Daurin Boye 55
55
ko duban asma’u baiyi ba ya dauke kan motarshi ya canza hanya
“Wai malam ina zaka dani ne?” Banza yayi da ita donshi kadai yasan tashin hankalin da yake ciki
“Kaga malam ka saukeni ina zaka dani nina gaji fa”tsawa ya daka mata sannan yace
“kiwa mutane shuru,ke bakisan abinda yake damunsu ba zaki cikasu da surutu,koma meye kema kin taimaka wajen faruwar abinda ya farun,dole muje dake kema ki saka baki” ganin yana yi kamar zai daketa ya sanyata yin shuru kawai tana huci,haka suka ci gaba da tafiya har suka cimma daddy,cikin tasu motar ya shiga suka tafi yabar motocinsa nan wajen wani cin abinci dake lodge road din.
Qararrwar falon daketa kadawa ya sanyashi miqewa don zuwa duba wanda ke neman izinin shigowa
“Kinga yanzu kikai alqawari ba zaki sake kuka ba,karki karya” kai ta gyada mishi tana binshi da kallo,har cikin ruhinta tana jin wani alfahari na kasancewarsa miji a gareta,daya tamkar da dubu.
Daya daga cikin masu tsaron qofar gidan ne yake shaida masa yayi baqi,baisan su waye ba hakanan suma sun gaya mishi cewa baisan da zuwansu ba
“Qyalesu su shigo” ya bawa mai tsaron qofar umarni,falon ya koma yana dubanta
“Kinga duk kinsa coffen yayi sanyi,dan sake hadamin wani zanje naga wasu baqi,nasan ba jimawa zasuyi ba tunda banyi dasu zan gansu ba,nan da minti biyar zan sallamesu saiki kawomin coffe din a can zan sha”amsa mishi tayi yayin daya dan sunkuya ya sumbaci goshinta sannan ya zura takalminsa ya fice.
Tunda suka shigo gidan gaba daya ya tafi da imaninta,tasan cewa za’a rina hakan,don tun a mota ta fuskanci wajen uban gidan mijin nata zasu je,sai take ganin gidan kamar ta sanshi,sai taga yana mata zubi da gidan aysha da aka kawota,girgiza kai tayi wani bari na zuciyarta na gaya mata
“Haba wane mutum,ta ina khalipha yake da kudi kamar na mutumin nan,ta inama zai ginawa ayshan gida har haka?” Ko kusa bata ankare da khaliphan ba har suka gama parking suka fito,saboda idanunta nakan jerin motocin alfarma dake pake a inda aka tanada saboda ajiyar motoci na gidan.
Hamid da daddy suna gaba tana binsu a baya,zuciyarta cike taf da qyama da dana sanin auren hamid,bata taba tunanin kudin da suke tinqaho dashi ba nasu bane na rance ne ba sai yau,da zasu kula da ita da kyau ta baya kallon wulaqanci take jifansu dashi,gab da zasu isa wani guri datake hango wani mutum can zaune hamid ya dakata ya jata gefe
“Ki tabbatar da cewar kin bude baki kin bada haquri,idan ba haka ba wallahi Allah kinji na rantse miki duk wani abu da nasan na siya miki ke har motar da kike hawa saina saidata,saboda duk da kudin da muka karba da bikinki na cire wani abu a ciki na siya miki” dubanshi kawai take,a fuska gashinan mutum iya mutum,saurayi dan gaye maiji da kanshi,saidai a ciki duka hoto ne kuma kango ne,sam hamid baya burgeta yanzu dai dai da qwayar zarra,hakanan mamaki ma suke bata shida ubanshi duka a yanzu,koda zata bar gidan hamid batason ta rasa abinda ta shigo da shi,ta koma gida a tsiyace,wannan ne dalilin kawai da zai sanyata ta bada bakin,saidai bata ce masa uffan ba har suka qarasa wajen.
