Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Daurin Boye 54

54

Duk wata juriyarta taji tana neman ta qare,saboda haka saita sauko ta soma zuba mishi abinci
“Sannu,ko zaka daure kaci wannan?” Kai ya girgiza mata yana bata hannunshi alamun ta taho



“Bashi nake buqata ba ke nake buqata….” Idanunta ta janye daga cikin nashi tana jin yadda zuciyarta ke zillo,tana addu’a cikin ranta,Allah ya sanya abinda take ji game da khalipha shima yana ji a kanta,Allah yasa yadda take fama da qaunarshi cikin zuciyarta shi dinma haka ne,tana tsaka da wannan tunanin ta tsinceshi zaune gefanta,yana gab da ita qwarai ta yadda har cinyoyinsu na gogar juna,hannunta ya laluba ya saka cikin nashi bayan ya fuskanceta sosai
“Uwaishah….bazan iya boyemiki abinda nake ji a kanki ba,wata iriyar qauna da banda anni ba wata diya mace da nake jin ina yiwa irinta,abun tamkar jarrabi,duk yadda naso na kauda shi abun ya ci tura,dukkanin qarfina ya qare akan kauda afkuwar abun don baki cikakkiyar dama,ina ganin tamkar idan naci gaba dajin haka a kanki kamar na cutar da damar da nace zan baki ne…kamar na karya alqawarin da nayi na cewa zan dauke ki ne tamkar qanwata…eh duk da cewa har yau ina ganin wasu dabi’un naki ina kuma kallonki kamar hajar din saboda kamanceceniyar dabi’unku,kunyi kama sosai ta wannan fannin….uwaishah….inaji a jikina kamar Allah ya aikomu cikin rayuwar juna ne saboda mu taimaki juna,saboda mu qaunaci junanmu,saboda kuma ya duba koken kowanne dayanmu,yaga cewa mu zamu fi kowa fuskantar yana yinmu da irin rayuwar da muke da buqata….uwaisha zuciyata ya soma qaunarki a wani lokaci da bansan yaushe bane,ban tantance hakan ba sai daga bisani,kota yaya nema humaira kin cancanci soyayya,kin tsallake dukkan wasu tarakuna dana d’ana,wanda mata da yawa suka gaza tsallakeshi,kinci jarabawar da mata bila’adadin suka kasa jumurin cinta,hakan kadai ya isa ya tabbatarmin da cewa kedin ta daban ce….humaira ina miqo qoqon barana da ki soni ki qaunace ni,bana son ki soni saboda wani abu na daban,bana son ki duba komai ko kice zaki soni saboda kaza,nafison ki soni saboda ni nidin khalipha,ina son ki soni saboda zuciyar taki tana sona bawai don wani dalili ba na daban,don Allah…..uwaish….ki soni,kiso khalipha”tuni hawaye ya jiqe mata fuskarta,ta kasa barin idanunta abude,yau wai ita aysha ake furtawa cewa ana sonta?,yau ita ake bayyanawa wasu kalamai da bata tsammanin samuwarsu ba cikin duniyarta?,ita akewa wannan matsanancin son?,wai yau itace mutum mai daraja kamar khalipha ke roqon ta soshi?,wace irin qauna haka khalipha ke mata a rayuwa?,koda bai roqi ta soshi ba tana ji jini da tsoka khalipha halittar da za’a sota ce,tana ji har cikin zuciya tuhi da gangar jikinta khalipha wani abu ne na musamman da Allah S W T ya ajewa rayuwarta ne,to waishinma idan bata so khalipha ba wa zata so a rayuwarta?,baisan cewa ta jima tana qaunarshi ba amma saita tsammaci saboda kyautata matan da yakene take jin haka akanshi?,son khalipha ya zame mata wajibi cikin rayuwarta haka take ji
“Pls uwaisha…..idan ban miki ba kika ce bakisona zan haqura don na cika alqawarinki…..saidai bani da tabbacin yadda rayywata zata kasance anan gaba….bansan ta yadda akai soyayya ta yimin shigar ba zata ba…..” Ya fada raunin da bata taba ji cikin muryarsa ba yau ta jishi muraran
“A duniya baya ga anni bana jin akwai wata halitta dake sonka sama dani…!”ta furta kalaman na fita daga cikin ruhi da zuciyarta.

