Daurin Boye 58
58
Wani jiri taji yana niyyar kayar da ita sanda taga tarin al’umma da rumfuna tun daga qofar gidan daddy zuwa cikin harabar gidan dake a wangale,kusan tunda tazo gidan ta gama rayuwarta ciki bata taba ganin an wangale qofar gidan irin haka ba
“Ya khalipha?,me yake faruwa?,me ake haka a gidan?” Ta tambayeshi cike da tsoron amsar da zata fito daga bakinsa
“Kinga saukarmu kenan nace bari na kawoki kiga jikinsa don hankalinki yafi kwanciya,wataqila maqota ke wani sha’anin koma daurin aure ake ne,amma kinsan me za’ayi?,shiga ciki ina nan ina jiranki idan kun gaisa saiki fito mu tafi”
“To” tace tana fitowa bayan ya bude mata murfin motar da kanshi,haka kawai ta dinga jin kamar zata fadi qafafunta sunyi laushi kamar ba’a jikinta ba haka ta dinga takawa har cikin gidan.
Anni ta soma cin karo da ita,mamaki dukka saiya kamata,meya kawo anni gidan to me akeyi?,ko dama ta sansu?
“Allah ya jiqan alhj,ba shakka anyi babban rashin da aka jima ba’ayi irinsa ba” kunnenta ya dauko mata muryar wani daga can wata rumfa dake bayanta da yazo gaisuwa,bata gama wannan ba ta dinga jiyo ihun asma’u tana kiran sunan daddy,da hanzari ta taka don shiga tabi ba’asin meke faruwa sai taji gangar jikinta ta kasa daukarta,ji tayi tana sulalewa zuwa qasa,daga haka bata sake sanin abinda ke faruwa ba.
Sanda ta farka dakin ta dinga bi da kallo sai daga bisani ta gane a asibiti take,a hankali abinda ya faru ya dawo mata kanta,saita fashe da kuka tana fadin
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” a hankali wanda hakan shi ya fargar da khalipha dake saman abun sallah cewar ta farka,gaba daya hankalinshi a tashe yake cikin hanzari ya isa gabanta anni dake zaune can kan kujera ta taso itama,ta dakatar da khalipha dake shirin dagata ta zauna,saiya fasa ya tsaya saitin kanta yana shafa sumar kanta a hankali yana tayata fadin innalillahin,har tsahon wani lokaci bai hanata kuka ba hakanan basu fasa maimaita innalillahin ba tare dashi,daga bisani ne ta saki ajiyar zuciya tana cewa
“Da gaske ya khalipha daddy ya mutu?,dama sallama jiya mukayi dashi kenan a waya?” Ganin shima ba wani a nutse yake can ba saboda yanayin da ayshan ke ciki ya sanya anni matsowa
“Allahn daya haliccemu shi ya fimu sonshi,ya kuma fimu sanin dalilin daya sanya ya dauke abinshi,kada mu yiwa Allah daya bamu shi butulci”
Kai kawai take gyadawa tana ci gaba da ambaton sunan Allah,wanda shi ya dafa mata ta samu nutsuwa,sai da anni ta tabbatar ta nutsu sannan ta taimaka mata ta tashi ta zauna,khalipha ya sanya daya daga cikin yaranshi suka yiwa likitar magana,macace likitan dalili kenan ma daya sanya khaliphan ya kawota wannan asibitin,ta tabbatar mishi komai ya koma normal,saidai ta kiyaye damuwa da bacin rai ta rubuta sallama.
Gidan anni suka wuce kai tsaye tayi wanka,saidai har a sannan hankalinta bai jikinta,ta matsa sai an kaita can gidan makokin,haka khalipha ya dauketa ya kaita.
Karon farko data sake sallamawa Allah lamuranta ta tabbatar lallai mutum koshi waye ba’a bakin komai yake ba,kwana daya tak mummy da asma’u sunfi kowa fita hayyacinsu,tausayin kanta da tausayinsu ya kamata,kuka ta dinga sosai ta manta da duk wani sharadi na likita,anty safiyyace kawai mai qarfin halin lallashinsu,ranar mummy ce ke cewa aysha ta yafe mata,saboda gabanta ita da asma’u daddy ya rasu,sun tsorata matuqa da yadda mutuwa take,fitar rai ba wasa bane,kowanne dan adam lallai saiya taba yaji a jikinsa,saidai fata Allah yasa mu dace.
