Daurin Boye 57
57
Dukkan abinda ya faru a rayuwar aysha daga wanda ta bashi lbr kama da wanda ya faru yanzu ya dinga tariya cikin kwanyarsa,jinjina kai kawai yake,sai yaji yana son magana da anni wadda satin da zasu zo ta gama tata
umarar ta wuce dubai inda ruqayya da take aure saboda haihuwa da tayi,shima yana saka ran daga nan can zasu wuce da aysha suga juna,don bata taba ganinta ba,ta kuna takura tana son ganin nata.
Suna soma magana da annin ayshan ta fito,saita koma gefa daya tana kallonshi hannayenta sarqafe da juna,wani iri so nashi da qimarshi na hauhawa cikin zuciyarta,sai yanzu ta fahimci shiya shirya komai,shiya shirya haduwarta da mahaifiyarta kamar yadda ya biya musu umara suma ya biya musu donsu hadu a nan,wanne irin mutum ne shi wanda bai gajiya da alkhairi?,wanne irin so yake mata da har kullum yake bibiye da lamuranta da dukkan mutumin daya rabeta yana aikin faranta musu?,bata dawo daga duniyar tunani ba saidaya miqa mata waya yana cewa zasuyi magana da anni,ta amshi wayar zata kai kunneta can qasa yace
“Ki rage wannan kallon da kikemin idan baso kike ki qarasa zautani ba” murmushi ta saki mai sanyi wanda yasa kumatunta lobawa,saiya shagala da kallonta sanda suke magana da anni,harta gama ta miqo masa bai sani ba
“Nima zaka zautani dinne?” ‘Yar qaramar dariya ya saki yana karbar wayar
“Na gode,kin rama munyi one one ko?” Ya fadi yana dage mata gira,wani murmushin ta sake saki
“To yaya?,komai yayi normal?” Ya fada yana wara hannayenshi,kai ta gyada,sai hawaye ya soma bin fuskarta
“Ashe haka uwa take sa dadi ya khalipha?”kai ya shiga girgiza mata
“nooo…kuka kuma dai?,ashe zaki sanya na fasa barinki ki kwana wajenta da nayi niyya” idanu ta fiddo tana share hawayen
“Da gaske zaka barni?” Girarsa ya daga
“Yes,kwana daya zakiyi,amma kiyi alqawarin tanadarmin dukkan wani farinciki a sanda kika dawo ko?” Bata gane me yake cewa ba,saidai tunda yace zai barta ta kwana wajen umminta ya gama mata komai,haka kuwa akayi,ya dauki abba suka wuce nasu masaukin,suka bar uwar da diyarta suka kwana babu bacci suna hira
“Bansan irin qaunar da basma take miki ba,tun daga ranar da kikazo naqi kulaki ta daina walwala har yau” murmushi aysha tayi
“Ki barta,zanyi magana da ita da kaina gobe zan kirata” ranar haka suka kwana dungurgur a zaune aysha na bata labarin yadda ta rayu,kuka wiwiwi ummin ta dinga yi,ta rasa inda zata dora ranta,tayi alqawarin yafewa inna yelwa ne aduk sanda ta gane kurenta ta nemi afuwa banda haka data yi mata Allah ya isa,ta kuma nemi Allah ya fitar mata da haqqinta,ranar ko masallaci basu sake komawa ba,haka suka kwana tare,duk wani motsin ummin aysha na biye da ita,ko hijabinta bata bari ta dauka da kanta,yayin da ummin kebin ayshan da kallo duk inda ta motsa,tausayinya na ratsata,ta goge qwalla a boye tafi sau nawa,itakanta a karan kanta idan ta tuna yadda tabar ayshan tun batasan kanta ba sai taji dama ta tariyo baya ta goge komai,me yasa tabar musu ‘yarta bayan tasan basa qaunarta?,me yasa bata tafi da ‘yarta ba kome zasu ce suce,da duk wani shiri nasu bayi tasiri ba,data rayu da ‘yarta tasan gatan uwa,saidai qaddara ta riga fata,hakanan bawa baya iya gujewa qaddararta,mai yiwuwa data tafi da ita din da a yau ayshan bata samu khalipha ba,da wataqila bata samu matsayin da take dashi na rayuwa ba a yanzu.
