?”
“Allah ya riga daya fada ya kuma gargademu cewa,duk wanda yake cin dukiyar maraya da zalunci haqiqa wuta yake ci a cikinsa,da sannu kuma xai shiga wutar sa’ira,zai iya yiwuwa Allah ya nuna ishararsa ne saboda sauran abokan barnarsa su kawu hamza dake raye”
“Sun girgiza ya khalipha…..kafin a dauki gawar kawu idriss saida suka warwarewa anni komai suna kuka wiwi da neman gafararta saboda yadda sukaga gawar kawu idris ta koma,ya tabbata su suka jefamu a halin talauci a baya,su suka tattare komai namu suka cinye”
“Ai ubangiji baya bacci,kuma gashinan sun gani zahiri,Allah yasa mu dace,yasa muyi kyakkyawan qarshe”
“Amin ya Allah yaya” daga haka sukayi sallama ya kashe wayar yana ajiyar zuciya,gaskiya ne Allah baya zalunci daidai da qwayar xarra,ko yaya ka zalunci musulmi ko kaci masa haqqinsa koda qwayar gero ce bakai ba aljanna saika biyashi,koda iya ladar data rage maka kenan ka shiga aljanna ba ruwan ubangiji saika biya haqqin wani daka ci.
A haka aysha ta shigo dauke da coffe sai tururi yake
“Ya khalipha…..”
“Shshshshs….” Ya fada yana katseta
“Daga yau banason wannan sunan,yanzu fa haidar ya gama cemin yaya kema ki fada,meye banbancin kenan?” Ya fada yana dage girarshi yana kallonta,wani sassanyar murmushi daya ratsa zuciyarshi ta saki tana aje coffen a gefanshi,cikin zuciyarta tana jin dadin yadda ya sake,gadon ta hau sosai ta kama hannayensa gaba daya cikin lallausan tafin hannunta tana murmushi
“Ka zabi dukkan sunan da kakeso ni kuma zan kiraka dashi ko a gaban waye” murmushin shima ya saki,yana jin dadin yadda take fifitashi fiye da kowa,take fifitashi fiye da duk abinda takeso a duniya,take zabar farincikinsa saman nata,kamo fuskarta yayi ya sumbaci goshinta cikin alfahari da ita
“Na baki zabi matata,na amince miki ki zaba min dukkan sunan daya dace da ra’ayinki” murmushi ta sakar masa tana matsa ‘yan yatsunshi
“Bazan iyakance wani suna qwaya daya da zan kiraka dashi ba,ka cancanci dukkan wani suna dake nuna qauna da soyayya your royal highness” idanu ya zaro yana jin dadj,ba shakka ta cika mace ta gari macen qwarai,wanda ma’aiki S A W yace idan ka kalleta zata faranta maka,idan ka umarceta zata yi maka biyayya,idan kayi rantsuwa zata kubutar dakai,idan kayi tafiya ko baka nan zata kare maka kanta da dukiyarta,shikam me zaya ce da ubangijinsa banda godiya?.
????????????????
Da sallama ya shigo dakin nata bayan ya bar mahaifiyarshi da qannenshi a babban falon gidan,a hankali ta sauke ajiyar zuciya bayan dogon tunanin data gama yi kana ta dago tana dubanshi,gaba daya daddy kafin rasuwarshi ya gama yi mata dabaibayi da kalamanshi kamar yana sane da abinda take shiryawa na barin gidan hamid,ya gaya mata cewa muddin babu ce zata sanyata barin aurenta indai shi ya haifeta bai yafe mata ba,matuqar mijinta na bata kulawa iyakar qarfinsa to yana umartarta ta zauna gidanta,saidai idan yazo da wata cutarwa da shafeta ko addininta,to a yanzun hamid din ya sauya,ba rashin ci babu rashin sha,duk da cewa duk wani jin dadi dada yake dashi yanzu babu,dalili kenan daya sanya yawan yawan halayensa sauyawa,saidai ita sam ya fita a kanta,kallonshi kawai take.