Ya amsa musu sallamarsu saidai ya maida kanshi kan wayarshi yana turawa aysha tex kamar ba yanzu ya barota cikin gida ba,baiyi tsammanin su bane da bazai bada damar su shigo ma cikin gidan ba,qamewa asma’u tayi yayin da take qare masa kallo,wani tashin hankali taji yana gewaye ilahirin qwaqwalwarta,wai dama khalipha ne wanda sukazo roqa?,dama alhj kutama surukinta da hamid mijinta dukkansu a wajen khalipha suke amsar bashi?,dama da dukiyar khalipha aka aurota?,take dukkan wani qaimi da kwadayin rabuwa da hakid ya sake ninkuwa cikin zuciyarta,taci gaba da qarewa khalipha kallo tun daga zara zaran yatsun qafarshi zuwa kanshi,tana kuma tantance banbanci tsakaninsa da hamid wanda ya yiwa kanshi mazauni daura da khaliphan,karon farko data soma jin haushin kanta da kanta a rayuwa,tun daga siffa khalipha ya gama cinye hamid murus,me ya kaita yin wannan ragon azancin?,wai me yasa ma batasanya daddy ya nashi jari gida da mota ba asanda take tunanin talakane ta aureshi ba?,inuwar daya gani kusa dashi ya sanyashi dagakai,sai yaga asma’un,yayi mamaki don baisan meye alaqarta da alhj kutama da kuma hamid ba,Allah yasanya ba son kudinta ya kaita qulla alaqa dasu ba,ya furta cikin zucuyarsa
“Ki zauna mana,ya zaki tsaya qerere kan mutane?” Hamid ya fada cikin fada fada,saita ja kujera a kunyace ta zauna,a mutunce ba wulaqanci ya gaida daddg sannan suka gaisa da hamid,duk da bai bashi hannu ba,don a yanzu qyamatarsu yake,yana mamakin yadda kana musulmi zaka iya saida abinda zai zama cutuwa ga al’umma,infact ma ruguza al’umma gaba daya kayan shaye shaye yake,saboda matasa sune qashin gadon bayan al’umma to an ruguzasu me yayi saura?.
Daddy shi ya soma bada haquri sannan hamid,murmushi kawai khalipha yayi sannan kai tsaye ya kira sunan daddyn
“Aikin Allah kayi da kudin da kake tunanin samun sassauci daga gareni?,idan na sassauta maka ma na bada goyon bayan kaci gaba da aikata dukan abinda kake aikatawa kenan?” Gyaran murya asma’u tayi wanda ta gyara zama gami da lanqwasa muryarta ta sona zayyanowa khalipha maganganu,wanda kusan rabi hannunka mai sanda take masa a karan kanta,yadda ya hade yatsunsa waje guda yana kallonta yasa ranta yayi fari qal taci gaba da magana tana juya idanu,sai data gama yaja wani.matsiyacin tsaki sannan ya juya ya dubi alhj kutama bayan ya kira sunanshi
“Kada ka sake nemana idan ba kudina ka kawomin ba nan da kwanaki uku,idan ka tashi kawomin kuma ka daure ka dauko mutane masu hankali su rakoka” ganin yana niyyar miqewa yasa hamid zungurar asma’u kan tayi magana,don iyaka saninsa da khaliphan yana da tausayin mata qwarai,ta fuskanci abinda yake nufi itama kuma ko banza batason rasa dukiyarta,saboda haka ta soma roqonshi,daidai sanda aysha dake dauke da wata butar shayi mai kyau da qananun kofuna,saita soma takawa a hankali ganin kamar baqin nashi basu bati ba,bata ma gane su waye ba,shi ya soma ganinta,saiya miqa hannunshi yana cewa
“Kawo my uwaishahh” cikin nutsuwa take takowa ta dora yalwataccen mayafi mai kyau saman kayan jikinta,qamshin turaren data sake fesawa jikinta na kadawa zuwa ko ina,maganar khalipha ita taja hankalinsu kanta,take kowanne tunaninshi ya banbanta,alhj kutama na farinciki tare da jin dadin ganin fitowar uwar gidan,ko banza yasan idan ya roqeta ta sanya baki wala’alla khalipha ya dage musu qafa ko ya qyalesu,ya danganta da yadda yake jin maganarta,hamid mamaki ne ya daskarar dashi a wajen,dama aysha muhammad khalipha mai goro ta aura?,ya akayi haka?bayan asma’un tasha bashi labarin irin mijin da ayshan zata aura ta qyalqyala dariya tana fadin shi ya dace da ita ai,ya tabbatar asma’u bata da masaniya da tabbas ba zata qyalewa aysha shi ba,idan ko aysha ce matarshi lallai abubuwan zasu zo da sauqi,tun ba yauba ya santa da tausayi da sanyin hali,ba shakka mai yiwuwa tasha musu kan khalipha.