Washegari khalipha ya dawo bayan sallar azahar,don abba yazo tunda safe ya gansu ya wuce masallaci,a sannan aysha na ramuwar bacci ummi ta tasheta tace maza taje,haka ta dauraye fuskarta ta fita harabar wajen da yake zaune,idanu ta zuba mata wani abu na tsirga masa harta qaraso inda yake,ji yake kaman ya sureta,yana kallonta yasan bacci take aka tasota,saiya narke mata tun kafin tayi magana
“Wato an samu ummi an manta dani ko?,ba saqon saoda safe,ba saqon barka da safiya,babu na barka da rana,shikenan na gode…kice kawai ba zaki iya kula dani ba tunda kin samu ummi na auro wata kawai” har cikin ranshi da wasa yake,amma abun mamaki saiga qwalla aisha ta fara,abunma kamar yayi dariya amma ganin da gaske kuka zata mishi saiya daure,bai taba zaton yadda ake cewa masu suna aysha nada kishi sosai gaske ne ba kamar yanzu,da qyar yasha kanta,saiya koma seriouse dinshi sosai
“Ki shirya anjima zanzo ki rakani inyi wata siyayya” kai ta langabar
“Ya khalipha….ban gaji ba da ganinta”
“Rakiya nace zakimin ai ko?” Kai ta gyada
“Shikenan” kadan suka taba hira ya wuce shima masallaci,saboda addu’a yakeso yayi yau sosai kan rayuwarsu shida ayshan,harkokin kasuwancinsa,iyaye da ‘yan uwanshi.
Gab da magariba ya dawo,yayi kyau sosai cikin shigar larabawa jallabiyya baqa harda hirami,ita kuma ta sanya abaya maroon da baqin niqaf bayan ta nade kanta da mayafin abayar kai kace hijabi ta saka,kallonta yake saboda wani kyau data yi masa,idanuwanta da suka fito ta tsakiyar niqaf din kamar an qara musu girma da kyau,tun a lokacin jikinsa gaba daya ya amsa har cikin zuciya tuhi da gangar jiki,duk wani kuzarin daya taho dashi ya bace,a haka suka lallaba masallaci sukayi magarina da isha’i sannan yace ta fito su tafi.
Katafaren shagon saida kayan ado ne na mata,binsa tayi kawai da kallo sanda ya nufi bangaren kayan bacci bayan ya gama siyan turaruka masu dan karen kyau da tsada,tana kallonshi don yace ba ruwanta ya dinga zaben kayan bacci kala kala,sai daya dauki wajen kala goma dukkansu babu mai qaramin kudi sannan ya biya suka wuce.
Wani shagon suka sake tsayawa nan gaba da wajen kadan,gwalagwalai suke siyarwa,kana ganin yadda suke gaisawa da bashi qima kasan babban custumer ne,hakanan akwai alamun sabo sosai tsakaninsu,kujera yaja mata yace ta zauna,sample aka kawo mata kala kala na sarqa da dan kunne,zobe da banguls khaliphan yace ta tayashi zabe,ta tambayeshi guda nawa yace kowanne bibbiyu,tana zaton anni ko wani zai saiwa saboda haka ta zage ta zabi masu kyau,ita kanta sun bala’in burgeta,basu dade sosai ba ya biyasu sukayi sallama suka fita.
Daganan wajen saida kayan maqulashe ya tsaya shima,yayi siyayya sannan suka shiga motar suka wuce,ta dan gaji hakanan ga kewar ummi,Allah Allah take su isa ya ajeta ta ganta sannan ta huta,sai taga dirven ya dauki wata hanya daban,ba ha yar hotel din da suka sauka ba,hakanan ba hanyar hotel din su ummi ba,dubanshi tayi
“Ina zuwa kuma ya khalipha”
“Masauki zamu koma nayi kewarki uwaisha….kiyi haquri gobe saina maidaki wajen ummi,ni kadaine bana jin dadi” batason bata masa dai dai da rana daya,duk yadda taso ganin ummi saita kada masa kai kawai,sai a sannan ta tuna ma yace mata dama kwana daya zatayi,amma batasan ba zata dawo ba data sake magana da ummin.
