Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Bamagujiya 27-28

BMGJY 27-28
_Masu buÆ™atar a tallata musu hajojinsu ku yimin mgn cikin farashi me sauÆ™i_

_Haramun ne a juyamin wannan labarin ta kowacce siga ko a karantamin shi a YouTube channel_


_Alhmdllh daga wannan Page ɗin na gama happy sallah duk me so saiya bi hanyoyin dake ƙasa ya biya ya karanta cikin aminci_

 

_Don ci gaba da karanta wannan littafin ki biya ta 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank, ko hoton kati MTN ta WhatsApp number 09013718241 idan a Niger kike zaki tura katin Airtel na 400CF ta wannan number +227 95 04 58 22 sai kiyi screenshot ki turomin nasaki a group._

_Please don Allah kiyi hÆ™r idan baki shirya ba karki min min kiga kamar na wulaÆ™antaki wallahi ba wulaÆ™anci bane mutanen ne da yawa very important nake bawa attention in littafi kikeso 300 Spcl 700 evidence of payment kawai ya wadatar idan talla kikeso page 1k status 500 per day_

★★★~~~★★★~~~★★★

 

Kama hannunta Rasheedah tayi ta zaunar da ita itama ta zauna tace “Amma meye yasa aurenku ya zama a haka meye alfanun É“oyewar?” Kawar dakai tayi tace “Wani sirri ne daban idan lkcn sanin yayi zaki sani saidai Nima banason wannan yanayin kawai dai naji na karÉ“a nayi biyayya ne badon son raina ba sai dan hakan shine ya dace da nayi”
Daga haka ta miÆ™e ta nufi bathroom wannan ta tabbatar wa da Rasheedah Beebah bazata Æ™ara cewa komai ba, ruwa ta watsa ta fito lkcn bakwai na dare ta ishe Æ´ammatan sun shirya suna jiranta a É—akin Khalisa tace “Haba kekuwa Beebah kinsan takwas da rabi zamu tashi amma kinyi bulunbuÆ™wi a É—aki ko tunanin kada mu makara bakiyi” lumshe idanuwanta tayi ta É—auki kayanta tasa ta tayar da sallah bayan ta idar ne ta dubesu tace “Afwan nafa É—an shiga yanayi ne muje waye zai kaimu airport É—in?” Haushi bai bar Khalisa ta bata amsa ba tayi ficewarta itama tabi bayanta Hudah na cewa.
“Waini gurÉ—ewa kikayi a Æ™afarki ne naga bata takuwa sosai?” Itadai bata bata amsa ba tayi ficewarta suka shiga Mota Kilishi nayi musu fatan alkhairi suka wucce airport Beebah Zuciyarta tab tunanin Hero É—inta shima yanzu haka yana can yana keta gajimare.

 

Da wannan tunanin suka isa airport É—in duk wani abu da akeyi akayi musu sukayi zaman jiran cikar lkc sannan jirginsu ya É—aga zuwa birnin Jidda, tunda suka taho kanta ke juyawa har suka sauka Ita dai Æ´ar kallo ta zama har sukaje masauki ta rage kayanta ta kwanta gajiya ta rashin sabon doguwar tafiya na tambayar jikinta.
Sun kwanta sun huta gajiya sosai kafin Hudah ta fara tashinsu tana cewa “Ku tashi kuyi sahur kada ku makara” Khalisa ce ta fara tashi sannan Beebah suka É—auro alwala sukayi sahur É—in duk jin abin takeyi bawai, karonta na farko a rayuwarta da zatayi azumi, bayan sun nutsa ne sukayi raka’atainul fajri suka gabatar da asuba sannan suka sake kwanciya bacci me nauyi sukayi har wajen azahar sannan suka tashi sukayi wanka suka nutsa cikin garin Beebah ta zama Æ´ar kallo koda sukaje shop na abubuwan da zasu buÆ™ata komai sune suka É—aukar mata tana gefe manne da waya tana waya da Hero É—inta tanata dariya sukan banda kallonta babu abinda sukeyi suna mamakin yanda yanayinta ke nuna nutsuwarta da wanda take wayar dashi.

