Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Cuta ta Dau Cuta 12

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na goma sha biyu_


 

……….Tafe take cikin nutsuwarta tamkar wadda ke tsoron taka ƙasar. Hijjab ne a jikinta har ƙasa fari tas. Idanunta da siririn farin gilashi da kasancewarsa bai hana bayyanar ƙyawun idanunta da girmansu ba gamai kallo. Sam bata da alamar hayaniya akan fuska, sannan da ga ganinta kasan bata da yawan magana akwai kuma kunya da tarbiyya tattare da ita.
“Woow! Ya arrahaman kaga wata halitta!”. SJ ya faɗa. Da ga JJ har MB ɗagowa sukai suka kallesa. Dan su hankulansu nakan wayar JJ ne suna kallon hotunan da suka ɗauka a wajen idi. Maimakon magana ita ya nuna musu da yatsa, dan harta gotasu kaɗan. Su dukansu babu wanda zuciyarsa bata harba ba, sai dai kafin su farga har JJ ya zabura zumutt, tamkar ƙyaftawar ido sai gashi a gabanta.
“Assalamu alaikum ƙyaƙyƙyawa”. Ya faɗa cikin wani irin murya mai taushi da amo. Ko kallonsa batai ba, sai dai ta motsa jajayen ƙananun laɓɓanta da babu komai a kansu sai lips gloss alamar amsa masa sallamarsa batare da yaji sautin muryarta ba. Rabashi tai ta wuce, kafin ya zabura ta buɗe wani farin gate dake gab da su ta shige abinta. Kansa ya dafe cike da takaicin kansa da kansa. Yayinda MB da SJ ke faman masa dariyar ƙeta. Yana tsaye a wajen suka ƙaraso suna cigaba da dariyarsu. SJ ya ce, “Tuku-tuku mugun icce! daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi. Banda ma cin amanar abota nifa na fara ganin yarinyar nan amma ka zabura kamar wani kafilfilo kazo kamun yankan baya. To sai ka kama kanka ai dan wannan fa ba irin motocin titi bace ba”.
Harararsa JJ ya ɗan yi, batare da yace komai ba yaja guntun tsaki ya barsu wajen. Inda motarsu ke ajiye ya dawo, ya jingina cike da damuwa yana mai lumshe idanunsa. Sake biyosa su MB sukai nan ma suna dariya, har sai da ya ƙufula ya shige mota. Ganin zai tada suka shige suma, dan kaɗan daga aikinsa ya tafi ya barsu a wajen duk da kuwa motar tasu ce su uku, dan tare suka haɗa kuɗu suka saya dan kawai burge ƴammata.
A hankali JJ ke murza steering fuskar yarinyar na masa waiwayi a cikin idanu, ko sau ɗaya ya gagara saka baki a zancen su MB har sai da yaji SJ ya ce, “Ai inaga fa Gwaggo Ladi na mutunci da mutanen gidan, dan ina ƙyautata zaton ko abincin data bamu take faɗin daga maƙotan can natane masu farin gate to daga gidanne kuwa”.
ƙuwww!! Kake ji JJ ya taka birki. Har sai da sukai gaba su duka suka bigi jikin motar. MB dake baya ya dafe goshinsa yana murzawa a hasale ya ce, “JJ halan kana hauka ne nikam? Yanzu dan ALLAH saboda mace kake neman kashemu a ranar salla”. Shima dai SJ masifar ya balbalesa da shi, amma a mamakinsu ko’a jikin JJ, sai ma ƙoƙarin gangarawa gefen titi da yay saboda yanda ake masa horn ya tsarema mutane hanya.
“Wai lafiya kake kuwa?”. MJ ya sake tambaya a ƙufule. Kai JJ ya girgiza musu a karo na farko. Muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Gidan Gwaggo zamu koma dan ALLAH”.
Kallon juna MB da SJ sukayi. Sai kuma suka kwashe da dariyar shaƙiyanci. JJ bai damu ba, da kuma kafiya-lafiyane masifa zai fara musu. Suna ji suna gani ya karya kan mota suka koma gidan Gwaggo Ladi. Shi ya fara fita a motar ya nufi gidan, dan ba baƙonsu bane ba kasancewar sun saba zuwa duk salla. Wani irin zuzuzu JJ yaji sakamakon yin tozali da yarinyar nan zaune a tsakar gidan Gwaggo tana cin abinci. Fuskarta ƙawace da wani irin murmushi da ya sake fiddo ƙyawunta.
“Jazool kunyi mantuwa ne?”.
Gwaggo data farga da shi ta faɗa. Cikin sauri yarinyar ta ɗago kanta, dan sam ita ba ƙofa take kallo ba. Idanu ta waro, sai kuma ta fisgi hijjab ɗinta dake saman jarkar ruwa a gefe ta shiga kiciniyar sakawa. A dai-dai nan su MB suka shigo suna dariya. Suma turus sukai da ganin yarinyar, sai kuma suka wayance tare da kamo hannun JJ da yay sumar tsaye baima amsama Gwaggo Ladi tambayarta ba. Shigewar yarinyar falon Gwaggo ya Bama SJ damar matsawa kusa da Gwaggo yana ƴar dariya. “Gwaggo ɗanki fa yay gamo, dan yarinyar nan fa ta dawo damu”.
Da mamaki Gwaggo Ladi ta dubi hanyar falonta, sai kuma ta juyo ta kalla Sj. “Wai Anoosh?!”.
“Wannan dai data shiga falonki yanzu. In dai sunanta kenan to ita”. Tsaff ya kwashe komai ya sanarma Gwaggo. Murmushi Gwaggo keyi tana kallon JJ. Sai kuma ta kamo hannunsa ta zaunar kusa da ita. “Kaga kwantar da hankalinka Jazool. In dai Anoosh ce da yardar ALLAH ka samu kuwa. Na kuma tayaka murna dan yarinya ce mai tarbiyya da hankali. Sai dai bebiya ce dan bata magana amma tana ji. Tana kuma iya baka amsar da zaka iya fahimta ta motsin laɓɓanta. Zanfi kowa farin ciki da wannan al’amarin kuwa”.
Ba JJ ba hatta su MB kallon Gwaggo suke jin wai Anoosh bebiya ce. Sai dai a cikinsu babu wanda yace komai. Gwaggo da bata lura da yanayin nasu ba ta ɗaga baki ta kira Anoosh dake cikin falo. Kusan mintinan biyu sai gata ta fito tana rabe-raɓe. Fuskar Gwaggo da murmushi ta nuna mata su JJ. “Anoosh waɗan nan ƴaƴana ne, sun zo min gaisuwar salla ne”.
Jin jina kai Anoosh da idanunta ke ƙasa cikin gilashi tayi, sai kuma ta motsa ƙyawawan lips ɗinta a hankali alamar gaisuwa a garesu. Gwaggo ce ta sanar dasu tana gaishesu, cikin rawar lips suka amsa su duka, JJ kam yama kasa sai kallonta da yake kamar idanunsa zasu zubo ƙasa……