A nan khalipha yake barinta,kullum sai dare yake zuwa ya dauketa su koma gida,har a sannan aysha bata daina kukan rasuwar daddy ba,saidai tanayi a boye yadda khalipha bazai gani ba hankalinsa ya tashi,don dukkan wani qoqari nasa yana yi don ganin ta sake,saidai ita kanta batasan ma meke damunta ba,hatta da taste din bakinta ya sauya tun daga randa akayi mutuwar.
Ranar sadakar uku su inna yelwa suka zo,tunda sukazo aysha ta lura da ta sauya gaba daya,sai da ana hira takejin bata da cikakkiyar lafiya kwana biyu,yau da lafiya gobe babu,ba’ayi azahar ba umminta ta iso itama ita dasu basma,don ita kanta mutuwar ta daketa,taso qwarai ace Allah ya hada ganawarsu da mutumin daya ceci rayuwar ‘yarta,taso sosai tayi masa godiya koda sau daya ne a rayuwarta amma Allah bai nufa ba.
Shuru dakin da suke zaune ya dauka gaba daya,baka jiyo komai sai muryar wata baiwar Allah dake harabar gidan tana wa’azi kan mutuwa,tun daga sanda mala’ikan mutuwa dubi bawa,zarar rai,wankan gawa kwanciyar kabari da yadda mala’iku kebi suna jin yadda jama’a ke fadar halayyar mamaci,da yadda hakan yake tasiri a kansa da sauransu,sosai jikin inna yelwa ya sake laqwas,tunda tazo gidan bata ji mutum daya daya fadi mummunan hali akan daddy ba,yau ga inna yelwa ga ummi,abinda ya dauki tsahon shekaru rabon daya faru,sai inna yelwa ta kasa sakewa gaba daya,sai satar kallon ummi take,ba dadewa fa fashe da kuka,ita kadai tasan me take ji a lokacin,ba abinda take tunawa sai abinda ta aiwatar a rayuwarta a baya,yanzu idan mala’ikan daukar rai ya cimmata fa?,tabbas tasan kadanne masu fadin alkhairi a kanta,idon kowa sai yayi kanta,Allah yasa dukka ‘yan takai ne da wadanda suka jibanci aysha,anzo mata sosai saboda yanzun kowa neman fada yake da ita
“Don girman Allah ki yafemin naja’atu,wallahi na cuci kaina na cuci rayuwarki keda diyarki” abinda inna yelwa ta dinga fada kenan tana zabga kuka da majina,tsit dakin yayi,yayin da ummi tayi shuru tana hadiyar wani abu mai tauri,zuciyarta quna kawai take tana yunqurin danneta da cika alqawarin data dauka a gaban dakin Allah.
Inna yelwa ta jima gaban ummi tana kuka gami da gaya mata ita ta rabata da baffale,ita ta shiga tsakaninsu,lumshe idanu ummi kawai tayi,zuciyarta nason tuna mata irin abubuwan da inna yelwan tayi mataba rayuwa,yayin da daya sashen na zuciyarta ke tunasar da ita ni’ima baiwa da kuma musanyan alkhairi da Allah yayi mata ayanzu
“Na yafe miki” kalmar data baiwa inna yelwan mamaki,don bata taba tsammatar haka daga wajen ummin da sauqi ba,hakan ya sake karya mata zuciya,nadama ta shigeta sosai,tana son kallon aysha dake zaune waje daya tana jan carbi tace ta yafe mata amma tana jin kunyarta da nauyinta,tana jin idan tace ta yafe matan tamkar ta zama mai son kai ne,amma ita kadai tasan yadda akwanakin take yawan mafarkin baffale,yana kuka yana ta cuci su aysha,ta gaggauta hada tsakaninsu,ta gaggauta neman afiya da yafiyarsu,ta raba uwa da ‘ya,saidai kuma cikin kyakkyawan yanayi take ganinshi,saidai kukan kawai da yake mata,babu randa zata kwanta bacci ta tashi batayi mafarkinsa ba,abun ya takurata qwarai,kusan shi ya haifar mata da lalurar da take fama da ita a yanzu.
