Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Auren Shehu Book 2 Page 13

Auren shehu 2.

Tanko na dariyar mugunta ya dauki Zainab ya ?aura a kafada, ko kallon in da Rahila ta ke be yi ba bare ya lura da yanayin da ta shiga na sanadiyar zantukan da ya ke fada game da Zainab. Da sauri ta sha gaban sa, cikin bambami ta furta


“Me ka ke nufi Tanko? Ina fatan kalaman da ka ke akan tarewa da wannan ka?on ba gaskiya ba ne, In kuwa da gaske ka ke wallahi ba ka isa ba! Ba ka isa ka tara da wata mace wacce ta ke ba halas din ka ba gaban idona na”

“In kuma na yi fa? Me za ka yi? Ku ji mu da shashasha! Jiki duk ya bushe ya jeme ki na tunanin zan ga jiki kamar na kado na bari? Sakarya kawai!”

Cike da bacin rai Tanko ya maida mata da martani yana mai cigaba da tafiya, ganin da gaske tafiya yayi da Zainab nan take wani turirin kishi ya yi gaba da ita, gaba ?aya ta daina ganin gabanta, juyawa ta yi a guje, tana tafe kamar kububuwa, daga Tanko har yaran sa ba su lura da juyawar Rahila ba, halin su ya raja’a kan nasaban da su ka ci kan Shehu, ga kuma Kado an samu, idan Tanko be yi san zuciya ba kila su ma su sami raban su daga jikin ta.

Inda ake sharo Rahila ta koma a guje, ihu take ba ta ko iya tantance mai take fadi. Ganin yanda ta iso filin da ake sharo ?in ne ya dawo da hankalin mutane gareta

“Me ya faru? Me aka yi?”

?an matasan da ke wajen su fadi a tare suna masu ?aga sanduna da addunansu. Haka Kuma Muhammad Bello ya shiga raba idanu, nan ya ankare da rashin Usman da Zainab a filin.

“Tannn… ko! Kaaaa?o!! Sheehu ruwa!!!”

Rahila ta ce muryarta na ha?ewa. Nan wajen ta fa?i tana mai kuka cike da ?unan zuciya, tana jin labarin kishi amma Sam ba ta san haka ya ke da ra?a?i ba, ta san ko kusa ba za ta ha?a kanta da abu ba, ta san matukar Tanko ya lashi zumar ka?o tabbas ba za ta sake ji ta kansa ba. Kuka ta ke yi mata na rarrashinta duk a tunaninsu su zainab ta ke tausayi.

Su Bello kuwa tare da sauran ?an matasa har ma da wasu daga cikin manyan da su ke da saurin ?arfin su, Rarraba kansu su ka yi cikin daji Allah suna neman zainab, wainda su ka iya ruwa a cikin su kuwa su ka far ma ruwan da Rahila ta ce an jefa shehu.

Wajen zaman Tanko aka fara zuwa nan su ka iske babu kowa a wajen, har tawagar su Bello za su juya su ka hangi wata sabuwar bukka can nesa ta gabas daga inda su ke, ba su yi ?asa a guiwa ba su ka isa, mazan da su ka gani a tsaitsaiye ri?e da bindigogi ya sanya su yin turus, sai da su ka ?araso ne su ka ga ashe ba ma bukka ?aya bane sun kai biyar.

?aga bindigogin su ka yi suna mai sai ta su, dakatawa su ka yi da fari, amma tunawa da su ka yi Shehu ya sa an ha?a maganin bindiga sun sha kwanaki ya sanya su dosar bukkar ba tare da ko wace shakka ba.

Karar fitar harshashi ne ya sanya Zainab farfadowa daga suman da ta yi. Ta mai raba idanu cikin kokarin gano in da ta ke, idanun ta ya sauka kan Tanko, wanda ke tsaye kan ta ya na shirin afka mata kenan ya ji alamun isowar su Bello.

Cike da bakin cikin an katse masa abin da ya ci buri ya ja tsaki, ya dau bindigar sa a fusace ya na duban Zainab ya ce

“Ki gyara sosai kafin na dawo! Yau sai na more abin da na ke mafarki! Na tabbatar mi ki sai kin kasa takawa! Bari na gama da wancan karamin kwaron!”