____________★

Wani irin shurinta yay da ƙafa tare da cilla mata mayafi yace, “Tashi dan …” ya mulmula mata ashariya. Ganin bata da niyyar tashi yay wani irin fisgarta tana tirjewa yana janta kamar wata dabba har waje. Kasancewar anguwar babu wuta gashi wata yay nisa ya buɗe motarsa ya cillata baya ya rufe. Gidan ya kulle shima ya zagaya mazaunin driver yaja motar a fisge. Har suka iso katafaren gidan Khadijah na kuka. Maigadi ya wangale musu gate ya shige. Koda ya fito nan ɗin ma janta yay zuwa ciki kamar abar banza, a wani haɗaɗɗen falo ya shigo da ita, ɗaki na farkon shigowa ya buɗe ya cillata ciki ya maida ƙofar ya kulle ya wucewarsa sama abinsa…

Gaba ɗaya kukan da take ya tsaya cak saboda azabar wahalar buguwar da kanta yayi da gado a dalilin wullota da Dafeeq yayi. Tuni goshinta ya fara ɗigar da jini saboda fashewar da yayi. Kwanciya kawai tai yaraf tana sauke wasu irin ajiyar zuciya kamar wadda numfashinta ke barin gangar jikinta. Kafin dogon lokaci jikinta ya ɗime da zazzaɓi mai zafin tsiya. Gab-gab ta fara rawar ɗari saboda ac dake aiki a ɗakin. Tana kwance a cikin wannan wahalar take jin shigowar motoci da guɗe-guɗe alamar yanzu ne ma ake kawo amaryar. Zuwa can taji sun shigo falon. Yanda suke shewa da arerewa yasata fahimtar bama su da yawa ƴan rakkiyar amaryar. Zuwa can taji kiɗa ya fara tashi, sai kuma ta jiyosu suna ihu da shewar ango-ango. Hakan ya tabbatar mata da Dafeeq ne yaje inda suke kenan, da alama ma rawa yake shi da amarya kamar yanda take ji a kalamansu. Kusan awa biyu da wasu mintinan suka ɗauka a gidan, dan sai sha ɗaya taji gidan ya ɗauki shiru. Daga haka bata sake jin motsin kowa ba har dare ya raba tana dai kwance a wajen jinin dake ɗiga a goshinta ya fara rinjayar idanunta alamar jiri…