Da tausayinta kan fuskarshi ya zauna hannun kujerar da take kai,yanzun ya gama tsawatarwa qannenshi kan rashin kunyar da suke mata
“Kiyi haquri asma’u,na tsawatar musu kuma in sha Allahu daga yanzu hakan ba zata sake faruwa ba,kimin addu’a Allah ya sake buda min ba don halina ba,in daukeki na sauya miki gida” kallonshi kawai tayi ta miqe ta shige bedroom dinta,yayin da shima ya bita da kallo,gaba daya ta sauya tun daga mutuwar daddyn tayi wani mugun sanyi,sai ya miqe ya bita,tana zaune gefan gado,kallonshi take da mamaki don ta manta yaushe rabon da tayi masa irin hakan ya biyota
“Ki daure ki yafemin asma’u,nasan cewa harda haqqinki na takureki da nakeyi da rashin wadataki bayan ina da damar haka shi yasa Allah ya jarabceni,duk da cewa ni maison kudi ne amma takaicin yadda kika dinga tatsata,quru quru ya bayyana ba don Allah kikesona ba,hakanan ba zaki aureni ba idan ban miki barin kudi ba yasa nima ma takuraki sanda mukayi auren,ashe Allah ba ruwanshi,na sauke haqqinki kawai dake kaina shine mafitata,ki yafemin asma’u don Allah” kwanciya tayi kawai ta juya mishi baya,a zuciyarta tanason tayi yaqi da khalipha ta karbi hamid,saidai hakan na nufin su zauna a qaramar rayuwa?,to idan ma bata amshi hamid ba ya za’ayi ya samu khalipha?,mutumin data tabbatar daya tsallake baya qasar,ko baya ga haka ita kanta idan ta zauna tana tuna abubuwan da tayi mishi a rayuwa saita dinga jin nauyin abubuwan da mamakin yadda akayi ma tayi wani abun,a lokacin duniyar nayi da ita,duka a ture wannan ya zatayi da nasihar daddy,da wannan tunanin zuciyarta ta yanke mata tilas zama da hamid ya kamata,saidai tasan yadda zata lallashi kanta ta amshi tayinsa ta sabunta sonshi cikin zuciyarta,don idan ma tace batason hamid din ita kanta tasan ta yiwa kanta qarya.
????????????????
Ya jima sosai tsaye cikin kitchen din yana kallonta bata sani ba,dafa wancan dan dana kiji baiyi miki ba ki aje,ta dora abu kusan hudu dukka lokaci guda saman gas din,wanda daga qarshe ta cakuda kifn gwangwani da irish patatoes dafaffe ta zuba bama a kai shita dinga diba tana ci tana kada kai,alamun duniya tayi mata dadi,dariya ya saki tana rufe bakinshi,donshi mamaki take bashi da dariya,kwanakin nan sam bata da wani tsayayyen abincin ci sai kame kame,kusan tunda sujazo cprus haka abun yake gashi sun cinye watanni biyu
“Ba dole ki dinga qiba ba haijarsu,duba fa duka tukwanen nan hudu abincinki ne,to wanne zaki ci a ciki ne?” Ya tambayeta yana riqe haba,saitayi narai narai da ido kuma tabar cin dankalin tana dubanshi
“Bafa ni kadai zan cinye ba baby….” Idanunya zaro
“Ke dawa zakuci?,badai dani ba wannan jagwalgwalon” aifa saita saki kuka
“Innalillahi” yace uana danne dariyarshi,ta zama kaman wata baure,’yar qaramar magana zaiyi yanzu saita sakar masa kuka,mantawa ma yayi shaf da bai toneta fada ba
“Zo nan,zo kiji,haba mana tawan,ta wajen ya khaliphanta” sai yaja kujera cikin kitchen din ya zauna ya dorata saman cinyarsa
“Nifa wasa nake miki,bayan duk duniya Allah har yau banji abincin da yakai naki dadi ba da tsari baya ga na anni”
“Nifa komai naci bana jin dadinsa,bakina kamar anmin satar taste” dariya ce sosai ta taso masa dama ana satar taste?,amma yasan da yayi yanzu cibi zai zama qari,don haka sukayi dazun da safe,daga tazo saka kaya sun mata kadan yayi dariya ta zauna ta dasa mishi kuka,qarshe dai sai data jawo ya makara a makaranta bai fita akan lokaci ba
“To yanzu ya za’ayi kenan baby nima fa na damu” ya fada yana kwabe fuska can qasa dariya na cinsa,daita tsura mishu ido tana kallonsa tana son gano dariya yake mata?,ci gaba yayi da qunshe dariyarsa don yaga alama rigimar take ji sosai,har wani kalen laifi taje masa
“Dariya kake kin ko?”