“Nasan ban cancanci ki yafemin ba indo,amma na gamaki da Allah duk sanda kike jin kin huce na cancanci yafiya toki yafemin” ta fada tana fashewa da kuka,kai aysha ta kada kawai,itakam me zata cewa Allah banda godiya,komai aduniya da zai samu bawa koya sameshi yana damfare da yanayin rayuwarshi na baya,ba don qalubalen data fuskanta ba da babu lallai daddy ya daukota ya kawota nan,da bai kawota din ba da babu lallai asma’u ta hadata da khalipha,duk da yakedai duk inda bawa yake rabonsa baya kubuce masa
“Na yafemiki,Allah ya yafe mana gaba daya” kusan wannan shi ya kawo daidaito tsakanin gabar inna yelwa da ummi naja’atu.
Qarfe hudu da minti ashirin na yammaci yasa aka kira mishi ayshan,can wani waje da babu kowa cikin gidan suka zauna saman darduma,ya tsareta da idanunshi bayan ya aje abinci a tsakiyarsu,saita zuba mishi ido itama sonshi da qaunarshi na sake karyar mata da zuciya,hawaye ya cika idanunta,haka kawai take jin wani abu ya cunkushe mata wuya wanda shike hanata cin abinci
“Oya,bude bakin” ya fada bayan ya debo abincin a cokali yakai bakinta,sai kawai ta sake masa kuka mara sauti sai sheshsheqa
“Ya salam” ya fada yana aje cokalin cikin damuwa,ya rasa me yasa har yau zuciyarta taqi saki,a yanzun kuka baiyi mata wani wuya,yanzu yanzu ne zata saki abinta,bai manta ba jiya suna kici kicin tahowa zai kawota,zata sanya wata riga taqi shigarta tayi mata kadan,sai zuwa yayi ya sameta a zaune dirshan tana sharbar kuka abinta,daga lallashi nan ma cibi ya zama qari,hannunshi ya miqa mata batayi wata wata ba ta taho,cikin jikinsa ya sanyata tana shafar bayanta a hankali
“Uwaisha ba zaki sanya haquri cikin zuciyarki ba ehmm?,bakisan yadda zuciyata ke quna ba a duk sa’in dana ganki cikin damuwa?,so kike wani abu nima ya sameni?” Saita fashe da kuka tana girgiza kai tana fadin a’ah
“Ya Allahu…..kin zama makokiya gaba daya?” Ya fada yana share mata hawayen dake sauko mata
“Na daina….” Ta fada cikin muryar kuka,murmushi kawai ya saki yana ci gaba da riqeta cikin jikinsa,bai barta ba sai daya tabbatar taci abinci ta kuma sake sannan ya qyaleta.
Kwana goma da rasuwar da wani dare tana zaune gaban anni suna hira,tun dazu khalipha ke kaiwa da kawowa tsakanin sashen annin zuwa nasu,ya gaji yakai maqura yau haqurinshi ya qare,so yake ya dauki matarshi kawai su wuce gidansu amma ayshan tayi qememe kamar ma bata gane me yake nufi,sake miqewa yayi ya nufi sashen cikin qwarin agwiwa.