Ficewar sa da manganganun sa ne ya sanya Zainab dawowa cikin hayyacin ta.

“Usman! Na shiga uku ni Zainab sun kashe min Usman!”

Cewar Zainab yayinda ta tashi tsaye cikin neman mafita, kuka ta ke wiwi daya na bin daya. Gani take duk abin da Tanko zai mata ba zai kankare rabin zunubi da ta aikata ba na cin amanar shehu. Karar harsashe da ke ta shi be sa ta tsora ta ba, sai ma kokarin tusa kai waje da ta yi, a tunanin ta in ma mutuwan ne gwara harsashi ya kashe ta da ta mutu hannun Tanko.

Duk yanda Tanko da yaran sa su ka so cin galaba kan su Muhammad Bello kasancewar su na da bindiga hakan gagara yayi saboda maganin bindigar da ke aiki jikin su, dama ma su iya magana sun ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, tuni su ka sami nasarar kwace bindigun yayin da su ka kwantar da su da dukar kawo wuka. Inda su Bello ke kururruwar daukar fansa, su Tanko ihun neman doki su ke, su na fadin

“Mun tuba ku yafe mu! Mun tuba!”

“Kar ku raga mu su! Kar ku tausaya mu su! Sun jefa min Usman a ruwa! Sun kashe min Usman!”

Cewar Zainab cike da tsana yayinda su Muhammad Bello su ka dada tsage dantse wajan jibgar su Tanko da gora, gaba daya su ka mu su jini da majina amma hakan be sa Zainab ta tausaya mu su ba, sai ma dada cewa ta ke a kara mu su. Ana cikin wannan halin ne daya daga cikin wanda su wanda su ka je kaiwa Usman ne ya cimma su ya na mai ihu

“An dauko Shehu! Muhammad Bello an dauko Shehu!”

Ya na fadin haka ya juya a guje. Zainab ce ta fara yin gaba cikin gudu gudu sauri sauri, yayin da Muhammad Bello ya ba da umarnin daure su Tanko a taho da su, shi ma ya bi bayan su Zainab.

Nan bakin ruwa su ka tadda an fito da Usman, ana kokarin fitar da ruwan da sha. Ganin Bello da Zainab tuni aka dara mu su hanya wasu da ga cikin jama’ar na fadin

“Allahu akbar ruwan Rugar Shehu ba ya ci Shehu ba! Shehu ikon Allah! Allahu akbar!”

A tsorace Zainab ke kallan Usman da ke kwance tamkar matacce yayinda Muhammad ya cigaba da matso cikin sa, sai da yayi hakan kusan sau uku sannan ruwa ya fito daga bakin Usman cikin karfi, hakan ya sa Usman tari ya na mai bude murfin idan sa cikin magagi, jama’a aka sa kabbara, haka kuma mu su ihu da sowa na yi. Cikin kankanin lokaci ya sake mayar da murfin idanun ya rufe. Cike da tashin hankali Zainab ke fadin

“Kar ku bari ya rufe idanun shi! Kar ku bari ya mutu ya bar ni! Na shiga uku na lalace!”

“Ba zai mutu ba, ki kwantar da hankalin ki”

Cewar Muhammad Bello yayin da ya cincibi Usman ya aza a kafada. Babu wanda be tausayawa Zainab ba ganin yanda ta ke cikin tashin hankali. Ta na biye da Muhammad Bello har su ka koma bukkar Shehu. Da kyar su Iyalle su ka ja ta gefe lokacin da mai magani ya ke duba Shehu. Allah ya so babu karaya, in aka dauke raunin da Tanko ya masa akai, sai kuma ciwon jiki sanadiyar dauri da dukan da aka masa.

Sai da ya tabbatar Usman ya farfado ya bashi magani sannan ya kara bari ya koma baccin azabar da ke daukar sa. Su Tanko kuwa cikin garkon Shanu Bello ya sa aka daure su, ba dan halin da Usman ke ciki ba da tuni ya gama da su.

Murna da farin cikin biki ya koma bakin ciki, Rugar Shehu ya koma tamkar ana makoki. Washagari da sassafe Rahila ta saci hanya ta gudu, babu wanda ya damu da tafiyar na ta saboda Zainab kadai ta san wainar da su ka toya.