Area ce mai wani irin kyau mai kwantar da zukata,hakanan hotel din shima kansa tun daga gininshi da tsarinsa kasan na musamman ne,bata sake tabbatarwa ba sai da suka shiga dakin,duk kayansu yana ciki a shirye,shi ya maida qofar ya sanya muqulli ya rufe,haka kawai a ji jikina yayi sanyi,ta daga kai ta dubi khalipha dake kallonta yana murmushi
“Dakin yayi miki?,ko mu sauya waje?” Murmushu tayi mai sanyi sannan tace
“Sosai ya khalipa”
“Wayyo Allah” ya fada yana aje kayan siyayyar hannunshi,don bai barta ta dauki komai ba kamar yadda bai bar wani ya dauka musu ba
“Wanka da alwala….wazai fara ni koke?” Idanu tadan fiddo
“Ya khalipha…nikam haka zan kwanta bana jin yin wanka”
“No…dole kiyi,so kike ki zama qazama?” Ya fada yana kada kanshi,haka kawai take jin fargaba,saboda kallon da khaliphan yake mata saitake ganin kamar ba wanda ya saba yi mata ba,saita noqe kafada
“Toka fara yi sannan ni” hannunshi ya ware
“Well,hakan yayi” jallabiyar jikinsa ya soma zamewa,saita dan rintse ido kamar yadda ta saba,yana kallonta saidai wannan karon dariya ta bashi,ya qunshe abarsa yana kada kai ya shige toilet din.
Kaman yadda ya saba aqalla yana daukan minti talatin sannan ya fito,tayi wuf ta shige bandakin ganinsa daure da dan guntun towel yau sabanin da da yakan sanya rigar towel,sanda take qoqarin rufe qofar ya sanya hannu ya tokare qofar ya rufa mata baya
“Ya khalipha….don Allah” saita gaza qarasawa ganin ya cimmata ya kaita bango,ya mata rumfa gaba daya,tsoronshi da kwarjinsa wanda bata taba jiba yau ya kamata,so yake lallai ta kalleshi amma taqiya,nunfashinsu ya dinga cakuduwa da juna,murya can qasa yace daita
“Wannan saurin da kike kika fada toilet duk na meye,to sai kin nunamin abinda kike tsoro” kamar zata sanya masa kuka take masa magiya
“Babu komai don Allah kayi haquri,nidai babu komai” wani murmushi ya saki wanda shi kadai yasan ma’anarshi ya janye baya yana cije lips dinshi,saiya nufi famfo ya sake daura alwala sannan ya juy ya dubeta,har yanzu tana tsaye inda ya ritsata
“Kiy sauri ki fito na baki minti goma,idan ba haka ba,zan shigo na daukoki ko baki gama ba”murmushi tayi a kunyace,juyawa yayi ya fice sannan yaja mata qofar toilet din.
Sanda ta fito tuni yana saman abun sallah,sanye da jallabiyya fara qar har daukan ido take,kansa saye da hula tashi ka fiya naci baqa,dakin ya bule da wani irin sassanyan qamshi,wani kyau taga yayi mata sosai,don karta shagala da kallonsa saita kauda kanta,riga ta gani aje ta bacci da kuma after mai kauri gefanta,girgiza kai tayi sanda taga yadda rigar take,amma data tuna zata dora after din saita dauka ta koma bandaki ta shirya acan,ta mulke jikinta da wani turare daya aje mata wanda qamshinsa da dadinsa ya dinga sanyata kasala.