“Ka cancanci dukkan wata soyayya ta diya mace,bawai don abinda ka shiga rayuwata ka yimin ba,a’ah dukkan nagartarka na tattare da kai kuma ita zata iya siya maka kowacce irin soyayya,ina qaunarka ya khalipha…..” Dukkanin idanunshi ya waro waje yana jin yadda zuciyarshi take qara bugawa da sauri da sauri wanda hakan ya qara tsananta ciwon kanshi,daga gefe daya kuma wani irin yanayin farinciki da baxai iya fasalta irinshi ba ya dinga sauka cikin zuciyarshi a hankali,sai ya sake matsawa jikinta sosai muryarshi na dan rawa
“Da gaske uwaishhhh….da gaske kina sona?” Kai ta gyada masa don tabbatar masa,saboda bakinta ya kasa cewa komai,itama bugun da zuciyarta yake ya sanya jikinta yi sanyi,baiyi wata wata ba ya rungumeta cikin jikinsa tsam,a cikin kunnenta yake rada mata saboda baya jin zai iya magana mai qarfi,ji yake kaman numfashinsa zai dauke,yana jin kamar kanshi zai rabe biyu
“Na….gode uwaishhh….na gode” abinda bakinsa ya dinga furtawa kenan tsahon wani lokaci ba tare daya barta ta bar jikinsa ba.

A hankali ta lura da yadda jijiyar kansa ke harbawa d’il d’il da yadda jikinsa ya dauki zafi,zare jikinta tayi cikin damuwa tana dubanshi,cikin wata murya mai laushi
“Ya khalipha……jikinka ya dauki zafi sosai,ciwon kan nan ya kamata ya barka haka,ya kamata kaje kaga likita,bakaci abinci ba tunda ka dawo?,na zuba maka abinci kaci don Allah kasha magani saika kwanta,wala’alla ka sake samun relief”
“Kece abincin kuma kece maganin gaba daya uwaishhhh,zamanki a jikina ya fiye min komai” ya fada yana bata hannunshi,batayi musu ba ta miqa masa yayi mata jagora zuwa jikinsa na sake rungumeta fiye da d’azu
“Rungume ni sosai uwaishaahh….sanyi nake ji” ya furta cikin rada,hannayenta ta sanya itama gaba daya ta zagayeshi da shi,duk da bai ratsashi ba amma hakan ya qara masa dumi a jikinsa yadda yakeso,shuru ne mai dadi ya ratsa dakin,wanda ya bawa dukka zukatan yin tunani mai kyau yadda ya kamata,ta tsakiyar shurun bacci ya shigo yayi awon gaba dasu gaba daya,wani bacci wanda ya zama na musamman a garesu ita dashi baki daya.

????????????????

Tara saura na safe tana tsaye cikin kyakkyawan kitchen din tana shirya musu breakfast,kusan mintuna ashirin kenan data sato jiki ta fito ta barshi a cikin daki,aikinta take hankali kwance tana yi tana sake kallon kitchen din,ko ina cikin gidan mai kyau ne,iya bedroom din kawai zuwa kitchen data gani ya tafi da ita sosai,komai ya tsaru yadda ya kamata,kana kallo kasan aikin masu ilimi ne.