Kwana uku Usman yayi sai dai a kwantar a tayar, duk wani abin da ya shafi karfi su Bello ke masa amma fa a kan idan Zainab, ta kasa ta tsare ita take jinyar sa dan kuwa gani ta ke idan har ta matsa Tanko zai iya shigowa ya karasawa mata shi. Haka shi ma Usman din tsakanin sa da Zainab sai ido. Kuka kuwa ta yi har ta gaji, tun su Iyalle su na ba ta baki, har su ka gaji su ka sa mata idanu.

Da yammaci Zainab zaune bakin bukka ta yi uban tagumi gaba daya duniyar ta mata zafi. Kamar daga sama ta ji muryar Usman ya na kwallawa Bello kira, fadi ya ke

“Muhamadu! Muhammadu! Muhammadu!”

A zabure Zainab ta tashi ta shige dakin. Ta tarar ya na yunkurin tashi tsaye ya hada zufa sosai. Zainab ta karasa gare shi da sauri da niyar taimaka ma sa. Yanda yayi saurin janye hannun shi sa’ad da ta kai hannun ta jikin sa, da kuma irin kallon da ya bi ta da shi ya sa Zainab ja da baya jiki sanyaye, yayinda Muhamadu Bello ya shigo cikin sassarfa. Ganin Usman na kokarin tsayawa ya karasa gare shi da sauri, ya taimaka masa ya tsaya ya na fadin

“Hankali Shehu, ya aka yi ki ka bari ya tashi Uwargida?”

“Ina Tanko? Ina Tanko na ce??”

Usman ya fada a fusace ya na mai raba idanu.

“Ya na can cikin shanu tare da yaran nan, dama jira mu ke ka sami sauki sai a san yanda za a yi da su”

Cewar Bello cikin shakkar yanayin bacin rai da ya lura Usman ke ciki.

“Ba na son ganin Tanko, wallahilazim ina iya kashe shi har lahira….”

Cewar Usman ya na mai danna kwayar idanun sa cikin na Zainab, wacce ta ke duban shi cikin yanayi mai wuyar fasaltuwa. Usman be gushe ba ya kara da

“Idan akwai abin da na koya cikin rayuwa ta da wannan baiwar Allah (ya nuna ta dan yatsa) shi ne rashin faidar ramuwar gayya, domin kuwa yakan jefa dan Adam ga halaka, ku kai Tanko da duk wanda ya rabe shi ga hukuma dama sun jima suna neman shi”

“Toh Shehu”

Cewar Bello. Usman be gushe ba ya kara da
“Sannan kuma ranar Juma’a na mako mai zuwa, ka shirya zan sake aika ka Mambila ka saka ta tashar da zai kai ta Taraba ina ga daga nan za ta iya kai kan ta gida….”

Ji ta yi tamkar an kwara mata ruwan kankara. Shi kan shi Bello dagowa yayi firgice ya na duban Zainab da Usman. Cikin in ina ta furta

“Wa…wa… ce… ce za a kai tasha?”

“Shehu ina ga zai fi…..”

Hannun da Usman ya daga masa tare da fadin

“na sallame ka”

Ya sanya Bello kokarin ficewa da sauri, ga mamakin sa sai ji yayi Usman ya furta

“Ku yi kokarin kiyaye lafiya ta ta hanyar hana jama’a shigowa in da na ke, ina nufin idan ba kai ba ko Iyalle ban yarda wani ya shigo min ba”

Idanun Bello kan Zainab wacce idanun ta ke shekin kwalla, ya furta

“Toh Shehu”

Amma ya kasa cewa Zainab ta fita, dan haka sai yayi saurin juyawa ya fita. Usman ya koma yana kokarin zama, ganin yanda ya ke cikin ciwo sai da ta yi da gaske wajan dauke kan ta gudun kar ya kyamace ta kamar yanda yayi mintinan baya.

“Wacece za a kai Mambila?”