Ta gefan asma’u kuwa wani dan banzan kishin aysha shi ya taso mata,komai na ayshan ya sauya,dukkan wani jin dadi da hutu ya gama bayyanar mata,babu shakka ayshan nason tsere mata tayi mata fintikau a rayuwa,lallai ba shakka ya zame mata tilas tasan dukkan mai yiwuwa ta samu cikar burinta a rayuwa,cikin salo da kwainane asma’u ta sake lanqwasa murya tana roqar khalipha,wani abu kadan hamid yaji ya taba ranshi na kishi,sai kuma yake ganin tunda mijin ‘yar uwarta ne me yiwuwa ya haqura din.
Aysha na shirin juyawa ta koma don bai bata damar gaida kowa ba cikinsu khaliphan ya damqe hannunta,cikin yaqe hamid yace
“Aysha ki….”
“Kar na sake jin sunan matata a bakinka,kasan ba kowane ke kishin matarshi ba amma ni nasan me nakeyi” ya gaya mishi magana a fakaice,cikin kwantar da kai yace
“Kayi haquri boss,ranki ya dade ki sanya mana baki mana don Allah boss yayi haquri ya daga mana qafa,kuskure ne munyi da yardar Allah ba zamu sake ba” duban khalipha tayi ranta duk a jagule,sai take jin babu dadi,daddy take tunawa,bai kamata ace diyarshi da mijinta na neman wani abu wajensu ba su gagara yi musu komai,idanu suka hada yana kurbar coffe dinshi,ya fuskanci tana son tankwa ne
“Kayi haquri don Allah ya khalipha ka daga musu qafa duk da bansan akan meye ba am……”
“Wuce ciki ina zuwa ya fada yana sakin hannunta,yanayin maganar tashi ya sanya ta juya zuwa ciki,amma duk bata ji dadi ba a ranta,sai dayaga bacewarta sannannya juya ya dubi alhj kutama
“Kar ka sake.gangancin zuwa min gida,saboda gida na iyalinane ba office bane,donsu kawai na gina,sannan nan da kwanaki uku idan baku dawomin da kudade na ba to ku saurari kiran hukuma” maganarshi ta qarshe duka ta kada hanjin hamid da alhj kutama,hukuma su da suke guje mata ta yaya zasu yarda ya jona su da ita?,haka suka miqe suka wuce gwiwa a sage,ran asma’u a dagule,bacin ran roqon da suka bata lokaci sunayi har a gaban aysha,ga rashin cikar buri,ga kuma burinta akan khalipha da bata ga wani sauyi ko ci gaba ba.
A falo ya sameta sanda ya shiga,ta daga kai tana amsa sallamarshi hadi da aje takardat hannunta,waje ya samu ya zauna kana ya kalleta sosai
“Humairaa”
“Na’am” ta amsa masa a sanyaye
“Banaso ki sake saka baki cikin lamarin da bakisan ya yake ba”
“In sha Allahu” ta fada kanta a qasa ba tare da musu ba
“Na dauki kudina na halak na basu saboda su juya su samu abinda zasu riqe kansu da iyalinsu,sai gashi daga baya suna siyo abinda zai cutatawa al’umma,ya ruguza rayuwa da future din al’ummarmu,kayan maye,kayan shaye shaye,dole na karbi kudina saboda shine kawai hanyar da zan karya su koda hukuma bata cafkesu ba,daga ranar basu da wata dama ta siye da siyarwar kayan mayen” ranta taji ya sosu,tabbas sun cancanci wannan hukuncin na khalipha
“Kayi haquri duka bansan wannan ba da bazan saka baki ba,lallai sun cancanci irin wannan hukuncin”.