A qalla ya dauki mintuna goma tsaye yana morewa kallonta,karon farko da yaga ayshan sosai,cikakkiyar mace wadda Allah yayiwa baiwar kyau sura da diri,yadda yake ganin dabi’unta kyawawa masu kyau haka Allah ya kyautata halittarta,yana son ya isa gareta ya rungumeta cikin jikinsa suyi aikin tare,saidai kuma ya tabbatar idan yayi hakan dukkan wani lissafinsa da yake qoqarin tattarawa zai ruguje ne,hakanan zai kasa cika muradi da alqawarin da ya dauka ma ranshi,wani alqawari da yake fatan Allah ya cika mishi shi nan kusa,duk da haka sai ya gaza daurewa,ya saki hannayenshi ya soma takawa cikin sanda har ya isa bayanta dab da ita,caraf yayi ya ruqo qugunta sannan ya dan karata a jikinsa yana cewa
“Assalamu alaiki” ba qaramin firgita tayi ba wanda har yasa ta kusa yin bari,saidai Allah ya tsare farantan gabanta ne guda biyu kawai na roba suka biyota,sallamarsa ita ta sanya mata nutsuwa,ta sauke gauruwar ajiyar zuciya,dariya ya dinga mata mai kama da murmushi bayan ya juyo da ita yana duban qwayar idanunta,sai ya tuna sanda ta shiga bandaki ta kulle kanta,yana qoqarin biye dariyarshi yace
“Ba shakka uwaisha tah gwanar tsoro ce,na manta sanda aka gudu bandaki ana nada haquri fa” ya fada yana kashe mata ido daya,murmushin daya qawata fuskarta ta saki tana dan cije lebanta,tana son ta rama tana dan jin nauyinshi,sai kawai tadan saka tafin hannunta ta bugu qirjinsa kadan
“Wash!” Ya fada yana saka hannun nasa yana dafe inda ta doka din,cikin zaro ido tace
“Lafiya meya faru?”
“Zuciyata” ya fada yana narkewa gami da zuba mata narkakkun idanunshi da suka zame mata kamar dabaibayi,cikin qarfin hali tace
“Me ya sameta?”
“Kin mata rauni bad’ini shine zaki sake mata wani a zahiri” murmushi ne ya subuce mata,saita dan taka kadan ta hade tazarar dake tsakinsu,
“Ni bakasan tawa zuciyar ta zama raurananniya ba kake son sake razana ta?”bakinta saitin wuyanshi take maganar,yadda hucin numfashinta dana bakinta yake sauka saman wuyan nashi,lumshe ido yayi tsigar jikinsa na tashi,ajiyar zuciya ya sauke ya bude idon nashi,sai sannan ya lura data janye daga yadda ta tsaya dazu,kamota ya sakeyi gab dashi sosai suka soma musayar numfashi,idanunshi cikin nata suna kallon juna na wani lokaci,da sauri ya saketa yana maida numfashi gami da qoqarin yiwa kanshi linzami da saiti,aikinta taci gaba da qoqarin ci gaba dayi saidai ta lura ta soma hada shirme.

Dariya ya dan saki yana tsaye bayanta yana kallonta bayan ya gama samo nutsuwarshi,ya gama karantarta tsaf,saidai dole dukansu su jira lokaci,hannunta ya riqe da sauri
” yi haquri madam,wallahi kika zuba wannan abincin bazai ciwu ba yau kam”sai a sannan ta dubi abinda take,gishiri ne ta ciko cokali dashi zata zuba cikin qwan da baifi hudu ba,saita sakar masa cokalin gishirin kunya tana kamata
“Nikam.bansan ma waya cs miki ki taso kibar aikinki ba ki barni ina jin sanyi kizo dora abinci,mu tafi kawai an yafe miki” ya fada yana shirin kama hannunta,saita langwabar da kai a narke tana cewa
“Pls ya khalipha….na kusa gamawa,ka bari na qarasa idan ba haka ba zai zama asara,abincin jiya da darema saidai abadashi Allah yasa ma ba mai yawa bane”
“Kai…gsky to matsa na tayaki ki qarasa,wannan muryar bazan iya tafiya nabar mai ita ba” dariya yaso bata,haka ya iya soyayya?,dama haka masoya suke ji cikin zukatansu?,haka ya tsaya daga bayanta yana tayata qananun abinda zai iya,duk da kusan wayo yayi mata morewa kallonta kawai yake,idan ya kasa daurewa yadan matsa kadan ya rage zafi da haka suka kammala komai tare.