Maimakon ya bata amsa, sai yayi kwanciyar sa kamar be ma san ta na dakin ba. Ran ta yayi rauni, ta kara furta

“Kai waye! How dare you! Wa ya ba ka damar ka dauko ni ka mayar da ni sanda ka ga dama! Zaman Rugar nan yanzu na fara kai ka yi ka kadan! Ka ci moriyar gangan ko? Toh zama daram!”
Usman ya mata banza, ya na mai juya mata baya. Ganin haka ta yi saurin fita daga dakin. Su Iyalle na mata barka Shehu ya fara warwarewa ko tan ka su ba ta yi ba ta tsallake su da saurin ta ta shige dakin Iyalle. Nan ta fashe da kuka mai karfin gaske har da shesaheka, su Iyalle da su ka biyo bayan ta ne ma su rarrashi, fadi su ke

“Yo toh yar nan ai murna za ki yi ba kuka ba, tunda Allah ya sa an tsira da rai ga shi har ya farfado….”

Hansai kuwa fadi ta ke

“Ina ga kuka ai na murnar ne, ai mun tarba arziki kwarai kuwa”

Zainab kuwa ita kadai ta san radadin da ran ta ya ke yi, yau an wayi gari Usman da kan shi ya ce zai mayar da ita gida, maimakon ta yi farin ciki, kishiyar haka ta yi, dan Allah ya dasa mata son Usman, sai da Allah ya jarabce ta da kaunar sa shi ne ya ke ikirarin zai mayar da ita gida, kamar yanda ta ce babu in da za ta je, babu in da za ta je.

Su Iyalle ba su kara karaya ba sai da su ka dare yayi, Bello ya fito da akwaitin Zainab ya mayar da shi wata bukka daban wacce babu wanda ke kwana ciki, da kan shi ya gyara yayiwa Zainab shimfida. Ko da Iyalle ta tambaye shi dalili, ya ce umarnin Shehu ya ke bi. Jin haka su ma su ka fara shan jinin jikin su, lalle wannan lamari mai wuyar ganewa ne.

Sai da Zainab ta yi da gaske sannan ta iya runtsawa. Har cikin ran ta so ta ke ta sami Usman ta bashi hakuri, ta fada masa ta yi kuskure ta kuma bayyana masa sirrin ran ta, dan kuwa ba ta iya ji za ta iya rayuwa babu Usman ba, bayan ganin yanda ya kusa rasa ran sa a sanadiyar ta, lalle za ta iya rasa ran ta idan ya rabu da ita. Amma wani bangare na zuciyar ta ne ya hana ta tashi ta same shi. Haka tai ta juyi dab da asuba bacci ya sace ta. Sai tashi ta yi ta ga an tafi da su Tanko, haka kuma Usman ya ba da umarnin kada wanda ya shigo masa daki idan ba Iyalle ba, idan kuwa aike za a masa, za a iya aiko matar da Bello zai aura, wato Raaqeeba.

Ganin yanda Raqeeba ke kai kawo cikin dakin Usman fashewa ne kadai zuciyar Zainab be yi ba tsabagen kishi. Sai a sannan ta gane tsabagen kishi ya rufe mata idanu ne ta aikata abin da ta aikata. Tun tana iya jurewa har ta kasa ta je ta sami Iyalle ta ce da ita

“Iyalle ina ga zai fi in ki na da sako gun Shehu ki ba ni, ki dena aika Raqeeba ai tunda ni ce matar shi ko?”

Daga jin maganar Iyalle ta gane kishi ne na mata karara, dan haka sai ta murmusa cike da siyasa ta ce

“Wai da nauyin aiken na ki na ji, Amma ai an gama kai komai, zuwa gaba idan da aike na ba kira ki”

“Toh Iyalle, na gode”

Cewar Zainab amma har ga Allah ba haka ran ta ya so ba. Haka ta wuni ta ja jiran tsammanin kiran Iyalle, ba ta san an yiwa Iyalle gargadin kada ta sake ta bari Zainab ta kusance shi ba, dan haka ne ma Iyalle ta gwammace da ta aiki Zainab din ko kuma Raqeeba da Zainab ta nuna kishi akai, gwara ita din ta yi kai kawo zai fi mata sauki.

Balain so ta ke ta gan sa, ta ji ya jikin sa amma jin kai ya sa ta kasa shiga hakan nan, ta gwammaci ta jira a sami dalilin shigar na ta, Amma abin ya gagara har ta na shirin fita daga hayyacin ta. Haka ta hakura ta na mai neman sauki daga Allah dan kuwa shi ya jarabce ta, jarabawar ma kuwa babba.