Binta yayi da kallo sanda ta fito daga bandakin,sai yayi mata nuni da gefansa,matsawa tayi ta saita sahu yadda ya dace ya kabbara sallah cikin mamakin sallar meye itama ta tayar,raka’a biyu sukayi sukayi sallama,yaja doguwar addu’a sosai wanda ke tattare da roqon dukkan alkhairi sannan ya shafa,jiyowa yayi ya zauna yana fuskantarta gami da tanqwashe qafa,janye idanunta tayi daga nashi tana jin zuciyarta na bugawa,wata fargaba na shigarta,sunanta ya kira wanda ya sanya ta daga kai ta dubeshi,a nutse yake mata tambayoyi game da abinda ya shafi addininta,sallah tsarki da wanka,kada kai kawai yake yana gamsuwa da bayaninta,kai karantse wata malama ce,sai data kammala sannan ya dora hannunshi ya karanta addu’ar nan da annabi ya umarcemu ga duk wanda Allah ya horewa yayi wani sabon abu,ko mata ko abun hawa,har ya gama tana saurarenshi,hannunsa ya sanya ya janyo ledar dake gafansa wadda suka siyo kayan ciye ciye a ciki,ya fidda komai ya aje a gabansu,itadai nata ido jiki a salube,donta shinshino wani abu,da kanshi ya dinga ciyar da ita,duk da taso ta turje da farko yayi kicin kicin ya nuna yayi fushi,cikin hikima ya dinga janta da hira wanda ya sanyata ta sake,sai gata tana qyalqyala dariya,bayan sun gama ita ta gyara wajen kafin ta kammala ya haye gado abinshi
“Malama a cire hijabin nan da after din mana haka?,banfa ga kwalliyar ba” sai ta dan diririce kadan saboda tuna yanayin rigar dake qasa,girarshi ya dage mata
“Yes….ko so kike nayi asarar kudina?” Ya fada yana zuba mata idanu,hakanan ta dinga fidda kayan kunya na saukar mata,sai daya ragw saura rigar baccin kawai,zuwa sannan numfashinsa ya soma masa nauyi,tunda Allah ya halicceshi bai taba ganin sura irin haka baka,ashe ayshan ta zarta dukkan yadda yake tunani,hannunshi ya miqa mata yana daga zaune saman gadon,bayanshi jingine da fuskar gadon qafafunshi miqe
“Kai zo nan muga wani abu….ya maqale miki a gashi meye haka kamar qadangare?”gaba daya basirarta ta tafi,dama atsorace take haka kawai,sai ta kwasa tayi wajenshi babu shiri,batasan cewa wayo yayi mata ba sai data ji ta shigo hannu,saqonni yake aika mata masu wuyar bijirewa,masu nauyi a qwaqwalwa,masu rikita lissafi,sai daya warware mata dukkan wani lissafinta sannan ya rada mata
“Zanso darenmu na farko ya zama cikin wannan garin mai albarka kamar yadda na jima ina burin haka a rayuwata a duk sanda Allah ya bani matar aure,saboda kwadayin albarkar dake cikin garin,kin bani damar cika wannan buri nawa uwaisha?” Kai ta gyada mishi tana rufe idanunta,tana son ta yaqi tsoto da fargabar dake taso mata
“Na gode,na gode” ya dinga maimaita mata yana cusa kanshi tsakanin wuyanta da sumar kanta ta sauko tayi musu rumfa duka su biyun.
Cikin wannan sassanyan daren,khalipha da ayshan suka zama abu guda,khaliphan ya samu ayshan fiye da yadda yake tsammani duk da cewa shi din farin shiga ne,ya bita a sannu yanda ya kamata saidai hakan bai hanata jin jiki ba,tunda ita dinma baquwa ce a fannin,saidai yanayin yadda ya riritata ya taqaita mata wahala qwarai da batasan yadda zata kaya mata ba.