A nutse ya tura qofar yayi sallama,cikin sa’a ayshan ce kadai zaune tana shan fruit salad na musamman da aka zuba mishi zuma da madara,wanda a fakaice anni ta hada mata shi saboda qarin ni’imar jikinta,ita kuwa tunda ta d’an d’ana taji yayi mata shikenan ta samu abinyi,idonta ta daga ta kalleshi sanda shima yake dubanta bayan ya kalli bowl din gabanta mai dauke da fruit salad din,murmushi ta saki tana nuna mishi kwanon
“Ya khalipha bismillah” harara ya dan watsa mata qasa qasa yadda anni ba zata ji ba yace
“Bana sha…ki tashi ki shirya mu wuce gida” saita langwabe kai,tana jin dadin zamanta da anni sosai
“Ya khalipha ka bar…..” Sai ya dora yatsanshi akan lips
“Shshshshsh…..bana son jin komai ki tashi kawai”
“Yaya dai khalipha?” Anni dake fitowa daga toilet ta ambata tana dubanshi,sai ya dan sosa kanshi kadan yana cewa
“Babu komai anni” juyawa yayi ya sake jaddadawa aysha maganar da ido sannan ya juya zai fice
“Zo nan” anni tace dashi tana qoqarin zama,dawowa yayi
“Ka kora min yara shine zaka wuce kubarmin gida ni daya kenan ko?” Ta fada tana dubanshi,sai yayu shuru yana shafa kanshi
“Zauna” ta nuna mishi waje,zaman yayi yana kaucema kallon annin
“Duk inda musulmi yake ana son ya zama mai manta sharri,mara manta alkhairi,anason idan mutum ya maka sharri kai ka saka masa da alkhairi,a sanda duk Allah ya maka sauyin yanayi na alkhairi ganin damarshi ne,sanda Allah yayi maka arziqi ka wadata mabuqata,sabida wannan arziqin ba kai kadai ya bawa ba ya baka ne harda su,sai ya sanyashi a hannunka,babu abinda zai rageka dashi donka kyautatawa wanda ya zalunceka,sai qarin daukaka da zaka samu wajen ubangiji,na yaba maka sosai da yadda kayi haquri kuma kabi maganata,ka dauki ragamar kyautata musu kamar yadda mahaifinka yayi kafin yabar duniya duk da nasan tanqwara zuciyarka kawai kake,a yanzu bazan sake takuraka kan zamansu amal cikin gidan nan ba,don na tabbatar gudun faruwar matsala yasa kayi haka,nima kuma daga bisani na hangi hakan,zuwa yanzu dama yaci ace kowacce ta maida hankalinta jikinta ta fitar da mijin aure tunda gaba dayansu sun kai munzali”
“Hakane anni,kiyi haquri idan kinji babu dadi…yanzu haka mun gama magana da mijin anty ruqayya zai baki nadiya ‘yarsa in sha Allahu taci gaba da zama dake,saboda ina tunanin….” Sai kuma ya kasa qarasawa ya soma shafa qeya,tasan yana jin nauyin abinda zai fada mata ne,saita saki murmushi
“Uhmmm”
“Cyprus zamu wuce nida humaira” har qasan zuciyar anni farinciki ne ya lullubeta,abinda take zato ya tabbata,tun ranar farko data gansu taga burbushin haka,dukkan alamu sun suna akwai wata dangantaka mai qarfi atsakaninsu,akwai wani lamari mai girma daya yiwa junansu dabaibayi,amma donson ta sake tabbatarwa sai tace
“Wani irin cyprus?,nata karatun fa?,ba inda zaka daukemin diya ka kaita”
“Wallahi anni bazan iya tafiya na barta ba don Allah karkice na tafi na barta,in kika ce haka kona tafi bazan iya qarasa nawa karatun ba kuma nawa yafi nata muhimmamci….”yayi subutar bakin fadan wadannan kalmomin ba tare daya shirya fadarsu ba
“Dakata…” Tayi hanzarin tsaidashi karya ballo maganar data fi haka nauyi
“Saikun dawo Allah ya kiyaye hanya,ke ayshatu tashi maza ku wuce gidanku nima nan kwanciya zanyi,idan kun fita ku turomin mus’ab ko atika” sai a sannan ya tuna abinda yace mata,kunya duka ta kamashi,amma da yake namiji ne saiya murje ya shigar da godiyarsa,don kada ma ayshan ta bata masa lokaci sai ya tsaya yana jiran ta gama laqai laqai dinta ta tashi,haka ta gama din kuwa ta yiwa anni sallama suka fice.