Sai washagari su Bello su ka dawo. Ranar har tsakar gida Usman ya fito amma ko inda Zainab ta ke be tambaya ba, bare ya yi yunkurin shiga wajan ta. Ta na daga cikin daki ta ke jiyo hirar shi da mutan gidan da harshen fulatanci, wanda har ta fara tsintsinta kadan kadan. Jin har ya karaci hirar shi ya koma be neme ta ba, ita ma ta sha alwashin ko da kuwa zuciyar ta za ta fashe ba za ta neme shi ba. Cikin kankanin lokaci sai ta kara zama bare a Rugar Shehu, kullum ta na cikin bukka idan ba dai uzuri ne ya fito da ita ba, haka kuma ta lura ko giftawa ta yi gaban Usman matukar ya na fara’a sai fuskar sa ya hade ya murtuke tamkar hadari, ya guje ta ya juya mata baya farat daya, yayinda ta ke bukatar shi, ta ke kaunar sa tamkar ran ta. Idan akwai ranar da ta ke tsoro ya bi bayan juma’ar da Usman ya ce za a tafi da ita, duk ran da rana ya fadi garin Allah ya waye sai ta yi kuka, ranar alhamis kuwa ko kafa ba ta iya sakawa tsakar gidan ba, bukkar ta ta wuni cikin bakin ciki da adduar Allah ya sa Usman ya canza ra’ayi.

Ranar Juma’a da asubar fari sai ga Iyalle dauke da irin kayan da Usman ya bata ranar shadi. Ta tarar Zainab zaune kan tabarma in da ta idar da sallah ta na jan jarbi, Iyalle ta zauna kusa da ita tare da fadin

“Ayya Abu, ashe hukuncin da Shehu ya yanke kenan? Mun yi bakin ciki kwarai ke abin alfahari ce a Rugar nan, ba mu ji dadin sakin ki da yayi ba…..”

A kidime cike mummunar faduwar gaba Zainab ta yi saurin fadin

“Saki! Cewa yayi ya sake ni? Wa ya ce ma ki ya sake ni?”

Ganin yanda ta kidime Iyalle wacce dama da biyu ta yi maganar ta maganar ta furta

“Ashha babu wanda ya fada min, ganin ya bani kaya ya ce na kawo mi ki, tare da sheda min Bello zai mayar da ke birni ki koma can uwa uba Kano na yi zaton ko hakan aka yi, dan kuwa aure ke kina can shi ya na nan kusan sai a ce ya mutu, ki yi hakuri da azanci na”

Ta karasa maganar ta mai fatan Zainab za ta bijire ta ki yarda da maganar Usman. Aikuwa nan Zainab ta ce sam ba ta san zancen ba ta juya ta mayar masa da kayan sa, babu in da za ta je.

Bayan fitar Iyalle Zainab ta koma ta yi kwanciyar ta. Jim kadan ta ji muryasa a kan ta ya na fadin

“Za ki tashi ki sanya ko na sanya mi ki ta karfi?”

Tsaye ya ke hannun sa dauke da kayan da Iyalle ta mayar masa, yanda ta gan shi tsaye babu wani alamar ciwo a tattare da shi ta ji dadi har ran ta. Ta na daga kwance ta furta

“Sai ka sanya min din na gani ai….”

Ba ta kai gama rufe bakin ta ba ya durkusa ya wufto ta ya na kokarin raba ta da kayan jikin ta, ihu ta fara sosai cikin kokuwar kwatar kan ta, Amma ko a jikin sa har sai da ya raba ta da rigar ta. Ga shi ko rigar mama babu jikin ta, be san sanda ya bi kirjin ta da kallo ba, sanyin da ya ziyarci fatar har ya kai ga sanya ta dan rawar dari da kuma yanda ya zuba mata idanu ya saka ta yi saurin shigewa jikin sa, Usman ya runtse idanu lalle zuciya ba ta da kashi, ganin Zainab da kuma yanda ta kamkame ya sa gaba daya gwiwarsa ta yi sanyi. Cikin zafin nama ya zare ta daga jikin sa, yayinda ya ke kokawar danna rigar kan ta, Zainab ta dada bijirewa ta hanyar yin rawa da kanta, ta na samin damar kwatar kanta ta yi saurin sake shigewa jikin sa, ta rungume shi kam kamar me shirin shigewa jikin sa, cikin kuka ta ke fadin

“Dan Allah kar ka bari a tafi da ni, ba zan iya komawa gida ba”

Usman ya runtse idanun sa cikin karfin hali, shi kan shi ya na jin zafin tafiyar ta, Amma bayan abin da ya faru ta tabbatar ma sa ba ta da makiyi da ya wuce shi, ta kuma tabbatar masa yanayin tsanar da ta masa da kuma tsanar zama da shi a Rugar Shehu….