“Wa?,ni na isa?,yanzu anni ta hukuntani ai,kinga zo muje kiji wani abu mai dadi,na siyo miki ma wannan abun da kika fiso”ya fada yana tashi da ita a jikinsa ya kashe dukkan gask djn suka fita a kitchen din,toulet ya jata ya hada ruwan wanka cikin bathtube,bata tsammata ba saiji tayi sun zunduma ciki ita dashi,ba yadda ta iya haka ta haqura,saida suka gama baje kolin soyayarsu sannan sukayi wanka suka fito,zuwa sannan ta ware sunata hirarrakinsu.
Ita ta tayashi ya shirya cikin boxer da longsleeve t.shirt,amma ta shurya cikin wasu ruga da skert na wadansu irin yadi mai rawa,shi ya gyara mata kanta ya matse mata cikin ribbom sannan ya sanyata ta dauko system dinta yana cewa
“Tun jiya aka turo miki email da hotuna daga shagonki anma baki duba ba,wannan wacce irin lazy M.D ce?” Tana turo baki ta dauko system din don ita ta gaji bacci bacci ma takeji,amma tayi shuru ta cije don tana fada ta samu abun tsokana wajenshi,don yace raguwa ce sosai,ba dama a gaisa saita hau bacci.
Saman gado sukayi dare dare tana lafe a jikinsa,don a duniya babu inda yakai nan yi mata dadi,ya bude naman daya siyo mata ya aje mata gabanta yace
“Gashinan” sosai taji dadi,tana masifar sonsji,cikin zumudi ta bude,yayin da shi kuma ya kunna system din tata ya soma duba saqonnin,wanda kusan duka kan kayan da suka shigo da wadanda suka fita ne,irin uwar ribar datake samu,Allah ya sanyawa wajen albarka sosai,yana cikin yi mata bayanin wasu abubuwa yaji dif bata amsawa,saiya waiwaya,ga mamakinsa bacci ne ya dauketa,ta bingire a kafadarshi,naman ma bata wani yi masa cin kirki ba,dariya ta kamashi,saidai can qasan ranshi yana mamakin meya sameta ne haka?,tunda suka zo yanayinta kenan,a hankali ya gyara mata kwanciya ya dora kanta saman cinyarshi bayan ya kwashe naman ya adana mata a kan bedside drower,ya sumbaci goshinta da tattausan lebansa yana furta
“I love you uwaisha” ya dan jima yana kallonta kafin ya dauke idanu yaci gaba da aikin shi daya,yana jin wani sonta ja wujijjigashi,har mamakin kanshi yake,bai taba son wani abu a rayuwarshi kamar haka ba,da wannan tunanin ya dinga duba komai daki dako yana baiwa mai riqe da shagon amsa,inda daga qarshe yaga dole ya cire kudinta na ribar da take daga accnt dinsa ya maida mata nata saboda yawansu,bayan an fitarwa da sauran ma’aikatan haqqinsu.
Har ya kammala tana bacci abinta,saiya zare jikinsa ya shiga kitchen da kansa ya sama musu dan abinda zasuci tunda ya fuskanci tunda ta shiga kitchen din bata iya dafa komai ba sai qwalama data yi,hakan khaliphan yake,matsayinsa bai sanyashi girman kai ba,dukkan wata hidima ta gida indai ya iya kanyiwa kanshi ko yayi mata,wani lokaci har hanashi takesonyi amma ya dakatar da ita da cewa
“Sunnah ce ta annabi salallahu alaihi wa sallam,ko bakyaso na samu kadan koyi da sunnah”
‘”Inaso mana babay”
“Good,kinsan mu mazan hausawa idan kikaji muna kumfar baki muna jawo aya da fadin zamu dabbaqa sunnah to qarin aure zamuyi” dariya ta kubuce mata yanayin yafda yayi maganar,murmushi yayi yana ci gaba da cewa
“Allah kuwa,bama tashi tuna Allah yace sai munzo qara aure,mun mance da dukkan wadan nan sunnonin masu tarin lada,wanda wani ma zaka samu a qa’ida dukkan sharudan qarin auren bai cikasu ba amma yana fadin sunna ne zai qara”
“Haka maganarka take” ta fada tana jinjina kai,tana tuna rayuwar matan karkara,ba inda aka maida qarin aure da sakin aure ba’a bakin komai ba irin a can,cikin ranta take sake yima Allah godiya,wanda koda yaushe bakinta baya shuru da gode masa walau cikin zuciyarta ko a fili,ya mata baiwa iri iri kala kala.