 

Koda taga sun nufota saita kashe wayar babu wanda ya tambayeta domin sunsan ko sun tambayeta ba amsa zata basu ba saidai tayi murmushi ta basar dasu.
Cikin kwanakin ibadar da sukayi a ƙasar Saudiyya Hudah da Khalisa sunji daɗinsu Ita ko tunda sukayi sati biyu ta fara rasa walwalarta saboda wani irin yanayi da ya sarketa bacci da kasala su kansu abokan tafiyar tata Saida abin ya fara damunsu ganin ko masallaci sukaje wani lkcn saidai in sun gama abinda zasuyi su tasheta.
Satinsu uku a Saudiyya suka wucce Dubai tunda sukaje Dubai kullum yanayinta Æ™ara ta’azzara yakeyi ko abinci bata iya cin na kirki da suka gaji ne suka shirya domin zuwa suga likita batare da tunanin komai ba saboda Æ™uruciya zuciyarta bata taÉ“a kawo mata komai ba ta.
Haka ta rinƙa bawa likitar amsa tana rubutawa gwaje-gwaje tayi mata masu yawa sannan ta biyosu reception inda suke zaune dake Khalisa ce jagorar zuwa asibitin ita likitan ta kira tayi mata bayani bayanin da ya nemi kai Khalisa ƙasa saboda kaɗuwa da tashin hankali ta dubi Beebah gabanta na tsananta faɗuwa tace .
“Ku tashi mu koma masauki” yanda tayi mgnr a hargitse yasa Hudah miÆ™ewa itama Beebah ta mike suka nufi motar data kawosu suka shiga babu me cewa wani har suka Æ™arasa masaukin.
Suna isa Beebah ta samu ƙasan tiles ta kwanta tana ajiye numfashi kasancewar ko yaya tayi wani motsi me wahala sai tayita haki ko kuma ta rinƙa jin kanta na juyawa.

 

Bata gama saituwa wa ba ta tsinkayo Muryar Khalisa na cewa “Tabbas mutum ba abin yarda bane mutum bashi da kyau ko kaÉ—an nikam bansan da wanne bakin zan fara furta wannan mugun labarin ba, waima dan Allah Habeebah meye ya jaki ga aikata wannan mummunan aikin har tabonsa yake neman tsira a jikinki?”
Tunda Khalisa ta fara mgnr Beebah ta kafeta da idanu batare data fahimci inda zancen Khaly ya dosa ba, batakai ga magana ba Hudah tace “Wai don Allah meye ne yake faruwa kike ta yi mana hanya-hanya Ni wallahi banason zanje da jan lafazi kawai ki faÉ—a musan abinyi tun muna mu uku kafin mu zama mu huÉ—u”
Da sanyi jiki Khalisa ta zauna ta dubi Hudah tace “Huddatu binciken Æ™wararrun likitoci ne ya tabbatar da Habeebah tana da shigar juna biyu na kwanaki arba’in da biyu….” Basu aune ba sukaga Beebah a tsaye cikin tashin hankali tace “Innanillahi Khalisa dan Allah daina banson wannan wasan ciki kuma…?” MiÆ™ewa Khalisa tayi tace “Hakane cikine dake Habeebah Ni dama tun farkon yanayin da lalurarki ta fara nunawa zuciyata ta karye amma sai na danneta saboda bakiyi kama da wacce zata aikata ba Habeebah waye kika yarda ya cutar da rayuwarki haka har ya É—ura Miki me zafin?”

 

Cikin kuka tace “Garin yaya meye yake shirin faruwa dani hakane ciki fah ni Habeeba….” Kukan da yaci Æ™arfinta ne yasata katse maganar da take yi ta miÆ™e ta nufi É—aki da gudu saboda aman da yake taso mata ta faÉ—a bathroom ta rinÆ™a shekashi kamar zata amayar da hanjinta.
Hudah itace taje ta taimaka mata ta gyara jikinta suka fito ta kwanta kan gado tana nishin wahala zuciyarta na zafi kanta na juyawa batajin haushin Habeeb akan komai ƙoƙarin ganin ya gujewa ɓacin ran mahaifinsa ne yasashi barinta a matsayin daya barta ita kuma gashi ta raba gari da Mahaifanta akansa.
Kuka takeyi sosai harda shassheÆ™a Khalisa ta shigo ta zauna a kusa da ita ta sanya hannu ta share mata hawayenta tace “Kinyi kuskure da kika amincewa yaudarar maza har kika sallama mawa wani fasiÆ™in kanki yayi Miki babbar illah yanzu ba lkcn kuka bane Habeebah lkcn neman mafita ne kafin lkc ya Æ™ure mana gsky akwai babban tashin hankali idan muka koma 9ja da cikinnan a jikinki dole muyi duk me yuwuwa mu É“atar dashi inyaso sai a kiyaye gaba….”
Har Khalisa tayi shiru idanun Beebah akanta yake amma bata fahimtar komi cikin kalamanta saboda Zuciyarta ta tafi wata duniyar daban.
Hudah ce ta katse mata tunanin da taÉ“ata tace “Ina hankalinki ya tafi ne ana baki mafita kina yiwa mutane kurma” ajiyar zuciya ta sauke ta tashi zaune idanunta na zubar da hawayen tausayin kanta tasan bazasu fahimci duk abinda zata faÉ—a musu ba tunda baa so su fahimta É—in ba ta miÆ™e ta kuma nufar bayi tayita kakarin amai Saida tayi me isarta sannan ta fito tanajan kafa na alamun galaÉ“aita ta zauna kan stool ta kifa kanta saman dressing mirror tanaci gaba da gursheÆ™en kukanta.