Wani irin wuni ranar sukayi tare da juna yana sake bayyana mata kanshi,hakanan itama,kowanne na sake jin dan uwanshi cikin niki da zuciyarshi,so yake ya cire mata dukkan wata kunya tashi da nauyinsa,ya gaya mata soyayya yake da buqatar ta nuna mishi zalla babu algus,qunahe qunahe ko ‘yar kunya,yana son ta zama shi ya zama ita,yana son su zama sirrin juna kamar yadda Allah S W T ya fada cewa
_”Su(mata)tafafi ne a gareku,haka kuma(maza)taufafi ne a garesu”_ hatta da wayoyinshi duka a kulle suke,bai bude ba sai bayan sallar la’asar,mahmoud ne mutum na farko daya soma kiranshi
“Haba haba boss,ya za’ayita nemanka amma a rasa ka?,ka bace sama da qasa” murmushi ya saki idanunsa na kan aysha dake hada masa system dinshi
“Kai mahmoud,na gaji wallahi,daga dawowata?,ina buqatar na huta shi yasa,zan hau yanzu zan duba dukkanin saqonnin”
“Alright….mutumin nan fa ya matsa min daga jiya zuwa yau?”
“Wa fa?” Khaliphan ya tambaya
“Alj kutama mana” dogon tsaki yaja
“Rabu dashi don Allah,mutumin banza,ya bani mamaki wallahi,irinsu ne ke amfani da damar da Allah ya basu suke ruguza rayuwar matasanmu ta hanyar shigo da miyagun qwayoyi,bazan qyaleshi ba mahmoud saiya d’an d’ana kudarshi,sai ya dawomin da dukka kudade na cikin kwana uku”
“Banga laifinka ba,koni iya mutuncin da zan iyayi masa kenan,sam mutane basa yiwa kansu da rayuwarsu adalci,ta yayaAllah xai albarkaci bayan irin wadannan?”
“Ka gani” cewar khalipha yana jan tsaki,nan suka kammala tattaunawarsu kafin suyi sallama daga bisani.

Kwanansu uku cikin gidan yana koya mata wani darasi mai wuyar mantawa,wata wutar qaunarshi yake rura mata azuciyarta,soyayya mai tsayawa a rai,tamkar zata zauce wani lokaci haka take ji,yasan dukkan wani salo da matakan gina soyayya cikin zuciyar abokin rayuwa,badon yajin aiki daya ratso musu suke zaune a gida ba ta tabbata mawuyacine taci gaba da fahimtar karatu idan ta koma makaranta,duk wannan abun khalipha na baya baya ne saboda komai ya tafi dai dai da plan dinsa.

Cikon kwana na hudun da wani yammaci tana kitchen tana hadawa khalipha salad,ta baroshi a falo yana kwance yana hutawa,wanda da qyar ya yarda ya zauna don cewa yayi sai yazo ya tayata,tayi kyau qwarai cikin wani lace mai kyau daya zaba mata yau yace shi zata sanya mishi,ba zafi yau garin sai hadarin daya hado,ruwa bai samu sauka ba saiya juye yake bada wata iska mai sanyi da dadi,haka yake kullum a rana sai tayi masa kwalliya uku hudu,bata masa qasa da hala,ta fuskanci mutum ne shi maison mace mai ado,sai Allah yasa ra’ayin nasu ya kusan zuwa daya,ko a baya rashin sukunin rayuwa ne yake hanata kwallia,a yanzu kam duk wanda yasanta ya santa da ado,abin ya mata dai dai,sao kawai ta baje kolin kwalliyarta so ranta.