????????????????????
Tashinta kenan daga bacci suka kammala waya da aliya kan zancan turowa gidansu da mahmoud yakesonyi umminta ta kirata,sun jima suna hira don khalipha bai barin wayarta ba credti duk don kiran ‘yan gida,daga nan ta baiwa basma wadda suke shirin yin candy itama suka taba hira,sai shukra da sauran ‘yan mazan kafin daga bisani suyi sallama
“Baby zonan” khalipha ya fada yana aje biron hannunshi da yake wani assigment bayan ya gama nazarin ayshan tsaf,ba musu ta isa gareshi ya miqe tsaye ya kama hannunta yana dubanta
“Shirya muje asibiti ban yarda da wannan qibar taki ba,kada sakacinmu ya jawo mana asara” narkewa tayi zata sa mishi kukan nata
“Banda lafiya hubbi,nima ina jin haka a jikina”
“Don’t cray baby,shirya muje”.
Suna zuwa ba wani jira ko bin layi sukayi ba sabanin yadda qasarmu take direct suka samu ganin likita,bayan ya gama mata dukkan tambayoyi cikin qanqanin lokaci ya gama bincikensa,cikin murmushi yake shaidawa khaliphan ayshan na dauke da juna biyu na tsahon sati goma sha daya,ji yayi kamar baiji me yace ba saida ya sake maimaita masa
“Alhamdulillahil lazi bini’imatihi tatimmus salihat” ya dinga ambata,itakam aysha qamewa tayi a zaune,yau itace ke dauke da ciki?,ciki fa?,saita sanya hannunta tana shafa cikin nata kamar cikin shi zaiyi magana ya tabbatar mata da kanshi.
Kaman zaiyi kuka haka ya sanyata a gaba yana kallonta,ya rasa irin godiyar da zaiwa ubangiji,ita kanta ayshan jinta take kamar ba ita ba,wai itama zata zama uwa,zataji yanda iyaye keji,wanda daga qarshe sallahr nafila khaliphan ya tashi ya dinga jerowa,itama sai taji joining dinshi suka yi tare.
Bayan anni da ummi babu wanda suka baiwa labarin cikin,haka suka ja bakinsu suka tsuke suka ci gaba da rainon kayansu,dukkan wata kulawa bakin tana samunta daga wajen khalipha,bai barta ta nemi komai ta rasa ba,jinta yake ko ina ajikinsa,ya tabbatarwa kanshi mahadin numfashinsa ce ita.
*_bayan wata tara_*
Tsakanin anni da ummi data dawo kano da zama kowa so yake a bashi aysha ta haihu wajensa,yayin da shi kuna gogan yayi mirsisi da idanunshi yaqi dawo da ita har cikinta ya shiga watan haihuwarta,saida annin tayi masa jan ido sannan ya yarda zai kawotan,hakanan yana dacin rain ya daukota suka taho nijeria,sam shi ba haka yaso ba,so yayi annin ta barshu tunda sun kusa kammala karatun nasu idan ya gama su taho tare gaba daya koda bayan ta haihunne tace sam bai isa ba.
Ranar da zai koma din yanata kumbure kumbure ita kuwa aysha nata masa dariya da tulelen cikinta da haihuwa ko yau ko gobe,hararta yayi a wasance sannan cikin dakakkiyar muryarshi yace
“Idan baki wasa ba zan daukeki ne bada saninsu ba na koma dake”
“Allah ya baka haquri bani nakar zomon ba”kai ya gyada yana ciza lebe
“wato ke sam baki ma damu da rabuwarmu ba ko?” Kai ta kada dariyarta nason fitowa
“A’ah,ni ba haka nace ba,ba haka nake nufi ba,Allah ya baka haquri” qaramar jakarshi daya zuba muhimman abubuwanshi ya zuge
“Shikenan…..kiyita zama anan,saina samo wata na qara mu mu zauna a can” tofa,take ya tunzura mata zuciya,ta cika tayi fam,kuka takeson saki amma yaqi fitowa,saidaya gama shirinsa tsaf ya sumbaci lebanta da goshinta sannan hawaye ya subuce mata,ya gani amma ya juya ya fice abinsa,abinda ya qara tunzurata kenan ta rushe da kuka.