Hakan gaba dayansu bai hanasu tashi sallar asuba ba,tare sukayi jam’i,ya waiwayo yana kallonta sanda suka idar cikin tausayawa da wata tarin qauna,saidai taqi yarda su hada idanu,wata kunyarsa mara misali take ji,murmushi ya saka a sirrance don yasan kunyar me take
“Khalipha zan mutu,ashe dama baka sona?” Ya fada a hankali,sarai ta jishi kuma tasan ita yake tsokana,saitayi banza dashi saidai bakinta data dan zumburo
“Ina sonki mana my uwaisha,Allah sai yanzu ma nake sake jin wani sabon shauqi game dake,uwaishaahhh zan iya mutuwa saboda ke…” Salon yadda yayi maganar cike da tsokana da shagwaba ya sanyata sakim dariyar dole,shima tayata yayi kafin daga bisani yayi nasarar sanyata cikin jikinta yana shafar gashin kanta,addu’a ya dinga jero mata godiya da fatan alkhairi tana amsawa can qasa kanta na saman qirjinta,a haka har bacci yayi awon gaba da ita,shimfideta yayi a wajen yana gyara mata kwanciya idanunshi a kanta,ya jima ahaka yana kallonta kafin ya miqe yana shawagi kadan kadan a dakin kamar mai gadinta,zuciyarsa fes qal,wani farinciki na musamman na ratsashi,ashe da can ba rayuwa yake ba gashinan ne dai kawai?,ya godewa Allah da tasahon shekarun ya tsareshi ya kuma kare ayshanshi,duk irin gwagwarmayar rayuwar da suka fuskanta hakan bai sanya sun fada gonar daba tasu ba.
Bai taisheta ba sai dayaga lokacin sallar azahar yayi,tana zaune inda tayi sallar yana aukin kallonta yace
“Ko zaki shirya na kaiki wajen ummi?” Kai ta girgiza alamun a’ah,don tana ganin kamar idan taje ummin zata gane wani abu daya faru.
Da la’asar ta sanke wanka da ruwa mai zafo don taji dadin jikinta,taji din kuwa,har ta dan samu tayi mishi kwalliya,tana daura dankwalin kanta taji hannunshi a wuyanta,sarqar gold din da suka siyo ce wadsa duk ciki tafi kowacce kyau da tsafa,bata ce komai ba itadai tana tsaye tana kallonshi,yasanya mata dan kunnenta sannan ya kama hannunta ya zira mata awarwarayen,baya ya danja yana kallonta
“Kamar yadda na zata kin haskasu sosai” ido ta zare tana daga gira alamun neman qarin bayani
“Eh,kin haskasu,don kinfi qarfin su haskaki aysha basu da wannan kyan saidai ke haskasu” tilas ya sanyata dariya,idan yana yabonta wani lokaci yakan sanyata dole taji kanta ya kumbura,taji duk duniya babu macen da tayi sa’ar miji kamar ita
“Wannan shine dan qaramin tukuicin da zan baki kan farincikin da kika sanyani daren jiya” ya rada mata wanda kunya ta sanyata saka tafin hannunta ta rufe fuskarta,kamar yadda ya saba ya hanata godiya yace amma wannan karon ta adana godiyarta sai haduwa ta biyu,murmushi ta saki kawai,khalipha na sata jin kunya shi kuma babu ruwanshi.
Haka sukayi zamansu yana jinyar abarsa yana lelenta,saida sukayi kwana biyu cur sannan suka fita,zuwa sannan ta samu sauqi bata jin komai a jikinta,don ya bata tazara bai sake neman komai daga gareta ba,ranar tare da ummi suka wuni a masallaci,don suna saka ran a satin zasu bar saudiyya.
Cikin satin kuwa khalipha ya dinga daukarta suna zuwa siyayya,har gajiya tayi da siyayya,ya dinga sanyata tana diban kaya kamar banza,batasan cewa ba nijeria zasu wuce ba sai ana ya gobe zasu tafi,ya shaida mata suma zasu suga ruqayya ne,langabe masa tayi tana kallonsa
“Nayi missing din anni pls ya khalipha….”