“Ka riga ka gama bata min rayuwa shi ne za ka yada ni, wallahi ba ka isa ba…..”

Maganar da ya dawo da shi cikin hayyacin sa kenan, yayi saurin banbare ta daga jikin ta, ya tashi tsaye, a dake ya furta

“Ki shirya nan da awa daya Bello zai tafi da ke…..”

“Na san ka so ni Usman, ka fada min kuma na gani a idanun ka, me zai sa ka guje ni? Na san na ma ka laifi……”

Hannu ya daga mata tare da fadin

“Ba na son ki! Dama na dauko ki ne ina cikin magagin bakin cikin rashin mahaifiya ta, wacce a sanadin ki ban gana da ita ba, yanzu kuma na huce ba kuma na bukatar ki!”

Wani irin zafafan hawaye ne su ka gangaro daga idanun ta. Zanin jikin ta ta kunce domin janyo shi samai yanda za ta rufe kirjin ta, ta tashi ta yi ta sha gaban sa ta na mai kokarin sanya idanun ta cikin na sa, murya kasa kasa ta furta

“Ba gaskiya ba ne, ka ce min ka yi nadama, ranan a bakin ruwa, ka ce min ka na so na……”

Ya na mai girgiza kai yayinda maganganun sa da Tanko ke kara saka zuciyar sa radadi su na mai masa ya yawo a kunne

“Zainab me ya sa? Duk zaman nan da mu ka yi da ke, duk kwanciyar hankalin da mu ka samu…. Zainab… Zainab me ya sa…? Dama kin yi ne dan ki cutar da ni?”

“Ta yi ne domin haka na ce ta yi! Kai a tunanin ka yarinya kamar wannan za ta taba san gidahumi irin ka? Ai ka godewa Allah ma ka sami raban ka!”

“Ki manta da abin da na fada mi ki rannan na fada ne bisa kuskure…….ba na san ki…..”

Maganar ya soke ta tamkar takobi. Cikin dauriya ta furta

“Ka na so na Usman, fushi ka ke da ni kawai in ka huce komai zai wuce..”
Kai ya girgiza mata, kana ya ce

“Ba zan iya zama da ke ba……”

“Ko da kuwa ina dauke da juna biyu?”
Kallan ta ya ke cike da bakin cikin karyar da ta ke sharara ma sa, har ta kai za a iya karya ciki, maganar Tanko ya kara ratsa zuciyar sa na

“Ta yi ne domin haka na ce ta yi! Kai a tunanin ka yarinya kamar wannan za ta taba san gidahumi irin ka? Ai ka godewa Allah ma ka sami raban ka!”

Ya sake juyawa zai fice Zainab ta dakatar da shi ta hanyar fadin

“Ka sake ni toh! Idan har za ka mayar da ni gida ka sauwake min wannan auren na masifa!”

Ga mamakin ta sai ga shi ya juyo, hannu ya sanya cikin aljihu ya fitar da takarda, ya na mai ruko hannun ta ya sanya takardar tafin hannun ta. Ba tare da ya bari sun hada idanu ba ya juya zai fita, har ya kai kofa Zainab ta furta

“Ka yi min yanda ka yi sanda za ka dauko ni, dan Allah ka gusar da hankali na Usman…..”

A sanyaye ya juyo ya na duban ta, sai a sannan ta lura da yanda idanun sa su ka yi jajur. Cike da nadama ya furta

“Ina fatan za ki yafe min….”

Ya fice da sauri in da ya bar Zainab durkushe hannun ta rike da takardar da ya bata ta na kuka mai tsuma zuciya.

 

 

 

 

Post a Comment for "Auren Shehu Book 2 Page 13"