 

Khalisa ta miÆ™a mata wayarta tace “Bro na kiranki tun É—azun 10 misscall yayi Miki tun muna parlour” ko arziÆ™in É—agowa bata samu ba tanajin wayar tanata vibrate amma taÆ™i karÉ“a sanin halinsa yasa Khalisa É—agawa tana É—agawa yace “Kuna ina a Dubai?” Cikin tsoro ta sanar dashi inda suke ya kashe wayar ta dubi Beebah data koma saman gado taja bargo ta Æ™udundune tace “Duk da nasan É—abi’arki ce shariya banyi tunanin akan mafitarki zaki shareni ba Beebah cikin shege fah ne a jikin….”
ÆŠaga mata hannu tayi cikin zafin zuciyar da basu taÉ“a zaton tana dashi ba tace “Dakata Khalisa cikina ba shege bane kamarni kamarki kamar Ubansa shima haka yake halattace bawai ina kuka ne don gudunsa ba a’a ina kukane saboda banso yazo a wannan yanayin ba naso na samu ciki lkcn da kowa da yake da alaÆ™a da cikin zaiyi farin ciki da fatan alkhairi amma yanzu nasan ba lallai ne mamallakinsa ma yayi farin cikin samuwarsa ba wannan shine kawai damuwa ta…..”

 

BuÉ—e Æ™ofar sukaji anyi an shigo Æ™amshin turarensa ne ya fara yi mata sallama kafin muryarsa ta furta “Assalamu alaikum” gabanta ya yanke ya faÉ—i zuciyarta ta shiga harbawa da Æ™arfi lkcn da ta É—auki idanunta ta É—ora akansa shima ita yake kallo da manyan lulu eyes nasa ya É—an yi mata wani murmushi gajere daya sanya dimple nasa lotsawa ya tako cikin takunsa na isar nutsuwa wanda yake cike da jin izzar sarauta a jini ya tsaya a gaban gadon ya buÉ—e Æ™aramin bakinsa yace “Wellcome My Wyf” saurin kallon Æ™annensa tayi suma kallon juna sukayi sannan suka kallesu Hudah ta jinjina kai ta nufi hanyar barin É—akin.

 

Itama Khalisa juyawa tayi ta fice a É—akin saboda yanda taga ya tsugunna a gabanta yasa hannunsa ya tallafo fuskarta ta janye da sauri ta fakaiceshi ta fice daga É—akin itama da gudu tana Æ™unshe kukanta, binta yayi da sauri yana kiranta amma taÆ™i sauraronsa har saida ya haÉ—a da gudun shima yacimmata tana shirin hawa lifter ya cafke ta ya dubi Khalisa dake waya tayi saurin katse wayar tayi Æ™asa da idanunta tace “Bro….”
Tsareta yayi da manyan idanuwansa ya buÉ—e bakinsa kamar wanda akayiwa dole yace “Meye damuwarta?” Cikin in…ina ta fara magana “Uhm…dad…dama bat…a da lafiya….” Da sauri Hudah tace “ke kuma ya zakiyi mawa mijinta Æ™arya ai abin alfahari ne am dama Bro ba komai bane Æ™aruwa muka samu shine duk tabi ta damu kanta….”
Duk da yasan da gatsali Hudah ta faÉ—i mgnr amma baiji haushinta ba saima wani farin ciki me haÉ—e da sanyi daya ziyarci ruhinsa ya janyo Beebah ya haÉ—ata da jikinsa ya É—ora kansa a saman kanta ya lumshe lulu eyes É—insa yana shafa kwantaccen gashin da yayima fatar bayanta ado yaja ajiyar zuciya yace “Shine kike kuka saboda Allah yayi mana babban arziÆ™in da nakejin a raina shine raba gardama cikin wannan cukurkuÉ—aÉ—É—en auren namu me tattare da Æ™alubale? Kinaso ki fahimtar da ruhina bakiyi murna dani ba bare kiso fitar tsatsonki daga gareni?”