“Na sani nima haka,amma inaso muje mata ne da babbar tsaraba” sam bata gane ne yake nufi ba sai tace
“Akwai tsarabar dana siya mata,kuma abinda tafiso shi na siya mata,nasan zataji dadinta” bakinsa ya tabe yana kada kai
“Duk tsarabar da zaki kai mata bata kai wanna ba,so nake ki samar mata jika…..” Ai bai qarasa ba ta saki ihu tana rufe fuskarta,yayin daya bita ya danneta yana qoqarin saita bude fuskar ya qarasa gaya mata ita kuma ta qiya,daga qarshe shi yayi nasara dole sai rintse idanunta tayi tana saurarenshi a haka.
Karon farko da suka soma haduwa da ruqayya tayi aysha ta kwanta mata sosai,kamar yadda itama anty ruqayya ta kwanta mata,ta rasa inda zata saka ayshan,ta lura akwai sabo da qaunar juna sosai tsakaninta da khalipha,yaranta kamar aysha ta qwacesu,yara masu kyau da tarbiyya.
Tun anty ruqayya na mata hira kan dabarun zama da miji tana jin kunya har daga qarshe ta haqura,a nan ta samu sirrika masu tarin yawa a wajenta,dauka mata wannan tasha,dauko mata wancan ta lasa duk wasu hadin na larabawa ne,sai data tsima ayshan da kyau cikin dabara,donta lura da take taken khalipha wanda ta fuskanci ayshan sam batasan me yake nufi ba,ana sallar magariba ta sanya ayshan tayi wanka da kyau cikin ruwan turaruka,ta bata wata rigat bacci mai kyau saidai tana da dan kauri wadda tasha turaruka kala kala,bayan ta gama shiryawa suna gefan gadon anty ruqayyan ayshan na sauyawa qaramin yaron anty ruqayyan pampers khalipha ya shigo dakin wanda dakin spare ne na baqi mata dake cikin gidan,dubanshi anty ruqayya tayi samda yake tsaye ya tokare bango da qafarsa guda daya daya yana tsaye a kanta,hannunsa harde a qirji ya dan shagala da kallon aysha wadda antyn ta gyara mata kanta yayi kyai qwarai
“Ya ne alhj halifa?” Saiya saki ajiyar zuciya a boye ya maida kanshi gunta
“Zuwa nayi ki bani matata,tunda na fuskanci so ake a qureni ana zaton bazan iya magana ba” dariya ta saki
“Allah ya baka haquri,aysha tashi ki bishi tun bao daukeki da kanshi ba” sauke qafarshi yayi yana tattare hannun rigarshi
“Kamar kuwa kinsan abinda nake nufi kenan ba?”kafin suce meye su duka ya daga ayshan cak yana fadin
“Allah ya bamu alkhairi saida safe anty” kunya kamar aysha tayi me?,sauqin abun daya duka yaran antyn na dakinsu suna assigment,tun daga hanya qamshinta ya soma rikitashi,suna zuwa daki ya qarasa birkice mata,ranar ya more angoncinsa qwarai,taso tayi dauriya amma daga qarshe saidata nuna raki,duk da akwai sauqi akan karon farko,shikam ji yayi kamar ma ranar yake ango.
Washegari qememe ya hanata fita sai daya sake morewa,kunya tasa ma ta kasa fita gaba daya,’yar halak anty ruqayyan saiga aiken breakfast ta turo babban danta ya kawo musu,koda yamma da suka fito zai zaga da ita gari antyn fuskewa tayi kamar ba’ayi komai ba,wanda hakan ya sanya aysha itama ta sake.
Kwanansu bakwai a dubai suna amarci sosai,randa suka dawo daga wani mall tana fitowa daga wanka saiga kiran wayar hanan,ta tsaya da tsane ruwan kanta da take ta amsa wayar,ta gaya mata an dawo daga yajin aiki,suka dan taba hira sannan sukayi sallama ta aje wayar tana duban khalipha dake ninke kayan da suka cire shi da ita,haka yake baida qyuyar aiki,wani lokaci har mamaki yake bata,baida girman kai ko kadan,baya jin yiwa iyalinshi aiki ko wata hidima,wani abunma kafin tayi musu shi yayi
“Komawa gida yazo kenan,kaga hanan ce ta kirani tacemin an koma strike” kanshi kawai ya daga ya kalleta,saiya maida yaci gaba da abinda yake ba tare daya ce mata uffan ba kamar ma baiji abinda tace ba,dubanshi kawai take,ta tabbatar yaji din,amma batasan me yasa yayi banza da zancan ba,saitaja bakinta itama tayi shuru taci gaba da sabgarta,saidai jikinta gaba daya a sanyaye yake.