Tunda ya tafi take kuka tana duqunqune a daki,wani kishi da bacin rai yake cinta,tun anni bata fahimta ba har ta gane kuka take
“Tofa ni aishatu,aysha kodai ticket za’a yanko miki ki bishi ne?” Ta fada tana riqe haba,kaita girgiza da sauri hawayen da take riqewa suna saukowa
“Ko an siyo bazan bishi ba anni,yaje ya qara auren” dariya taso subuce mata saita danne,sai yanzu ta dago abinda ke faruwa,kai ta kada cikin fada tace
“Shi yace miki aure zai qara?” Kasa bata amsa tayi sai wani sabon kukan
“Zaici qaniyarshi ne nida shi ne,wannan wanne irin shashancin banza ne?,yarinya na cikin wannan halin kana gaya mata wannan maganar,to don gidansu ya qara auren mu gani,shahsasha kawai,rabu dashi ayshatu zaya zo ya sameni” anni ta fada tana dan bubbuga bayabta,don ta fuskanci harda tension da pressure ta masu tsahon ciki,haka ta dinga lallashinta sadata tabbatar tabar kukan sannan ta bar dakin.
Tsaye yake cikin falon yaja tsaki yafi cikin carbi,komai baya masa dadi gaba daya,abu na farko hawayen aysha da yake gani wanda shine abu na farko daya hanashi sukuni,abu na biyu kuma tashin hankalin rashin jin muryarta,tunda yadawo ya kasa zaune ya kasa tsaye sai daya kirata amma wayar harta qari burarunta ba’a dagawa,abinda bai sani ba anni ce ta amsa zata tayata horashi,abu na uku rashin ayshan a gidan,sai yaji gaba daya qasar ta fice masa aka,ji yake tamkar yana kan qaya ne,sam ko dawowa gidan baya sonyi saboda idan ya dawo din sai ya rasa abinda zaiyi.
Da wannan tunanin ya samu da qyar ya kurbi tea wayarsa na hannunsa yana ci gaba da gwada lambar ayshan saidai koda ta shiga ma ba’a amsawa.
Daga bangaren aysha kuwa basu jima da gama waya da ummi ba ta wayar anni taji mararta da bayanta sun soma riqewa da ciwo kadan kadan,saita zaci fitsari ne ya cika mata mara,hakan ya sanya ta shiga bandaki don tayi,saidai fitsarin duka ba wani mai yawa bane tayi ta dawo ta sake kwanciya,a hankali ciwon ya soma qara yawa,tun tana daukarshi kadan har ya soma matsa mata ta miqe ta fara safa da marwa,daidai lokacin da baba atika ta shigo dakin,donko anni bata shigo da kanta ba zata turo baba atikan,bata taba bari tayi minti talatin ba’a dubota ba
“A’ah uwar masu gida kardai abunne ya taso?”
“Wallahi ban sani ba baba atika,marata ce ke ciwo kamar zata tsage” ta fada tana yarfe hannunta
“A’ah,bari na sanar da hajiya” baba atika ta fita da hanzari don shaidawa anni,saidai kafin a gyara mota a fito da kayan haihuwa ciwo ya kankama tafiya ba zata yiwu a wajen aysha ba,tilas aka haqura anni tabar baba atika a dakin,don sam kunyar annin ta hana ayshan ta sake sosai dole ta fita ta barsu a dakin,saidai bata matsa ko nan da can ba tana tsaye qofar dakin baba atikan na yu qurin ganin ta qarfafi ayshan ta tashi su qarasa asibiti,nishin data soma shi ya tabbatarwa baba atika haihuwa tazo,ta gyara wa ayshan zamanta tana qarfafarta tayi nishin don babyn ya samu ya fito,cikin ikon Allah nishi uku kacal kukan jaririyar ya karade gidan
“Alhamdulillahi” anni ta furta murmushi mai hade da qwalla da na bayyana a fuskarta.
Dai dai sanda khaliphan ya saki nannuyan ajiyar zuciya yana sake gyara zamanshi,tsahon daren duka bacci yaqi zuwa idanunshi hakanan,so yake kota halin qaqa yau yaji muryan uwaishanshi,yasha attempting din kiran anni amma baiso ta gane laifi ya yiwa aysha taqi daga wayarshi,ayau kam yana jin an kai matakin da dole ya kira annin,idan ma fada zata yi mishi tayi masa indai zata hadashi da aysha yaji muryarta da lafiyarta,sai kawai ya danna lambar annin yasa handsfree ya ajeta a gefe yana jiran yaji an amsa.