Tunda ta fito a kitchen din ya zuba mata ido yana kallonta,kullum sabuwa take a wajensa,kullum tayi masa ado sai yaga na yanzu yafi na dazu kyau,sai yaga kamar bai taba ganin kwalliya iri tata ba,tana isowa kusa dashi ta aje tray din hannunta saman teburin gabanshi,batakai ga gama ajewar ba ya miqe ya zauna sosai yana murza ido,murmushi ta saki,tasan da walakin tana fiddo idanunta waje tace
“Uhmmm…”
“Ji nake kamar na hadiyeki na huta wallahi,kinga indai hakan ta faru ba wanda ya isa ya sake ganinki saini kadai” murmushi ta saki mai taushi,harga Allah kalaman khalipha ko da yaushe na sake dilmiyata ne cikin kogin qaunarshi,koda yashe kalamansa na sake nuna mata itama cikakkiyar macace wadda ta cancanci taso kuma a sota
“Ina godewa Allah koda yaushe daya qaddara zaka wanzu cikin rayuwata” shima murmushi yake mata,yana jin kaman ya janyota jikinss,saidai yana tsoron kada qiluta jawo bau,duk da yana fata komai yazo qarshe,saiya daga pillow din kujerar da yayi matashin kai dashi,ya ciro passport ya buda sannan ya miqa mata,hannu ta saka ta amsa,gabanta na faduwa zuciyarta na dukan uku uku,addu’a take Allah dai yasa ba cewa zaiyi zai koma ba,idanunta takai kai,visa ce ta shiga qasar saudiyya,wadda bata kowa bace face tata,idanu ta fiddo zuciyarta kamar zata fito,babban burinta a duniya?,mafarkinta ne zai zama gaskiya koko dai?,kai ta daga tana dubanshi da alamun tambaya,shima ya tattara dukkan hankalinsa da nutsuwarshi akanta,farinciki na ratsashi sakamakon farincikin daya sanyata a ciki
“Ya khalipha….da gaske?” Kai ya jinjina mata
“Da gaske ne uwaishata,rana ita yau in sha Allahu zamu tafi,kije ki gayawa Allah dukkan matsalolinki da damuwarki tsakaninki dashi,sannan mu roqawa kanmu samun dukkan wata rayuwa ta farinciki da ma’aurata kewa kansu fata,ya bamu zuriyya ta gari,yasa zamu fara rayuwarmu a sa’a” rungume passport din kawai tayi a qirjinta ruwan hawaye na bin kuncinta,abinda bata taba tsammatarsa ba cikin rayuwarta,dubanshi kawai take ta rasa bakin magana,idan ta bude baki ma me zata mishi?,dukkan wata kalma da zata fada ya riga daya saba jinta,walau a bakinta ko a bakunan al’umma,ya fahimci haka,saboda haka saiya ware mata dukkan hannayenshi alamar ta taho,ba taba lokaci kuwa ta kwasa zuwa gareshi ta zube a jikinsa tana sheshsheqar kuka,hannunshi ya sanya ya zame dankwalinta wanda tun dazu dama yaso zamewar ta hanashi,ya dinga shafar gashin kanta kawai yana shaqar qamshin jikinta,ganin ta kasa shuru sai ya soma rada mata
“So kike ki fasamin zuciyata kenan” idanunta dage jiqe da hawaye ta dago ta dubeshi dasu,saiya kanne mata ido daya yana murmushi
“Eh mana,kinsan abu mafi muni da kunnuwana zasu ji shine sautin kukanki?” Jin yace haka saitayi qoqarin hadiye kukan,ta kwantar da kanta saman qirjinsa tana goge hawayenta
“Na rasa me zance maka ne,na rasa me zanyi,dukkan wata kalma da zan fada gani nake bata gamsar ba,ka zamemin fitila a rayuwata,ka zamarmin haske mai kore duhu,kai daya ka bani farinciki da daruruwan mutane suka kasa bani,dame zan saka maka nikuwa aysha bayan bani da komai ban mallaki komai ba”
“Ke kike da komai,kuma kece kika mallaki komai” saitayi shuru tana sauraronsa gami da tunanin abinda yace
“Zuciyarki rayuwarki da gangar jikinki nakeso ki mallakamin,ki bani dukkan wata yardarki,ki soni ki qaunaceni,kici gaba kuma da sona domin Allah kamar yadda kikayi a baya” cikin sanyi da kwantar da murya tace
“Indai wannan ne ka gama samunshi har gaban abada”
“Kinyi alqawari?” Saita zauna sosai tana dubanshi cikin ido,wanda hakan ya sanyashi shima gyara zamanshi yana dubanta
“Duk duniya babu wanda ya cancanci samun wannan matsayin sama dakai,idan ma akwaishi bana fatan Allah ya nuna minshi har abada,zan rayu dakai cikin kowanne irin yanayi,bana fata na saba maka dai dai da rana guda kona sauya maka matsayi daga wanda na doraka akai a yanzu,idan wannan yana cikin qaddarata shima ina roqon Allah ya dauki raina kafin lokacin” wani murmushi ya saki,yana jin wani farinciki na ratsashi,tabbas baiyi wuyar banza ba,addu’a bata faduwa qasa banza,hakanan dama Allah yake lamarinshi,haka ya fada cikin qur’aninsa _sau da yawa zaku qi abu amma alkhairi ne a tare daku_ gashinan tabbas hakan ya tabbata a kanshi,saitin zuciyarshi ya dafe da d’aya hannun nasa
“Karki kasheni ni mana tun yanzu,idan kika mutu uwaisha in zauna dawa?” Yadda yayin ya bata dariya,saita saki murmushi mai sauti tana dubanshi sanda yake cusa hannunshi cikin aljihun wandonshi ya ciro wani dan qaramin akwati mai kyau,tana kallonshi ya bude,ya ciro wata nannadaddiyar dubu daya da aka yiwa ninki mai kyau,saiya dagata yana dubanta sannan ya dubi ayshan
“Kin tuna wannan?” Kudin hannun nashi sosai ta kalla kana ta dubeshi tana dan tabe baki gami da girgiza kai,wani kishi take ji yana dan sukarta,tana tunanin ko wata budurwarshi ce ta bashi?,murmushi ya saki yana maidata ciki sannan ya dubi ayshan
“Tun daga ranar da kika bada ita a matsayin biyan bashi a gareni na tabbatar da cewa akwai banbanci mai tarin gaske tsakaninki da asma’u,sannan akwai wata boyayyar halayya da baiwa da kike da ita data sha banban data sauran mata,yau bari na baki labarin da baki sani ba” daiya gyara zamanshi yana daukar cup din coffen data zuba mishi ya kurba,sannan ya soma bata labarin dukkan ‘yammatan daya tabayi da yadda suka qarke dasu,mamaki.ne ya kama ayaha,tsoron duniya da mutanen cikinta ya sake kamata,kowa ya lalace?,kowa mai kudi yakeso?,idan a familynka ne sai.kana dashi kake sa wata babbar daraja?,idan saurayine kai ko qur’ani kake hadiya saboda sanin Allah da tsoronshi ba mai baka aure idan baka tara koka aje ba koda kana da sana’ar rufawa kai asiri?,wannan wacce iriyar rayuwace mukeyi?,tunaninta ya katse mata sanda ya tura mata system dinshi gabanta yace
“Duba” ba musu taja ta soma dubawa,order ne da yayi mata daga store na rahamalls wanda tuni suka iso,har an bude katafaren wajen siyayya gashinan da hotunansu an tsara komai dauke da sunan UWAISHAH MALL
“Duk abinda kika gani a nan naki ne humairah ke na tanadarwa,na yiwa kaina wannan alqawarin tunda dadewa bawai yanzu ba,nayi alqawarin ninka miki dubu dayanki tun ba yanzu ba,wannan shine tukuicin da nayi niyyar yi miki a matsayin taimakon da kika yimin sanda ake bina bashin dari biyar kika sadaukar min da dubu daya duk da bakisan waye ba ni” kasa magana tayi wannan karonma,sai ta rufe bakinta kawai da tafukan hannayenta,kai ya girgiza yana jifanta da tattausan murmushinsa
“Karki ce komai,don bana buqata,na riga dana gaya miki abinda nake da buqata” ya fada yana ware hannayenshi,sai kawai ta rungumeshi tana sakin kuka.