 

Wata ajiyar zuciya ya sauke me nauyi ya É—ago fuskarta da har yanzu idanunta a lumshe suke hawaye na fita ta gefensu har zuwa cikin kunnenta ya sanya kuncinsa ya share mata ya sake cewa “Wallahi tallahi Habeebatullah koda za’a kasheni bazan taÉ“a Æ™in abinda na fitar a jikina ya shiga jikinki ubangiji ya kasantar dashi daga ruwa zai zama halitta ba, Habeebah inasonki kuma zan zauna dake a kowanne yanayi zan baki kariya ta kowacce siga nidai fatana kada ki gaji dani kada ki Æ™osa da hÆ™r da mijinki…..”
Rushewa tayi da kukan da ya sanya su duka suka matso garesu shima ya saketa cikin tashin hankali ya buÉ—e baki zaiyi mgn tayi saurin katseshi da cewa “Ban gaji da zama Æ™arÆ™ashin inuwar aurenka ba Hero saidai cikin watanni bakwan nan na gaji da zama a matsayin É“oyayyiyar mata yaushe ne zakayi yunkurin samamin Æ´anci ne don Allah Nima na rayu kamar kowacce mace a gidan mijinta? Yaushe ne zan samu sauÆ™in damuwa É—aya inji da É—aya Hero koda ace ka gabatar dani a gurin kowa na Ahlinka sun amince dani ban huta ba domin nasani tsakanina da mahaifana gaba ce wacce daÉ—in furucina bai isa gogeta ba, idan kuma Ahlinka sukaÆ™i karÉ“ata to bansan makomata ba saboda na barranta da nawa ahlin hukuncin kisa ne akaina idan na koma garesu bare ma bazan iya komawa ba Habeeb kaji Æ™aina ka tausaya min ka bayyanani matsayin matar Sunnah gareka don nasan matsayina nasan inda rayuwata ta gaba ta dosa, wallahi nayiwa ubangijina alÆ™awarin ko zan mutu a wahale bazan taÉ“a yin ridda ba na shigo musulunci kenan bakin rai bakin fama kuma ko a wanne hali bazan manta dakai ba domin kaine sila…..”

 

Kalaman nata nema suke su sashi hawayen da bai shirya ba hakan yasashi cafkar hannunta ransa a jagule ya nufi wani É—akin dake kusa da asalin nasu tun lkcn da suka faÉ—a masa inda suke da number room É—in yayi borking ya kuwa yi saa É—akin a sake yake suka bashi.
Mayar da Æ™ofar yayi ya rufe ya saketa ta zube a gurin yabita da sauri yace “Oh God Wyf da kinsan halin da nake ciki da baki Æ™aramin damuwa da wannan Æ™aramar damuwar ba, aure ne mun riga munyi shi cikine ya riga ya shiga ki faÉ—amin meye zai sauyu cikin abubuwan da kikewa kukan Please ki tausayamin kada zuciyata ta buga na rantse tsaf zan iya rasa rayuwata akanki”
Yana mgnr yana matsarta tare da zame hular kanta gashinta data tattare ta tura ciki ya baje a bayanta sai Æ™amshi yake buÉ—aÉ—awa ya tsumu da turaruka masu manyan kuÉ—i, iya haka ta saukarwa da Habeeb wata kasala ya matsa sosai jikinta ya janyota ya É—orata a cinyarsa yana sunsunarta ko ta ina yana sauke wata irin Nishi da yake firgitata ta fara tsorata da yanayinsa a haka tasan isarta da dabararta bazata taÉ“a Æ™watarta ba…….

 

_Idan kika karanta min littafi baki biyani ba ban yafe Miki ba, idan ka/ki karantamin littafi a YouTube batare da izinina ba Allah ya fitarmin da haƙƙina a kanki/kanka da gaggawa_
[5/9, 7:07 PM] AM

Post a Comment for "Bamagujiya 27-28"