Kukan babyn daya cika kunnenshi a sanda aka daga wayar shi ya sanyashi tashi tsaye cak kamar wanda aka yiwa allurar sojoji
“Allaaaaaahu akhbar” ya ambata,ko ba’ace masa komai ba,ko ba’a gaya masa ba yasan cewa tabbas wannan jininsa ce,diyarshi ko diyanshi ne yau ya shaqi iskar duniya
“Khalipha,yau Allah ya albarkace da samun diya mace”
“Alhamdulillah,Alhamdulillah anni hajar ta dawo”
“Ma sha Allah” ta fada tana jin dadi har cikin ranta,tana jin kewar diyarta da tuna mutuwarta
“Anni ya humaira take?”
“Tana lpy atika tana shiryata”
“Alhmdulillahi ya dinga maimaitawa sai anni ce ta kashe wayar,kasa zaune yayi ya kasa tsaye,cikin lokaci kadan ya soma turawa ‘yan uwa da abokan arixiqi cewa ya samu qaruwa,nan da nan saqonni suka dinga shigo masa ta ko ina,duk yadda yaso jin muryar ayshan anni taqi hadasu tace saita huta,kamar zaiyi hauka,har kusan kuka ya yiwa annin amma ta shareshi.
Sanda anni ta shiga dakin an gama shirya baby da mamanta tsaf,tuni babyn ta shiga bacci,bismillah anni tayi ta dauketa idanunta kan kyakkyawar fuskar yarinyar,khalipha sak haka ta gani,kamar sanda ta haifeshi,komai nata irin nashi ne hatta da yatsun qafafunta,
“ma sha Allah,Alhamdulillahi”Qaunar yarinyar ta ratsata lokaci guda,fuskarta qunshe da murmushi ta dubi aysha dake zaune tana shan tea mai zafi
“Sannu indo aysha”a kunyace ta amsa ma annin
“Allah ya albarkaceta,ya qareku da lafiya,ubangiji yasa cikon musulunci ce”
“Amin” ta furta can qasa yadda annin ba zata ji ba,saboda kara da kunya,
“Ki huta zuwa anjima sai muje asibiti a dubaki da kyau a tabbatar komai lafiya ko?,sai……” Bata kai aya ba kiran khalipha ya shigo wayarta,wannan shine kusan kira na bakwai da ya yiwa annin
“Ungo,karbi mijin nan naki,na tabbatar idan ba bakin nayi ba bazai taba qyaleni na huta ba” ta fada ta ajje mata wayar gefanta,sannan ta dora babyn kusa da ita ta fice a dakin tana kiran baba atika.
Tana kallo sai daya kira kusan sau uku sannan ta daga,kiran sunanta ya fara yi sai tayi fakare dashi kaman bata jiba
“Nasan kina jina uwaisha,na godr,amman don Allah kowanne hukunci zakimin kimin amma banda hanani jin muryarki naji lafiyarki” har ga Allah har a sannan ranta adan bace yake dashi,baisan yadda take kishinsa bane shi yasa ya gaya mata haka
“Me kakeson nace?,kai da zaka auro amarya tunda ni na haihu na tsufa?”
“Wayyo uwaisha don Allah karki sa na kasa bacci yau…..am sorry uwaisha bana son abinda zai sa mu raba muhalli dake uwaisha….yanzun haka wallahi bazan iya zama ba dole na sake biyo jirgi nazo na ganku keda baby na” idanunta ta lumshe,har abada tana alfahari da soyayyar da yake mata
“Ya jikin naki ina baby na dawa tayi kama?” Ya furta cikin sanyin murya dake nuna zumudi zallah
“Dani tayi kama” dariya ya qyalqyale da ita cike da nishadi
“An gaya miki ni rago ne?,to na sani nita debo komai da komai,kina kishi ne ko?” Saita tura baki kamar yana ganinta
“Nida wahala kai da kwashe kamannin” dariya ya kuma yi sosai wanda hakan ya sanya nishadi a zuciyarshi
“Tukunna ma,duka sauran wadanda zasu biyo baya ki zuba ido zaki gani”,tun tana sharewa har ta saki jiki sosai,kafin suyi sallama sai daya wanke kanshi fes da soso da sabulu.