Tun a gidan annin dama takejin son tayi kuka,wani abu ya takoreta a wuya,tun a can take toshe kukan,suna shiga falon gidansu ta kasa haquri kawai saita saki kukan,juyawa kawai khalipha yayi yana kallonta baki sake,kamar wadda akayiwa wahayin kuka?,bai wani bata bakinsa ba wajen lallashi kawai ya sunkuci abarsa,bai direta ko ina ba sai dakin bacci,sai daya gama budurinsa ya biya dukkan bashin dake kansa sannan ya soma aikin lallashi,nan ta narke masa itama ta zuba shagwabarta son ranta shi kuma ya biye mata,sai daya sha rarrashi sannan ya samu kanta suka shiga wanka tare,wanda kusan al’adarshi ce haka,saboda koyi da fiyayyen halitta annabi muhammad S A W.
Bayan kwana biyu akayi bikin bude katafaren shagon nata,wanda walima tayi dai dai gwargwado,donta rage wani abunma saboda mutuwar daddy amma tayi walima sosai anci an sha anyi sadaka.
Kwanaki bakwai suka qara a nigeria suka shirya don komawa cyprus ita dashi,ana washegari zasu koma taje gidan daddy donta qara ganin mummy.
Ba qaramin tausayi mummyn ta bata ba yadda ta rame tayi baqi ta zabge lokaci guda kamar ba ita ba,ba qaramin duka mutuwar daddy tayi mata ba,fuskarta a sake ta amshi ayshan har hakan ya bata mamaki,don bata tsammaci haka daga gareta ba
“Allah ya kiyaye hanya yasa aje a sa’a” mummyn ta fada cikin sanyin jiki,abinda bai taba hadata da mummyn ba,jakarta ta bude ta ciro kudi dubu dari da khalipha ya bata ta basu ta miqawa mummyn,kai ta girgiza
“Bazan iya karbar komai naki ba ayshah,na gode”
“Idan kika ce haka nima baki daukeni kaman asma’u ba kenan?” Kai ta kada hawaye na cika idanunta ta amsa
“Allah yayi miki albarka,ki yafemin aysha dukkan wata cutarwa dana taba yi miki a rayuwa,shaidan ya rufe idanuna,a sanda kike kyautata min idanuna sun rufe,bana ganin dukkan wani alkhairi naki,duk yadda kika kai ga kyautata mana bamu qareki da komai ba face sharri da makirci da muke bibiyarki dashi,mutuwar daddy babbar izina ce a wajena,tabbas dan adam ba’a bakin komai yake ba”
“Ban taba riqonki ba mummy dai dai da rana daya,na yafemiki mummy,Allah ya yafe mana gaba daya” da haka ta fito daga gidan jikinta a sanyaye,daga nan gidan anty safiyya ya kaita,sosai tayi murna da zuwan ayshan,ta dan jima zaune suna hira da ita,sannan ta gaya mata zancan tafiyarsu gobe,sosai ta mata fatan alkhairi
“Nikam kaman qiba naga kin soma aysha,karfa ki zama bindiga?” Murmushi ta saki
“Haba anty,nida na rasa uba wacce qiba zanyi?”murmushi anty safiyya tayi,har cikin zuciyarta tana jin dadin dace da aysha tayi
” ba daga nan take ba aysha,shi ciwon mutuwa Allah yake daukewa bawa shi,banda haka da mutane da dama sun hallaka saboda ciwon rasuwar makusantansu,kekam kinyi haquri a rayuwarki wanda ya zamemiki alkhairi”sai tayi shuru tana aje numfashi,ta gefe guda tana jin tausayin asma’u,tana jin ciwon rayuwar da take ciki,saidai bata karanci komai na nadamarta ko rashin nadamarta ba
“Ki daure ki yafewa asma’u koda bata nemi yafiyarki ba,ki kuma sanyata a addu’a”
“Ni babu komai tsakanina da ita anty,kusan zan iya cewa itace silar matakin dana ke kai yanzu”
“Batayi don alkhairi ya sameki ba,amma dai ki daure ki yafe mata”
“Nikam na yafe mata duniya da lahira” saida khalipha ya kirata sannan ta fito suka tafi.