Cikin tashin hankali su hamid suka isa gida,inda suka zauna daga baya shida mahaifin nasa,sun tabbatar da cewa matuqar ya hadasu da hukuma babu abinda zai hana ba’a gane sune aka kama yaransu ba wajen safarar miyagun qwayoyi
“a shawarce mu siyar da gidajenmu da kadararmu matuqar muna son tsira da rayuwarmu bama son qareta a gidan kaso mu sallameshi,idan yaso sai mu sami inda zamuci bashi mu fidda yaranmu mu tsallakar da kayanmu,indai hakan ta kasance kasan zamu maida ninkin abinda muka rasa harma da riba akai”kai hamid yake gyadawa,tabbas wannan itace shawara,don su siyi kaya na maqudan kudade kuma kadan suka bayar a fita dasu,idan har suka samu saidasu to zasu iya ninka kudinsu na yanzu,don dama abinda ya sanyasu siyan kayan kenan kwadayin kudi da zasuyi.
Yana isa gida ya shaidawa asma’u ta hada iya kayan sawarta kawai zasu sauya gida ne basai ta dauki komai ba,baiyi gigin gaya mata gaskiya ba saboda tabbas yasan idan ya gaya mata inda zasu koma to ta gama zama dashi,shi kuma har yanzu yana son abarsa bai kuma shirya rabuwa da itaba ko kadan,musamman idan ya tuna abinda ya kashe kafin ya samu nasarar aurenta,duk da tana shirin rabuwa da shine amma hakan yayi mata dadi,ko banza darajarta zata qaru tadan wani lokaci,kuma khalipha koda zai aureta yasan cewa ba daga qaramin gida ta fito ba,bataso ma ya gane wahala tasha hannun hamid,tafison su tafi akan cewa kawai sonshi take yanzu shi yasa taqi hamid.
Haka kuwa ya shirya iya kayan sawarta kawai sai dan abinda ba’a rasa ba suka bar gidan,don hatta da motarta a gidan ta barta,bata tashi gane cewa ajine zai fado qasa warwas ba sai da taga gidan daya sauke ta,plate house safecontain,wanda a haka ma zasu zauna ne da uwar mijinta da qannen hamid hudu,babban falo mai dauke da dakunan bacci masu toilet,sai kitchen a falon da wani spare ban daki,toh nata dakin akwai falo kafin bedroom din,wani kallo ta watsawa hamid
“Waime kake nufi banfa fahimceka ba,ina ne nan?”
“Nan shine sabon gidanmu,nayi gwanjon wancan gidan da duka kayan cikinsa zanyi biyan bashi dasu” tuni fuskarta ta sauya saiya juya da jakarta zata fice,tareta yayi cikin hargagi
“Ina kuma zaki?”
“Gidan ubana mana,don bamuyi haka dakai ba ai,idan ka gama uzurinka ka biyoni da takardar sakina,don wallahi bazan zauna dakai ba na gama zama dakai”
“Amma dai ke ba’yar halak bace ba macen zama bace,muci dadi tare kice ba zamuci wuya tare ba,ni zaki yiwa butulci?,kudin da zan biya kusan kece silar cinyewarsu”
“Kai ka sani kuma kai ka jiyo” ta fada tana rabeshi kamar zata bankeshi ta fice,dariya ya saki bayan ta fita
“Idan kinsan wata bakisan wata ba,bari na gama cinikin gidan” kusan duk wata kadara tasu saida suka saida,yayin da suka cika mutane da cewa ai zasu bar nigeria ne shi yasa.