Zuwan aliya shiya katse musu hirar dole ba don sun gaji ba,aliya murna kamar tayi me
“ke bamusan kin dawo ba sai labarin haihuwa muka ji”
“Hmmm,kedai bari aliya,kwana ma biyu fa da dawowa,Allah nema yayi bazan haihu ba a can” tare suka zauna da ayshan,ranar haka baqi suka dinga tittudowa,toh abinka da idan kana dashi anayi dakai kowa burinsa yazo yaga jaririya,wasu soyayya ta domin Allah wasu ta abun hannun iyayenta,a ranar ummi ma bata iya kara ba sai datazo da dukka yaranta,basma ta qanqame babyn tana cewa itakam anan zata zauna sai anyi suna,ranar anni da ummi sunsha hira sosai,yawan baqin ya sanya basu samu damar zuwa asibitin bama sai dare,alhmdlh komai lafiya ita da babyn,sai magunguna kawai da suka rubuta mata don qarin lafiyarta,suka siya suka dawo gida.
Washe gari saiga hanan da mmn hunaifa,ranar kam an sha hira sosai,sunyi missing aysha,karatu yanata gangarawa
“Ai dama na fada wallahi,irinku su aysha sumumu kasau din nan baku iya soyayya ba,sai gashi ke data tashi damqarki ma karatun kika aje gaba daya” hanan ta fada tana hararar aysha cikin wasa,dariya aka sanya gaba daya,mmn hunaifa tace
“Ni banga laifinta ba,nima don bbn hunaifa keso,da zaice nima na aje jewar zanyi”.
Da azahar saiga mummy abun mamaki harda asma’u,duban tausayi aysha take musu su duka,don duk wanda ya kallesu yasan rayuwa bata gara musu kamar da,duk sai ayshan taji ta tsargu,kaman ta zubda su duk da cewa basa sati basuyi waya da mummyn ba,ran aysha saiya koma duka a bace,har suka gama yi mata barka suka tafi,asma’u tace sai ranar suna mummy kuma tace sai gobe zata dawo.
Kafin washegarin ta sanya daya dags cikin yaran khalipha ya mata bincike kan halin da ake ciki,rashin tattali ya sanya sun sanya su mummy sun sanya gadonsu a gaba sun cinye sai d’an abinda ba’a rasa ba,sai kuma abinda su anty safiyya ke taimakawa mummyn dashi,asma’u kam nata juyawa take,dashi suke kashe buqatun kansu ita da hamid din,don a yanxu ya koma ya zauna,bashi da wata qaqqwarar sana’a,da kanta ta cira kudi cikin accnt dinta wanda ita kanta tasan ba qaramin kudade bane a ciki tayi musu siyayya,don khalipha ko riba ya samu mai yawa a wani harkan saiya fitar mata da wani abun,dukkan wani abu da tasan sun rasa saida aysha ta tabbatar sun sameshi,hakanan ta qarawa asma’un jari yadda zata riqe kanta sosai,kunya ta kama asma’un har taso taqi amsa amma ayshan ta turje
“Ni kamar ‘yar uwa na daukeki anty asma’u,qin karbarki bashi ne zaimin dadi ba” hawaye ta dinga sharewa tana kada kai
“Ban cancanci naci arziqinki ba ko wanne iri aysha,bansan ma ta yaya zance ki yafemin ba”murmushi aysha tayi saboda dama tasan abinda ke cinta kenan
“Karki taba sawa a ranki kinmin komai,koma me kike tunani yanzu ina yake anty asma’u,koma meye ya zamemin silar alkhairi,ya zamemin silar haduwa da mijin da samun kamarshi sai an tona,na yafemiki kome kika yimin duniya da lahira” hakanan ta amsa tana mata godiya gami da jin kunyar kanta kan dukkan wani abu data aikata,bata taba zatan cewa a rayuwa wataran wanda kake samanshi zai iya zamowa shine a samanka kai a qasanshi,koda yaushe ka zama mai kyautata mu’amalarka saboda babu wani abu dawwamamme.