A ɓangaren amarya Kainaat da ango Dafeeq kam bayan wucewar ƙawayenta su Nadwa cak ya ɗagata daga tsakkiyar falon cikin kuɗin da suka musu liƙi yay sama da ita. Dan Kainaat dai bata da jiki sosai can, amma fa a murjenta take suɓul-duɓul kamar alalar gwangwani. Kai tsaye ɗakinsa ya wuce da ita suna faman sakarma juna murmushi, ya direta a tsakkiyar gadon yana hakki, dan duk da bata da ƙiba tanada nauyi, ƙarfin haline kawai da son ya birgeta ya sashi jurewa har ya kawota nan. Haƙuri ya bata akan bari yaje ya ɗakko wayoyinsu. Ta jinjina masa kai tana murmushi. Gudu-gudu sauri-sauri ya dawo falon, sai da ya waiga bayansa ya tabbatar Hajiya bata biyosa ba sannan ya durƙusa ya tattare dollars ɗin da ƙawayenta suka musu liƙin da ƴan dubu-dubu sabbi ƙal. Taf ya cika hularsa harda dannawa da ƙyar, bakinsa a washe dan yasan waɗan nan kuɗin ba ƙaramin kuɗi bane ba. Wayarsa da tata dake a Centre table ya ɗauka ya koma saman bayan ya kashe fitulin falon da kwasar ledojin kayan sayen baki. Da dabara ya zira hannu daga waje ya kashe wutar ɗakin sannan ya shiga, kai tsaye gaban gadon yaje ya tura hularsa mai ɗauke da kudin nan ƙarƙashin gadon sannan ya ajiye sauran kayan yana ƴar dariya da faɗin wasu maganganu wa hajiyar tashi irin shi ya kashe fitilar ne duk a cikin soyayya. Kainaat bata damu ba, dan itama dai zuciyarta ta tafi wajen tunanin ta yanda zata zille masa ne. Sai da ya gama ɓoye kudinsa da ƙyau ya kunna fitilar…

Anci ansha tsakanin amarya da ango. Sannan ya buƙaci suyi salla. Kai tsaye tace masa tana period. Ƙarara taga damuwa a fuskarsa, a ranta tace shege ai maganinka zanyi, dan daga gani mayen yaro za’ai anan. Suna haɗa ido ta sakar masa murmushi, shima dai mayar mata yayi cikin yaƙe. Jiki babu laka ya tashi ya canja kayansa zuwa na barci, itama yaje ɗakinta ya ɗakko mata. Amsa tai ta shiga bayi ta canja, bata fito ba sai da ta turama Abaan saƙo kamar yanda ta saba a kullum naban haƙuri da good night. Koda ta fito bata kula Dafeeq ba ta kwanta, dan zuciyarta ta tafi wajen Abaan ne kamar yanda ta saba a kowane dare bata iya barci sai da tunaninsa, mafarkinsa shine abin yinta a kullum kuma. Babu zato babu tsammani taji Dafeeq a jikinta, hankalinta ne ya tashi, ta shiga son turesa, amma ya tabbatar mata shifa ko rage zafine sai yayi gaskiya. Bataƙi ba anan, dan koba komai tana kewar abokin rayuwarta, musamman daya kasance ita bata iskanci ko’a yanzun.
Dafeeq shegen yaro ne, dan sai da yay yanda yay ya shagaltar da Kainaat har ya binciketa yaji babu wani period da takeyi batare data fargaba sai jinsa tai yana ƙoƙarin kai hari. Hankalinta ya tashi matuƙa, ta shiga turesa amma ya nuna mata shi sabon jinine, sannan ƙarfi ba’a shekaru yake ba, namiji kuma duk ƙankantarsa dai sunansa namiji…

★ Busowar iskar asuba mai sanyi da ni’ima ta farfaɗo da Khadijah. A hankali ta shiga buɗe idanunta tana karanto addu’a. Ganinta ba’a ɗakinta take ba ya sata maida idanunta ta rumtse komai na dawo mata dalla-dalla. Hawayene suka shiga sakko mata, itafa har yanzu kallon komai take kamar almara. Sannan wani gefe na zuciyarta na tabbatar mata Dafeeq ɗinta baya cikin hayyacinsa. Dole ne matar nan asiri ta masa. Ɗari bisa ɗari ta yarda da wannan tunanin, dan haka ta yinƙura ta tashi da ƙyar. Goshinta ta shafa, jinin ya tsaya, sai dai wajen ya mata nauyi kuma yana mata raɗaɗi. Mikewa tai gaba ɗayanta cikin ƙarfin hali ta nufi bayi. Bata damu da kallon ko’ina ba dan komai baya birgeta a gidan duk da ita kanta tasan ya haɗu. Ta jima tana kallon kanta a madubi kafin ta wanke busashen jinin goshinta zuwa fuska. Ashema raunin da taji ba wani babba bane can sosai. Alwala tayo tazo tai sallar asuba. Daga haka ta jingina da gado ta fara rera kuka, sai da taji kanta na barazanar tarwatsewa sannan ta haƙura. Har rana ta hasko windown ɗakin bataji motsin kowa na gidan ba, ga shi ya kulleta ta baya, dole ta haƙura ta zubama sarautar UBANGIJI ido kawai…….✍️

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Post a Comment for "Cuta ta Dau Cuta 12"