Sanda asma’u ta isa gida qarya da gaskiya ta zauna ta shiryawa daddy,bata damu da rashin cikakkiyar lafiya dabai da ita ba ta zauna ta tsara masa maganganu na qarya,tun baya mutum ne shi mai dattako da sanin ya kamata,saboda haka yace ta koma gidanta zuwa gobe zaizo ya samesu ita da hamid din yaji ta bakin kowa,saidai tana shiga ciki ta sanar da mommy gaskiya,ta kuwa dire tace ba inda diyarta zata koma,dakinta nada tasa aka bude aka share mata ta shige ciki,farinciki.kamar ta taka rawa,tana ganin nesa gab take da zuwa kusa,hankalinta kwance taci abinda ranta yakeso tayi kwanciyarta,sai a sannan take ganin me ya kaitama auren nan don Allaj,ashe rayuwar gidansu tafi dadi.
Qarfe takwas na daren ranar a cikin gidansu asma’u ta yiwa hamid gaban daddy,idanunshi cike fal da qwalla yake cewa daddy
“Jarrabawa ce ta fado mana,munci bashin banki mun siyi kaya suka nutse a ruwa,jirgin wancan satin da aka fada a labarai kusan rabi duka kayanmu ne,banki suka tasomu a gaba mu biya bashin da muka ci,daddy kasan sarai halinsu ba mutunci ko daga qafa,hakan ya sanya muka saida duk abinda muka mallaka nida daddy donmu rufawa kanm asiri muka biya,yau muka koma gidan da muka siya daddy bansan asma’u da gaske take ba zata zauna dani ba wai na zama talaka sai dana dawo na tadda bata gidan,ko hajiya bata yiwa sallama ba tayi ficewarta” ran daddy yayi matuqar baci,wato saboda raini daya ce ta koma gidan ma bata koma ba,waya ya dauka ya kira mummy yace ta turota,tana jin hakan tasan da walakin,saboda haka suka shirya dukkan abinda zata fada sannan ta iso falon
“Daddy….wallahi macuci ne,tun kafin sannan ya dauki dukkan kadarata ya saida min,yanzu haka bani da komai”
“Mijin naki kike kallan tsabar qwayar idanuna kike cewa macuci asma’u?” Daddy ya fada cikin bacin rai,saitayi laqwas data tuna barnar data tafka
“Ashe ke baki cikin matan dake rufawa mazajensu asiri idan babu ta samesu?,koma.meye ya saida nakin ina cewa shi ya malllaka miki shi ko?,idan kuma akwai wansa na mallaka miki shi bani na siya ba?,to na bar mishi har zuwa sanda Allah zai hore mishi ya musanya miki da wani,maza tun muna mu biyu ki tashi kibi mijinki,kiyi haquri sa samunshi da babu,wannan shine cikar mace ta gari” kuka take wiwi kamar ance ga ranar mutuwarta,hamid ya zame mata qarfen qafa kenan,bayan fitarta daddy ya dubeshi shima,yana sane da yadda yakema asma’un qanqamo saboda haka cikin hikima yamasa dan jan hankali
“Duk mutumin dake yalwatawa iyalinshi ba shakka zaka sameshi ko yaushe cikin budi shima da samu,Allah baya taba hanashi,saboda ma’aiki ya bamu labari cewa,ako da yaushe kullum ta Allah wasu mala’ikun Allah biyu na sauka,dayan yana cewa,ya Allah wanda yake ciyarwa ka ninka dukiyarshi,yayin da dayan yake cewa,ya Allah wanda yake riqe dukiyarshi baya ciyarwa ka hadashi da asara,zai iya yiwuwa sanadin quntatawa.iyali da qin yalwata musu Allah ya saukar maka da asara cikin dukiya,ya hana arziqinka ci gaba” sai yaji jikinsa yayi dam sanyi,don na wanda ke masa magana ta wannan sigar,sosai ya yiwa daddyn godiya,qimarshi ta dadu a idanunshi,wanda sanadiyyar haka yayi damarar gyarawa ko yaya ne,sa zasu tafin ya sallami asma’un da wasu kudin haka shima hamid,duk daba’a gaban asma’un ya bashi ba amma sai daya ji girman kan karba,sai kace wanda talauci ya kama?,yake gayawa.kansa,ni kuwa nace uhmm me kake ci na baka na zuba?,tukunna dai,haka ya dauketa tana bala’i da zumbure zumbure suka wuce.
Post a Comment for "Daurin Boye 55"