Har sukazo kwanciya jikinta a mace yake,yayin da shi kuma har a sannan baice da ita komai ba,sai daya gama addu’at kwanciya ya shafa itama ya shafa mata sannan ya janyota jikinsa,a hankali can qasa yace da ita
“Karki wani zafafa da yawa,kar ki saka buri da yawa,Allah ya sani ni kadai nasan me nakeji a zuciyata a kanki,kici gaba kawai da addu’a kan ci gaba da karatunki a wudil,idan babu alkhairi Allah ya zaba miki abinda yafishi alkhairi”sosai gabanta ya fadi tana tsoro da fargabar fa yace ba zata koma ba,amma duk da haka saita danne kawai,tunda shine sila na komai hatta da karatun nata ma.
Cikin dare ta tashi a firgice sakamakon mafarkin da tayi,gidan daddy ya cika anata kuka,shi kuma yana zaune yana ta bin mutane yana basu haquri,ita kuma waisai ta shigo ta fadi tana kuka,saiya dagata yana cewa ta fada kan maciji,sai macijin ya sareshi shima ya fadi anan sai kuma akayo kanshi anata jijjigashi amma ya daina motsi,tana cikin bawa khalipha labarin kawai saita saki kuka,harga Allah zuciyarta tayi gida a sannan,da qyar ya lallabata ya nuna mata sharrin mafarki ne,shi ya sanyata tayi alwala shima yayi suka dasa sallar nafila har asuba,bayan tayi sallar ne bacci ya dauketa.
Tana farkawa kuwa layin daddyn ta soma kira,babu jimawa ya daga,wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki sannan ta soma gaidashi,a sake yake amsawa ta tambayeshi jiki yace jiki da sauqi sosai,don bai taba jin dadin jikin nasa irin yau ba,hira sukayi mai tsaho sannan sukayi sallama tace ya gaida mutanen gidan,yace zasuji don safiyya ma mutuniyarta nakan hanya tace saitazo ta kawo masa wani dahuwar nama,tana dariya tace idan tazo daddy kace ta ragemin,yayi dariya yana fadin
“shikenan kuwa zata ji,sai wani lokacin kuma”
“Zan sake kira daddy anjima in sha Allahu”
“Allah ya bamu aron rai”
“Amin” da haka suka rabu,khalipha na tsaye saman kanta yana kallonta yana dariya
“Yar daddy,kin kirashi dai kinji dadi ko,kuma kinji lpy lau yake sharrin mafarki ne,haka kawai jiya kika wani birkice,ina shirin da asuba adan sanmin na d’ana duka aka hanai” juya qwayar idonta tayi cikin kunya tana murmushi
“Hankalina ya tashi ya khalipha,ina son daddy” gefanta ya samu ya zauna
“Mutum ne na qwarai sosai” daga haka hirar daddyn ta balle a tsakaminsu,kowannensu na tuna alkhairinsa gareshi.
A ranar da yamma tana tare da anty ruqayya suna hira khalipha ya shigo yana shaida.mata ta shirya nan da wa daya zasu wuce nigeria,cikin mamaki anty ruqayya kanta take kallonshi bama ita ayshan ba
“Lafiya daiko?” Ta tambayeshi
“Lafiya,aikime kawai ya taso min a kamfani kiran gaggawane ya samu”
“Auto,har naji dadi” ta fada tana sakin ajiyar zuciya,itakam.aysha ba wani zumudi dataji wanda ta tsammaci zataji duk randa zasu koma gida,saita miqe zuwa dakinsu da zummar hada musu kayansu.
[3/17, 7:57 AM] Binta Mustapha:
Post a Comment for "Daurin Boye 57"