 

Tafe suke a motarshi saidai kana duban fuskarta kasan tsantsar baqinciki da bacin rai ke cinta,a yanzu ba abinda ta tsana irin auren hamid,neman kawai hanyar da zata yakiceshi take,saidai ta lura da idan natayi takatsantsan ba haqarta ba zata taba cimma ruwa ba.

Daga barkar haihuwa suke wanda ita sam batasan ma wadda suka jewa barkar ba,saidai ta cika da mamakin uban kayan da hamid ya siya din yakai,dama shidin ba dai neman suna da son burgewa da gwaninta ba,tunda sukayi aure bai taba yi mata siyayya irin hakan ba,sai gashi yayi ya kaiwa wasu,dai dai nan wayarshi ta dauki kuwwa,ganin kiran babanshi ne ya sanyashi dagawa,bayanin da daddyn nashi yayi masa ya daga masa hankali qwarai,ya tabbatar cewa gagarumar matsala ce take fuskantosu
“Yanzu daddy meye mafita?,ya zamuyi?”
“Ya kamata mu soma dakatar dashi,yanzu haka ancemin yana gidansa,idan kana kusa ka sameni nan titin lodge road saimu qarasa mu bashi haquri,ko qafa ne muce ya daga mana sai muyi tunanin abinda zamuyi a dan taqin”
“Shikenan daddy ganinan zuwa yanzu,ina kundila amma bari na qaraso”

*_wanan littafin na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki tura,ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number_*

08030811300

*mrs muhammad ce*??

Post a Comment for "Daurin Boye 54"