Suna shirin kwanciya bacci saiga kiran anni ya shigo wayar ayshan,a ladabce cikin kulawa suka gaisa
“Bani khaliphan aysha na kira lambarsa a kashe”
“Toh anni” ta fada tana miqa masa dai dai sanda yake fitowa daga wanka,amsar wayar yayi da daya hannun nashi dayan kuma ya janyota cikin jikinshi ya rungumeta,runtse idanu tayi sanda fatar jikinta ta hadu da tashi,lemar ruwan dake gashin qirjinsa ta ratsa towel din jikinta zuwa fatarta,suna tsaye a haka suka gama gaisawa da annin
“Idris ne fa ba lafiya”idanunsa ya dan lumshe,ko sunanshi baison ji
“wanne idris”
“Gidanku,idris kawunka mana,bashi da lafiya sosai yana jin jiki,lafiya akwa kwanta dashi sai ihunshi aka ji,yanzu haka yana asibi an kwantar dashi,kayi qoqari gobe kafin ku wuce kuje ku dubashi”
“Zanje in sha Allahu”
“Yauwa saida safe”
“Allah ya bamu alkhairi” ya kashe wayar yana sake jan ayshan cikin jikinsa yana sauke ajiyar zuciya,dukkaninsu shuru sukayi,tasan yanzun zaya shiga damuwa daga ambato masa sunan idris,daga bisani ayshan ta juyo da wani irin hanzari ta rungumeshi sosai tana cusa kanta cikin qirjinsa,da qafa daya ta janyo tum tum din dake gefansu ta haye sannan ta samu tsahonsu yazo daya,saita riqe kanshi sosai ta hada hancinsa da nata,bakinta tasa tadan ciji lebansa kadan saiya saki qara
“Wayyo bakina anni zata cinye miki bakin yaro” dariya ta qyalqyale da ita tana daneshi
“Kasan kaci bashina jiya,kuma saika biya?….” Bai barta ta qarasa maganarba ya dauketa cak ya cilla saman gado ya bita yana cewa
“Aga matsoraci tsakanina dake,ke kike tsoron biyan bashi bani ba” tattare jikinta ta soma yi tana dariya gami da bashi haquri,bai yarda ba saida suka fafata ya gajiyar da ita tubus sannan yace ya haqura,tayi shuru na maida numfashin kokawar daya sanyata,tana jin dadi cikin zuciyarta na nasarar shafe masa bacin ran daya so yin tasiri cikin zuciyarsa data yi
“Yarinyar nan qiba naga kin fara yi fa” khalipha ya fada yana dora kanshi saman cinyarta,gami da zagaye qungunta da hannayensa,baki ta zumburo
“Ni ba wani qiba,bayan kaine duk ka hanani qibar,kai baka ga yadda ka soma tumbi ba” qayataccen murmushi ya saki yana maida kwanciyarshi rigingine yana shafa cikinsa da tafin hannunsa daya,ta yadda hakan ya bashi damar kallon fuskarta sosai
“Ni aike nakeso na gani da tumbi,irin tumbin da zaki bani baby fa” kukan shagwaba ta sake masa tana bubbuga hannayenta
“Da wuyafa ya khalipha da wuya…” Dariya ya saki
“Kinsan kuwa jiya nayi mafarki kin haifamin twince masu kama dani?kuma duk mata”
“Sonkai?” Ta fada tana zaro ido tana dariya
“Kona tashi maza zan haifa masu kama da anni koni” idonshi shima ya waro
“Da gaske baby girl nakeso ki haifamin uwaisha…”
“Ni kuma baby boy nakeso,so nake na haifa daddy”
“Shikenan,idan kika haifa mace ni zan saka mata suna,idan namiji ne ke zaki saka”
“Na yarda”
“Mu qulla alqawari” ya fada yana miqa mata qarmin yatsanshi,sai ta miqa masa ita wanda ya shammaceta ya jawota ya maye gurbinta.
[3/17, 7:57 AM] Binta Mustapha:
Post a Comment for "Daurin Boye 58"