Ba zato saiga khalipha ya sauka ranar suna da yammaci,yazo ganin little hajar,wanda ake kira da farha,aysha na cikin jama’a amma sai daya sanya aka kira mishi ita,hadasu yayi duka ya rungume ita da baby farha yana ajiyar zuciya,sai daya dauki a qalla mintuna biyu a haka sannan ya saki ajiyar zuciya yana dagata daga jikinsa yana fadin
“Alhmdlh,Alhmdlh” yana kissing dinta a goshi,murmushi ta sakar masa tana masa sannu da zuwa,a qalla saida ta kusan kashe awa biyu a wajensu yana kallonta kawai baby farha na wajensa,ga jama’a daketa tururuwar zuwa suna anata nemanta,da qyar da sudin goshi ya barta ta fito bayan anni tasa baki,tare da alqawarin gobr xasu wuce gidansu.
Taro ya tashi lafiya baby hajar farha tazo da goshi da alkhairi mai tarin yawa,washegari da magariba ta shirya tsaf ita da farha suna zuba qamshi suka wuce gidansu,suka bar anni da yasmin ‘yar anty ruqayya da aka kawo mata.
Baby farha nada wata biyu yace zasu koma ya kammala jarrabawarsa,da fari anni taso yabarsu a gida yaje yayi ya dawo,amma daga bisani ya gaya mata akwai yiwuwar zamanshi a can hakanan suka tarkata suka tafi kowa na kewat baby farha,sun zagaya sallama har takai,zuwa wannan lokacin inna yelwa ta sake sanyi qwarai,ta tabbatar jahilci ya taka muhimmiyar rawa wajen faruwar dukkan abinda ya faru,khalipha bai tafi ba sai daya assasa islamiyya can garin ta matan aure da yara,wanda ya dauko ingantattun malamai masana sunnar Allah da ma’aiki suka hau koyar da al’ummar garin ka’in da na’in,suka yi nasarar yaqar duk wani baqin tunani,da baqar alaqa da dangantaka dake tsakanin fulani da manoma,basu bar qasar ba sai da aka sanya ranar aliya da mahmoud,wanda ya matsa qwarai yana ganin kamar zai rasa aliyar ne ko kuma taqi bashi dama.
Ta bangaren haidar ma tunda yaga basma ya soma kai kawo,wanda daga qarshe ya bayyana muradinsa,ayshan dai batasan ya ake ciki ba har suka bar nigeria zuwa cyprus.
Randa zasu tashin suna tsaka da shiri aka ce ana sallama dashi,hakanan ya fito bai kammala shiryawa ba don yayi mamakin wanda ke nemansa a irin wannan lokacin ya fito zuwa falon da yake ganawa da baqinsa.
Kawu hamza,kawu munzali,kawu habibu da kawu saminu,dukkansu suna zaune qasan tile din dake malale a dakin,suna zaune tsumu tsumu kamar wadanda aka tsoma kaza cikin ruwa,kallo daya zaka yi musu kasan cewa dukkaninsu suna jin jiki na rayuwa dana abinda suka aikata.
Dubansu yake yayin da kowa ya gyara zama yana miqo gaisuwa,amsa musu yayi kadaran kadaham kafin shuru ya biyo baya an rasa wanda zai soma magana a cikinsu,kawu saminu ne yayu qarfin halin soma neman musu yafiyar khalipha,don dukkansu mutuwar idris ta zame musu izinina,daga qarshe ya rufe
“Haqiqa shaidan ya taka muhimmiyar rawa wajen yi mana huduba,da banzayen zukatanmu marasa son Allah,muka bijire muka kwashe dokiyoyinku muka cinye,sannan uwa uba muka kasa kula daku muka yiwa mahaifinku butulci,mutuwar idris kawai ta isa ta nuna mana makomarku matuqar baka yafe mana ba kuma bamu nemi yafiyar Allah ba,iya halin da muke ciki ma yanzu kawai munga ishara babba,bamu da nutsuwa cikin gidajenmu da rayuwarmu,yaranmu duka kowanne da tashi matsalar Allah ya jarrabemu,ka daure badonmu ba badon halinmu ba ka yafe mana”
Iska mai zafi ya furzar da ita daga bakinsa yana qoqarin controlling kanshi,tsahon mintuna biyar shuru ya ratsa falon
“Allah ya yafe mana gaba daya” dukkansu qwalla suke sharewa suna godiya,yana tsaye yana kallonsu har suka gama ficewa daga falon sannan ya juya ya koma ciki,zuciyarshi cike fal da tunani kala kala,rayuwa ita haka take,dukkan yadda ka dauketa haka take zuwa maka,mafitarka daya kabi Allah kabi dukkan dokokinsa.
*mrs muhammad ce*??
Post a Comment for "Daurin Boye 59"